Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   26 / 26

75K to 77.3K   out of 77.3K words

kam mazan da ta afka irin tarkon da take son jefa shi.
Sai dai nasa ya fi muni, don raba Amina da shi da ta ƙudurta ba ƙaramin abu ba ne, wanda ta
ce ba ta taɓa raba kowa da matarsa ba, sai dai ta juya mazan da ta riƙe gam ta yadda duk
samunsu yana hannunta. A sanadin wannan babbar sana'ar da ta riƙa tana tutiya da ita, ta
mallaki gidan kanta inda take cin karenta babu babbaka, kuma ta sanar da ni tana da manyan
filaye sama da biyar ba tare da kowa ya sani ba."

"Cabɗijam!" Baba ya faɗa yana jinjina kai. Nur ta ƙara da cewa, "Tsoron ta raba Amina da
Jamal ta sigar da ta so ya sa na baro gida bayan na bugi cikinta na san komai da ta shirya.
Sannan kafin na zo na sanar da Adamu abokin Jamal komai, da taimakonsa aka sa mata ido a
kan duk wani takunta da na Jamal idan ya zo wurin. Sai dai tabbacin da ta ba ni a kan bai zo
ba, amma lalle zai je wurin a cikin kwanakin, saboda kiranyen da ta sa aka yi masa. Hakan ya
sa ni ma na kasa haƙuri na biyo hanya babu shiri don a yi komai a gabana, na manta shaf da
matsalar da za ta faru biyo bayan hakan. Duk da ƙaryar da na yi a kan cewa wata kakata ce ta
kira ni, waton ƙanwar mahaifiyar Babana. Da wannan dalilin na baro Niger cike da zummar
komawa cikin lokaci tun kafin asirina ya tonu. Kwanana biyu a nan ba tare da kowa ya sani ba,
sannan ina zuwa gidan cin abincin na wuni tare da Hajiya mai abincin amma ita muguwar ba ta
san ni ce ba. Saboda hoton wata ɗiyar yayan Babana na tura mata a matsayin ni ce kuma ta
yarda...."

Daga nan ta kwashe komai da ya faru bayan tonuwar asirin Zulaiha ta faɗa wa Baban Amina.
Ya shiga jinjina kai tare da goge wata ƙwallar da ta cika masa ido tsabar mutuwar jikin da
maganganunta suka haifar masa. Sai da ya nisa sannan ya yi magana cikin raunin zuciya ya
ce,
"Tabbas ke 'yar halas ce A'isha kuma mai ƙoƙarin rama halacci. Sannan kin yi gadon
mahaifinki tun daga kan kamarsa har zuwa kyawawan halayensa. Saboda kin so wa Amina abin
da kike so wa kanki, kuma kin guji abin da zai lalata mana farin ciki duk da abin da uwarta ta yi
miki a baya, sannan kuma tana ƙoƙarin ɗora sabo a yau. Allah Ya yi miki albarka A'isha, sai dai
abin da na kasa ganewa, shin ya ya aka yi da auren da kika ce za ki yi yanzu, bayan matsalar
da kike tare da ita? Ko shi ma.."

"An yi bincike Baba, wannan zancen duka ƙage ne ko kuma na ce an yi komai ne a bisa

kuskure da ƙaddara. Amma ba ni ce asalin wadda abin ya faru a kanta b..."

"Alhamdulillah! Allah mun gode maka!"

Baba ya yi maganar tare da kai goshinsa ƙasa yana sujudar godiya ga Ubangiji. Zuciyarsa
wasai ya yi maganar da ta saka ta hanzarin kai kallonta gare shi baki buɗe. Bayan bugun da
ƙirjinta ya shiga yi babu ƙaƙƙautawa.

"Halinki na kirki ba zai taɓe ba A'isha, don haka a yanzu na yanke hukuncin aura miki mijin
Amina ko da kowa ba ya so. Da ma can na yi wannan alƙawarin saboda ganin yadda
hankalinsa ya tashi a kan rashinki sannan da auren Amina. Don ina da iko a kan aurar da ke,
saboda mahaifinki Alhaji Haroun ya ba ni wannan damar da kansa kuma a bisa yardarsa.
Saboda haka ba zan bari ki rasa wanda kike so yake son ki tsakani da Allah ba, ko da a garin
yin hakan zan rasa raina matuƙar ke za ki samu farinciki."

"Baba.."

"Yi shiru kawai A'isha, Allah Ya sani ba zan bar rayuwarki ta yi tangal-tamgal ba. Dole ne ke ma
a samar miki da farin ciki ko da hakan zai jawo matsalolin da suka fi waɗanda ake hasashen
faruwar su."

Shiru Nur ta yi masa, saboda ganin ya fiddo wayarsa a aljihu cikin rawar jiki hannunsa yana
rawa ya danna wa Jamal kira. Sai dai har ta gama ringing bai ɗaga ba, yana ƙoƙarin sake yi
masa wani kiran ta durƙusa gabansa tana magiya, hawaye yana zuba bayan ta haɗa
hannuwanta ucealamun roƙo.
"Don Allah Baba, don Allah kada ka bari a a jefa Amina cikin tashin hankali. Allah Ya sani na
bar mata Jamal har abada, kuma zan yi ƙoƙarin raba zuciyarsa da sona ko don ta ji daɗin
zaman aurenta....na yi maka wannan alƙawarin Baba, don Allah ka bar Amina da mijinta su rayu
su kaɗai ba tare da na shiga tsakiyarsu ba."
Tashi kawai ya yi ya fice daga ɗakin ba tare da ya ce ƙanzil ba. Ya bar ta zugum ta tagumi
tana nazari. Har ya dawo ɗauke da kwanon jalof ɗin shinkafa ya ajiye mata gabanta yana faɗin,
"Fara ci, bari na je na kawo miki ruwan sha." Nur ta kalli abinci kawai amma ko kaɗan zuciyarta
ba ta buƙatar cin komai. Baba ya dawo da kofin ruwa a hannunsa yana waya. Kai ɗaga tana
kallonsa cikin wani sabon tashin hankali saboda saƙon da ta ji yana miƙa ga Jamal.

"E, ka zo na amince zan aura maka auren A'isha gobe idan Allah Ya kai mu."

****
Ɓangaren Jamal kuma, yana barin gidan kai-tsaye wani masallaci ya tsaya ya yi sallar Asr,
lokacin ƙarfe biyar har ta gota, sannan ya yi gidan ƙanen Babansa ya tsinke zuciyarsa a
ƙagauce da son ƙaddamar cikar burinsa. Cikin sa'a ya tarar da shi gida suka gaisa sama-sama.

Don ya fahimci Jamal ba ya cikin nutsuwarsa tun daga kan kallon farko da ya yi masa.

"Baba wurin ka na zo!"

"To, ga ni Jamal, Allah Ya sa lafiya?"

"A kan maganar yarinyar nan ce da na so aure a farko aka musanya mini da 'yar'uwarta...."

"To, to na dai gane."

Ya gyara zama yana faɗin, "Baba ta dawo yau. Kuma a yadda na ji ta faɗa gobe ne ɗaurin
aurenta da wani. Sannan wallahi Baba na sani ba za ta so kowa bayan ni ba...don ina da
tabbacin ba ta son ko ma wane ne auren haɗi ne za a yi mata. Baba don Allah..."

"Dakata Jamal." Baba Hassan ya katse shi tare da ɗaga masa hannu kafin ya sake cewa,
"Ka manta da abin da aka ce ya hana ku auren tun a farkon da aka so yi Allah bai nufa ba?"

"Ban san komai ba Baba, babu abin da na sani a kai don ba a sanar da ni ba."

"To ka je ka tambayi Hajiyata, ita ta sani don ta san komai tun kafin a aura maka yarinyar da
ke gudanka a yanzu. Kuma idan ta amince ka auri yarinyar a yadda taken, ka ce ta kira ni da
kanta ni ta sanar da ni zan je na yi wakilcin auren."

Baba Hassan ya ƙare maganar yana miƙewa tsaye saboda sanin abin da ya zo da shi ba zai
taɓa karɓuwa a wurin su ba. Kuma da gangan ya ce sai Hajiya ta amince don ya san ba za ta
amince ya auri Nur a yadda suka san ta ba. Har ya fara yi masa magiya Baban ya katse shi da
cewa, ya je kawai ya roƙe ta idan ta amince a cikin daren ma zai nemi a ɗaura auren kafin
safiya.

Jiki babu kuzari Jamal ya nufi gidan Hajiyar, daidai lokacin kiran Baban Amina ya shiga
wayarsa, a nan ne yake sanar da shi batun amincewarsa. Farinciki fal zuciyarsa ya dinga tuƙi
wani sanyin daɗi yana ratsa masa zuciya. Bakinsa a washe ya isa ƙofar gidan Hajiyar, sai dai
tun kafin ya shiga maigadi ya sanar da shi ba ta nan. Waya ya ɗaga ya kira ta, a lokacin ana ta
kiraye-kirayen sallar magrib. Babu ɓata lokaci ta sanar da shi tana gidansa tun da rana. Katse
wayar kawai ya yi ya nufi gidan zuciyarsa cike da tunanin abin da ya kai ta gidan duk da
zumuɗin da yake yi a kan sanar da ita abin da ke ransa. Sai a lokacin tunanin halin da ya bar
Minal ya faɗo ransa, kansa ya dafe tamkar ya kwarara ihu ya ce,

"Ya Salam! Minal kin ɓaro mini aiki tun da kika kira Hajiya."

Gudun motar ya ƙara tare da buga wani uban tsaki yana faɗin, "Me ya sa ba ta bari har na
dawo ba za ta kira Hajiya? Bayan kuma ta sani dole ne sai ta yi mini faɗa.... mitsssss! Wannan
tonon asiri har ina? An yi mace babu sirri ita a komai sai ta yi abin da zai sa Hajiya ta ga laifina."

Haka ya dinga sambatu masu ɗauke da ganin laifin Minal a kan tunanin da ya tsaya masa a
zuciya. Don ya tabbatar wa ransa ita ce ta nemo Hajiyar don jin haushin ya bar ta tsawon lokaci
bai dawo ba. Sai da ya tsaya masallacin unguwarsu ya yi sallah sannan ya nufi gidan ƙirjinsa
yana bugawa. Gunjin motarsa da Minal ta jiyo ƙirjinta ya buga dam-dam, tsam ta yi da ranta, abincin da
Hajiya ta saka ta gaba sai ta cinye ma ta ji ya gundure ta. Fahimtar hakan ya sa Hajiya ta yi
magana cikin haɗe fuska tana cewa,

"Ki ci abincinki, kada ki ce komai ki bar ni da shi na ce."

Minal ta yi marau-marau da ido tana zuƙe majinar kuka, saboda wa'azin da suka saka ta
gaba suna yi mata a kan haƙuri da dauriya ya rage mata zafin da ke ranta.

Da guntuwar sallamarsa ya shigo falon yana sosa kai, ganin Hajiya da Minal a cikin falon,
saboda Inna Ade ta yi gida bayan ta gama girka musu abincin dare. Da muzurai ya isa gaban
Hajiyar ya durƙusa cikin wani sabon ladabi yana cewa,

"Allah Ya huci zuciyarki Hajiya. Na san na yi laifi amma don Allah don girman Ubangiji a yafe
mini."

Wani kallo ta yi masa cikin haɗe girar sama da ta ƙasa kafin ta ce, "A yafe maka ka dinga
rungumar mata a tsakiyar titi ana yi maka bidiyo?"

Baki ya rufe cikin tashin hankali, saboda ba zatar da maganar ta zo masa. Don bai taɓa
tunanin abin da ya faru har ya yi watsuwar da Minal z ta sani har Hajiya ta ji labari ba. Ƙoso biyu
Hajiya ta yi masa a tsakiyar kai kafin ta nuna shi da hannu tana faɗin,
"Wai har yaushe za ka daina bar wa rayuwarka abin faɗi? Yanzu mene ne amfanin yin abin
da ka aikata ko daga kai sai ita fanɗararriyar yarinyar ballantana a gaban jama'a?"

"Wallahi Hajiya..."

"Babu abin da za ka faɗa na yarda da kai, yarinyar nan kuma tun da na sanar da kai babu kai
babu ita, muddin aka ce an sake ganin ka da ita sai na tsine maka! Kai ko ƙanwar ubanka ce na
raba ka da ita babu kai babu ita! Idan kuma ka ƙi ji sai dai ka zaɓi ɗaya ko ni ko ita."

Shiru kawai ya yi yana kallon Hajiyar kafin ya miƙe tsaye yana furzar da iska mai zafi a
bakinsa. Hannuwansa duka a cikin aljihunsa bayan kan da ya duƙe yana nazarin abin da zai
faɗa, duk ya sani ba daidai zai yi ba, amma kai-tsaye ya ɗago kansa fuskarsa a cure ya kalli
Minal yana faɗin,
"Na haƙura da aure, kuma na haƙura da rayuwa da kowace macen da za ta amsa sunan
matata . Don haka ki haɗa kayanki ki je gidanku na sake ki saki ɗaya."

Cabɗijam! Yanzu littafin ya fara. Kuma daga nan na tsaya ƙarshen FANSAR ƘAUNA BOOK 1.
Wanda na bayar a free tun daga farko har fejin ƙauna.
Sai bayan sallah idan Allah Ya kai mu za mu haɗu a cikin BABI NA BIYUN LABARIN. Wanda
nake yi muku albashir abubuwan da ke cikinsa har ya fi wanda ya faru a farko. Don a cikin
labarin akwai ban tausayi, ban haushi, sannan da ban al'ajabi bayan kalolin abubuwa masu
tsayawa a zuciya. Kada ku manta, har yanzu ba mu san asalin wace ce Nur ba, sannan ba mu ji
labarin dalilin da ya sa ta fansar wa Minal Jamal ba. Amma za mu ji komai a cikin BOOK 2 idan
Allah Ya ara mana lokacin ganin bayan sallah lafiya.

Sannan ba zan sake posting groups ba daga yau, asali ma ko WhatsApp ba zan sake kawo shi.
Za mu haɗu Telegram da ku a sabon group ɗin da zan buɗe saboda tsaro.
Ga masu buƙata ku biya ₦1k kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi
ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.


D. AUTA CE✍

26 / 26