Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 26

3K to 6K   out of 77.3K words

inda n'take ba ta motsa ba, kafin ta ja
ƙafafuwanta n'ta ɗosana ɗuwawunta a bakin gado. Amna ta dawo da foodflaks a hannunta ta
ajiye gabanta cikin sauri ta fice, ba tare da ta ce da ita komai ba.

Shiru ya ratsa falon sai sautin agogon bango da ke ta aikinsa yana harbawa ƙit-ƙit. Hakan ya sa
ta cira kai tana ƙare masa kallo cike da mamakin ganin adadin lokacin da agogon ya nuna
mata. Karfe É—aya da minti goma na dare 1:10am, amma ba ta gasgata ba har sai da ta duba
ƙaramar wayarta da ke cikin jakar hannunta, a nan n'ta ga zahirin abin da agogon ya sanar da
ita babu ƙarya.
Nan take wani sabon tsoro ya shige ta, saboda ba ta da masaniyar ita kaÉ—ai ce a cikin gidan
ko akwai wasu mutanen. Saboda ko kaɗan ba ta yi zaton ƙiyayyar da Jamal ya nuna mata ta
bar shi kwana a cikin gidan ba. Sai dai tuno akwai maigadin da ke kula da shiga da ficen gidan
ta ɗan rage jin tsoron. Amma tabbas ba ta tunanin zuciyarta za ta samu nutsuwa matuƙar ba ta
yi ido biyu da Nur ta amsa mini tambayoyin da ke zuciyarta ba.
Hakan ya sa ta shiga ƙwala wa lambobinta kira ɗaya bayan ɗaya amma babu wadda n'ta
samu. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare da furzar da wani iska mai zafi daga bakina.
Gadon ta sauko ta rafka tagumi hannu biyu, don ta gaji da zaman har ƙafafuwanta sun fara
kumbura. Saboda ba ta san ta yi zurfi a tunanin da ta lula ba sai da ta sake duba agogon
wayarta ta ga 2:30am ƙarfe biyun dare daidai. Kenan ta kwashe awa ɗaya har da wasu ɗorin
mintuna a zaunen ba tare da ta sani ba. Guntun tsaki ta ja tare da Allah wadai a kan abin da ya
faru, musamman da ta tuno maganganun Nur a lokacin da aka ce ga motocin É—aurkar amarya
sun zo. Da irin diriricewar da ta yi ta faɗa bayin da ke cikin ɗakinsu har ƙawayensu suna
tsokanarta.
Jimawar da ta yi a bayin ya sa Minal bin ta tana faÉ—in, "Malama ki fito ke fa ake jira!"
Nur ta buɗe bayin tana dariyar yaƙe, domin alamunta duka ya nuna kuka ta yi a cikin bayin,
cikin wata kalar murya sassanya ta ce,
"Ba sai kin kore ni ba, na sani yau za ki yi kwanan farinciki."

"Ke fa wata irin mutum ce wallahi, yanzu rabuwa da ke shi zai sa na yi kwanan farincikin?"

Minal ta jefa mata tambayar tana hararar ta cike da jin haushin abin da ta faÉ—a. "Kwantas
Hajiyata, in sha Allah daga yau sai kin jima ba ki saka ni cikin idanuwanki ba."

"Ke dai kika sani, kuma komai za ki faÉ—a ki faÉ—a, daga yau dai mun sauke nauyinki a kanmu."
Zancen Minal kenan wanda ya saka Nur juyawa tana yi mata wani kallo mai É—auke da
ma'anoni da yawa. Kamar ta ce wani abu amma ta yi hanzarin tsuke bakinta gum, fuskarta a
cure ta bar wurin tana ƙoƙarin saita kanta a lokacin da mata suka cika ɗakin da guɗa.

Wannan nazarin ya ƙara ɗaukar lokaci kafin Minal ta gano kwanan zaune ta yi. Saboda bacci
bai ɗauke ta ba sai da asuba ta kawo jiki. Kasancewar ana yanayin zafi hakan ya sa ta ƙara
bajewa ƙasan tayis tana nannauyan baccin mai ɗauke da mafarkai kala-kala.
Ba ta tashi farkawa ba sai da ƙarfe 9:11am na safiya. ko shi kiran waya ne ya tayar da ita, a
firgice ta farka tana dube-duben da ya tabbatar mata ba gidansu ba ne, kuma da gaske abin da
ya faru ba almara ne.
Cike da ƙuncin zuciya ta nufi bayi, saboda kiran ya katse kuma lokaci ya ƙure mata ba tare
da ta yi sallar asuba ba. A gurguje ta nemo hijabi a cikin wardrobe ɗin kayan Nur, ta miƙa raka'a

biyu ta tofa addu'ar da ba ta san me ta roƙa ba. Allah Ya taimake ta tun kafin a fito da amarya ta
yi sallar Isha. Da ba ta yi sallar ba wataƙila tashin hankalin da ya kunno mata kai ba zai bar ta
nutsuwar yin sallar a cikin daren ba.
Ta jima saman sallayar da tagumi kafin wani kiran ya sake shigowa cikin ƙaramar wayarta.
Muryar Hajiya ta jiyo ta yi hanzarin gaishe ta ba tare da ta amsa ina kwanan da take yi mata ba.
Saboda ganin ita ce ya dace ta gaishe ta a matsayinta na babba.

"Ki ƙara haƙuri kin ji! Na aiko miki da abinci ki sauka ƙasa ki karɓa. Kuma ki ƙara haƙuri da
yardar Allah komai zai daidaita."

"Babu komai."

Iya abin da Minal ta faÉ—a kenan saboda bakinta ya yi nauyin da ba za ta iya cewa komai ba.
Sannan ta sauke wayar idonta a kan abincin da Amna ta kawo mata cikin dare wanda ko
buɗewa ba ta yi ba ballantana ta san mene ne a ciki. Jiki babu kuzari ta miƙe ta ɗauki foodflaks
É—in ta fice, zuciyarta tana jin babu wani abinci da zai burge ta a daidai lokacin. Saboda ko
yunwar ma ba ta ji kuma ba ta jin sha'awar cin komai. Amma dole ta isa harabar gidan tana
wara ido kafin ta hango maigadin gidan yana nufo ta da wani madaidaicin kwando.
Cikin ladabi ya gaishe ta ita ma ta amsa babu yabo babu fallasa kafin ta karɓi kwandon ta
miƙa masa foodflaks ɗin ta juya ba tare da ta ce da shi ƙanzil ba. Tana ƙoƙarin shigewa cikin
gidan ta ji sautin maigadin yana cewa,

"Me za a yi da wannan Hajiya?"

"Abinci ne, ka je ka ci."

Amsar da ta bayar kenan ba tare da ta juya ba. Ranta yana tafarfasa ta koma saman ta zauna a
kan bedside tare da rungume hannuwanta a ƙirji tana cizon leɓenta. Hawaye ta shiga gogewa a
kan fuskarta saboda kanta ya yi ƙullewar da ba ta san ta ina za ta fara ba. Saboda tunanin a
wane hali saurayinta yake wanda bai zo a ranta ba sai da safiya ta waye ta tabbatar abin da ya
faru babu wasa a ciki. Saɓanin kallon da take yi wa abin kamar shirin da zai ƙare Nur ta dawo
É—akinta ita ta koma gida.

Zumbur ta miƙe, ta shiga watso kayan Nur da ke cikin wardrobe ɗin ɗakin ta shiga birgima a
cikin su. Saboda tuno lokacin da take jera mata kayan da hannunta cike da farincikin burin
aminiyarta ya cika ta auri wanda take so. Kayan ta shiga runguma tana shinshina ƙamshin
turaren Nur da ta feshe mata kayan da shi yayin jera su. Wani sabon kuka ya zo mata, wanda ta kwashe lokaci tana juya zantuka a ranta babu mai
rarrashin ta. Kafin ta ji takun tafiyar mutane yana nufo É—akin da sautin maganganu sama-sama.
Amma ko kaɗan hakan bai saka ta motsawa ba, har aka fara ƙwanƙwasa mata ɗaki ba ta yi
magana ba ballantana ta tashi ta buÉ—e.
Muryar Innarmu ce a gaba kafin ta jiyo muryar gwaggonta Salame, waton ƙanwar Babanta.

Da ido kawai ta bi su, ganin salatin da suke yi a kan hango halin da suka iske ta cikin sa.

"Ahir É—in ki Amina! Wallahi ki kiyaye ni tun muna shaida jun..."

"Dakata Binta, abin fa sai da rarrashi. Kuma abin da kike so ta bi ba zai biyu ta daÉ—in rai ba.
Don haka ki bar mini komai ni zan shawo kan matsalar."

Zancen gwaggonta Salame kenan cikin tausasa murya. Sannan ta nufi inda Minal take kwance
cikin kayan Nur, ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye tana faɗin,

"Kwantar da hankalinki Amina, ai ita rayuwar duniya mai sauƙi ce idan aka bi ta a hankali.
Yaushe za ki hana kanki zama lafiya a kan abin da ke ma kina da ikon taimakon kanki da kanki?
Don Allah yi shiru share hawayenki lamarin duniya ba a yi masa gaggawa. A sannu ake bin
komai har cim ma nasara cikin iyawar Allah."
Da waÉ—annan kalaman Gwaggo Salame ta yi nasarar hana Minal wani kuka, sannan cikin
dabara ta zuba mata abinci ta shiga tsakura duk da shesshekan kukan da take yi jefi-jefi. Amma
ko kaÉ—an ba ta son haÉ—a ido da Innarmu, saboda hararar da take wurga mata kamar ta rufe ta
da mugun duka. Bayan ta É—an ci abincin ta kai ta bayi da kanta ta haÉ—a mata ruwan wanka ta
baro ta, tare da ba ta lokacin da za ta kammala ta fito tana jiran ta.
Minal ba ta ɓata lokaci a bayin ba, ta yi wankan a gaggauce ta fito. Gwaggo Salame ta miƙa
mata É—aya daga cikin kayan Nur da ta gama gyara ta mayar wardrobe kamar yadda suke tun
farko. Minal kayan ta kalla sannan ta kawar da kai ƙirjinta yana bugawa ta ce,

"Ba kayana ba ne."

Gwaggon ta matsa kusa da ita cikin ƙarafafa gwiwa ta ce, "Duk abin da kika gani a cikin gidan
nan naki kuma haƙƙinki ne. Don A'isha da ta bar miki mijin har da komai nata ta bar miki, tun
daga kan kayan É—akinta har zuwa suturarta."

"Gwaggo kayan Nur..."

"Kada ki ce komai saka kayan kawai."

Ta yi hanzarin katse ta saboda ganin tana so ta kawo mata wasa. Minal ta buÉ—e doguwar rigar
lesin ta saka, wadda ta sha adon aiki mai É—auke da É—inki stone work. Sannan gwaggo Salame
ta É—aura mata É—ankwali tana faÉ—in,

"Ko ke fa! Kin ga yadda kika yi kyawu kuwa? Ma sha Allah ki tsaya a haka kada na sake
ganin kuka a idonki."

Nur ta yi marau-marau da ido ƙwalla ta cika idonta ta saka gefen hannunta ta share. Sannan
ta zuƙe majinar kukan tana cewa,

"Don Allah Gwaggo ku tausaya mini, wallahi ba zan iya zama a gidan nan ba. Saboda
mutane za su zarge ni a kan na ci amanar Nur. Sannan shi kansa angon nata ba zai taɓa karɓa
ta a matsayin matarsa b..."







Ohh Allah 😔




D. Auta ce🙋
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*Masu neman littafaina ga su kamar haka; ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI, JIKI DA JINI
(A'ISHA), AMFANIN FITILA, MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA, RUWA DA ƘANƘARA,
GIDAN AURE. BAKAN GIZO, ZUBAR HAWAYENA, DAKAN ÆŠAKA.., MUSAYAR ZUCIYA,
TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran su. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan lambar;
08022014771.*

*LAMBA TA UKU.*

"A hir ɗin ki amina! Wallahi ki fita idona na rufe. Yaushe arziƙi yana kiran ki tsiya tana korar ki da
gudu! To ban son shashancin banza, don ke Allah ya bai wa mijin ba A'isha ba, kuma ita da
kanta ta bar miki shi ba matsa mata aka yi dole sai ta aikata ba, yo ɓata lokacinki na me za ki
dinga yi a kan abin da kina zaune allah ya ba ki ba tare da kin roƙa ba?"
Fusatattun kalmomin Innarmu kenan waɗanda tsabar haushin da Minal ta ba ta ya sa ta miƙe
tsaye tana neman hanyar kai mata duka. Ƙur Minal ta kafe ta da ido cike da zargi ta sake cewa,

"Yanzu ya zan yi da Aminu? Wanda kowa ya san yadda yake faÉ—i-tashi a kaina?"

"Yi mini shiru sakarya! Shi Aminun idan kika aure shi zai ajiye ki irin gidan nan ne? Ki faÉ—a
mini a kaf cikin danginmu waye ya samu arziƙin zama irin wannan gidan? To ba ki isa ki yi mana
baƙinciki ba, dole ne ki zauna ko kina so ko ba kya so! An riga an ɗaura aurenki da shi, kuma
babu uban da ya isa ya kunce auren nan! Ke ko mutuwa za ki yi sai dai a fitar da gawarki ehe!"

Innarmu ta ƙare maganar tana kumfar baki da zaro wa Minal ido, alamun ƙiris ya rage ta jibge
ta don ta gama kaiwa bango a kan lamuranta. Minal ma tsaye take kanta a duƙe tana kallon
yatsunta fuskarta a kumbure bayan bakin da ta turo tana gunguni. Tafasar da zuciyarta ke yi ya
sa ta yi maganar da take jin dole sai ta amayar da ita ko za a kashe ta. Domin idanuwan da
Innarmu ta kafe ta da su ba su hana ta furzar da abin da ke cikin bakinta ba.

"Ni fa wallahi ko kaÉ—an kuÉ—insa ba sa gabanta..."

"Mu su ne a gabanmu! Na ce miki mu su ne a gabanmu ki je ki faÉ—a wa duk uban da za ki
faɗawa. Kuma za mu ci sai inda karfimu ya ƙare, matuƙar muka samu damar cin sai mun ci...ke
Amina wallahi na kusa nakasa ki! Ni za ki gwada wa ƙarfin imani da taƙawa? To idan kin so ki
ce da mu kwaÉ—ayayyiya ai ba a kanmu aka fara son abin duniya ba. Wawuyar banza ana nuna
miki hanyar arziƙi kina runtse ido. Kuma Aminu da kike zancensa a yanzu babu ke babu shi har
abada! Saura kuma na ji labarin kin neme shi ko shi ya neme ki ki ga irin matakin da zan É—auka
a kanku. Sakaryar banza sai na shayar da ke gubar mamaki matuƙar ba ki shiga taitayinki a kan
auren nan ba....Salame ni na tafi idan kin gama ki same ni waje ina jiran ki..."

Martanin Innarmu ya ƙara lalata nutsuwar Minal, ta kasa shanye zafin maganganun a ranta
tun kafin ta dire zantukan, waÉ—anda ta ji mugun É—acinsu a zuciya har cikin bakinta. Bayan ta
gama kumbura ta fashe da wani kalar kuka cikin É—aga murya tamkar wadda ake tsula wa bulala.
Innarmu tana gama faÉ—ar batutuwanta ta fice daga É—akin a fusace tana ci gaba da faÉ—ar duk
abin da ya zo bakinta cikin faÉ—an da sautinta yake tashi.
Ajiyar zuciya Gwaggo Salame ta saki mai ƙarfi kafin ta riƙo Minal ta zaunar da ita a kan gado.
Jarumtar rarrashin ta ta shiga yi har ta samu ta rage sautin kukan da take yi. Sannan ta yi jim na
tsawon mintuna kafin ta yi ƙarfin halin faɗin,

"Kowace rayuwa da kalar tata jarabawa, ke taki jarabawar ita ce wannan. Don haka ki bar
wa Allah lamuranki kada ki yi jayayya da ƙaddararki, saboda ba a sani ba ko ita ce alherinki kina
ƙoƙarin turewa."

Shiru Minal ta yi ba tare da ta ce uffan ba, saboda maganganun Gwaggo Salame sun shiga
jikinta, ta share hawayenta ta koma ajiyar zuciya wata bayan wata. Duk da a ranta ba ta jin ta
karɓi cushen da aka yi mata a matsayin ingantaccen auren da ake yi wa kowace mace. Amma
kuma ta fi jin daɗin maganganunta a kan na Innarmu masu kama da ana yaƙi.
"Abu biyu zuwa uku nake so ki riƙe gam kafin mu ga kamun ludayin tafiyar." Maganar
Gwaggo Salame ta farauto hankalinta wuri É—aya, ta nutsu tana sauraron ta ba tare da ta yi
motsin kirki ba

"Na farko ki yi haƙuri a kan ba a nemi amincewarki ba, amma ki kalli hakan a matsayin gata
ne da wasu iyaye suke yi wa 'ya'yansu. Na biyu ki riƙe Ya Wadadu ɗari huɗu bayan kowace
sallar asuba, tana ƙara danƙon soyayya da kwarjini bayan farinjini na yankan shakku. Na uku

kuma ki lizimci raya dare da nafilolin biyan buƙatu a wurin Ubangiji. Na san kin sani akwai su
kala-kala, amma kafin mu je ɓangaren abin da za ki yi ki jawo hankalin mijinki; zan sanar da ke
nafilar da nake yawan yi, wadda ni ma na gwada kuma nake ganin amfaninta, saboda ina so ke
ma ki amfana."
Shiru ya ziyarci É—akin tsawon sakonni kafin Gwaggo Salame ta sauke nannauyar ajiyar
zuciya ta ce. "Ki tashi misalin ƙarfe ɗaya na dare zuwa biyun daren, ki yi nafila raka'a biyu kacal
kuma kowace ki karanta fatiha da Suratul Ahad, waton surar ƙulhuwallahu Ahad. idan kika
sallame sai ki yi wata sujuda kada ki É—ago kanki sai kin karanta La'ilaha Illa antassubhanaka
inni kuntu minazzalumina sau arba'in. Kada ki bar sujudar har sai kin faɗa wa Allah buƙatunki.
Ina mai tabbatar miki za ki ga aikin addu'ar tamkar yankan wuƙa da yardar Allah...."

Kiran wayar da aka yi wa Gwaggon ya sa ta yi hanzarin fito da ita daga aljihunta, ganin
Innarmu ce mai kiran; hakan ya sa ta tuno ashe ita take jira a waje. Ta miƙe tana gyara zaman
lulluɓinta ta ce,

"Mu za mu tafi, zuwa anjima za a aiko miki wasu daga cikin kayanki, sauran kuma za a raba
wa ƙannenki da wanda Allah ya ciyar. Amma don Allah ki tsayar da hankalinki wuri ɗaya ki nemi
zaɓin Allah. Ubangiji Ya ba ku zaman lafiya,

2 / 26