Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 26

21K to 24K   out of 77.3K words

saka shi razana
ko ya ji tsoron abin da take ƙoƙarin aikatawa ba. Haushin ko-in-kular da ya yi hakan ya ƙara rura
wutar tashin hankalin da take ciki.
Hannunsa ta damƙa tare da cusa masa wuƙar a ciki hawaye yana zarya a kan fuskarta ta ce,

"Ba don na san hukuncin wanda ya kashe kansa ba, da tuni na kashe kaina na huta da
zaman ƙaddarar da nake yi. Don haka ka taimake ni ka kashe ni kawai ka huta da gani na, zan
fi farinciki da hakan fiye da abubuwan da kake yi min..."

Ta durƙushe a gabansa tana wani irin gunjin kuka tamkar wadda aka lakaɗawa mugun duka.
Ido ya bi ta da shi cikin wani yanayi mara misali, saboda jikinsa ya yi sanyi ƙalau kuma kukanta
yana taɓa masa zuciya. Zumbur ya miƙe ganin tana ƙoƙarin karya masa zuciya ta ƙarfi, da

wuƙar a hannunsa ya nufi kitchen ya kwashe duka sauran wuƙaƙen da ke nan. Zuciyarsa cike
da tsoron tsautsayi ya sa ta kashe kanta ta jiƙa masa aiki ya koma masa sabo, don komai ya
faɗa ba zai goge kansa daga zargi ba. Saboda ko Hajiya ba za ta yarda a kan ba shi ne ya
kashe ta ba.
Ɗakinsa ya shige ya datse ƙofa, sannan ya ɓoye wuƙaƙen sannan ya zauna yana furzar da
iska daga bakinsa. Ya shiga tunanin yadda zai rabu da Minal cikin sauƙi ba tare da ya cutar da
rayuwarta ba. Ya miƙe cikin sanyin jiki ya ɗauko wayarta a inda ya ajiye ta, tun bayan ɗaukar ta
saboda binciken da yake so ya fara yi domin ya tabbatar akwai hannunta a cikin guduwar Nur
ko babu.

Kai-tsaye ya shiga binciken saƙonnin da ke cikin wayar, tun daga kan waɗanda take turawa
har waɗanda ake turo mata. Jikinsa ya yi sanyi ƙalau ƙirjinsa ya hau bugawa, saboda cin karo
da saƙon da ta tura wa Gwaggo salame a kan ta zo zai kashe ta. Hamdala ya yi ga Ubangiji a
kan dabarar kwashe wuƙaƙen da ya yi, amma hakan bai saka shi nutsuwar zuciya ba, sai da ya
ajiye wayar ya fito ya same ta a inda ya bar ta har lokacin ba ta daina kukan ba.
Tsaye ya yi a kanta hannuwansa zube cikin aljihu ya yi gyaran murya sannan ya ce,

"Ki tashi ki zauna za mu yi magana."



Ga link;

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/ICmrsyihZBzLrpXfmM7DyQ

Masarauta group ne ga masu tambayar a saka su group da masu buƙata su ma su yi joining.



D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

FANSAR ƘAUNA FAN'S GROUP. Idan kun ji joining ku jira zan yi approving.

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa

*LAMBA GOMA.*

Tsawon minti biyu yana tsaye a kanta ba tare da ta motsa ba kuma bata daina kukan ba.
Furzar da iska ya yi daga bakinsa ya gyara tsayuwarsa ya sake cewa,
"Nace ki tashi zamuyi magana, saboda wannan kukan ba shi ne mafita ba, kuma nemo
mafitar da kanmu shi ne abin da ya fi dacewa a wannan lokacin."

Minal ta rage sautin kukanta, saboda sautin da ya yi amfani da shi wurin maganar ya yi
nasarar shiga jikinta. Hakan ya sa ta tashi daga kifen da take ta zauna tana shassheka tare da
ƙoƙarin goge hawayen da suka ɓata mata fuska. Ga idanuwanta sun yi jajir alamun duk wurin
ranar da kuka ta yi shi.
"Please! Ki daina kukan nan kuma Ki nutsu magana ce za mu yi mai muhimmanci."

Sai sai da ya ba ta minti daya zuwa biyu ta saita kanta nutsuwarta ta dawo jikinta ta koma
zuƙar majinar kuka. Sannan shi ma ya zauna a kan kujerar da ke fuskantar ta bayan ya rage
muryar Tv ya yi gyaran murya ya ce,

"Ina so ki faɗa mini gaskiya tsakaninki da Allah. A kan ba za ki ɓoye mini gaskiyar duk abin da
zan tambaye ki ba, don ina son mu tattauna da kyau kuma mu shawo kan matsalar ni da ke."

Ba ta ce masa komai ba, amma shirun da ta yi tana kallon yatsun hannunta hakan ya nuna tana
jin sa, kuma a ranta ta saƙa za ta faɗa masa iya abin da ta sani. Amma saboda bai ji furucin
bakinta ba hakan ya sa bai gamsu da shirun da tayi masa ba. Kai-tsaye ya sake jefa mata
tambayar kamar yadda ya yi tun a farko.
"Kin yi alƙawari za ki faɗa mini gaskiya?"

Kai kawai ta ɗaga masa ba tare da ta yi magana ko ta ɗago kai ta kalle shi ba. Hakan ya ƙara
masa ƙarfin amayar da abin da ke cikin bakinsa cikin ƙumaji da takaicin da ke cizon ransa.

"Ke ce babbar ƙawar Nur idan aka cire Amna, kuma 'yar uwarta wadda na sani mafi kusanci da
ita. Don haka kin fi kowa sanin wace ce Nur da yadda matsayina yake a wurin ta. Shin me ya sa
ta gudu ta bar ni a daidai lokacin da na fi buƙatar ta? Kuma mene ne dalilin da ya sa ta haɗa
aurena da ke bayan ta san ita kaɗai ce macen da na yi wa rayuwata tanadi?"
Dam-dam ƙirjin Minal ya buga, ta yadda ba ta san mafarin zuwan wani sabon firgicin da ya
farmaki zuciyarta ba. Saboda tambayoyinsa ba ƙaramin taɓa mata zuciya suka yi ba, kuma sun
dagula mata duk wani lissafin da ke cikin kanta. Don ta sani komai za ta faɗa ba zai taɓa yarda
a kan babu sa hannunta cikin abin da ya faru ba. Amma hakan bai hana ta yin magana cikin
ƙarfin hali da jarumta ba.

"Allah shi ne shaidata ko da kowa bai yarda da ni ba. Saboda ban san komai a kan abin da ya
faru ba, yadda ka ji zancen a sama haka ni ma na ji. Kuma ban san me ta tsara ba sai bayan
afkuwar abin da ya faru."
Daga haka ta ja bakinta ta tsuke, saboda zuciyarta ta karye wani sabon hawaye mai zafi ya
fara bin fuskarta. Hawayen da ya ƙara lalata wa Jamal sauran kuzarin da ke ransa. Saboda har
zucinsa ba ya son ganin kukan da take yi.

"Yanzu dai a taƙaice kina nufin ba ki san komai a kai ba?"

Shiru ta yi masa don maganarsa ba ta buƙatar maimaicin amsa, a kan abin da ta riga ta yi wa
rantsuwa. Kallo ya ƙura mata tsawon lokaci yana nazarin ta, don zuciyarsa ta yarda da ita a kan
babu hannunta a cikin haɗin auren da guduwar da Nur ta yi. Kuma ya gano hakan tun a kalolin
saƙonnnin da ya gani a cikin wayarta. Waɗanda take tura wa Nur ba tare da ta yi shawara da
kowa ba, kuma ba ta san zai iya taɓa wayar ba ballantana ya gani ya goge tsatsar da zuciyarsa
ta yi a kanta. Tana tura mata saƙonnin ne kawai a duk lokacin da ƙuncin zuciya ya hana ta
sukuni.

"Hmmm!" Ajiyar zuciyar da ya sauke kenan yana jingina bayansa jikin kujera, tare zamewa ya
kwanta tsawon mintuna kansa a sama yana nazari.

"Yanzu wane hukunci kika yanke wa zamanmu?"

Ya jefo mata tambayar, wadda ta zo mata a ba zata ba tare da ta shirya wa zuwanta ba. Amma
hakan bai hana ta dakiya cikin nuna ko in kula ba ta ce,

"Komai a hannunka yake."

"Kina nufin duk abin da na zartar hakan ya yi miki?"

Ya yi maganar ƙirjinsa yana bugawa, saboda ko kaɗan ba ya son fushin Hajiya. Sannan kuma
ba zai iya zaman aure da ita ba a bisa ra'ayin kansa. Ita ma ƙirjinta ya buga dam-dam, duk da
auren ba ta tabbatar da ingancinsa ba, amma ko kaɗan furucinsa bai yi mata daɗi ba.

"Ba zan so na ci gaba da cutar da ke a banza ba. Ki faɗa mini kawai ni duk abin da kike so zan
bi shi ko da ba na ra'ayi."

A nan ma shiru ta yi masa ƙirjinta yana bugawa, saboda tuno kalaman Innarmu. Waɗanda take
yawan yi mata a duk lokacin da ta kira ta a waya.

'Duk kika kuskura kika kashe aurenki ba za ki taɓa samun mijin da ya kai Jamal ba. In don
Aminu kike borin yanzu haka an yi masa baiko da wata. Kuma daga ranar da ki bari Jamal ya
sake ki ki sauya uwa don ni ban haɗa komai da ke ba.'

Furutan Innarmu kenan, waɗanda ke raba mata hankali gida biyu. Tana son yi mata biyayya
kuma tana jin takaicin raba ta da Aminu da aka yi ta ƙarfin tsiya.

"Ko kina da ra'ayin zama da ni mu ci gaba da zamanmu a yadda muke kai yanzu?"

Ya dawo da ita daga duniyar nazarin da ya fahimci ta lula. Amma ban da dukan da ƙirjinta yake
yi ba ta iya motsa ko ɗan yatsanta ballantana ta ba shi amsa. Hakan ya sa ta yi masa gum
kamar ba ta ji me ya faɗa ba. Har sai da ya sake yin maganar da ta kasa haƙurin shanyewa
ɗacin furutan, sai da ta furzar da abin da ke cikin bakinta.
"Ga shi ke ba kya so na ballantana ki koya mini son ki na jaraba na gani, ko da zan iya ba ki
kaso biyar a cikin goman son da nake yi wa Nur."

"Ba na so!"

Ta yi maganar a fusace fuskarta a cure, sannan ta miƙe a ƙufule da niyyar barin falon, don ta
fahimci lamarinsa akwai kalolin rainin hankali a ciki.
Caraf ta ji ya damƙo hannunta ta baya, ta yi hanzarin sandarewa wuri ɗaya ba tare da ta motsa
ba. Saboda riƙon da ya yi mata ba ƙaramin jan ranta ya yi ba. Duk da ta so ƙwace hannunta
amma ta bi umarnin zuciyarta ta kasa motsawa, sai bugun numfashinta da ya ƙara wa kansa
gudu. Ɓil-ɓil zuciyarta ta shiga bugawa jikinta ya hau tsuma, yanayin da take ji ya saka ta ɗora
hannu ɗayan a ka ta fashe da kuka iya ƙarfinta tana faɗin,

"Wayyo ni kaina!"

Zumbur ya tashi zaune bayan ya sake ta idonsa a kanta ya ce, "Me kuma na yi miki kike ƙoƙarin
tara mini jama'a? Ko yau ɗin ma za ki jawo maigadi ya bubbuga mana ƙofa ne? To bari ki ji ni
babu abin da zan sake nema daga gare ki. Jiyan ma tsustsayi ne da ban san dalilin da ya sa na
yi abin da na yi ba. Amma in dai ni ne ki kwantar da hankalinki ko wane irin kallo ba zan sake yi
miki ba a cikin gidan nan. Idan kika cire kallon Musulunci shi ma irin wanda shari'a ta tanadar. Ai
hakan ya yi miki ko?"

Ya ƙare maganar da wata kalar murya kamar wani sakarai. A ƙoƙarinsa na son kwantar mata
da hankali take-yanke. Saboda tsoron ta cutar da kanta a banza ko kuma ta yi wa kanta wata
illar da za ta jawo masa shiga komar tuhuma. Minal kam ita kaɗai ta san abin da take ji a ranta,
hakan ya sa ta kasa daina kukan da take yi kuma ta ƙi barin wurin kamar yadda ta yi niyya a
farko.
Tsam ya miƙe yana sake roƙon ta yi haƙuri ta daina kukan, tun da ba ta son maganar da safe za
su ƙarasa kafin ya fita wurin aiki tun da ta ƙi bari su kai matsayar zancen. Tana kuka ƙasa-ƙasa
har ya gama kashe komai na wuta ya shiga ɗakinsa ya ɗauko wayarta ya ajiye gefenta, sannan
ya koma ɗakinsa ya datse ƙofa zuciyarsa cike da damuwa. Jikinta yana tsuma ta buɗe wayar ta danna wa Gwaggo Salame kira. Ta yi ƙoƙarin saita kanta
wurin magana amma hakan bai hana Gwaggon gano kukan da ta sha ba tun daga sallamarta.

Ranta a ɓace ta yi magana tun kafin ta ji dalilin kiran da ta yi mata ta rufe ta da faɗa. Sai da ta
tsagaita faɗan Minal ta yi magana cikin sanyin murya ta ce,

"Gwaggo ya ba ni zaɓi a kan zamanm..."

"Damuwar me za ki dinga yi Amina? Bayan Allah ya ba ki dama ki yi rawar gaban hantsi
yadda kike so."

"Idan na yi haka na ci amana Gwaggo."

"Tun da har A'isha da kanta ta bar miki shi ya dace ki riƙe da kyau ta yadda ke ma zai so ki
kamar yadda ya so t..."

"Ta ya ya zai so ni Gwaggo? Bayan soyayyarta ta daskare masa zuciya."

"Kina mace amma ki zauna namiji yana gasa miki aya a hannu Amina? To ki sauya takunki,
kuma ki iya hannunki ta yadda zai yaba wa aya zaƙinta ke ma ya san darajarki."

"A'a ba zan iya ba."

Daga haka ta katse wayar, cike da zargin ko dai Gwaggon ta gano abin da ke damun zuciyarta.
Ta jima a wurin zaune tana saƙawa da kwancewa, tare da zance daga ita sai kanta, inda zuciya
ke nuna mata hanya amma tana ƙoƙarin kaucewa. Ta goge busassun hawayenta sannan ta
miƙe ta yi nata ɗakin jiri yana ɗibar ta. Kuma cike da tunanin yadda za ta yi ta sanar da shi ba ta
son ya sake ta za ta jira har ranar da Nur za ta dawo gare shi. Zuwa lokacin za ta goge duk
wani laifinta a gun sa har ta dasa masa tausayin ta a ransa. Sannan kuma Innarmu za ta ji daɗi
idan ta ga ta daina bore da ƙoƙarin guje wa zaman auren saboda son koma wa Aminu.

Amma fahimtar wane ne Jamal da kalolin rainin hankalinsa ya sa ta ga gara yi masa shiru a
kan ta sanar da shi ƙudurinta. Yayin da wata zuciyar ta ba ta shawarar kawai ta sanar da shi
don ya san irin zaman da yake yi da ita. Ko don ya sassauta mata zaren wulaƙancin da yake ja
ba tare da ya tausaya wa halin da take ciki ba. 'Idan abu ya dame ki, ki hana idonki bacci ki kai kukanki ga Allah. Saboda shi kaɗai ne wanda
zai warware damuwarki cikin sauƙi.'

Wata nasihar Gwaggo salame ta faɗo a ranta, hakan ya sa ta nufi toilet ta ɗoro arwala cike da
kuzari ta shimfiɗa sallaya. Don ta gamsu da babu mai maganin abin da ke ranta da matsalarta
face shi.

Nafilar da Gwaggon ta koyar da ita ta fara yi kamar yadda ta yi mata bayani, tare da kai
kukanta ga Allah a kan shi ya fi sanin abin da ya fi dacewa ga rayuwarta. Don haka ya zaɓa
mata mafi alheri zama da Jamal ko barin gidansa.

"Idan zama da shi ne alheri Ubangiji ka cusa masa so na ko zai dinga jin tausayi na."

Addu'ar da ta dinga yi tana maimatawa kenan, har ta ci rabin dare sannan ta kwanta cike da
tsammanin ganin sauyi a tattare da shi kamar yadda ita ma za ta sauya masa kalar nata takun.
Duk ta sani za ta sha wuya kafin ta shawo kansa, saboda kafiyarsa da nacinsa a kan Nur da
duk abin da ya shafe ta. Da wannan ƙudurin ta kwana cike da ɗokin safiya ta waye. Asubar farin ta tashi duk da ba ta gama biyan bashin barcin da take ci ba. Ta shiga gyaran
ɗakinta har zuwa wardrobe ɗin kayanta da akwatunan Nur ta sauya musu mazauni. Sannan ta
fito filo ta hau gyara duk da babu wani abin da ta ɗauke, kasancewar komai yana mazauninsa
amma sai da ta ƙara wa komai saiti. Sannan ta jawo wayarta ta shiga YouTube binciken kalolin
breakfast.
Kitchen ta faɗa a gurguje ta shiga fere doya tare da farfasa tarugu tattasai da albasa, a gefe
ɗaya kuma ta ɗora tukunyar dafa doyar bayan ta koma fere Irish cikin sauri.
Cikin lokaci ƙalilan ta fara haɗa yam ball ta soya faka-faka. Sannan ta koma kan miyar ƙwan
da za a ci da zallar farar doyar, wadda ta sha kayan haɗi sai ƙamshi ke tashi. Bayan ta soya
wainar ƙwan hatta ruwan zafin tea sai da suka sha haɗin kayan ƙamshi. Sannan ta ɗebo komai
ta jera a falo ta koma kitchen gyaran inda ta ɓata da wanke kayan da ta yi aiki da su. Zuciyarta
cike da ƙaguwa a kan son ganin sa da irin yanayin da zai tarbi bajintarta. Duk da ta sani abu ne
mawuyaci ya ci girkin, amma ta yi don kawai ta auna baiwarta kamar yadda Gwaggo Salame ta
zaburar da ita.
Harabar gidan ta fita, babu ɓata lokaci ta shiga wanke masa mota maigadi yana kallon ta ta
gefen ido. A ransa yana jinjina ƙarfin hali irin Jamal saboda ganin yadda yake ƙoƙarin mayar da
aure bauta. Ita kam ko a jikinta ta wanke motar tas ta goge masa, sannan ta koma sharar
harabar gidan cike da ƙumaji ta tattara sharar, sai a lokacin maigadin ya ce ta bari shi zai
kwashe sharar ya zubar.

8 / 26