Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 26

18K to 21K   out of 77.3K words

cewa,

"Yarinyar nan ita kanta damuwa ce mai zaman kanta Hajiya. Kuma idan ina tare da ita ciwon
da likita ya faɗa yana gaf da afkuwa komai ya faru a kaina. Saboda zama da ita tamkar
barazana ce ga rayuwata Hajiy..."

"Ka yi haƙuri, ni da ma farincikinka nake nema. Amma tun da nawa tsarin bai yi maka ba ka je
ka yi duk abin da kake so. Sai da ka sani ko da Nur ta dawo ba zan taɓa bari ka yi zaman aure
da ita ba, tun da har ta iya tsallakewa ta gudu alamu ya nuna ba ta son ka. Kuma duk wanda ba

ya son ka ni ko lahira ba na fatar haɗuwa da shi."

Tana ƙare maganar ta ja bakinta ta tsuke bayan ta haɗe rai da fuska alamun babu wani
sauran sassaucin da za ta yi masa a kan hakan.

"Haba Hajiya, ke fa kika sanar da ni ba da Nur aka ɗaura aurena ba na ɗauki ƙaddarata a
yadda ta zo mini, sannan kuma a yanzu ki koma ganin laifinta ki koma a kan guduwar da ta yi
don ba ta so na ne? To me zai hana ta guduwa bayan an raba ta da abin da take so? Ina son
Nur Hajiya kuma zan nemo ta a duk inda take, ko da a yanzu ita ta daina so n...."
"Ni kuma matuƙar ba ka kula da Amina kuka zauna lafiya ba; ban yafe maka ba idan har ka
tafi neman wadda ba ta san muhimmancinka ba. Sannan kada ka manta; ko danginta sun gaji
da neman ta sun bar wa Allah saboda tsarinta ne aka bi kuma ganin damarta ne...kai a taƙaice
aurenka da Amina ma ita ce ta haɗa komai...to a kan me za ka lalata damar da Allah Ya ba ka a
kan neman wadda ba ta ra'ayin ka?"

Shiru ya yi mata ba tare da ya ce komai ba, saboda maganganun sun shiga jikinsa sun dakar
masa zuciya. 'matuƙar ba ka kula da Amina kuka zauna lafiya ba, ban yafe maka ba idan har ka
tafi neman wadda ba ta san muhimmancinka ba.'
Ya shiga maimaita zancen a ransa nan take damuwa ta ƙara yi masa lulluɓin tashin hankali.

"Ta ya zan zauna lafiya da Amina bayan babu so a tsakanina da ita? Me ya sa za ki yanke mini
irin wannan hukuncin bayan kin sani Nur ita ce rayuwat..."

"Ka mutu a yau ɗin nan Jamal idan har da gaske ita ce rayuwar taka! Saboda wallahi ka ji na
rantse da Allah ba zan taɓa yafe maka ba matuƙar ka bar matarka ta sunna ka je yawon neman
wadda ba ta san darajarka b...shin har sau nawa zan faɗa maka ita ce ta nemi haɗin aurenka
da Amina? Ko so kake yi sai na yi ta shela da lasifika ina bayani sannan za ka fahimce ni? To
Nur ba ta son ka, don da tana sonka ba za ta nemi a cusa maka Amina ita kuma ta tsallake ka
ta bi duniya ba. Na faɗa na koma faɗa ba zan lamunci ganin cigaban rayuwarka ya tsaya a
sanadin wata macen banza ba Jamal!"

Tana ƙare maganar ta bar masa falon ta shige ƙuryar ɗakinta tana goge hawaye, hawayen
kukan da ta so dannewa tana kokawar kada su fito amma suka kasa ba ta haɗin kai.


Wai ya abin yake ne?


Ga link;
https://chat.whatsapp.com/ICmrsyihZBzLrpXfmM7DyQ

Masarauta group masu tambayar a saka su group da masu buƙata su ma su yi joining.

D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

*Follow the D. AUTA NOVELS channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029Vb2zCo5JUM2bDSfRzW01*

*Na buɗe channel fatar za ku dinga leƙawa akwai wasu littafaina da zan saki ta can.*

*LAMBA TA TARA.*

Jikinsa ya yi sanyi ƙalau, saboda zubar hawayen Hajiya Mummy ba ƙaramin tashin hankali
ba ne a wurin sa. Musamman a ce kuma shi ne ya yi sanadin saka ta kukan da babu farinciki a
cikin sa. Ya jima a wurin bai motsa ba, zuciyarsa ta shiga saƙa masa abubuwa da dama. Kafin
ya nisa cikin ƙaƙƙarfan sauti ya miƙe cikin sanyin jiki da na gwiwa. A haka ya ja ƙafafuwansa
zuwa cikin ɗakin nata fuskarsa a yamutse. Saboda hango ta a bakin gado tana goge ƙwalla da
gefen ɗankwalinta.

"Kukanki tamkar ɗigar dalma ne a jikina. Me ya sa kike so Allah ya yi fushi da ni Hajiyarmu?"

Ya yi maganar cikin sanyin murya a lokacin da ya kai gwiwowinsa ƙasa a gabanta ya dafa
cinyoyinta. Sharr hawaye suka shiga malala a kan fuskarsa ba tare da ya damu da sharewa ba.
Kansa ta dafa ita ma hawayenta bai daina gangara a kan fuskarta ba, amma hakan bai hana ta
yin magana cikin muryar kukan ba.
"Duk abin da ka ga na yi ina yin sa ne saboda farincikinka Jamal. Ba burina ba ne saka ka
kunci ko damuwa kawai don ina son ka yi mini biyayya. Idan ka riƙe Amina a matsayin mata in
sha Allahu za ka yi alfahari da hakan ko a bayan rain...."

"Daina ambaton mutuwa Hajiyarmu...ba yanzu ba, kuma ba za ki mutu ki bar mu ba sama da
shekaru masu yawa. Sai kin ga 'ya'yana da jikoki kamar yadda kika ga Amna kina shirin ganin
aurenta da yardar Allah."

Shiru ta yi masa, saboda kukan da ke taso mata a zuciya tana ƙoƙarin dannewa. Idonsa a kan
fuskarta ya ce, "Ina son Nur Hajiyarmu, amma tun da ba kya son na je neman ta ba zan je ba,
sai zuwa lokacin da kika amince mini."

Gefen hannunta ta saka ta goge fuskarta sannan shi ma ta goge masa nasa hawayen tana
cewa,

"Ubangiji Ya yi maka albarka."

Daga haka ya miƙe yana yi mata sallama, bayan faɗar amin a bakinsa ya fice gidan. Zuciyarsa
cike da ƙuncin da bai san ina zai saka kansa ya ji sanyi ba. Hakan ya saka shi shawagi a
saman tituna idan ya sauka wannan ya koma kan wancan. Ba tare da ya san ina ya nufa ba
saboda kansa ya ƙulle ta yadda bai san abin da ya dace ya yi ba a lokacin. A ƙarshe tsayuwa
ya yi a gefen titin wani junction, ya ɗora kansa saman sitiyari yana kukan zucin da babu hawaye
ko sauti.

'Me ya sa Hajiya za ta yi mini iyaka da Nur?'

Tambayar da ya yi wa kansa kenan wadda babu mai ba shi amsa. Ya jima a duƙen yana nazarin
yadda zai shawo kan Hajiya ta fahimci abin da yake ji a cikin zuciyarsa. Saboda yana da
tabbacin ko mutuwa ya yi ya dawo duniya ƙaunar Nur ba za ta bar zuciyarsa ta huta ba.
Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi, sannan ya zare wayarsa da ke caji ya shiga danna wa Adamu
abokinsa kira. Bayan barkwancin da suka fara ya katse shi da tambayar inda zai same shi, ya yi
masa kwatance sannan suka yi sallama. Iska ya furzar mai zafi a jikinsa kafin ya buga motar ya
sake hawa kan titin.
Tafiya yake yi a hankali har ya isa Jami'ar Bayero University ya yi parking a harabar
makarantar. Wuri ɗaya ya ƙura wa kallo, kamar mai nazari a kan mabambanta mutanen da ke ta
shawagi. Amma ko kaɗan zuciyarsa ba ta wurin, asali ma ba ya hangen kowa face fuskar Nur
da sautin maganganun Hajiya. Kiran da aka yi masa a waya ya saka shi kai kallonsa a kan
fuskar wayar. Ganin wanda ya zo nema ne ya saka shi hanzarin ɗauka yana faɗin,

"Kai nake jira."

Daga haka bai sake cewa komai ba ya katse kiran, tare da bubbuga goshinsa yana hucin iska
daga bakinsa. Buɗe motar Adamu ya yi yana 'yar dariya ya ce,

"Ango ka sha ƙamshi, na Amina ba da kanka a sare.."

Kallon da Jamal ya yi masa ya saka shi barin zancen ya koma murmushin yaƙe saboda
fahimtar ba ya cikin yanayin mai daɗi. "Magana nake so mu yi mai muhimmanci, don haka ba
na son abin da zai ƙara ɓata mini rai a banza, zancen ango ko wata Amina duka ka jingine shi a
gefe mu yi abin da ya kawo ni."
"Ok tom, me ke tafe da kai?"

Adamu ya yi maganar cikin shiga nutsuwarsa. Nisawa Jamal ya fara yi mai ƙarfi sannan ya

rungume hannuwansa a ƙirji ya ce, "Ina so na gama da Hajiya lafiya, amma ba zan iya yin abin
da take so na yi ba. Wannan dalilin ya sa na taso ƙafa-ƙafa zuwa neman ka domin ka nemo
mini mafita."

Kallonsa kawai Adamu ya yi ba tare da ya ce da shi komai ba, hakan ya bai wa Jamal damar
sake cewa, "A wannan lokacin da muke ciki ko mace aka yi wa auren dole idan ba ta so za a ga
ta'addanci ballantana ni ina namiji a nemi saka ni zama da wadda ba na so. Sannan idan ma
aka jingine matsalar gefe raba ni da Nur tamkar saka almakashi ne a datse mini igiyar da nake
shanya farincikina. Ba na jin zan iya yi wa Hajiya biyayya a kan rabuwa da son Nur ko da na yi
haƙurin zama da Amina. Shin ya zan yi Hajiya ta gano illar abin da take ƙoƙarin yi ba abu ba ne
mai sauƙi?"

Ya ƙare maganar cikin wata kalar murya mai ɗauke da yanayi mara daɗi tun a kan fuskarsa.
"Hmmm!" Ajiyar zuciya Adamu ya yi kafin ya sake cewa,
"Babu abin da zan faɗa illa na ce ka yi haƙuri, sannan ka nemi zaɓin Ubangiji maji roƙon
bawansa n.."

"Kalmar haƙuri ta yi kaɗan ta rarrashi zuciya Adamu. Don haka ban ji wannan ba, idan ba ka
da wani abin faɗa sai haƙurin; to kawai mu bar zancen gabaɗaya."

Murmushi Adamu ya yi sannan ya yi magana cikin nutsuwar da ya gayyato ya yafa wa
jikinsa. Saboda shi kansa ba ya jin daɗin halin damuwar da abokin nasa yake ciki. Hakan ya sa
yake roƙon Hajiyar a kan ta sassauta ƙiyayyar da take yi wa Nur duk da ya sani abin da ta
aikata dole ne a ji haushin ta.
"Lamarin iyaye ba abu ba ne na wasa, na sha sanar da kai Hajiya ba za ta so abin da zai
ɓata maka rai da gayya ba. Saboda uwa ce, kuma irin wadda samun irin ta a wannan lokacin
abu ne mai wahala. Ta ƙi aure tun tana da ƙurciya ta tsaya kai-da-fata a kanku duk don kada
rayuwarku ta lalace. Me ya sa a yanzu ba za ka iya yi mata halacci ba? Ka ba ta dama a kan
abin da take so sannan ka bi da addu'a in sha Allah komai zai warware cikin sauƙi. Don haka ka
yi haƙuri ko ba ka son Amina ka karɓe ta a matsayin matarka, wataƙila alheri ce gare ka ba tare
da ka sani ba."

"Idan na karɓi Amina na yi ya ya da Nur?"

"Lokaci zai sanar da kai makomarta a gaba. Don haka ka bar wa Allah komai shi zai yi
maganin matsalolinka gabaɗaya."

Adamu ya yi maganar cikin yanayin da ke tabbatar da yin amanna da duk abin da yake
hasashe. Jamal ya yi shiru tsawon mintuna kafin ya ce,

"Ni zan wuce, amma ban gama shawara a kan lamarin ba. Sannan zan yi cigiyar Nur ko a
cikin gidana ba tare da na tsallake dokar Hajiya ba."

"Allah Ya zaɓa abin da ya fi alheri."

Adamu ya yi maganar tare da miƙa masa hannu suka yi musabaha kafin ya fice yana ƙara
jaddada masa komai zai wuce idan an saka wa zuciya haƙuri. Kai-tsaye ya koma bakin aikinsa,
kasancewarsa ɗaya daga cikin malaman Jami'ar kuma masu ruwa da tsaki a cikin makarantar.
Jamal ya ja motarsa zuwa wani masallaci ya yi sallar Asr, sannan ya zarce wani gidan abinci,
sai da ya yi ƙat sannan ya riƙo abin da yake buƙata ya nufo gida yamma sakaliya. Zuciyarsa a
cunkushe saboda ya kasa nutsuwar da zai yarda da tsarin Hajiya.
Misalin ƙarfe shida saura ya shiga gidansa, hannu kawai ya ɗaga wa maigadi sannan ya shige
da ledodinsa a hannu. Minal ya gani tsaye a falon tana cika tana batsewa alamun jiran
shigowarsa take yi. Amma ganin ta bai saka shi bi ta kanta ba ya nufi hanyar shigewa ɗakinsa.

"Malam, wayata za ka ba ni."

Ta yi maganar a sama saboda ta zo wuya a kan takaicin yadda ya saka ta zaman kaɗaici bayan
zaman ƙuncin da take yi a gidansa. Bai nuna ya ji abin da ta faɗa ba, ballantana ya tsaya
tankawa. Ɗakinsa ya shige da guntuwar sallama ya ajiye ledodin hannunsa ya faɗa toilet. A
gurguje ya yi alwala ya fito babu shiri ya yi turus saboda ganin ta a tsakiyar ɗakin riƙe da ƙugu
tana jijjigar jiki. Yi ya yi kamar bai gan ta ba ya zagaye ta yana mayar clips a hannun rigarsa.

"Ka ba ni wayar akwai abin da zan yi."

Ɗakin ya buɗe yana ƙoƙarin ficewa ba tare da ya bi ta kanta ba, caraf ta riƙe masa riga ta
baya hawaye ya fara wanke mata fuska ta shiga rera kukan da ya saka shi daskarewa a wuri
ɗaya, ya kasa gaba kuma ya kasa juyowa.

"Duk girman ƙiyayyar da kake yi mini ba ta isa ba sai ka ƙara saka ni a damuwa? Mene ne
laifina bayan ba ni ce na maƙalaww wa kaina zama da kai ba? Me ya sa ba za ka tausaya mini
ba, bayan ka sani ni ma ina da wanda nake so.."

Maganarta ta ƙarshe ba ƙaramin duka ta yi wa zuciyarsa ba. Hakan ya saka shi waigowa
idonsa a kanta cike da wani irin sabon yanayin da ya shige shi a lokaci ɗaya ya yi magana cikin
wata kalar murya.

"A cikin gidana kike zancen kina da wanda kike so?"

"E, kamar yadda kake son Nur haka ni ma nake son Aminu. Don haka babu adalci idan ka ce
za ka hukunta ni a kan laifin da ni ma an yi mini, kuma zaman maneji nake yi da kai ba don ina
sonka ba..."

A hargitse Jamal ya sake jifar ta da wani kallon mamaki ya yi magana cikin raunin zuciya ya
ce, "Ba kya so na?"

"Babu ranar da zan iya son ka Jamal. Saboda ba ka cikin kalar mazan da na tsara wa kaina
rayuwar aure da su."

Murmushin takaici ya yi, kafin ya kalli kansa ya koma ƙare mata kallo sama da ƙasa ya ce,
"Mace irin ki ba isa ta faɗar ba ta so na b.... don haka ko da wasa kika sake yi mini zancen wani
a cikin gidana; wallahi sai na nuna miki ba iri na ake yi wa iskanci b.."

"Gaskiyar kake so na daina faɗa ko son Aminu zan cire a zuciyata a cikin gidan nak..."

Karaf ta ji saukar yatsunsa biyar a gefen fuskarta, yana huci ya shiga nuna ta da hannu idonsa
a zare ya fara magana a birkice sannan cikin ɗaga muryar da ta ƙara saka ta jin tsoron sa ta
fashe da wani sabon kuka.

"Ba ki isa ki saka ni gaba kina faɗar abin da kika ga dama ba, kuma ba ki da matsayin da za
ki yi mini abin da kike so! Ba Aminu ba ko sunan anta na ji kin sake faɗa a cikin gidana sai na
zare harshenki na datsa shi gida biyu!"

Yana ƙare maganar ya kai mata harbi da ƙafa kafin ya buɗe ƙofar ya fice daga ɗakin zuciyarsa
tana tafasa. Tsabar takaicin rainin da take son kawo masa bayan ɗaurin talalar da Hajiya ta yi
wa rayuwarsa a kanta. A hargitse ya yi sallar ya dawo gida bayan sallar Isha. Saboda har
lokacin bai daina jin zafin kushen da ta yi masa a kan wani ƙaton banza ba. Kukanta da ya tarbe
sa bayan dawowarsa ya ƙara dagula masa lissafi. Hakan ya saka shi zama falo ya yi
kwanciyarsa ganin har lokacin tana cikin ɗakin nasa ba ta fito ba. Tv ya kunna aka yi dace MBC
Action suna wrestling ya miƙa hankalinsa a kan kallon, amma zuciyarsa ba ta daina jin zogin
abin da Minal ta yi masa ba. A gefe ɗaya kuma ba ya jin daɗin sauraron kukan da take yi, don
gabaɗaya ta lalata masa kuzarin jiki.

Tsawon awa ɗaya tana kukan kafin ta rarrashi kanta ta miƙe a ƙufule ta fito daga ɗakin.
Kai-tsaye kitchen ta nufa saboda ta gama kaiwa maƙura a kan halin damuwar da take ciki.
Wuƙa ta zaro sabuwa fil ta fito jikinta yana tsuma ta isa kansa ta tsaya. Idonsa a kanta Tv bai
ɗauke kansa daga kallon ba, duk da ya ga wuƙar a hannunta amna hakan bai

7 / 26