Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   5 / 26

12K to 15K   out of 77.3K words

da take son yi masa ta yi kada ya kwana da
yunwa. Ta ɗauki minti biyar a bakin ƙofarsa tana tunanin yadda za ta shiga ɗakin da irin
sakamakon da zai biyo bayan shigarta. Kamar wata mara gaskiya haka ta shiga É—akin nasa
tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ƙirjinta yana harbawa. Nesa da shi ta tsaya tsawon minti
biyu ba tare da ta iya furta masa ko kalma É—aya ba. Alamun mutum da ya ji a kansa ya yi
hanzarin tashi zaune yana ƙare mata kallo cike da mamaki. Kafin ya haɗe girar sama da ta ƙasa
ya yi magana cikin kakkausar murya ya ce,

"Malama lafiya kika shigo mini É—aki ko sallama babu!"

"Abin..ci...abin...cin...na ce.."

Kalmomin da ta yi ƙarfin halin harhaɗawa kenan cikin ininar da ba ta san ta iya ta ba sai a ranar.

Saboda ya kafe ta da ido tamkar wadda ya kama da laifin kisa ko ta yi masa babbar sata.

"Abinci-abinci kika ce me?"

Ya maimaita maganarta cikin sauya murya a sheƙeƙe alamun ya kai maƙura da takaicin ta a
ransa. Tana kallon yatsun hannunta ta mayar masa da amsa fuskarta a haɗe kanta a duƙe ta
ce,

"Abinci ne na dafa, idan za ka ci sai na kawo maka."

"Abinci!"

Ta yi hanzarin É—aga kai a tunaninta ta yi masa gwaninta, amma jin tsawar da ya daka mata da
maganganun da ya baibaye ta da su; ya sa ta yi hanzarin ficewa sum-sum daga É—akin cike da
tsoro bayan rawar da jikinta ya hau yi.

"Ni ne kike zaton zan ci abincinki? Ke mahaukaciyar ina ce da za ki yi tunanin zan iya cin
abin hannunki ma ballantana ƙazamin abincinki?"

Ganin ta bar masa É—akin ya fito falon yana ta balbala mata masifa duk da ta shige É—akinta,
amma bai haƙura ba cikin ɗaga sauti tamkar bai san dare ne ba ya zazzaga mata zafafan
maganganu tamkar ana yi masa wahayin su.

"Idan na sake ganin jemammun ƙafafuwanki a ɗakina sai na saka gitta na sare su gabaɗaya!
Daga yau kada ki sake shiga duk sabgar da ta shafe ni...idan kuma ganganci ya ja ki na illata ki
a banza na ga wanda zai tsaya miki baƙar wawuya bagidajiya! Kuma ki buɗe kunnuwanki da
kyau ki ji ni; matuƙar ba ki sanar da ni inda Nur ta je ba sai na ga bayanki baƙar munafuka mai
raba ƙauna!"

Minal ta rushe da wani irin kukan da ba ta san lokacin da ya suɓuce mata ba. Saboda
kalamansa na ƙarshe sun yi matuƙar gigita mata kwanya. Kuma sun shiga jikinta ta yadda ita
kanta ta shiga tunanin laifin me ta yi wa Nur ta yi mata irin wannan sakayyar, ta gudu bayan ta
É—ora mata jakar tsaba a ka kaji suna aikin caccaka. Tun tana kukan da hawaye har ta koma yin
na zuci tare da ajiyar zuciyar da babu komai a cikin ta sai nadamar zamanta gidan ba tare da ta
tsere kamar yadda Nur ta yi ba.

'Matuƙar ba ki sanar da ni inda Nur ta je ba sai na ga bayanki baƙar munafuka mai raba
ƙauna.'

Maganganunsa sun daki zuciyarta, hakan ya sa suka fara yi mata amsa-kuwwa a cikin
kunnuwa babu ƙaƙƙautawa ta shiga jujjuya kanta tana faɗin,

"Nur ki dawo tun kafin raina ya zamo fansar guduwarki."

Jiki ta ja tana jan É—uwawu ta isa bakin gado ta jingina bayanta tare da É—ora kanta saman
gadon tana haɗiyar zuciya da shesshekar kukanta a hankali. A haka barci ɓarawo ya sace ta
daga zaune tana tunani da ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci har a cikin barcin.

Shi kam sai bayan ya gama sababin da surutan shi kaÉ—ai sannan ya kwanta rigingine yana
kallon sili, zuciyarsa cike da tunanin ta wace hanya zai ci gaba da neman Nur. Zuciyarsa ta
tsayu a kan zai bayar da cigiyar ta gidan rediyo da kuma posting a social media. Ta yadda abin
zai zama viral ya watsu a ko'ina ko za a dace. Da wannan nazarin ya miƙe a lokacin da cikinsa
ya fara ƙugin yunwa. Kitchen ya nufa ya yi tsaye bakin ƙofa yana ƙare masa kallo bayan ya
kunna ƙwan lantarkin da Minal ta kashe a lokacin da suka gama aiki.
Bincike ya dinga yi har ya haɗa kan indomie ya haɗa ta da ƙwai biyu cikin ɗan lokaci ya
dafa. Kasancewar ya iya hannunsa tashin hannun Hajiya ɓangaren abinci abubuwa kaɗan ne
bai iya ba. Duk da gatan da take yi masa hakan bai hana shi koyon wasu ayukan mata ba.
Bayan ya cinye indomin ya tuna da kunun ayar Hajiya, ƙaƙƙarfan tsaki ya ja sannan ya fice
daga ɗakin ya nufi bakin ƙofar shigowa babban falon ya kwashe ledodinsa da ya watsar.

Kasancewar akwai wadatacciyar nefa kuma akwai ƙanƙara a cikin frizer da ke kitchen.
Wadda ya gan ta a ƙanƙare wajen binciken da ya gama yi lungu da saƙo har zuwa store da ke
ƙuryar kitchen ɗin. Sai da ya kwankwatsa ƙanƙarar ya jefa a kunun ayar, wanda ya bulbule a
cikin dogon jug sannan ya faÉ—a wanka. Zuciyarsa babu daÉ—i ya gama wankan ya fito yana
tsane jikinsa yana tsaki cike da takaicin Minal ya sake faÉ—in,

"Wawuyar banza mai ƙaton kai! Duk inda Nur ta je ta sani, kuma gobe idan ba ta sanar da ni
gaskiya ba sai na É—auki mummunan mataki a kanta. Ban san me ta yi mata ba don kawai ta
gudu ita ta aure n....don ubanta ko za ta mutu ba zan yi zaman aure da ita ba tun da ba na son
t...mitsssss!"
Ya ƙare maganar da jan dogon tsaki ya ja jug ɗin kunun a tsaye ya kafa masa baki ya fara
kwankwaÉ—a. GarÉ—i da daÉ—in kunun, haÉ—i da sanyin da ya yi bai san lokacin da ya tayar da jug
É—in ba ya ajiye kofin yana gyatsa. Bakinsa ya goge bayan ya koma toilet ya yi brush ya kwanta
da towel a jikinsa yana haki kamar wanda ya sha gudu.
Da tunanin Nur bacci mai nauyin gaske ya kwashe shi. Kamar almara cikin dare ya fara jin
jijiyarsa tana miƙewa, zumbur ya zabura saboda kakkarwar sanyin sha'awa da ya shiga yi.
Kansa ya dafe yana salati saboda yanayin da yake ji bai taɓa tsintar kansa a makamancinsa ba.
Zarya ya fara yi a cikin falon dafe da kai jijiyarsa a miƙe kamar mai koyon tafiya. Babu shiri ya yi
zaman 'yan bori a tsakiyar ɗakin saboda ya kasa juriyar tsayuwa da ƙafafuwansa da ke
kakkarwa.

"Ya Salam!"

Ya yi ta jerawa a bakinsa yana maimaitawa tamkar wanda aka saka yin hadda. Nan take gumi

ya hau keto masa yana sharewa da hannu har ta kai ya dafe mararsa yana salati. Tsabar
harbawar da jijiyarsa take yi tamkar numfashinsa zai shiÉ—e yake ji. Halin da yake ciki ya saka shi
miƙewa babu shiri ya fara tafiya yana layi ya faɗa ɗakin Minal jikinsa yana tsuma. Ƙafafuwanta
ya jawo da ke shimfiÉ—e a bakin gado, babu shiri ta baje a tsakiyar É—akin tare da farkawa a
haukace cikin wani sabon firgici. Saboda mafarkinsa take yi wai ya zo da wuƙa a kanta yana
faɗar ko ta faɗa masa inda Nur ta ɓoye ko kuma ya kashe ta.

Ihu ta fasa iya ƙarfinta ta buge shi ya faɗi ƙasa dabas tare da sakin towel ɗin da ke ɗaure a
ƙugunsa. Wataƙila halin da yake ciki ya mantar da shi babu komai a jikinsa, a haka ya miƙe jijiya
miƙe ya nufe ta gadan-gadan zai kamo ta. Ta sake ƙwalla ƙara tare da zurawa da gudu ta faɗa
toilet a sukwane, sai dai kafin ta rufe ƙofar suka shiga kokawa a tsakaninsu. Yana ƙoƙarin shiga
ciki yayin da ita kuma take ƙoƙarin tura ƙofar iya ƙarfinta a kan ba zai shiga ba, saboda
kuzarinsa ya rage ya kasa shigar kamar yadda ya so.
Ganin za ta ɓata masa lokaci ya yi baya da nufin banke ƙofar da jikinsa ko da za ta ɓalle in
dai zai samu biyan buƙatarsa. Sai dai yana yin bayan ta datse ƙofar tare da hanzarin saka
makulli ta rufe ruf jikinta yana kyarma tamkar mazari. Don a iya tarihin rayuwarta ba ta taɓa
shiga tashin hankalin da ya kai wannan ba, don ba ta taɓa yin ido da babban mutum babu tufafi
a jikinsa ba, sannan da yunƙurin yi mata fyaɗe ko a mafarki. Hakan ya ƙara ɗaga mata hankali
ta shiga zunduma ihun neman agaji.

Shirun da ta ji tun daga lokacin da ta rufe ƙofar bai nemi buɗewa ta ƙarfi ba; amma hakan bai
sa ta fasa kururuwar da take yi ba. Jamal kam ganin ta yi nasara a kansa ya koma É—akinsa da
sassarfa ya É—auko É—aurin kuÉ—i 'yan dubu-dubu har bandur É—aya sababbi kar ya tsaya bakin
ƙofar toilet ɗin yana magana cikin rawar baki tsabar yadda yake ji a jikinsa.
"Idan har ba za ki bari na yi don Allah ba to ga shi zan...bi.. biya ki...tun da...da ma can ke..ba
kya... tsoron Allahhhhh...."






Cabɗijam!🙆




Na yi kudi🏃
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA IBRAHIM D. AUTA*

*LAMBA TA BAKWAI.*


"Wayyo-wayyo Allahna!"

Abin da ta faɗa kenan daga cikin bayin dafe da kanta ta ƙwalla ƙara iya ƙarfinta. Ido ta shiga
zarewa tana ci gaba ihun da kururuwar faÉ—in ta shiga uku ta lalace a zo a kawo mata É—auki.
Wannan dalilin ya jawo hankalin maigadin gida ya fito a firgice ya isa bakin ƙofar shiga
falonsu yana bubbugawa babu ƙaƙƙautawa yana kiran sunan Jamal. Bayan ya gama zagayen
gidan lungu da saƙo da zungureriyar addarsa, yana ta neman inda zai ci karo da wani baƙon
fuska ko wata alamar da ke nuna an shiga gidan bai sani ba. Don duk hasken da ke gidan bai
hana shi ƙarawa da fitilar hannunsa mai matuƙar haske ba.

Sosai bugun ƙofarsu ya saka Jamal diriricewa, saboda zumbur ya miƙe daga ƙasan da ya
baje dafe da mararsa yana kakkarwa. Amma dole ya miƙe dafe da ƙugunsa yana tafiya kamar
mai tete, a haka ya sauka daga ƙasan benen da towel a ƙugunsa ya buɗe ƙofar. Don bai tsaya
wani jinkiri ba ko ɓata lokacin tambayar wane ne ba. Saboda jin muryar maigadi ya saka shi
shahadar buÉ—ewa babu shiri.

"Baba lafiya?"

Tambayar da ya wurga masa kenan a lokacin da ya gan shi tsaye da addarsa a hannu bayan
fitilar da yake haskawa gefe da gefensa.

"Ranka ya daÉ—e sautin Hajiya da na jiyo tana ihu tsawon lokaci ya sa na ji tsoron kada a ce
wani mummunan abu ne ya faru ban sani b..."

"Babu abin da ya faru je ka kwanta."

Ya yi maganar ransa a haÉ—e cike da jin haushin maigadin. Sumui-sumui ya bar wurin yana
faɗin, "Allah Ya ƙara tsarewa." Saboda fahimtar inda lamarin ya dosa babu wani abu sai
tsabagen rakin amaryar gidan. Duba da yanayin da ya gan shi a birkice sannan da sigar da ya
fito a yadda yake ba tare da ya ji kunyarsa ba. Tsaki kawai Jamal ya ja ya rufe ƙofar a
maimakon ya amsa masa da amin. Ya koma da sassarfa yana yamutsa gashin kansa da
hannun tare da faɗin Ya Salam a cikin bakinsa ta fi a ƙirga.
Ɗakinsa ya nufa tare da kulle ƙofa ya nufi bayi cikin ƙuncin rai ya yi ta sheƙa wa kansa
ruwan sanyi, sai da ya ji rabin nutsuwarsa ta shiga jikinsa hankalinsa ya dawo, sannan ya fito
kansa yana muguwar sarawa ya kife a kan gado. Ajiyar zuciya ya shiga saki É—aya bayan É—aya
yana nishi dafe da jijiyarsa da ke harbawa har komai ya lafa masa barci ya yi awon gaba da shi.
Asubar farin ya farka ya yi wanka da arwala ya fice masallacin da ke kusa da gidansa.
Zuciyarsa cike da tunanin irin hukuncin da ya dace ya yanke wa Minal idan safiya ta waye. A
gefe É—aya kuma cike yake da jin haushin kansa, har aka gama sallar ya dawo gida bai daina

tunanin dalilin da ya jawo masa shiga halin da ya tsinci kansa ba. Saboda tun a daren farkon
auren da Nur ta karya masa zuciya bai sake saka wa kansa zai iya shiga irin wannan yanayin a
kurkusa ba. Domin ya ci alwashin har Minal ta gama zaman banzarta ta bar masa gidansa ba
zai yi mata kallon mace ba. Amma sai ga shi ya kwafsa tun ba a je ko'ina ba.
Minal kam kwanan toilet ta yi idanuwanta sun yi jajir kamar gautan kaji tsabar barcin da ke idon
da kukan da ta sha tamkar hawayenta zai tsiyaye. A daddafe ta fito daga bayin a daidai lokacin
da ta ji ana kiran sallar asuba. Wayar Gwaggo salame ta shiga kira ana ce mata a kashe take,
amma hakan bai hana ta tura mata saƙon taimakon gaggawa ba, da zummar tana buɗe wayar
idan ta gani ta kawo mata É—auki, idan kuma zakara ya ba ta sa'a ta aiwatar da nufinta kuma shi
kenan. Saboda ta gama tsorata da lamarin Jamal don ta yi amanna da shaye-shaye yake yi. Shi
ya sa da ya bugu a daren jiyan ya so juye mata mayen giyar a saman kanta. Bayan ya gama
cewa idan aka cire shigar matan da ke jikinta babu wani bambanci tsakaninta da namiji
É—an'uwansa.

'Gwaggo ki zo da 'yansanda Jamal ya sha giya yana ƙoƙarin kashe ni.'

Saƙon da ta tura mata kenan jikinta yana rawa tsabar ta gama tsurewa da lamarinsa
gabaɗaya. Kamar ɓarauniya ta fito daga ɗakin cikin sanɗa ta sauka ƙasa da dabara gudun ya
jiyo takunta ya sake ya lalata ƙudurin da ta kwana da shi a cikin zuciyarta.

Turus Jamal ya yi a lokacin da ya zo shiga gidan ya ji ƙofar a ƙargame. Kiran sunan
maigadin ya yi cikin sauri ya buÉ—e masa yana faÉ—in,

"A yafe ni ranka ya daÉ—e, Hajiya ce ta so tserewa na hana ta fita."

Hango Minal ya yi a tsaye riƙe da ƙugu tana kumbura fuska, bai bi ta kan maigadin ba face
kallon sama da ƙasan da ya yi mata ya watsar, sannan ya wuce zuwa cikin gidan ba tare da ya
ce da su komai ba. Hakan ya saka maigadin ya sake rufe gidan da kwaÉ—o ya zare makulli
saboda ya gama fahimtar yajin amare ne take shirin dakawa. A ransa ya jinjina lamarin, tare da
yin dariyar ashe akwai sauran mutan da masu gudun miji har zamanin da ake ciki a yanzu na
buÉ—ewar ido.

"Ki yi haƙuri ki koma daga ciki Hajiya, ni ma zan je na yi sallah na ɗan matse barcin idona.
Sannan ki bai wa maigidan haƙuri don alamunsa ya nuna bai ji daɗin ganin ki a nan ba."

Harara ta wurga masa a ƙufule duk da girmansa ta juya zuwa cikin gidan ranta a matuƙar
ɓace, saboda ta so tafiya ya hana ta kuma ta so Jamal ya kula ta ta yi masa tijara. Kamar yadda
ta so barin gidan ba tare da kowa ya sani ba. Aka yi rashin dace tun daga lokacin da ta fito cikin
gidan a kan idon maigadin. Don yanayin ta kaÉ—ai ya sa ya gano babu lafiya ya dakatar da
arwalar da yake yi. Musamman ganin abin da take ƙoƙarin aikatawa, kafin ta ƙarasa jikin ƙofar
ya kulle gidan da ƙaton kwaɗo cikin sauri. Duk yadda ta so ya buɗe ta fita cikin magiya; amma
kukan da ta yi masa bai saka shi tausaya mata ya buÉ—en ba. Saboda ya san kan aikinsa kuma

ya tuno lokacin da ta so barin gidan a karon farko ta ci karo da gwaggo Salame ta taka mata
birki.

Idonta a rufe ta fara ƙwanƙwasa masa ƙofa tsabar ta zo wuya tana son a yi komai a ƙare ta
kama gabanta. Jamal da ke bayi ya fito ransa a ɓace saboda ya san ba kowa ba ce face ita.
Kiciniyar buɗe ƙofar da ta ji yana yi ƙirjinta ya hau bugawa ta yi hanzarin ja da baya riƙe da ƙugu
tana girgizar jiki alamun ta shirya a yi komai. Saboda ta yi wa kanta alƙawarin barin gidan ta
halin tsiya ko arziƙi, sai dai duk abin da zai faru ya faru amma sai bar gidan ta kowace hanya
duk da tsinuwar Innarmu da ke cikin sharuÉ—an fitar tata.

"Ke wace irin daƙiƙiya ce?"

Ya yi magana cikin wata kalar murya mai ɗauke da ɓacin rai. Minal ta yi masa wani kallo
sheƙeƙe sannan ta kawar da fuskarta a gefe tana cewa, "Ka ce da maigadinka ya buɗe mini
ƙofa zan je gidanmu."

"Ni na ce da shi kada

5 / 26