Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
ya bar ki ki tafi gidan naku ne?"
Ya wurgo mata maganar yana zuba mata idanuwansa da suka yi mugun nauyi tsabar barcin
da yake ji. "To ai ya hana ni fita, kuma ni gida nake so na je.."
Ta ƙare maganar tana wurga masa wani kallo da murguɗa baki, hakan ya sake ƙufular da shi
karaf ya rufe ɗakinsa bayan ya buga mata tsaki, saboda ganin tana ɓata masa lokaci a banza.
Ɗakin ta sake bugawa tana faɗin, "Ni fa wallahi ba zan zauna a cikin gidan da ake barazana
ga rayuwata ba."
Banza ya yi mata duk da ya ji abin da ta faɗa, amma yawan bugun ƙofar da take yi tsawon
lokaci ya saka shi buɗewa gadan-gadan ya yi kanta. Maimakon ta gudu kamar yadda zuciyarta
ke ba ta shawara; sai ta kafe tana aika masa harara har ya ƙaraso ya cakumo kwalar hijabinta.
Ya ɗaga hannu da nufin faffalla mata maruka wata zuciyar ta yi gaggawar hana shi, tare da ba
shi umarnin ya ladaftar da ita ta hanyar za ta fi jin tsoron sa.
"Sai na nuna miki na fi ki zama riƙaƙƙen mara kunya...oya nil dawn!"
Ya yi magana cikin ɗaga muryar da tsoro ya saka ta kai gwiwowinta biyu a ƙasa babu shiri.
Jikinta yana tsuma ta shiga zubar da hawaye tare da haɗa hannu wuri ɗaya tana faɗin,
"Don Allah.. don darajar Manzon Allah..don albarkacin..."
"Yi mini shiru!"
Ta yi saurin haɗiye maganar bakinta jikinta yana kyarma ƙirjinta yana bugawa ta ƙura wa
gefenta ido.
"Ɗaga hannunwanki sama ki rufe idanuwanki. Kuma idan kika yi gangancin tashi dukan da zan
yi miki a yau sai na cire miki haƙorin gaba. Kada ki ga abin da ya faru jiya ki yi tsammanin ko da
son raina na aikata ki nemi raina ni...to ni ma ban san wace kalar ƙwaya na sha jiyan ba har ta
fitar da ni cikin hankalina."
'Da ma sai ƙwayar. Ashe da gaske shaye-shayen yake yi.'
Zancen zucinta kenan cike da alhini a lokacin da ya yi hanzarin komawa ɗaki saboda kiran
wayarsa da ake ta yi, cike da mamaki ya rarumi wayar yana tsaki ya danna kore ganin sunan
Gwaggo salame a kan fuskar wayar.
"Me ke faruwa ne tsakaninka da Amina?"
Jamal ya yi jim kamar ba zai bayar da amsa ba, sai da ta sake maimaita tambayar sannan ya
fesar da iska mai zafi daga bakinsa ya ce,
"Babu abin da ya faru, gida take son zuwa maigadi ya hana ta."
Ajiyar zuciya Gwaggon ta saki sannan ta ce, "Don Allah ka ƙara haƙuri da ita, saboda tana
buƙatar a tausaya mata ko don ta rage firgicin da take ciki."
"Babu damuwa."
Iya abin da ya faɗa kenan ya ajiye wayar, saboda ya gaji da magana kansa ya yi nauyi kuma
yana yi masa ciwo sosai. Amin kawai ya faɗa a can ciki a lokacin da ta gama yi musu addu'ar
zaman lafiya da haƙuri da juna.
Nannauyan barci ya ɗebe shi mai ɗauke da mafarkai barkatai har ƙarfe tara na safiya bai farka
ba. Caraf tunaninsa ya kamo masa Minal da ya bari a cikin falo tana karɓar horo, cikin sauri ya
faɗa toilet bai jima ba ya fito yana haɗe rai kamar wanda ya yi arba da kashi. Ganin ta a inda ya
bar ta baje ƙasa tana barci; cikin zafin rai ya kai mata harbi da ƙafa har sau biyu. Ta zabura tana
wara jajayen idanuwanta da ke cike da bacci tamkar wadda ta bugu da maye.
"Wa ya ba ki damar yin barci?" Ya jefa mata tambayar a fusace.
"Allah ne."
Ta ba shi amsa a taƙaice saboda tsoron sa bai hana ta mayar masa da raddi ba. Baki ya buɗe
cike da mamakinta ya shiga nuna kansa ya sake cewa,
"Ni za ki yi wa rashin kunya?"
"Faɗar Allah shi ne rashin kunya kuma?" Ita ma ta amsa cike da jarumta.
Ya yi kamar zai kai mata mangari ta yi baya cikin zafin nama ya fisgo gefen hijabinta, babu shiri
ta fasa ƙara jikinta yana rawa ta fara ba shi haƙuri tare da rantsuwar ita ma ba ta san barcin ya
kwashe ta ba. Tsaki kawai ya buga ya nufi kitchen bai ce da ita komai ba, mintuna a tsakani
ƙamshin girkinsa ya fara cikawa Minal hanci. Sai a lokacin ta tuna ashe fa ita ma tana jin
yunwa, musamman da ya kammala ya fito da tiren ya ajiye a kan dinning table yana faɗin wash
Allah.
A gabanta ya yi karin safiya ƙamshi yana dukan ta tana rakuɓe gefen kujerar da yake kai da
tagumi, har ya cinye komai tas ya miƙe yana gyatsa zai shige ɗakinsa ta ce,
"Zan iya tashi?"
Ta yi maganar jiri yana ɗibar ta, tsabar yunwa da baccin da ke cikin idanuwanta. Don ƙarfe
goma na safiya har ta haura.
Mugun tsaki ya ja sannan ya shige yana miƙa, jim kaɗan ya fito daga ɗakin fuskarsa a haɗe ya
kai dubansa ga ƙofar ɗakinta ganin babu kowa a cikin falon ta tafiyarta. Murmushin mugunta ya
yi sannan ya nufi ɗakin nata da niyyar ya sake tunzura ta da gangan.
"Ke!"
Abin da ya faɗa kenan cikin kakkausar murya a lokacin da ya hango ta bakin gado tana bacci.
Zabura ta yi tare da tashi zaune tana murtsuka ido saboda dishi-dishi take ganin sa.
"Tashi ki wanke mini motata, sauri nake yi fita zan yi yanzun nan! Sannan ki tabbatar kin share
mana harabar gidan kaf kafin na dawo."
D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
*Follow the D. AUTA NOVELS channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029Vb2zCo5JUM2bDSfRzW01*
*Na buɗe channel fatar za ku dinga leƙawa akwai wasu littafaina da zan saki ta can.*
*LAMBA TA TAKWAS.*
Babu shiri ta ƙara ware idanuwanta a kansa sannan cikin wata kalar muryar jin bacci ta ce
masa,
"Ni ce zan yi maka wankin motar?"
"Ke..ke..fa...ga ki nan! Ko kin fi ƙarfin ki yi wankin mota ne?"
Ya ba ta amsar a harzuƙe tare da nufo inda take cikin zafin nama, da niyyar ya cakumo wuyan
hijabinta ya koya mata hankali. A tsorace ta ƙura masa kallo ƙirjinta yana bugawa, ganin ya
nufo ta da gaske fuska babu annuri ta zabura daga kan gadon, jikinta yana rawa ta yi bakin
toilet tana faɗin,
"Ai ba cewa na yi ba zan yi ba...kuma ban san ma yadda ake yi ba n..."
"Mu je zan nuna miki tun da kin saba aikin wahala a gidanku ai wankin mota ƙaramin aiki ne a
wurin ki."
Ya yi maganar yana bin bayanta don ta riga shi fita daga ɗakin tsabar firgicin da ya saka ta,
tana zumɓura baki zuciyarta cike da takaicin rainin da yake yi mata kamar wata sokuwa ta kasa
bijirewa. Tare suka fito harabar gidan inda ta ja ta tsaya wuri ɗaya, yayin da shi kuma ya nufi
ma'ajiyar kayan wankin motar kai-tsaye. Bokiti ya kawo har inda take tsaye rungume da
hannuwa a ƙirji tana harare-hararen gefe da gefenta. Sannan ya gyara tsayuwarsa a gabanta
tare da riƙe ƙugu yana faɗin,
"Minti uku na ba ki ki yi sauri ki kammala komai kafin na shirya na fito. Kuma ki tabbatar kin
gama ba na buƙatar ɓata lokac..."
Ganin ta a tsaye babu alamun za ta yi aikin da gaske ya sake harzuƙa cikin ɗaga murya ya ce,
"Malama tsayuwar me kike yi a wurin da ba za ki wuce ki fara aikin da na saka ki ba?"
Wani mugun kallo ta yi masa ranta a matuƙar ɓace sannan ta ja bokitin ta nufi bakin famfo
cikin sauri, tamkar za ta tashi sama tsabar ƙufula da ƙudurin ta yi saurin gamawa ta ƙaddamar
da abin da zuciya ta kitsa mata.
Bayanta ya bi da kallo fuskarsa a cure har ta isa bakin famfon har ta tara bokitin ruwan ya
fara zuba. Sannan ya bar wurin da sassarfa ya koma cikin gida, zuciyarsa cike da alwashin
wahalar da ita har sai ta nemi saki da kaifin ƙafafuwanta idan ta gaji da zaman. A gurguje ya
faɗa toilet ya yi wanka, cikin minti goma sha biyar ya fito angonsa shar duk da babu cikakken
angwancin a zahiri. Domin ya yi kyau a cikin tsadadden farin yadin da ya saka tare da ɗora wa
kansa hular da ta ƙara fito da haibarsa a fili, kuma ɗinkin ma ya karɓi jikinsa sosai. Sai tashin
ƙamshi yake yi kansa a duƙe yana gyara zaman agogon da ke hannunsa ya iso wurin. Minal
kuwa kamar wadda aka kira takunsa ya sa ta yi hanzarin kai kallonta gare shi. Ƙirjinta ya buga
dam-dam a bisa tsautsayi ta rusa masa tsari. Domin garin kallon sa ta danna tiyon ruwan ya
fantsama a kan fuskarsa zuwa ƙirjinsa har ya bi tafin ƙafarsa ya malala ƙasa. A ƙoƙarinta na son
wanke kumfan da ke saman motar ta wanke masa jiki.
"Ya Salam!"
Abin da ya furta kenan a lokacin da ruwan ya sauka jikinsa, tare da yin wani tsallen da ya saka
shi jan gefe babu shiri ya hau buge ruwan da hannunsa. Rigar ya riƙo ransa a ɓace don ta
gama yin sharkaf da ruwan, cike da mamakin abin da ta yi masa ya dinga kallon jikinsa yana
ƙare mata kallo. A cikin zafin zuciya ya ya danna wata muguwar ashar, saboda ba ƙaramin ɓata
masa rai ta yi ba, hakan ya saka shi nuna ta da makullin motar da ke hannunsa yana faɗin,
"Na gaji da yawan surutun da kike saka ni...don na fahimci so kike yi ki zamo mini wani sabon
ciwon kai bayan wanda ke cikin kain..."
"Ka yi haƙuri wallahi ba gangan na yi b..."
Ta yi maganar cikin saurin baki jikinta yana rawa saboda ita kanta ta sani tabbas ba ta kyauta
masa ba. Katse ta ya yi da faɗin,
"Yi mini shiru shashasha! Ke har abada ba za ki taɓa wayewa ba! Komai naki a hargitse babu
wani tsari ƙauyanci ya yi miki yawa a zuciya."
Zancensa ya datse sauran maganar da ke bakinta, kanta a ƙasa tana sauraron yadda yake
magana cikin ɗaga murya tamkar ya rufe ta da mahaukacin duka.
"A yi mata haƙuri maigida."
Maigadi ya yi magana saboda gudun shaiɗan ya tunzura shi abin ya zamo babban abu. Don
duk abin da ke faruwa a gaban idonsa ne, tun fitowarsu har badaƙalar da suke yi bai ɗauke
ganinsa ba. Farko ya kalli abin a salon soyayya, amma faɗan da ya ga Jamal yana yi ya saka
shi jin tsoro, gudun ɓacin rai ya saka shi aiwatar da abin da bai dace ba. Bai ce wa maigadin
komai ba ya juya zuwa cikin gidan, da nufin sauya wasu kayan amma bai fasa tsine wa rashin
hankalinta ba.
"Allah ma ya sani ni ban yi da niyya ba."
Zancen Minal kenan a a lokacin da ta saki tiyon ruwan yana zuba ƙasa tsabar takaici. Ƙugu ta
riƙe tana girgizar jiki tare da kallon gefe saboda haushin maganganun da ya faɗa mata a gaban
maigadin sun tsaya mata a zuciya. Hakan ya saka Jamal jan birki ya tsaya cak a inda yake,
kafin ya waigo cikin fushi ya sake nuna ta da hannu fuskarsa a yamutse ya ce,
"Ki shiga taitayinki!"
Hararar gefen ido ta yi masa ba tare da ta ce komai ba ta ƙura wa wuri ɗaya kallo, har ya gama
tsayuwarsa ya dunƙule hannu ya kai wa iska naushi ba ta sake kallon sa ba.
"A yafe mata maigida ba za ta sake b.."
"Ka tsaya iya aikika!"
Jamal ya ƙare maganar tare da nuna shi da hannu, cikin sauri ya bar wurin amma bakin
maigadin bai yi shiru ba sai da ya sake cewa, "Allah dai Ya huci zuciyarka maigida." Ya nufi
mazauninsa da ke bakin ɗakinsa yana zancen zucinsa cike da jin haushin kansa a kan shiga
harkarsu.
'Ba zan sake shiga tsakaninku ba tun da bayar da haƙurin ma laifi ne. Aure sai ka ce wasar
yara daga matar gidan har maigidan kowa da kalar matsalarsa. Um..ku kuka sani dai ni ɗan
kallo ne." Daga haka ya kama sabgoginsa.
Minal kam bayan Jamal ta bi da kallo har ya shige ba ta ɗauke idanuwanta a kansa ba.
Zuciyarta cike da jin haushin kanta a kan me ma ya sa ta kalle shi har ta ɓata masa jiki. Jikinta
ya yi sanyi ƙalau duk da ba ta daina jin haushin maganganun da ya yaɓa mata ba. Kamar an
dasa ta a wurin tsawon minti biyar zuwa shida ba ta motsa ba. Har Jamal ya fito cikin wata
sabuwar shigar yana baza ƙamshi, tare da tsuke fuska tamkar bai taɓa dariya ba. Ta gefen ido
ta kai kallonta gare shi ƙirjinta yana bugawa amma hakan bai hana ta magana daga ita sai ranta
ba.
'Ka gode mini a yanzu har ka fi kyau m...'
A daidai lokacin ya buga wani ƙaƙƙarfan tsakin da ya saka bugun zuciyarta ƙaruwa. Saboda
hango ruwa a jikin motar ya nuna ba ta goge masa ba bayan ta gama wankewar. Cikin sauri ya
fito da wani towel a boot ya shiga goge motar a ransa yana faɗin,
'Wawuyar banza ita komai sai an ce ta yi sannan take yi.'
Ya faɗa motar bayan ya gama gogewa ta ya shiga ba ta wuta, maigadi ya yi hanzarin buɗe
masa gate tun kafin ya umarce shi. Saboda ya ci burin tsayuwa iya aikinsa ba zai sake shiga
sabgar da ke tsakaninsu ba. Minal kuwa kafewa ta yi a inda take duk ƙugin da motar ke yi ba ta
sa ta matsa ba. Ganin ba ta da alamun ba shi hanya ya wuce kamar yadda yake so, yana
ƙoƙarin yin kwana ya leƙo kansa cikin fushi ya ce,
"Ke wace kalar mahaukaciya ce da ba za ki janye ba sai na yi magana...zan kakkarya
shamulallun ƙafafuwanki a banza wawuya kawai...mitsssss..."
Ya ƙare maganar da tsaki a lokacin da ta ɗaga masa hanya ya nufi bakin gate yana ci gaba da
faɗar duk abin da ya zo bakinsa. Magana ya yi da maigadin ƙasa-ƙasa sannan ya fice gidan.
Allah Ya tsare ya shiga yi masa yana ɗaga hannu har ya wuce, amma kafin ya rufe babbar ƙofar
Minal ta ƙaraso wurin ita ma. Wuff ta yi da nufin faɗawa waje ta fice ta ƙaramar ƙofar gidan, don
ta gama haɗa komatsan tunaninta a wuri ɗaya, a kan yanke iyakar zama da Jamal har abada
don ya gama ci mata zarafi a banza.
"Ki yi haƙuri Hajiya, maigida ya ce kada na bar kowa ya fita a cikin gidan nan, yau babu shiga
babu fita."
Wani kallo ta yi masa sannan ta yi magana a ƙufule tana cewa, "Shi maigidan da ya fita me ya
sa ba ka hana shi ba sai ni da ka raina?"
Yana kulle ƙaramar ƙofar gidan bayan ya sha gabanta ta koma ciki ya ce, "Umarni ne daga shi,
kuma aikina nake yi Hajiya. Amma ko yanzu ya kira ni ya ba ni damar barin ki fita an gama
zance."
Ta jima a wurin tsaye zuciyarta sai ingiza ta take yi a kan ta yi masa rashin kunya ko zai bar ta.
Yayin da wata zuciyar ke ba ta shawarar ta zagaya ta bayan gidan ta haura katanga. Kafin ta yi
ƙwafa ta bar wurin tana cika tamkar wata kububuwa. A haka ta koma cikin gidan ranta a ɓace ta
faɗa ɗakinta tana kuka wiwi. Bayan ta rage ƙuncin zuciyarta ta nemi wayarta kaf ɗakin ta rasa,
bayan kuma ta san a kan gadon ta bar ta.
Idanuwanta suka kai kan agogon ɗakin babu shiri ta zaro ido, ganin lokacin ya yi gudu da
yawa ga kuma ƙugin yunwa da hanjinta suke yi. Don ƙarfe sha biyu na rana har ta wuce, waton
ƙarfe ɗaya saura kaɗan ake harare. Kitchen ta nufa faka-faka da niyyar neman abin da za ta ci,
jiri yana kwasar ta tsabar yunwa da bacci sun gama ladaftar da ita jikinta. A gurguje ta yi wanka
ta yi sallah sai zuba hamma take yi wata bayan wata, sannan ta baje tana wani irin mugun barci
mai ɗauke da kalolin minshari.
***
Sadam kuwa daga gidansa wurin Hajiya Mummy ya nufa. Saboda nazarinsa ya gama ba shi
akwai abin da Hajiyar ta saka masa a cikin kunun ayar da ta ba shi. Kamar yadda ta dinga ɗirka
masa maganin ƙarfin maza da sunan na sauƙin zuciya.
Bayan sun gaisa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya amayar da abin da ke cikin bakinsa
kai-tsaye. Inda ya sanar da ita bai ji daɗin abin da ta yi ba. Don bai shirya zaman aure da Amina
ba, sannan ya ƙara da