Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   10 / 26

27K to 30K   out of 77.3K words

lokacin da yunwar dare ta hana ta sukuni, sannan ta runtsa.

Motsinsa a falo da sautin Tv da ta ji hakan ya sa ta gano ba zai fita da wuri ba. Cikin sauri ta
gama shirinta kamar yadda ta saba kowace safiya, tana tashin ƙamshi ta fito da niyyar yi masa
ina kwana. Saboda ta ƙi bin umarnin wani sashen zuciyarta da ke gargaɗinta a kan kada ta je.

Kanta tsaye ta nufi inda yake zaune yana kallo, ƙamshin girkin da yake yi yana dukan
hancinta. Nan take wata sabuwar yunwa ta taso mata, tsayawa ta yi ɗan nesa da shi tana cewa,

"Ina kwana?"

Kamar ba zai ce komai ba tsawon sakonni, sannan ya cira kansa yana ƙare mata kallo sama da
ƙasa ya watsar yana cewa,

"Ke kam har zuwa yaushe za ki waye ne? Mace haka a tsaye babu wata lanƙwasa. Ko ke a
naku gidan kalar gaisuwar taku kenan?"

"Gaisuwar da ta dace da kai dai!"

Ta amsa masa kai-tsaye tana ƙoƙarin barin wurin ba tare da wani jinkiri ba. Kansa ya shiga
ɗagawa yana jinjinawa sannan ya sake cewa,

"Ehhhh...kuma fa kin yi gaskiya. Da irin wannan gaisuwar na dace a wurin mata irin ki,
waɗanda har duniya ta tashi ba za su taɓa wayewa b...kaico!"

Sharrr hawaye ya fara bin fuskarta cikin hanzari ta shiga gogewa da bayan hannunta cikin
muryar kuka ta ce, "Ban waye ba, kuma ba zan taɓa wayewa ba. A bar ni a yadda nake ai ba
jinda na yi aka ba ka sadakata ba. Da rashin wayewar aka gano ni ce wadda na fi dacewa da
zama da kai. Kuma a haka za ka zauna da bagidajiya kuna jera kafaɗa a wuri ɗaya."
Wata mahaukaciyar dariya ce ta suɓuce masa babu shiri, kafin ya shiga nuna ta da hannu yana
ƙumshe bakinsa alamun yi wa dariyar tasa waigi. Haushi ya sa ta bar wurin da gudu tana kuka,
tsabar takaicin ganin ya gama raina ta, kuma ba ta san me za ta yi masa ya yaba ba.
Jamal kam tsaf ya gama girkin ya cinye kayansa a cikin falon, da remote a hannunsa yana
canza channel zuciyarsa wasai kamar ba ya jin tashin kukanta. Saboda ƙoƙarin ƙarfafa kansa
da yake yi gudun faɗawa tarkon da aka yi masa a kanta.

'Mu je zuwa, don har yanzu ban gama yarda da ke ba, ba a banza kike son zama da ni ba. Ke
ko ma mene ne zan gano abin da kike ɓoyewa kafin wanzuwar ƙudurinki a kaina.'

Da wannan nazarín ya datse ƙofar tausayin ta a ransa. A gurguje ya yi wanka cikin shiga ta
manyan kaya, har ya nufi hanyar fita ya dawo ya shiga ƙwanƙwasa mata ƙofa. Banza ta yi masa
kamar ba ta san yana yi ba, sai da ya gaji don kansa ya murɗa hannun ƙofar ya shiga kansa
tsaye yana ce wa,
"Hajiya ki fito mu je ke nake jira."

Ba ta motsa ba, hakan kuma bai sa ya sake maimaita maganar ba ya fice tare da ja mata ƙofar.
Da sassarfa ya sauka ƙasa yana waya, fuskarsa a sake yake cewa,

"Ki zama cikin shiri da na sauke wata zan zo na ɗauke ki..ok ..bye."

Daga haka ya mayar da wayar aljihunsa cike da farinciki. Fuskarsa a sake suka gaisa da
maigadi sannan ya nufi motarsa a ransa yana faɗin,

'Yau kam mota ba ta samu gatan jiya ba.'

Ya yi wani kalar murmushi ya faɗa motar cikin karsashi ya shiga ba ta wuta yana horn wani
bayan wani. Saboda ya matsu Minal ta yi saurin fitowa ya yi abin da yake hangen shi ne babbar
makamarsa. Ita kam jikinta yana rawa ta danna wa Innarmu kira bayan fitarsa. Saboda tsoro da
fargaban da take ciki a Kan tafiyar da yake so ta yi, kada Innarmu ta ce don ba ta son zaman ne
ta yi abin da zai kawo ƙarshen aurensu da gayya. Bayan har zucinta ta ci burin zama da shi a
bisa wasu ƙwararan dalilanta da take ganin su ne makaman da za ta yi yaƙin ƙwato 'yancinta.

Aka yi sa'a kira ɗaya tana kusa ta ɗaga, saɓanin wasu lokutan da Innarmu take jefar da wayar
ta yi ta sabgoginta, ko idan tana hannun ƙannenta suna buga game su saka ta flight mood don
kada ma wani ya kira a kan uzurinsa ya katse musu game.

"Innarmu kada ki ga laifina ya ce zai kawo ni gida a yi komai a gabank..."

"Me za a yi gabanm...? Ke ki fita idona na rufe Amina! Shin Salame ba ta ce miki ki san
dabarun da za ki jawo hankalinsa ba ne?"

"Mun yi maganar."

Amina ta amsa fuskarta a cure, saboda horn ɗin Jamal da maganganunta sun ƙara dagula mata
zuciya. Musamman da Innarmu ta ce,

"To ki ce masa kin amince za ki zauna ba sai kun zo gidan b.. "

"Na faɗa masa fa wallahi...kin ma ji shi can yana ta horn Innarmu ni kawai yake jira na fito mu
z..."

"To ku zo ga ni ina jiran ku daga ke har shi ɗin...wallahi muddin auren nan ya mutu kada ki yi
tsammanin Zan sake zama da ke a gabana! Mutuncinki ɗaya shi ne ki san yadda za ki yi da shi
ki lallaɓa a bar batun nan kawai. Idan ba don ya gaji da halinki ba wane zaɓin zama ko rashinsa
zai ba ki...to ki bari auren ya mutu ki dawo gidan ki ga yadda zan yi da ke."
Ƙit ta kashe wayar, jiki babu kuzari Minal ta miƙe ranta yana ƙuna ta jawo jaka ta fara loda
kayanta cikin fushi. Bayan jarumtar da ta ara ta yafa wa jikinta ta shiga jan jakar iya ƙarfinta har
zuwa harabar gidan. A jigace ta isa bakin motarsa ta tsaya tana nishi fuskarta a cure. Ganin ta
da jakar kayan ƙirjinsa ya buga dam-dam, saboda tuno kalaman Hajiya kai-tsaye suna shiga
cikin kunnuwansa tamkar a lokacin take furta su.

'Ba za ka san darajar Amina ba sai ranar da ka yi gangancin rabuwa da ita. Kuma daga
lokacin haukar da ke cikin kanka za ta sake ka ka gano ka cuci kanka.'

"Ya Salam! Hajiya me ya sa kike ƙoƙarin Yi mini baƙin baki koyaushe?"

Zancen da ya yi kenan dafe da kansa cike da takaici, tsaki ya buga mai ƙarfi sannan ya buɗe
murfin motar ya fito ya fisgi jakar da ke gabanta ya wurga bayan boot cikin fushi, sannan ya
zagaya yana faɗin,

"Malama ki shigo mu je kin ɓata mini lokaci."

Minal ta buɗe bayan motar za ta zauna ya yi hanzarin faɗin, "Ba ki isa na zamo direbanki ba!
Idan har ba za ki zauna gaban ba ki fita na ba ki kudin adaidaita sahu mu haɗu can. Ƙauyanci
kawai ke a komai sai an ci gyaranki..mitsss."

Wani kallo ta yi masa na tsawon sakonni ba tare da ta ce komai ba, ta buɗe gaban ta shiga ta
zauna cikin tsuke fuska. Sannan ta koma danne kukan da yake ƙoƙarin bayar da ita a gabansa.
Don ta ci alwashin daina kuka a gabansa duk tsananin ƙuncin da ke ranta kuwa.
A haka suka fice gidan, yayin da suka bar maigadi da tunanin rabuwa auren ne ya yi ko wata
tafiya ce za su yi su dawo. Kowanensu fuska a cure har suka ci rabin tafiyar, kasanacewar
akwai tazara a tsakanin Nasarawa da Jogana. Amma har suka isa babu wanda ya ce da wani
uffan illa wayar da Jamal yake ta karɓawa lokaci bayan lokaci.
Dam-dam ƙirjin Minal ya shiga bugawa a lokacin da motar ta tsaya bakin lugun gidansu. Tana
ƙoƙarin buɗewa ta fice ya yi hanzarin riƙo hannunta yana cewa,

"Ko da wasa kada ki nuna akwai wata matsala a tsakanina da ke, idan ma kin faɗa ni ban san
komai ba kuma babu ni a cikin masu shaidu. Yanzu gaishe su muka zo yi zuwa daré zan dawo
na ɗauke ki mu koma gida, tun da kin amince za ki iya zama da ni a kowane hali."

'Innalillahi! Wai wannan wane irin mutum ne shi?'

'Ni mutum ne kamar sauran mutane aminiyar matata. Kuma na san darajar mahaifiyata kamar
yadda kike ƙoƙarin yi wa taki biyayya."

Ya ba ta amsa kai-tsaye tamkar ya shiga zuciyarta ya ji abin da take faɗa. Sai dai kallon da take
yi masa ya nuna zahirin ƙullewar kan da maganganunsa suka yi mata. Hannunta da ya riƙe gam
ta kalla, inda ta yi maganar ido a kan ya taimaka ya sake ta.

"Babu abin da zan ji ko da na kwana da ke a jikina ballantana riƙe hannu. Don haka ki je ki
sanar da su zan shigo mu gaisa sauri nake yi akwai abin da zan yi."

Sororo Minal ta yi ta kasa motsawa, tsabar ya gama kai ta maƙura ta yadda ba za ta iya
fassara manufar abin da yake nufi da ƙoƙarin aikatawa ba. Tana yunƙurin fita ƙannenta da yaran
unguwar, suka baibaye da motar. Yayin da wasu suka biyo su tun shigowarsu cikin layin har
suka tsaya bakin gidan. Tsalle suka fari yi suna ihu saboda ganin Minal tare da faɗin sunanta

suna yi mata oyoyo.

Tsaki mai ƙarfi Jamal ya ja a daidai lokacin da ya hango yaran sun yi wa motarsa dafifi, har da
masu shafa jikin motar suna leƙen sa. Kasanacewar tintac ya sa ba su gano ita ce cikin motar
ba har sai da ta fito suka gan ta. Da murmushin yaƙe ta tarbi yaran tare da kiran sunayensu
tana amsa gaisuwar da suke yi mata ɗaya bayan ɗaya. A haka ta shige gidan suka bi bayanta
ɗiii har da masu tirereniyar shan gabanta da niyyar su riga ta shigewa.

Innarmu riƙe da buta a hannu tun lokacin da ta ji ihun yaran suna oyoyo, tare da kiran sunan
Aminar. A gurguje ta fito bayin kuma ta kasa ajiye butar har ta yi ido biyu da Amina. Saboda
dukan da ƙirjinta yake yi tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki tun bayan wayarta da
Amina. Hakan ya jawo cikinta ya dinga murɗawa tana faɗa bayi cikin gaggawa a duk lokacin da
ta tuna suna kan hanyar zuwa gidan. Saboda ba ta san da wace Jamal ɗin ya zo ba.
Sai dai kallo ɗaya da ta yi wa Amina ta ji sanyi ya ratsa zuciyarta. Ganin sauyin da ta yi a
cikin 'yan kwanaki, fatarta ta sauya saboda zama wuri ɗaya, kuma alamun hutu da jin daɗi ya
fara kama jikinta. Amma ko kaɗan ramar da ta ga ta yi ba ta tayar mata da hankali ba, ta ɗora
hakan a kan fitinarta ce da rashin danganar da ta ɗora wa kanta.
"Innarmu ina Babanmu?"

Maganar da Minal ta tare ta da ita kenan, wadda ta dawo da ita daga duniyar nazarín da ta
afka.

"Ke ma kin sani a daidai wannan lokacin ba za a tarar da shi a gida b..."

"To, ki saka hijabinki ya ce a faɗa zai shigo."



SANARWAR!
INA NEMAN MUTUM 20 MASU SAYEN lLITTAFIN DAKAN ƊAKA.. COMPLETE BOOK 1-2
PRIZE 1K GA MAI BUƘATA YA TAƁA NI TA NAN; 08022014771 ZAN SAKE SHI A RANAR 3
GA WATAN FEBRUARY.




D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

Follow this link to join my WhatsApp community:
https://chat.whatsapp.com/I6nbHRDfqd05VKHdFpnfeB

*Assalamu alaikum*
*Na ce kuna neman inda za ku saya wa yaranku da kuma kanku kaya cikin sauƙi?*
*Shin kina neman kayan kitchen da bedsheet masu quality da sauƙi?*
*Tom ki shigo ki gane wa idonki idan price ɗin bai yi miki ba ki fece. Shaharariyar 'yar
kasuwa; Rukayya Musa Mahmud. Business name; Maman Suhaila. Dealers of all kind of kids
clothes. Kitchen Ware's. Necklace. Bedsheet. Shoes and bags.*
*Muna Kano Muna tura kaya ko'ina a cikin aminci da kula da amanar kayanku.*


*LAMBA SHA UKU.*

Wani kallo Innarmu ta yi mata kafin ta juya, jiki babu kuzari ta jawo hijabi ta saka tare da
ɗauko tabarma ta shimfiɗa. Sannan ta nemo 'yar tsugunno ta dasa a bakin ɗakinta, waton nesa
tabarmar. Minal kam tsaye kawai take rike da igiyar shanya a tsakar gidan nasu, kanta a ƙasa
tana zana haruffan sunanta da takalmin ƙafarta.
"To hamshakiya mandiya, ga ni na na shirya har na shamfiɗa masa tabarma, kice ya shigo na ji
da wace ya zo."
Zancen Innarmu kenan tana ɗage kai tare da aika mata hararar gefen ido. Minal ta saki igiyar
shanyar ta nufi hanyar fita gidan ƙirjinta yana bugawa. Cike da mamaki ta bi motarsa da kallo,
saboda ganin har lokacin bai fito ba. Tsaye ta yi bakin gidan tana aika wa motarsa harara
tsawon minti biyu, kafin ta isa jikin motar ranta a ɓace ta fara ƙwanƙwasawa. Duk da ta sani
yana sane da ita kuma tana da tabbacin ya gan ta sarai ta gilashi.

Zuge gilashin ya yi tare da aika mata wani kalar kallo ya yi guntun tsaki. Sannan ya mayar da
gilashin ya ɓalle murfin ya fito yana aika katsa wa wasu yara tsawa tare da aika musu daƙuwa.
Saboda dukan bayan motar ɗaya yake yi da bulala, yayin da wani yake dafe da boot yana
leƙen ƙasan motar. Kiran sunansu Minal ta yi tare da faɗin su bar wurin, saboda ranta ya yi babu daɗi. Duba da
halin Jamal tare da halin yaran ba za a jitu ba. Don tun da suka shigo layin da yaran suka biyo
su da gudu yake ta tsaki. Bai yi magana ba amma alamu ya nuna jin haushinsa ƙarara a kan
abin da yaran unguwar suke yi masa. Shigewarsa kawai ya yi ya bar ta tana yi wa yaran faɗa. Saboda ya ƙagu ya yi abin da ya
kawo shi ya tafi sabgogin gabansa.

Tun daga sallamarsa Innarmu ta fara rawar jiki da ganin sa, hakan ya sa ta shiga gaishe shi
bayan sannu da zuwan da yi masa baki washe. Ba tare da ta jira shi ya fara gaishe ta ba a
matsayinsa na suruki. Minal ta yi kasaƙe a ɗaki ranta a ɓace zuciyarta cike da jin haushin rawar
jikin da Innarmu take yi a kansa. Shiru kawai ta yi tana sauraron su har suka gama gaisawa

kafin kafin Jamal ya fara magana.

"Da ma na zo ne na gaishe su ku, amna na ga kamar Baban ba ya gida."

"E, ya fita kasuwa tun da safe. Amma idan ya zo za a sanar da shi zuwanka."

Jamal ya sunkuye kai yana faɗin, "Babu damuwa, sai a gaishe shi kafin na dawo a lokacin da
zan same shi."

Daga haka ya ja bakinsa ya tsuke yayin da yake mutsu-mutsun fito da kuɗi aljihunsa. 'yan dubu
sababbi kar ya ajiye mata a gabanta yana faɗin,

"Wannan naki ne, a yi haƙuri babu yawa."

Sannan ya mayar da hannun yana ƙoƙarin lissafo wasu suka ji sallamar Baban Amina. Dukan
su suka amsa a tare, yayin da Amina ta fito daga ɗakin cike da jin daɗin ganin sa tana gaishe
shi.
Baki har kunne ya amsa mata, sannan ya nufi inda Jamal yake zaune ya miƙa masa hannu
suka gaisa cikin mutumta juna.
Da murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce, "Kun zo ganin mu ashe?"

"Mun zo Baba. Fatar mun same ku lafiya" Jamal ya amsa cikin ladabi.

"To madalla, dukan mu Alhamdulillah! Ya wajen Hajiyar ita ma?"

Jamal ya sake amsawa cikin sakin fuska ya ce, "Tana gaishe ku Baba."

"Muna amsawa, Ubangiji Ya yi albarka."

Daga haka shiru ya ratsa, yayin da Jamal ya miƙe yana ƙoƙarin saka takalminsa Baban ya ce,
"A dai ƙara haƙuri, in sha Allahu alƙawarin da na yi maka yana nan matuƙar A'isha ta dawo gare
mu. Don haka kada ka ji komai da sannu Allah zai kawo mana mafitar da za ta warware
matsalolin gabaɗaya."
"Babu damuwa Baba. Ubangiji Ya bayyana ta cikin gaggawa."

'Ba Amin ba wallahi.'

Zancen zucin Innarmu kenan a lokacin da Baba ya dire nasa zancen. Amma daga Minal har
Jamal sun karɓa da 'Amin.'
Don dukan luguden da ƙirjin Minal yake yi bai hana ta saurin amsawa ba. Kai-tsaye wani sashe
na zuciyarta ta ji ina ma Nur ba ta tafin ba, wataƙila da halin da take ciki ba zai riske ta ba,
ballantana ta ci karo da abin da zamo mata barazana a gaba.

"Ke Amina! Me kike jira da ba za ki bi shi ku koma ba?"

Innarmu ta yi maganar tana zare mata idanuwa. Ganin Jamal

10 / 26