Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
yin su ba maganganu ba ne masu daɗi, saboda ko ba ki yi abin da
kika faɗa ba, idan wani ya ji zai iya yi miki mummunar fassara, a je garin ɓarin baki ƙaddara ta
sa wani abu ya same ta a ce ke ce. Don haka ki kiyaye faɗar kowace irin maganar da ta fito
daga bakinki idan har ba ki tauna ta ba. Ita rayuwar nan da kika gani komai mai sauƙi ne idan
aka ɗauke shi mai sauƙin. Saboda Jamal namiji ne, ko ba ita ba zai iya ganin wata ya ce yana
so, idan kina irin wannan furucin sai ki jefa kanki cikin matsala, idan har tsautsayin illar furucin
ya biyo kanki, Allah Ya kare. Don ita magana zarar bunu ce da ta fito ba ta komawa ciki, sannan
magana mai daɗi ma babbar sadaka ce, kuma Manzon Allah S.A.W ya ce; a faɗi alheri ko a yi
shiru. Idan kin san kina cikin fushi bakinki ba zai iya faɗar magana mai daɗi ba to ki daina yin
magana har sai kin huce. Ina roƙon Allah Ya ƙara miki haƙuri, kuma in dai Jamal ne zai zo gidan
ya same ni ki ga yadda za mu yi da shi, don ga ni cikin gidan naku ina jiran dawowarsa komai
dare. Kuma ko a waya ban ce ki ce masa komai ba, ki bar ni da shi kawai har sai ya zo."
Ajiyar zuciya Inna Ade ta saki kafin ta ce, "Ai wayar tata ma ta buga ta a ƙasa ta fashe
gabaɗaya. Don ina ganin kamar ba za ta sake moruwa da ita ba, bari na ɗauko miki ita ki ga
yadda ta koma."
Inna Ade ta fice daga ɗakin cikin sauri, mintuna a tsakani ta dawo da watsattsiyar wayar ta
miƙa wa Hajiya. Hajiya ta karɓa zuciyarta cike mamakin mahaukacin kishin Minal, wanda ba ta
taɓa tunanin hakan za ta faru a kurkusa ba, duba da yanayin auren nasu da kuma yadda ta sha
fama kafin a samo kansa, kuma ta san ita ma ba ta son auren dole aka yi mata."
"Shi dai namiji ba a cin alwashi da shi, koyaushe ki saka wa zuciyarki cewa mijin mace huɗu
ne. Kuma idan Allah Ya nufa zai tara matan sai dai ki kai zuciyarki nesa ki bar wa Allah komai.
Amma idan kika ce za ki yi ta nuna masa irin wannan zafin kishin gaskiya akwai matsala a
gaba, don wani a lokacin da kike haukar kishin a lokacin yake ƙara zaburewa. Saboda sun fi
son ganin mace tana kishi a kansu idan za su ƙara aure, kuma suna jin haushin mace ta nuna
musu ko-in-kula a lokacin da suke neman auren. Don wani a sanadin hakan yake rage rawar
kai idan ya fahimci auren ba ya gabanki. Saboda zai yi tunanin anya ma kina son sa kuwa? To
da irin waɗannan kissa ake samun kan miji a riƙe babu faɗa babu tashin hankali. Don haka don
Allah ki daina abin da na ga kin yi a yau, inda hali ma kada ki sake yi saboda mutuncinki zai
zube a gaban duk wanda ya ga abin da kika aikata."
Inna Ade kenan da jerin maganganunta da suka ƙara rura wutar takaicin da Hajiya ta cusa
wa Minal. Don ba ƙaramin haushi ta ji ba, a lokacin da take jefo mata tambayoyi sannan kuma
babu wani tashin hankalin da ta ga ta shiga a sanadin jin abin da Jamal ya aikata. Don ba haka
ta so ba, ta so ta dinga masifa ita ma ta ɗauki zafi sosai fiye da yadda ita ta ɗauka.
****
Ɓangaren Jamal kuma, minti biyar a tsakanin wayarsu Baban ya fito. Turus ya yi a lokacin da ya
yi ido biyu da Nur, don tun kafin ya ƙaraso motar ta fita cike da jin nauyinsa ta durƙusa har ƙasa
tana gaishe shi. Mamakin ƙarara a kan fuskarsa, amma hakan bai hana shi gayyato murmushin
dole ba ya yaɓa wa fuskarsa. Cikin sakewa ya yi magana tamkar babu abin da ya faru.
"A'isha, yaushe a garin namu?"
Nur ta yi fiki-fiki da ido cike da jin kunyarsa a idonta ta ce, "Ka yi haƙuri Baba."
"Tashi mu je gidan, mutane suna kallon mu."
Ya yi maganar tare da yin gaba yana sake gaisawa da Jamal. Gaban motar ya buɗe wa Baban
sai da ya shiga sannan ya rufe, ita kam Nur tsaye kawai ta yi zuciya tana yi mata gargaɗin kada
ta shiga motar, inda hali ta samu ta zille kawai musu kawai sai dai su shafa su ji babu ta.
Amma umarnin da Baban ya ba ta a kan ta shiga motar su tafi, hakan ya sa ta jingine abin
da ke ranta ta faɗa motar zuciyarta a cunkushe. Jamal ya ja motar cikin sanyin gwiwa tare da
tunanin yadda zai kaya tsakaninsa da Baban. Don ya gama sanin matsayar Innarmu yanzu tasa
kawai ta rage, kuma ita ce mai babban muhimmanci a wurin sa. Har suka isa gidan babu
wanda ya sake yin magana, sai dai tun kafin su shiga cikin gidan Innarmu ta sha gabansu tana
muzurai. Baban ya raɓa ta gefenta ba tare da ya ce komai ba, har ya yi gaba ya juyo yana cewa
da su Jamal su ma su shigo. Dole Innarmu ta ba su hanya suka wuce sannan ta bi bayansu da
ƙatuwar harara tana faɗin,
"Wallahi A'isha daga ni har Amina ba za mu taɓa yafe miki ba! Kin san kina son sa tun farko
uban waye ya saka ki dole a kan sai kin bar wa Amina shi? To ku gama duk wani ƙullen-ƙullen
da ya kawo ku mu yi ta a ƙare ni da ku."
Ta ƙare maganar tana ƙwafa ta nemo kujera ta dasa a tsakar gidan tana muzurai da tsaki
jefi-jefi. Baba kam bai bi ta kanta ba, kamar yadda Jamal da Nur ba su nuna ma sun ji me ta
faɗa ba. Wuri Baba ya nuna musu suka zauna, sannan shi ma ya raɓa jikin bango ya zauna
idonsa a kansu ya ce,
"Na gan ku tare, duk da ban yi tunanin hakan ba. Duba da yadda aka sha faman neman
A'ishar ba a gan ta ba. Ina ka haɗu da ita?"
Jamal ya gyara zama ya ce, "A wani gidan cin abinci muka haɗu. Duk da ta so tafiya ta sake
bari na Allah bai ba ta sa'a ba. Inda matsalar take dai na ji tana zancen gobe ne ɗaurin aurenta.
Bayan kuma ka mini alƙawarin duk ranar da ta dawo za ka aura mini ita da hannunka."
Shiru ɗakin ya ɗauka tsawon minti biyu kafin Baban ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Tabbas
mun yi haka da kai, kuma ina kan bakana a kan aura maka ita a duk lokacin da ta dawo. Sai dai
zancen auren da ka ce za ta yi, shin su wane ne suka bayar da aurenta ga wanda za ta yi auren
da shi?"
Kallon Nur Jamal ya yi cike da son ƙarin bayani, amma ba ta ce komai ba. Sai da Baban ya kai
kallonsa gare ta yana cewa ,
"Gare ki A'isha, muna son ƙarin bayani." Hakan ya sa ta cire tagumin da ta yi tana faɗin,
"Baba, bayan tafiyar da na yi, abubuwa da yawa sun faru. A cikin su har da haɗin aurena da
ɗan'uwana Sulaimane, wanda ya zamo ɗa a wurin yayan Babana, uwa ɗaya uba ɗaya. Shi ne
ya ba shi ni, kuma shi saka ranar auren da komai, bayan an sake samun saɓani a kaina,
tsakanin dangin Babana da mahaifiyat..."
"Idan har haka ne, ba zan iya aurar da ke kai-tsaye kamar yadda na so yi a farko. Duk da
mahaifinki da kansa ya damƙa mini ke tare da wasiyyar idan aurenka ya tashi na aurar da ke da
hannuna. Amma tun da danginsa suna raye, kuma har hakan ta faru; to ban isa na yi jayayya
da su ba. Saboda sun fi ni ƙarfi a kanki, kuma ba zan so na yi abin da zai jawo mini matsala
daga baya b..."
Cikin matsanancin tashin hankali Jamal ya yi magana tamkar cikin wata kalar muryar kuka ya
ce, "Baba, ka dubi girman alƙawarin da ka yi mini, tun da kana da iko da irin taka dama a
hannunka; don Allah ka taimake ni ka aura mini Nur a yanzun nan ba sai anjima ba."
Wani kalar murmushi Baban ya yi kafin ya ce, "Wallahi, da a ce wannan matsalar ba ta shiga
ba; da babu abin da zai hana ni ɗaura maka aure da A'isha. Amma a haka ina jin tsoron abin da
zai je ya dawo, ganin ban da ƙarfin jayayya da su a kant..."
"Ni zan tsaya a kan komai Baba, ko da wata matsalar ta taso ka bar ni da ita, zan taryi
gabanta kuma zan sha kanta da yardar Allah."
Kafin Baban ya ba shi amsa suka jiyo muryar Innarmu a kansu tana faɗin,
"Na sha ruwan bala'i ba ka isa ka yi wa Amina kishiya tana da wata biyu a gidanka ba. Dole
ne ka yi haƙuri har zuwa lokacin da za ta haifa maka 'ya'ya. Sannan auren ma idan da A'isha
aka yi ni da Amina ba za mu taɓa yafe muku ba daga kai har ita baƙar munafuka..."
Baba ya katse ta a fusace bayan ya miƙe tsaye yana nuna da hannu. "Kin ga...ki yi mini shiru
babbar kwabo! Ina ruwanki da shiga maganar da babu ke a cikin ta? Idan ma auren ne an faɗa
miki haukarki za ta sa a fasa n..."
"Ko ba a fasa ba shi kuma zai sauwaƙe wa Amina. Don babu ta yadda za a yi ta zauna
zaman kishi da A'isha. Wallahi dole ɗaya za a yi! Ko ita ko Amina, amma tun da ba macizai ne
ba za su taɓa haɗa zama cikin rami ɗaya ba ahe!"
Ta ƙare maganar tana riƙe ƙugu tare da jijjigar jiki alamun kaiwa maƙura a kan fushin da take
kai. Shi ma a fusace ya ba ta amsa da cewa,
"Muddin kika yi sanadin mutuwar auren Amina; to ke ma a bakin naki auren. Don na fahimci
sai an fito miki da yaren da kika fahimta za ki hakaltu."
Baki a sake cike da mamaki Innarmu ta ce, "Yanzu Malam a kan wannan feƙaƙƙiyar rayinyar
kake son saki na? A kanta kake iƙirarin bakin aurena idan na kashe auren Amina? To ita ta je ta
yi auren mu gani tun da ta fi kowa a wurin ka. Kuma aura mata shi ɗin ga fili ga mai doki."
Wata sabuwa!
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.
D. AUTA CE✍
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA TARA.*
Ta yi maganar tana kumfar baki, bayan ta gama fesar da zantukanta tana huci ta fito daga
ɗakin, tsabar tashin hankalin da ta shiga gabaɗaya ta rasa nutsuwarta. Takalmi ma ware
daban-daban ta saka, sannan ta ja hijabinta a birkice ta fice daga gidan tana surutai tamkar ta
tashi sama. Yayin da ta bar Baban Amina riƙe da baki a kan mamakinta, bayan kunyar da ta bar shi da ita
saboda tijarar da ta yi a gaban Jamal. Don Nur ta saba gani, ko kaɗan ba ta yi mamakin jin
ire-iren maganganun da ta furzar ba, saboda abin ba sabon abu ba ne a wurin ta ba.
"Allah Ya kyauta."
Baban Amina ya yi maganar bayan ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Sannan ya sake kai
kallonsa a kan Jamal yana cewa,
"Kana dai gani tun kafin a je ko'ina wata matsalar ta kunno kai. Duk da ba a fata, amma
matsalolin da za su biyo bayan ƙulla auren sai sun fi haka. Don da a ce zan samu damar
ganawa da dangin Baban A'isha; da zan roƙi alfarmar su ba ni izinin aurar da ita. To ina mai
tabbatar maka babu abin da zai hana ni ba ka aurenta, kamar yadda na yi yunƙuri yi a watannin
baya, Allah bai nufa b..."
"Baba ban katsi hanzarinka ba, amma matuƙar ba a ba ni auren A'isha ba; ni kuma ba zan
taɓa barin wani ya aure ta ba."
Yana gama furta hakan ya miƙe yana sake cewa, "Zan tafi na dawo Baba, kuma don Allah
kada ka bari ta je ko'ina."
Baban Amina ya bi shi da kallo kawai har ya fice, saboda bai san mai zai ce da shi ba, kansa
ya ƙulle ta yadda ya kasa gano wane kalar hukunci ya dace ya zartar a kan matsalar. Duba da
jin labarin auren da Nur ta faɗa za a yi mata idan safiya ta waye. Sannan yana jin tsoron dangin
Babanta su zarge shi a kan shi ne ya hure mata kunne ta gudo, bayan bai san komai a kanta ba
tun bayan barin ta Kano. Hakan ya sa ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan ya kira sunanta.
"A'isha."
"Na'am Baba." Ta amsa kai-tsaye tare da goge hawayen da ke bin fuskarta har a lokacin.
"Me ya dawo da ke garin nan, bayan kin tafi ba tare da kin sanar da ni ba?"
Zama ta gyara, tare da zuƙe majinar kuka cikin wata raunanniyar murya ta ce, "Ka yi haƙuri
Baba, ni kaina na san ban kyauta ba. Amma Allah shi ne shaidar na bar garin nan ne ba don ina
so ba, kuma na bar shi ne saboda na samu nutsuwar zuciya. Sai dai da a ce na san abin da zan
tarar a can, da ban yi gangancin yin nisa da ku ba. Saboda a sanadin bayyanata, bayan na
share shekara uku ba na tare da su, hakan ya jawo mini tashin hankalin da ban yi zato ba. Duk
da ba ni ce na kawo kaina a gidan nan ba, kuma ba ni da laifi don na yi wa wasiyyar mahaifina
biyayya. Amma an yi mini hukuncin da ya jawo mini danasanin komawata hannunsu. Sannan a
sanadin hakan na gano gaskiyar abin da ya haddasa mini tarnaƙin zuciya, wanda ba zai warke
ba har zuwa ranar mutuwat..."
Ta fashe da wani sabon kukan da ya ƙara ɗaga wa Baban Amina hankali. Ya shiga rarrashin
ta cikin kaɗuwa da rawar murya. Tsawon minti biyar kafin ya samu ta sassauta kukan ta sake
cewa,
"Baba ba zan iya auren Jamal ba, duk da auren da za a yi mini ba son mijin nake yi ba.
Amma na zaɓi zama da shi a kan zaman da zan yi kishi da Amina. Saboda ba na son duk abin
da zai cutar da ita, haka ma idan ina da iko ba zan taɓa bari Jamal ya auri wata ma ballantana a
ce ni na aure shi. Yanzun ma wata ce ta so lalata musu zama, shi ya sa na zo don na kare su
daga sharrinta. Saboda ina group ɗaya da ita, kuma tun ranar da hatsaniya ta haɗa ta da
Aminar na sani, don duk maganganun da suka yi a tsakaninsu ta kwashe ta tura a group ɗin.
Yayin da wasu suke ta zuga ta a kan ta ɗauki mummunan mataki a kan Amina ko don ta huce
takaicin abin da ta yi mata. Tun da na ji muryar Amina kuma na gano da ita ake yin rikicin, sai
hanalina ya tashi. Musamman da na bi diddigin mai son yi musu sharrin, na gano mugun nufin
da take son aikatawa. Don na ƙulla ƙawancen ƙarya da ita, inda na nuna mata ina tare da ita a
kan ɗaukar fansar da take son yi, don kawai na gano komai da take son shiryawa. Ita ma ganin
lambata ba ta Nigeria ba ce, hakan ya sa ta saki jiki da ni ta kwaye mini cikinta gabaɗaya. Don
ba ta ɓoye mini komai ba, ta sanar da ni halayenta da irin tuggun da take shiryawa a kan
Amina. Saboda ta sanar da ni a kan Jamal ta nemi aiki gidan abincin da yake zuwa cin abinci.
Don ta yi bincike sosai a kansa da Aminar, kuma babban shirin da take yi a kansu na farko shi
saka Jamal ya bi ta tamkar raƙumi da akala. Ta hanyar asiri don kawai ta raba shi da Amina, ta
yadda zai sake ta saki uku a lokaci ɗaya ba tare da ya yi shawara da kowa ba. Baba, a shirin da
ta yi musu ma, ta ce hatta mahaifiyarsa sai ta so ganin shi da idonta ba ta samu damar ganin sa
ba. Kuma yanayinta ya tabbatar mini za ta iya duk abin da take faɗa, don ta sanar da ni ba a
kansa ta fara ba, kuma ta ba ni labarai a