Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   17 / 26

48K to 51K   out of 77.3K words

tare da ta sanar da ita ba. Bai kashe hasken motar ba har ta
kai bakin ƙaramar ƙofar shiga gidan, sannan ya shiga buga mata horn ɗii! Saboda tuno wayarta
da ke hannunsa. Kamar ta juya amma sanin rainin hankalinsa ya sa ta shige gidan, ba tare da
ta bi umarnin zuciyarta da ke ba ta shawarar komawa ba.
Kiciɓis ta yi da maigadi yana ƙoƙarin buɗe gate cike da zaton gidan Jamal zai shiga da motar
shi ya sa yake zuba horn. Kai-tsaye ta shige cikin gidan ta bar su suna magana, saboda ganin
zai buɗe masa gate ya fito daga motar yana miƙa masa wayar Minal, tare da sanar shi gidansa
zai koma ba zai samu damar shiga gidan ba. Suka yi sallama tare da addu'ar Allah Ya tashe su
lafiya sannan ya faɗa motarsa ya juya zuwa gidansa. Zuciyarsa cike da tunanin yadda zai
kwashe da Hajiya idan safiya ta waye ya shiga yi mata ina kwana.

Minal kam jiki babu kuzari ta tsaya bakin falon tana muzurai, tamkar wadda ƙwai ya fashewa a
ciki ta murɗa ƙofar, zuciyarta cike da roƙon Allah Ya sa Hajiyar ba ta cikin falon don ta saɗaɗa ta
shige ɗakin Amna ba tare da ta gan ta ba.

Sai dai tana jefa ƙafarta suka yi ido biyu da juna, gabanta ya ƙire ya faɗi jikinta ya ɗauki rawa.
Sum-sum take taku kanta a ƙasa har ta isa inda take zaune ta tsugunna tana miƙa mata ledar ta
ce,

"Shi ya saya mini."

Wani kallo Hajiya ta yi mata fuskarta a haɗe, wanda ya saka hanjin cikin Minal murɗawa babu
shiri. Kafin ta baje ƙasa kamar mai neman yafiya ta fara magana cikin rawar murya ta ce,

"Wayata ya ɗauka shi ne na je karɓa ya tafi da ni ina ta roƙon ya dawo da ni kada ki yi faɗa,
amma sai da ya kai ni shagon da muka je ya yi mini wannan sayayyar..."

"Da ma na san zai aikata fiye da hakan. Shi ya sa na dame shi da kira a kan ya dawo da ke.
Saboda haka gobe kada ki sake bari yana fita yawo da ke bayan har yanzu bai san darajarki
ba."

Ta ɗan tsahirta da maganar kafin ta sake cewa, "Dole ne ki iya jan aji idan kina son ki ƙwato
martabarki ta mace, wadda yake ƙoƙarin wofintarwa a iska. Don haka ki daina sakar masa fuska

har zuwa lokacin da zai gano amfaninki."

Kai kawai Minal take ɗaga mata alamun gamsuwa da shawarar da take ba ta, ba tare da ta iya
haɗa ido da ita ba tsabar kunya da muzantar da ta yi a gabanta.

Sallamar da maigadin ya yi a bakin ƙofar shiga cikin gidan, ya sa Hajiya ta amsa tare da
miƙewa ta nufi ƙofar. Minal ta kasa motsin kirki ballantana ta tashi wurin har Hajiya ta dawo da
wayarta a hannu ta miƙa mata tana faɗin,

"Ga wayarki, ki je ki yi arwala ki kwanta. Ni ma na shige Allah Ya tashe mu lafiya."

"Amin." Ta amsa cikin maƙoshi jiki a sanyaye ta yi ɗaki da ledar don Hajiya ta bar ta da ita a
hannu ba ta karɓa ba. Ta jima zaune a bakin gadon da tagumi tana nazarin halin Jamal da
shawarar Hajiya. Sai da ta fahimci dare ya ƙara yi sannan ta koma buɗe ledar tana kallon
chocolate da kalolin biscuits da ke ciki. Murmushi ta yi babu shiri saboda tuna Jamal da
birkitaccen halinsa mai wuyar fassara. Sannan ta mayar da ledar gefe ta ajiye bayan ta ƙulle, da
nufin sai Hajiya ta ga abin da ke cikin ledar kafin ta taɓa. Daren ranar ma ta yi bacci mai ɗauke
da mafarkan Jamal a cikin yanayin da dole sai da ta yi wankan tsarki kafin ta yi sallar asuba.
Saboda sabon abu ne da ya zamo mata tamkar almara, wanda take kallon sa tamkar wani
babban zunubi, don ta kasa yardar wa zuciyarta aurenta da shi mai inganci ne kamar kowane
auren da ake ɗaurawa.

Ta yi lattin tashi bayan ta koma barci bayan asuba. Don har Umma Ade ta zo gidan ba ta
tashi daga nannauyan barcin da ya kwashe ta ba.
Hajiya da Umma Ade a falo bayan sun gama gaisawa ta miƙa mata lambar mai kayan matan
tana cewa,

"Na sanar da ita za ki kira ta. Ashe ita ma tana rubuce-rubucen littafai a cikin waya. Ni ma a
bakin matan su Nura na ji labarin kuma sunanta Surayy, su ma sun yaba sosai da ingancin
kayanta. A cewarsu babu asara ga sayen kayanta saboda amfaninsu ya linka ma ƙudin da za a
kashe."
"Allah Sarki, Ubangiji Ya ci gaba da dafa mana gabaɗaya. Kuma na gode miki sosai Ade, bari
na kira ta tun yanzu saboda yaron can ya fara wuce gona da iri a kan yarinyar nan. Ga shi kuma
ba na so ya same ta a yadda take, don zai fi raina ta idan bai kamu yadda ake so ba."

Umma Ade ta yi murmushi bayan ta ce amin, sannan ta ƙara da cewa, "A dai bi mini yaro a
hankali Hajiya kada a yi masa mugun kamun da zai kasa zuwa gaishe mu."

"In dai ta riƙe mana shi da kyau to ya sha zamansa mun yafe zuwan, mu za mu dinga zuwa
har gidansa ganin shi. Don ya fi alheri a kan ya ɗebo mana wata wutar da za ta gagare mu
kashewa."

Suka yi dariya gabaɗaya, saboda sigar da Hajiya ta yi maganar tare da kai wa Aden hararar
gefen ido. Kafin ta ƙara da cewa, "Ai Ade yaron nan naki babban riƙo kawai ya dace da Shi,
saboda kansa rawa yake yi ba ya shayin yin gaban kansa. Wannan dalilin ya sa na jinjina wa
budurwarsa Aisha, saboda ba ƙaramin aiki ta yi ba kafin ta raba shi da shashancin da ya mayar
ba a bakin komai ba."

"Hmmmm! Allah dai Ya ƙara shirya mana su Hajiya. Amma yaran zamani kowa da kalar
taɓararsa. Shi ma in sha Allahu daga wannan lokacin ya gama tasa kalar ƙurciya."

Hajiya tana 'yar dariya ta ce, "Ke dai ba kya so a ga laifinsa, tafi ki yi aikinki lokaci yana
tafiya."

Umma Ade ta wuce kitchen, yayin da Hajiya ta nufi ɗakinta da takardar lambar Surayya a
hannunta. Wuri ta samu a bakin gadonta ta zauna, bayan ta jawo wayarta ta fara saka lambobin
kamar haka 08032773332, zuciyarta cike da ɗokin samun biyan buƙatarta cikin sauƙi.

Ɗii! ɗii! Wayar ta shiga ringing a lokacin da Hajiya ta danna kira, aka yi sa'a babu jinkiri ta
ɗaga. Bayan sun gaisa Hajiyar ta gabatar da kanta tare da bayanin ita ce wadda ta saka Ade ta
nemo mata lambarta. Suka sake gaisawa a mutumce kafin Hajiya ta yi mata bayanin dalilin
neman ta. Ajiyar zuciya Surayya ta yi kafin ta ce,
"A shawarce, kafin a ba ta kayan matan da ta yi amfani da su, yana da kyau ta fara shan
maganin infection kafin su. Saboda wani lokaci ko an sha maganin mata idan akwai infection ba
zai bari a ga amfanin kayan yadda ake so ba."

"To, babu damuwa. Yanzu a cikin magungunanki bayan na infection wane da wane kike da
shi? Kuma nawa ne kuɗin kowanne?"

Surayya ta yi murmushi mai sauti kafin ta ce, "Akwai ingantattun kayan gyara na Chad daga
Bojuwa Herbals. Sai Sanyi flusher mai wanko dukkan sanyin da yake maƙale a mahaifa da
jijiya. Sannan akwai ingantacciyar kazar sababi ta saiwowin Chad mai ciko da mace ta haɗe
tamkar sabuwar amary..."
"Ita fa wannan amarya ce kuma sabuwar. A ganin ki babu wata matsala idan ta yi amfani da
maganin da zai ƙara haɗe ta?"

Hajiya ta yi hanzarin tambaya saboda jin ƙara matsewa gudun Jamal ya ji wa yarinyar
mutane ta shiga uku. Surayya ta yi murmushi sannan ta sake cewa, "Babu wata matsala Hajiya,
ai duka cikin gyara ne irin wanda kowace mace ake so ta yi tun daga kan budurwa har wadda ta
taɓa haihuwa. Kada ki damu zan haɗa mata da hakin daka mai kama jiki na mussaman. Tare da
tsumin saiwowin da sai isassum mata ke shan su. Don kayanmu duka na Chadi ne masu
matukar inganci da rashin illa."

Cike da jin daɗi Hajiya ta ce, "To, ma sha Allah, sai ki faɗo mini kuɗin nawa ne gabaɗaya?
Sannan sai ki turo account na ba ki kuɗin gobe Ade ta zo mini da kayan, ko kuma na aika
direba ya karɓo mini a hannunta. Ubangiji ya ba mu ladar gabaɗaya."

"Amin-amin Hajiya. Allah Ya ƙara rufa asiri." Daga haka suka yi sallama, Surayya tana
ƙoƙarin ajiye wayar Hajiya ta sake cewa, "Mun gama magana amma ba ki faɗa mini sunanki
ba."

"Sunana Surayya Dee, marubuciyar littafin HALIN YAU."

Sai a lokacin ta tuna ta ji sunanta a bakin Ade. Cike da jin daɗi ta ce, "Madalla Surayya, Allah
Ya yi albarka, in sha Allah zan haɗa ki da wata ɗiyata idan ta shigo garin. Ita ma tana son irin
kayanku sosai, daga nan har Sokoto ana aika mata kaya har zuwa Yobe. Amma tun da ga ki a
cikin garin Kano idan muka ji daɗin kayanki zan ba ta lambarki ku dinga zumunci, don na yaba
da kirkinki duk da ban taɓa ganin ki ba."

Surayya ta yi murmushi cike da jin daɗi ta ce, "Babu komai Hajiya, in sha Allah za ku yaba da
kayan fiye da yadda kuke zato. Saboda bayan abubuwan da na lissafa miki har da haɗin
amarya (Bridal package), haɗin maijego da uwargida duka ina yi."
"Allah Ya ƙara dafa miki, kuma ya tsare ki da sharrin da ke ciki. Kada ki manta ki turo mini
account zan sa a tura miki kuɗin yanzun nan."

Daga haka suka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Hajiya ta yi jim tana nazarin yadda za ta
tsayu a kan Minal ta yi amfani da kayan daki-daki. Ƙir shigowar saƙo a wayar ya sa Hajiyar ta
duba, a fili ta furta,

"Ma sha Allah, saura kai uban rawar kai, kai ne za ka biya kuɗin ko nawa ne daga aljihunk...."


GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.

DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta
nan 08022014771.

10 February zan sake shi da yardar Allah.



D. AUTA CE✍
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*LAMBA ASHIRIN.*

sallamarsa ta sa ta hanzarin kai kallonta a bakin ƙofar. Ta amsa masa fuskarta a cure tare da
amsa gaisuwar da ya yi mata a gajarce tana kawar da kai gefe. Kansa ya shiga sosawa bakinsa
ɗauke da 'yar dariya ya ce,

"Wurin aiki zan je Hajiyata. Shi ya sa na zo ki saka mini albarka."

"Wani kallo ta yi masa kamar ta ce wani abu amma kuma ta fuske, tare da komawa miƙa
masa wayarta sannan ta tashi tsaye. Nufar bakin wardrobe ɗin ta yi idonta a ciki kamai mai
neman wani abu, daidai lokacin ya yi magana cikin murmushi mai sauti ya ce,

"Wayar fa Hajiyarmu?"

Ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "Kuɗi za ka tura, dubu hamsin da shida a cikin account ɗin da
ka gani. Sai arba'in da huɗu a cikin nawa account."

Ido ya zaro tare da marairaice fuska yana faɗin, "Hajiy..."

"Ba na son wata doguwar magana! Tura kuɗin ka miƙo mini wayata."

Ta katse shi cikin sauri tare da kafe shi da ido har ya tura kuɗin sannan ta ɗauke kallonta
daga kansa ta koma binciken da take yi. Ya tako a hankali idonsa a ƙasa ya damƙa mata wayar
cikin hannunta yana ƙumshe dariya. Ganin yadda ta haɗe fuska alamun babu wasa amma
kuma tana so ta yi dariya.
"Yanzu fisabilillahi laifin me na yi da aka caje ni waɗannan kuɗin a matsayina na almajiri
Hajiyarmu?"

Ya yi tambayar a lokacin da ya koma bakin gadonta ya zauna cikin sanyin jiki yana haɗe fuska.
"Sa ranka a inuwa, ni ma ba amfani zan yi da su ba, matarka ce take buƙatar kuɗin saboda
biyan buƙatarku gabaɗay..."

"Amma dai yarinyar nan ta jaza mini aiki! Yanzu Hajiya saboda Allah duk me za ta yi da
waɗannan kuɗin? Yarinyar da ko dubu goma wataƙila ba ta taɓa riƙewa a hannunta b..tsakani

da Allah Hajiya ki daina sake mata damar da za ta lalace da son kuɗi a samu matsal..."

Juyowa ta yi a fusace tana faɗin, "Tafi wurin aikinka ba na son doguwar magana! Kuma daga
yau babu kai babu fita da ita yawo ban sani ba, ko da rana ballantana a cikin sulusin dare."

Ta yi maganar a fuske, sannan ta juya ta rufe wardrobe ta bi ta gefensa cikin sauri ta bar
masa ɗakin. Jim ya yi a tsaye riƙe da ƙugu kafin ya sauke numfashi mai ƙarfi yana faɗin,

"Shikenan Hajiya ta fi son ta a kaina."

Ya taka a hankali cikin sanyin jiki ya fice daga ɗakin shi ma, a ransa yana faɗin, 'Wayyo
kuɗina! Wannan muguwar yarinya ta san hanyoyin haɗa ni da Hajiya kala-kala. Kuma babu
damar na gwada ta sai ta ɗauki fansa...ba dai ni ba za ki shigo hannuna ne.'

Ya ƙare zancen zucin da ƙwafa, sannan ya fice falon ba tare da ya sake bi ta kan Hajiyar ba.
Harabar gidan ya nufa kai-tsaye ya isa wurin motarsa. Saboda irin kallon da Hajiyar ta wurga
masa a lokacin da suka yi ido biyu bayan fitowarsa ɗaki, hakan ya saka shi tafiya babu shiri da
niyyar ya bar musu gidan tun kafin ya ƙara yin wani laifin. Har ya isa wurin aiki bai daina tunanin
hanyar da zai bi ya huce haushin da Minal take ƙoƙarin ƙumsa masa ta hanyar Hajiya.

Hajiya kam yana fita ta ƙwala wa Ade kira, daidai lokacin da Minal ta fito daga ɗaki a ɗarare
da niyyar yi mata ina kwana. Ga shi lokaci ya ja ba tare da sun ga juna ba, saboda jin motsin
Jamal a cikin gidan ya sa ta ƙi fitowa daga ɗaki har sai da ta ji alamun tafiyarsa. Karin safiyar
ma a ɗaki Ade ta kai mata, saboda sanin Hajiya ba ta karyawa tun da safe ta bari sai ta nema
da kanta.
Har ƙasa Minal ta durƙusa gaban Hajiyar ta gaishe ta kanta a sunkuye, cikin sakin fuska
Hajiya ta amsa mata tare da faɗin,

"Idan kin karya ki shirya direba zai kai ki gidan lalle da kitso. Saboda na sa Amna ta yi wa mai
lallenta magana ta ce ki je cikin lokaci saboda a kammala miki da wuri. Zan ba ki kuɗi idan aka
gama ko nawa ta faɗa sai ki biya ta. Amma ki tabbatar an yi mai kyau, ba iya irin wanda Amna
take yi ba."
Minal ta yi dariya saboda tuno zancen Amnar a lokacin da take ba su labarin rikicinta da
Hajiyar a kan lalle koyaushe. Don ta fi son a yi mata na gargajiya ita kuma ko kaɗan ba ta son
shi, shi ya sa ko ta yi lallen ba ta yabawa sai faman kushen da take yi da harare-harare. Saboda
ko zanen fulawar ma kaɗan Amna take so ba ta son a cika mata lalle a jiki. Minal tana ƙoƙarin miƙewa ta ga Umma Ade a gefe tana murmushi, ta raɓa ta gefenta ta
wuce ita ma fuskarta ɗauke da murmushin kuma cike da jin nauyin su duka. Don tun da Hajiya
ta fara magana Aden ta iso wurin amma ba ta ce komai ba har suka gama gudun ta katse su.
Sai da Minal ta bar wurin sannan Aden ta ce,
"Ga ni Hajiya."

"Yawwa Ade, da ma sanar da ke zan yi mun yi magana da Suraira ɗin..."

"Surayya take Hajiya."

Ummu Ade ta yi maganar tana 'yar dariya, saboda jin yadda ta sauya sunan alamun ba ta gama
riƙewa ba. "To..to haka nan fa Surayya! Na ba ta kuɗin abubuwan da za ta harhaɗa mana, kuma
idan direba ya dawo daga kai Aminar zai kai ki ki karɓo mana sauran kayan kafin ta gama
dafuwar kazar sababin. Don ina so a yi komai a gaggauce gudun yaronki ya kawo mana
matsala ba tare da

17 / 26