Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   23 / 26

66K to 69K   out of 77.3K words

ya sake cewa, "Har abada ba zan manta abin
da ta yi mini ba Hajiya, saboda haka ba zan iya bayanin komai ba idan ba cin amanar da ta yi
wa rayuwata kike son ji ba."
"Assha! Ranka ya daɗe komai na duniya fa ɗan haƙuri ne. Kuma idan ka nutsu da kyau za ka
fahimci ita ma ba ƙaramin so take yi maka ba, duba da yadda ta baro ƙasarta takanas don
tseratar da kai daga matsal...'

Nur ta yi hanzarin katse ta cikin fushi tana cewa, "Ki bar shi..ki bar shi kawai Mama, ni duk
abin da na yi don Allah na yi da ceton rayuwar 'yar'uwata Minal. Kuma Allah shi ne shaidar ban
guje ka don ba na son ka ba. Kuma na yi abin da na yi ne da kyakkyawar niyya ko da kai ba za
ka fahimce ni ba. Sannan ban ce dole sai ka yarda da duk abin da na faɗa ba, amma ni dai na
sani har abada ba zan bari a cutar da kai ba, haka ma ni da kaina ba zan yi abin da na san zai
cutar da kai ba. Saboda haka ka kalle ni a yadda duk kake kallo na, kuma ka ci gaba da kallo na
da irin fassarar da kake yi mini babu komai."

Tana ƙare maganar ta miƙe tana goge ƙwalla ta bar wurin gudu-gudu sauri-sauri saboda
kukan da ke barazanar fallasa ƙuncin zuciyarta. Hakan ya sa duk kiran da Hajiya Innon ke yi
mata bai sa ta juyo ko ta tsaya daga ƙudurinta na son tafiyar ba. Daidai lokacin da kira ya sake
shigowa wayarta, inda tana ɗauka mai maganar ya sanar da ita jirgin da za ta bi har ya tashi,
don ya yi ta kiran ta ba ta ɗauka ba, kuma ya turo mata saƙo ba ta yi masa reply ba. Saboda ya
yi ta kiran ta tana danne kiran tun farkon zaman sulhun da Hajiya Innon ta so yi musu, har zuwa
lokacin da ta miƙe da nufin barin wurin a gaggauce ana ta kiran ta, don ta san dalilin kiran da
abin da ke gabanta idan ta koma Niger.

Hannu ta ɗora a ka cikin tashin hankali ta yi magana da wanda ya kira tana cewa, "Ina cikin
tashin hankali Adamu, saboda wallahi babu wanda ya san na zo ƙasar nan, kuma kai ka san
uzurin da kenan, wanda ko ba na so dole na yi tafiyar nan a yau, gudun na shiga wani sabon
bala'i."
Shiru Adamun ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce, "Idan babu damuwa ki zo na kai ki masaukin
da za ki kwana cikin sirri kafin lokacin mu ga yadda za a y..."

Cikin rawar murya ta ce, "Gobe ne ɗaurin aurena ka sani, ta ya ya zan iya kwana a nan asirina
ya tonu idan aka neme ni aka rasa? Ba zai yiwu ba Adamu, don Allah ka bincika mini idan
akwai jirgin da zai tashi ko da cikin dare ne zan bi sh..."

"Babu inda za ki je ballantana ki yi auren da kike faɗa!"

Ta ji maganar Jamal tsidik a cikin kunnuwanta, cikin hanzari ta juya tana kallonsa, ba ta ankara
ba ta ji ya fisge wayar tare da ɗora ta a kan kunnesa, inda yake ƙoƙarin yin magana amma kafin
ya ce wani abu ya ji muryar Adamu yana faɗin,

"Ki yi haƙuri, zan bincika miki, idan da halin tafiyar a yau sai mu gan..."

"Za ka gani kuwa baƙin munafuki! To ko ubanka ne mijin babu inda za ta je sai da igiyar
aurena. Kuma ka sani wallahi idona idonka sai na nuna maka ba iri na ake ha'inta ba."

Yana ƙare maganar ya ɗora jajayen idanuwansa a kanta, kafin ya fisgo hannunta cikin
matsanancin fushi tana tirjiya tare da buge masa hannun, amma hakan bai hana shi cusa ta
cikin mota ba. Hajiya Inno da ke kallon abin da ke faruwa ta biyo su tana faɗin,

"Ranka ya daɗe ka bi komai a hankali don Allah, ka san tunanin mace ba ɗaya ne da naku
maza ba. Kada ka yanke hukuncin da zai jawo danasani daga baya."

Uffan bai ce da ita ba, illa hannun da ya ɗaga mata yayin da zai bar wurin yana ƙoƙarin hawa
kan titi. Nur da ke zaune gaban motar tsuru-tsuru tana zarar ido, tsabar tashin hankalin da take
jin kanta a ciki tamkar ta fi kowa matsala. Ido ta ɗora a kansa tana faɗin,

"Ban san ina za ka kai ni ba, amma ka sani rashin komawata gida a yau, da abin da rashin
gani na zai haifar ya fi matsalarka girma. Don haka ka tausaya mini kada ka bari rayuwata ta
lalace a sanadin biye wa son zuciyarka."

Kalamanta ba su sa ya ji tausayin ta ba ballantana ya magantu, illa ƙarin baƙinciki da haushin
da suka jefa shi ciki. Gudu ya shiga shararawa a saman titin tamkar wanda zai tashi sama, bai
zame ko'ina ba sai a bakin wani Shopping Mall. A gaggauce ya fice bayan ya saka motar a key
gudun ta fice bai sani ba. Shigewarsa ke da wuya ta ɗaga waya ta kira Adamu, sai dai har ta yi
ringing ta gama bai ɗaga ba, cike da jin haushi ta tura masa saƙo tana faɗin,

'Kada ka tayar da hankalinka a banza, Allah Ya fi kowa sanin gaskiyar abin da ke tsakanina
da kai. Don haka duk matakin da zai ɗauka ka yi haƙuri don Allah kada ka biye shi."

Bayan ta tura saƙon ta yi shiru tana nazari tare da goge hawayen da ya kasa barin
idanuwanta. Mintuna a tsakani ya fito tare da wasu ma'aikatan wurin a bayansa da kayan abinci
niƙi-niƙi. Bayan boot ya buɗe aka gama zuba kayan ya rufe tare da buɗe motar ya shiga. Kuma
har lokacin fuskarsa a cure ya tayar da motar ya juya aguje ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba. Kasancewar ta yi zama garin Kanon tsawon shekara biyu zuwa uku, hakan ya sa ta fahimci
inda ya nufa da ita. Kallon sa ta yi cikin wani yanayi mara misaltuwa kafin wani sabon kuka ya
zo mata ta yi magana cikin raunin murya da zuciya ta ce,

"Me kake nufi da kai ni gidan su Minal?"

Bai amsa mata ba, kamar yadda bai kalle ta ba, gudunsa kawai yake yi da motar har zuwa
lokacin da ya saki babban titin ya gangara cikin layin su Minal. Sai da ya dira a ƙofar gidan
sannan ya yi jim yana kallon gabansa ya ce,

"Ki shiga ciki, idan Baba yana nan ki kira mini shi."

Ba ta fita kamar yadda ya buƙata ba, sannan ba ta ce da shi ƙanzil ba, illa zuƙar majinar
kukan da take yi tare da goge hawayenta jefi-jefi da mayafin doguwar rigar da ke jikinta.

"Ki kira shi na ce!"

Ya sake yin magana cikin ɗaga murya tare da ɗora kallonsa a kan kumburarriyar fuskarta,
wadda tsabar kukan da ta sha ta sauya kala zuwa ja. Ganin ba ta da niyyar fita kuma kukan da
take yi ba ƙaramin taɓa masa zuciya yake yi ba, hakan ya sa cikin zafin nama ya ɓalle murfin
motar ya fice. Wasu yara ya yafito suka zo da gudu, ya buɗe boot ɗinsa yana fito da kayan tare
da ba su umarnin su shiga da su daga ciki, kuma idan Baban yana ciki su yi masa sallama da
shi.
Sai da aka shigar da kayan duka sannan ya jingina da motar rungume da hannu kansa a ƙasa
yana nazarin mafita a kan hukuncin da yake son zartarwa. Duk da ya sani abu ne mai matuƙar
wahala, amma duk tsanani gara rayuwa da Nur a wajensa da a ce ya yi rashin ta gabaɗaya.

Jim kaɗan bayan shigar yaran suka fito Innarmu a bayansu lulluɓe da zani tana leƙe, don ta
gane wa idanuwanta mai mutunci da ya gwangwaje su da kayan abinci irin haka. Caraf ta
hango Jamal a bakin motarsa, baki buɗe ta fara rawar jikin gaishe shi tun kafin ya gan ta shi ya
fara gaishe ta.
"A'ah! Lale-lale marhabin da zuwanka. Allah Sarki ashe kai ne da wannan tagomashin alheri
har haka?"

Sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa ya kai kallonsa gare ta yana murmushin yaƙe. Kafin
ya bar jikin motar cikin sanyin jiki ya isa inda take ya rusuna kansa a ƙasa ya shiga gaishe ta, ita
kam tuni ta riga shi kai ƙasa tana godiya ba tare da ta amsa gaisuwar da yake yi mata ba.
"Amm.. Baban yana ciki kuwa?"

Ya yi tambayar kansa a ƙasa bayan ta gama godiyar shi ma ya ce babu komai yi wa kai ne. "Ai
ka san Malam ba ya zama a irin wannan lokacin sai dare ake samun sa a gida. Sai dai idan ya
dawo a sanar da shi ka zo shi ma ya kira ka ya yi maka godiya.
...ai mun gode mun gode sosai wallahi. Allah dai ya biya ka kawai ya ƙara muku zaman lafiya
da Amina."

"Amin-amin."

Ya amsa kansa a ƙasa kafin ya ɗago idonsa ya kalle ta cikin girmamawa ya ce, "Tare nake da
baƙuwa, za ta shiga ta zauna kafin zuwa daren sai na dawo mu yi magan..."

"Haba-haba! ai babu komai wallahi an zama ɗaya ta shigo ta zauna gidanku ne kai ma, kuma
kana da ikon kawo duk wanda kake so ya zauna a cikin gidan kamar yadda Amina take da iko
da shi."

Har cikin ransa ya ji daɗin furucin Innarmu, hakan ya ƙara masa ƙarfin gwiwar miƙewa ya isa
gefen da Nur take zaune ya buɗe mata ƙofa. Ido cikin ido suka kalli juna tsawon sakon biyu
kafin ya nisa, cikin wata kalar murya ya ce,

"Fito ki shiga ciki, zuwa dare zan dawo mu yi magana."

Sanin Innarmu tana ganin su don ta kasa ɗauke idanuwanta daga kansu cike bin ƙwaƙƙwafin
gano wace ce tun kafin ta iso, don har da leƙawa ta gilashin ta yi da zummar hango ta tun a
cikin motar. Sai dai kasancewar ba a ganin na ciki ta wajen ya sa dole ta bar zura wuyan ta
mayar da kallonta ta saman motar. Dam-dam ƙirjinta ya buga saboda ganin Nur ta fito daga
motar, baki buɗe ta ƙura mata kallo har zuwa lokacin da ta ƙaraso gabanta ta durƙusa har ƙasa
tana gaishe ta. Cikin kaɗuwa da zaucewa Innarmu ta riƙe ƙugu tana faɗin,

"Uban wa ya dawo da ke a cikin gidan nan?"

Nur ba ta ɗaga kanta ba, illa sabon hawayen da ya shiga bin fuskarta. Jamal ne ya yi ƙarfin
halin isa wurin cike da mamaki ya zuba wa Innarmu kallo kafin ya ce,

"Ita ce wadda na kawo ajiya kafin Baba ya dawo mu yi magan..."

"Dakata-dakata yaro! Ko dai ka manta nan gidan iyayen Amina ne matarka wadda kake
aure?"

"Ina sane ba mantawa na yi ba. Kuma kin faɗa ina da iko da gidan kamar yadda Amina take
da iko da sh.."

"Amina da kai daban! Sannan wannan tsintacciyar magen daban! Saboda haka ba za ta
shiga cikin gidan nan ta zauna mana ba ko da sakon ɗaya ne. Don ba mu haɗa komai da ita ba,
asali ma babu wanda muka taɓa gani a cikin danginta, shi kansa maigidan da ya ɗebo mana ita
daga baya ya gano kuskurensa a kan riƙon wadda bai san komai a kan asalinta ba. Saboda
haka ka kwashe ta ku matar da ita inda ta ɓoye tun kafin Malam ya dawo ku jawo mana wata
sabuwar fitina."

Shiru ya ratsa tsakani bayan maganarta, saboda sabon ɓacin ran da Innarmu ta cusa masa.
Bai ce da ita komai ba tsabar ƙimar Amina da ke ransa, sannan da darajar surukantaka da yake
kallo a idonsa.

"Tashi mu je!"

Abin da ya faɗa kenan kafin ya bar wurin ya faɗa matarsa yana ba ta wuta. Nur ta miƙe ba tare
da ta ce da Innarmu komai ba ita ma ta bi bayansa. Hakan ya ƙara rura wutar tashin hankalin
da Innarmu take ciki, ta shiga tsine wa Nur tare da miyagun lafuzza iri-iri, sai wanda bai zo cikin
bakinta ba. Har da iƙirarin duk ta sake ganin ta a ƙofar gidan hukuma ce za ta raba su.
"Kin san shagon Baban ne?"

Nur ta yi banza da shi har suka hau babban titin Jogana suka miƙi hanyar zuwa kasuwar da
Baban Amina yake zama. Saboda ya san kasuwar da yake zuwa tun zamanin yana neman
auren Nur, amma bai taɓa sanin wanne shagon da yake aiki ba.
Sai da suka je bakin titin kasuwar ya samu wuri ya yi parking, sannan ya ɗaga wayarsa ya
kira Baban. Sai dai har wayar ta nemi tsinkewa bai ɗauka ba, cike da jin daɗi Jamal ya amsa
sallamar da ya yi masa cikin mutumtawa bayan ya ɗauka. Suka gaisa tare da sa albarka ga
Jamal da yi masa addu'ar ƙarin zaman lafiya da Amina, bayan ya gama tambayar Hajiya da
saƙon gaisuwa gare ta.

"Baba akwai maganar da nake so mu yi da kai."

"To..too babu damuwa. Za ka iya zuwa da dare idan na koma gida sai mu tattauna."

Sosa kansa Jamal ya yi kafin ya ce, "Yanzu haka ina bakin kasuwarku Baba, idan da halin
fitowa ka zo mu tafi gidan tare, saboda magana ce mai matuƙar muhimmanci za mu yi."

"To, babu komai ka jira ni yanzu zan fito sai mu tafi."

Jamal ya katse kiran yana kallon Nur da ta yi tagumi tana kallon mutanen da ke ta
zirga-zirga ta gabansu. Amma zuciyarta ko kaɗan ba ta wurin, don ta tafi duniyar tunanin abin

da zai faru idan har aka neme ta ba a san inda ta je ba. Ga shi ta cire layukanta na Niger, ta
saka na Nigeria da niyyar idan ta gama abin da take yi ta zare shi ta adana kamar yadda ta yi a
ranar da ta bar garin.


Akwai kallo


Na gode sosai da addu'o'inku. Allah Ya bar zumunci.

GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.


D. AUTA CE✍
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*ASHIRIN DA BAKWAI.*

A ɓangaren Minal kuwa, tsawon miniti goma bayan fitarsa tana nazarin yadda ta samu
matsayin da ba ta taɓa tunanin za ta samu a wurin sa ba.

'Ashe ni ma mace ce?'

Ta yi zancen daga ita sai zuciyarta, yayin da ta shiga godewa Hajiya a ranta, da Gwaggo
Salame da ke dannar ta har zuwa kan Innarmu da ke danna mata ashar a kan wajibi ne sai ta
zauna.

'Allah Sarki Babana, ka mini nasiha kuma na ɗauka, in sha Allahu zan bi mijina kamar yadda
ka ba ni shawara.'

Ta ƙare zancenta na zuci tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tana runtse ido.
Saboda ta kasa manta rawar ɗuwawun da Jamal ya yi a kanta tsabar ya same ta cikakkiyar
mace bayan gyaran Hajiya.

"Idan ka ba ni zuciyarka ma ta wadatar da ni. Hakan ya sa ba na buƙatar komai sai kai
kawai....Nur kum.."

Ta yi saurin toshe bakinta tamkar wani zai ji ta, cikin sauri ta yi niyyar gyara kwanciyarta babu
shiri ta ce, "Ashh!" Saboda zogin da ta ji a ƙasanta dole ta lallaɓa a hankali har ta daidaita
kwanciyar sannan ta rufe idonta da niyyar yin barci.
Sai dai kafin barcin ya yi awon gaba da ita ta jiyo tashin murya a falo ana ta rafka sallama. Ta
ƙara lafewa a cikin gadon tare da kasa kunne tana son tantance muryar mai sallamar. Cikin
sauri ta zaro ido, saboda jin muryar Inna Ade tana faɗin,

"Matar gidan tana kusa kuwa?"

"Inna ga ni a ɗaki, ki shigo kawai."

Ta yi maganar cikin wata kalar muryar mara lafiya, tare da tsabar jin nauyi da kunyar Inna Aden,
gudun ta gano halin da take ciki har ta fahimci abin da ya wakana. Muryar Inna Ade ta so ɗakin
tana faɗin,

"Ai na ɗauka ke ma ba kya nan ganin yaron nawa ma ba ya gidan. Don na yi mamaki da
maigadinku ya ce kina ciki don na yi sallama ta fi goma ban ji motsin kowa ba."

23 / 26