Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   4 / 26

9K to 12K   out of 77.3K words

zuwa lokacin asibitin ta cika da danginsu, 'yan'uwa da abokan
arziƙi. Mutanen nesa da suka kwana gidan Hajiya mummy fiye da rabinsu suna asibitin ana
jajanta lamarin. Gidansu Minal ma Hajiya ta kira ta sanar da su halin da ake ciki, sannan ta bai
wa 'yan aikinta umarnin su yi abin karin safiya su kai wa Minla. Saboda tashin hankalin da take
ciki bai hana ta tunawa da amanarta da aka ba ta ba.

Wannan dalilin ya sa Innarmu da Gwaggo Salame suka dira asibitin ganin Jamal. Daga can
suka zarce wurin Minal bayan sun gama tattaunawa da Hajiya a kan yadda za a shawo kan
matsalar cikin sauƙi. Kuma an bar zancen a tsakaninsu ba tare da an sanar da Minal halin da
yake ciki ba, gudun ta ƙara tuburewa ta bijire wa auren kuma ta lalata musu sabon shirin da
suka tsara.

****
Minal kam maganganun Gwaggo Salame sun rage mata kaso huɗu a cikin goman
damuwarta. Kuma ta karɓi ƙaddararta, duk da tana jin ba ta gamsu da ingancin auren ba har a
cikin zuciyarta ba. Saboda iya sanin ta dakalolin tarihin auren da ta ji ba ta taɓa jin kalar abin da
aka yi mata ba. A take zuciyarta ta shiga ziga ta da shawarwari mabambanta, waɗanda ta tsayu

a kan wadda zuciyarta ta karɓa, kuma ta riƙe a matsayin makamin kare kanta daga farmakin da
ke cikin auren, sannan da riƙon amincin da take yi wa alaƙarta da Nur.
Jiki babu kuzari ta ja abincin da Hajiya ta aiko mata ta ƙara ci. Sannan ta fitar da sauran ga
maigadi yana ta godiya. Sai dai abin da ya so ƙara saka ta cikin damuwa zamanta shiru a cikin
gidan tun bayan zuwan su Innarmu, babu wanda ya sake zuwa gidan har dare. Sannan ta kira
Amna ya fi sau goma, amma har wayar ta gama ringing ba ta ɗauka ba. Hakan ya ƙara tunzura
ta, ta shiga neman lambobin Nur cike da ƙunar rai, da zaman turaata saƙonni da zummar ko da
za ta buɗe wayar ta gan su. Saboda duk kiran da ta yi a sanar da ita layukan duka a rufe suke.

Daren ranar ma ta yi kwana rabi da rabi, saboda rashin nutsuwar zuciya da kaloli tambayoyin
da take son amsarsu amma babu damar hakan. Abincin daren da Hajiyar ta sake aiko mata ma
sai cikin dare ta samu damar ci, a lokacin da yunwa ta hana ta sukuni saboda barcin ya ƙi ba ta
haɗin kai. Karfe biyun dare ta duƙufa kai kukanta ga Allah, a kan ya kawo mata sauƙin matsalar
da take ciki, sannan ya dawo da Nur ga mijinta ita ma ta auri wanda take so. Saboda katangar
kashedin da Innarmu ta yi mata da Aminunta ya hana ta neman sa a waya ta ji halin da yake
ciki.
Don abu ne da ta sani dole ne hankalinsa ya tashi a lokacin da ya ji an yi wa neman
aurensa ƙarfa-ƙarfa. Sannan ita ma Nur za ta dawo ga Jamal komai daɗewar lokaci, hakan ya
sa ta dinga amfani da kayanta na gida duk da ba su da yawa. Kayan Nur kuma ta mayar da su
akwatunan lefenta da ke ajiye gefen gado. Saboda ta saka wa ranta zaman wuccin-gadi ne za
ta yi a gidan ba zaman dindindin ba, don haka babu abin da zai ruɗe ta ta saki jiki a inda babu
lasisin zamanta.
Ba ta samu bacci mai daɗi ba har sai da ta gama sallar asuba, daga lazumi ta ɓingire a
wurin sai barci. Haka ta ci gaba da rayuwar kaɗaici ita kaɗai a gidan Jamal har tsawon sati
ɗaya, babu mai zuwa wurin ta idan ba Gwaggo Salame ba. Abin da ya fi ɓata mata rai kenan
ganin yadda aka wofintar da 'yancinta bayan an tauye rayuwarta da gingimemen laifi. Hakan ya
sa a cikin 'yan kwanakin gabaɗaya ta zuge, saboda ramar ƙarfi da yaji ta dira jikinta har
idanuwanta sun zurma tamkar mai ciwo. Saboda wa'azi da nisihar gwaggon Salamen, tare da
kulawar da Hajiya ke ba ta kowace safiya; ba su cire ta daga cikin ƙuncin da zuciyarta ke abota
da shi ba. Sai ga wani ƙarin tashin hankali, Hajiya ta kira ta a waya tana sanar da ita Jamal zai
dawo ranar ta shirya yi wa mijinta girki.

Shiru kawai ta yi bayan ta sauke wayar daga kunnenta ƙirjinta yana bugawa ta shiga sharar
ƙwalla. Saboda jikinta ya ba ta gara zaman gidan ita kaɗai da rayuwa wuri ɗaya da Jamal. Duba
da irin tozarcin da ya yi mata da yunƙurin kisan tun a tashin farko.

"Ba zan iya zaman aure da shi ba."

Furucinta kenan a lokacin da ta miƙe jikinta yana rawa ta ja dogon hijabi ta zumbula. Da
sassarfa ta sauka ƙasa jikinta yana tsuma ta isa bakin gate, maigadi yana tambayar lafiya ganin
yadda ta fito gidan kamar an koro ta. Amma ƙanzil ba ta ce da shi ba ta buɗe ƙofar za ta fice.
Kiciɓis ta yi da gwaggo Salame tana ƙoƙarin shigowa gidan har kansu ya gwabru da juna.

"Subhanallahi!"

Furucin gwaggon kenan a lokacin da ta yi ido biyu da Minal, nan take zuciyarta ta hasko mata
abin da take ƙoƙarin aikatawa. Fuskarta a cure ta dinga kallon Minal tana nazarin yanayinta,
ganin ta ja gefe tana kumbura fuska bakinta ɗauke da gungunin a saman leɓonta. Fuskarta a
cure ta yi mata magana cikin kakkausar murya ta ce,
"Me ya fito da ke kuma ina za ki je?"

Minal ta ɓare baki kamar ƙaramar yarinya ta yi magana cikin kuka ta ce,

"Wallahi ni ba zan zauna daga ni sai shi a cikin gidan nan b..."

Ta yi maganar tare da rushewa da wani sabon kuka har da buga ƙafafuwa. Baki a sake
gwaggon ta bi ta da kallo bayan ta shigo gidan ta rufe ƙaramar ƙofar. Ta fara fa hannnuwa tana
salati saboda ta rasa me za ta faɗa. Ganin maigadi yana tsaye yana kallon su ya sa ta ja
hannunta tana tirjiya da buga ƙafa har suka koma cikin gidan. A falon sama ta zaunar da ita kan
kujera ranta a matuƙar ɓace ta shiga nuna ta da hannu kafin ta samu damar faɗin,

"Yanzu Amina sau nawa zan ce ki yi haƙuri? Kenan duk abin da nake faɗa a bayan
kunnuwanki yake bi yana wucewa? Saboda Allah duk lokacina da nake ba ki a kwanan nan
ashe ba ki gani ba? Ko kin manta ina da tarin abubuwan da nake jinginewa na zo rarrashin ki?
Ashe ban sani ba kallon mara aikin yi kike yi mini da nufin na yi a banz.."
"Gwaggo ni ba na son zama da shi ne kawai...saboda ya faɗa ba zai mini kallon mace ba
kuma ya ce sai ya kashe n..."

"Ya kamata zuwa yanzu ki fahimci mijinki ba zai iya cutar da ke ba. Don ko kiyashi ba zai iya
kashewa ba ballantana mutum. Saboda duk tsawon kwanakin nan da ba ya kwana gidan yana
asibiti ana kula da lafiyarsa. Ya yi ciwo na tsawon kwanaki a yanzu ta kansa yake yi da abin da
ke damun sa. Don haka ki kwantar da hankalinki babu abin da zai iya yi miki idan ba alheri ba.
Idan ma ya yi miki Allah ma ba zai bar shi ba, kuma hukuma ba za ta ƙyale shi ya ci bulus ba
dole ne a ɗauki mataki kans..."

"Idan haka ne Gwaggo a sanar wa da 'yansanda tun yanzu, saboda su san halin da ake ciki
su hana shi kada ya sake yunƙurin kashe ni...don wallahi ranar ƙiris ya rage ya cire mini
maƙogwaro."

Dariya Gwaggo Salame ta yi sannan ta zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinta, saboda
zancenta ya sa ta fahimci firgicin da ya saka ta ne ya sa take jin tsoron zama da shi tun a daren
farkon auren. Hakan ya sa ta shiga kwantar mata da hankali har ta saki ranta. A gefe ɗaya
kuma tana jinjina ƙarfin son da yake yi wa Nur cikin tausaya wa halin da yake ciki. A ranta kum
ta shirya yadda za ta shawo kansa ya daina jin haushin ta su nemo hanyar da za a gano Nur a

duk inda ta shiga.

Saboda kwanansa uku a asibitin aka sallame shi, a kwana na huɗun ne Hajiya ta ce ya
kamata ya koma gidansa da kwana tun da ya ji sauƙi. Amma fafur ya kafe a kan shi da gidan
har abada, ta so tirsasa masa kwana gidan a ranar; amma wasu daga cikin dangin Alhajinsa
suka ce ta bi komai a hankali. Hakan ya sa ta ci alwashin kora shi gidansa cikin dabara, saboda
babu adalci a bar Minal ita kaɗai a gidan shi yana kwana gida.
A son ran Hajiyar ma daga sallamar sa a asibitin ya yi wa gidansa tsinke su sasanta da
matarsa, amma shawarar da likitan ya ba ta a kan a bi komai a sannu har zuwa lokacin da zai
warware ya sa ta ɗaga masa ƙafa. Sai dai kuma a gefe ɗaya ta shiga nata aikin da ta ce idan ya
san wata bai san wata ba. Don maganin ƙarfin maza ta dinga ɗirka masa yana sha ba tare da
ya san amfaninsa ba. Ko da ya tambaya kuma ce masa ta yi maganin ciwon zuciya ne, duk da
bai gamsu ba amma hakan bai sa ya yi kokwanto a kansa ba, saboda cikakken sanin da yake
da shi a kan ta fi shi son kansa, kuma ba za ta iya cutar da shi ba.
Abokansa ma ta ba su aikin dannar sa tare da rage masa damuwar rashin Nur. Hakan ya
sa suka shiga nuna masa alfanun haƙuri da kowace irin jarabawa. Saboda iya binciken da suka
yi sun tabbatar Nur ba ta garin, ta yi tafiyar da babu wanda ya san inda ta je. Da taimakon
abokan nasa masu ƙarfafa masa gwiwa ya dinga shan maganin Hajiya. Sai dai inda gizon ke
saƙar sauyin da ya fara ji a jikinsa, inda ya fara zargin maganin da tayar masa sha'awar mace.
Saɓanin yadda ya saƙa wa ransa har abada tsakaninsa da mace, matuƙar Nur ba ta dawo ba
babu shi babu kowace irin mace a duniya komai nagartarta.

Dole ƙanwar na ƙi Hajiya ta shawo kansa a kan zai koma gidansa da kwana. Daɗin
amincewarsa ta aika wa Minal cefane, tare da sanar da ita abincin da ya fi so ta girka masa da
kanta. A nan gidan ma Gwaggo Salame ce ta taimaka mata da girkin har suka kammala.
Sannan ta saka ta yin wanka da ado a cikin ɗaya daga cikin sabbbin kayan lefen Nur, waɗanda
sai da ta sha fama da ita sannan ta saka kayan. Sai dai a a ranta ta ci burin tana fita za ta cire,
saboda ta yi wa kanta alƙawarin zama d Jamal har zuwa lokacin da Nur za ta dawo.
Kunun aya Hajiya ta haɗa wa Jamal, ta ce ya tafi da shi ya sha tare da Minal, saboda sanin
yana mugun son sa, wannan dalilin ta yi masa tarkon da zai kama shi daren ranar. Bayan ta
gama yi masa wa'azi da jan kunne a kan zama da Minal bisa amana ko da ba ya son ta. Ganin
hawaye a idonta ya saka shi karɓar alƙawarin zama da ita a cikin gidan ba tare da ya yi mata
korar karen da ya kitsa wa ransa ba da ya je gidan.
Har ya fice da motarsa cikin gidan tana zuba masa addu'ar tsari da abin ƙi tare da neman
kwanciyar hankali a cikin rayuwarsa. Cike da jin daɗin addu'o'in nata ya baro gidan cikin karfin
zuciya, amma bai fasa hasko hoton murmushin Nur a idanuwansa ba. Hakan ya ƙarfafa masa
gwiwar zai ci gaba da neman Nur a duk inda ta je a faɗin duniya.



Wasar za ta fara

D. AUTA CE✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA IBRAHIM D. AUTA*

*LAMBA TA SHIDA.*


Minal tana zaune falo tana kallon ƙarfin halin da Gwaggo Salame ta saka ta yi. Saboda ita ce
ta ba ta umarnin zaman kallon har zuwa lokacin da Jamal zai shigo gidan, kuma ta ce kada ta
kuskura ta bar falon ba tare da ya dawo ta gabatar masa da abincinsa ba. Tare da jaddada
mata kada ta bari wahalar girkin da suka yi ta tashi a banza. Kuma duk abin da take ji kada ta yi
sakacin barin sa ya yi kwana da yunwa. Saboda Hajiya ta sanar da ita ba ta bari ya ci abinci a
wurin ta ba, saboda kada ya ƙi cin na gidansa.

A haka ta zauna tana kallon MBC2 da tagumi har zuwa lokacin da ta ji buɗe gate da shigowar
motarsa. Ƙirjinta ya ƙire ya faɗi a lokaci ɗaya jikinta ya hau rawa ta shiga wara idanuwa tana
neman inda za ta ɓoye, kada ganin ta ya sa haukar son Nur ta motsa masa ya nemi illata ta a
banza.
'Ko da wasa kada ki sake ki nuna kina jin tsoron sa. Saboda wannan ne damarki ta farko da
za ki yi amfani da ita ki nuna masa ke ma kin san kanki.'

Tuno kalaman Gwaggo Salamen ya sa ta fara faɗar hasbunallahu wa ni'imal wakil don samun
nutsuwar zuciyar da ta bar jikinta tsoro ya mamaye jarumtar da take ƙarfafa kanta. Saboda
sautin huɗubar gwaggon da take ji a cikin kunnuwanta tamkar a lokacin take yi mata jan kunnen
da gargaɗi. Hakan ya sa ta yi hanzarin gyara zamanta tare da tsuke fuska tana nanata kalmar
lahaula wa la ƙuwwata illah billah. Har ta ji motsin buɗe ƙofar falon ƙasa tare da takunsa yana
hawa saman cikin sauri.

Dam-dam ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri a lokacin da ya kunno kansa cikin falon.
Idanuwanta a kan tv ba tare da ta kai kallon ta gare shi ba gudun ya gano halin da take ciki ya
nemi cutar da ita babu mai ceton ta. Don a cewar Gwaggon idan ya fahimci tana mugun tsoron
sa zai raina ta yawa ta yadda zai dinga yi mata abin da ya ga dama koyaushe. Hakan ya sa
shigowarsa bai sa ta kai duban ta gare shi ba duk da hankalinta yana kansa. Sannan bai yi
sallama ba ballantana ta amsa, sai jin sa ta yi ya saki ledodin da ke hannunsa suka zube ƙasa,
bakinsa yana rawa ya kira sunan Nur cikin ɗaga murya yana cewa,

"Nur! Yaushe kika dawo ban sani ba?"

Wani kallo ta yi masa kamar ta yi masa babu yabo babu fallasa, amma a zuciyarta sosai ya ba
ta tausayin da ya so karya mata zuciya. Sai dai hakan bai hana ta waige gefe da gefe ba cikin
basarwa ta ce,

"Ina ka ga Nur a nan?"

"Ya Allah!"

Jamal ya faɗa cikin wata irin murya yayin da ya yi hanzarin dafe kansa da ke sarawa babu
shiri. Saboda hango Minal a matsayin Nur ya tayar masa da mikin da yake ƙoƙarin dannewa a
ransa. Saboda gizon da ta yi masa sak Nur da ƙamshin turaren Nur da ya ji a cikin falon,
wanda tun asali shi ne ya fara yi masa maraba kafin ya isa bakin ƙofar shiga falon. Ƙirjinsa ya
hau bugawa babu ƙaƙautawa ya shiga nuna ta da hannu yana faɗin,

"Ko da wasa kika sake saka turaren Nur a cikin gidan nan sai na sauya miki kamanni...kuma
kin ci sa'a na yi wa Hajiya Mummy alƙawarin zama da ke da a yanzun nan sai kin bar gidan nan
wallahi...ahhhh!"

Ya ƙare maganar yana dafe kansa ya wuce jiri yana kwasar sa ya faɗa ɗakinsa. Kamar da
gayya a ɗakin ma turaren Nur ne ya fara yi masa oyoyo. Gado ya yi hanzarin kwantawa dafe da
kansa yana murza goshinsa tare da bubbuga kansa a hankali. Ya bar Minal da ƙamewa wuri
ɗaya tamkar an dasa ta, saboda furutansa sun ƙara lalata ƙarfin halin da ke zuciyarta. Zumbur ta miƙe gudu-gudu sauri-sauri jikinta yana rawa ta faɗa ɗakinta, babu ɓata lokaci ta
hau cire kayan Nur da ke jikinta. Sannan ta nufi bayi da sassarfa ta shiga darzar jikinta da
sabulu tana haɗa kumfa, a ƙoƙarin ta na son raba kanta da ƙamshin Nur saboda gudun ta shiga
haƙƙinsa da yawa ciwonsa ya ƙara tashi ta yi sanadin sharri. Don Hajiya ba ta ɓoye mata komai
ba ta sanar da ita duk abin da likita ya faɗa a kan ciwon nasa tun kafin ya dawo gidan. Kuma ta
nemi alfarmar ta kula da shi tare da juriya a kan halayensa har a shawo kan matsalolin da ke
cure su warware.
Sai da ta ji fatar jikinta ta fara zafi sannan ta haƙura da wankan ta fito daga bayin. Jikinta a
mace ta sake shiri ta fice saboda tuno abincin

4 / 26