Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
an gama gyaran ba.
"Mutum da matarsa Hajiy..."
"A hakan kuma zai bar ta duk nacinsa tun da har ya yi laifin da ta dawo gabana."
"Ni dai ina raba ki da yaran zamani. Kin san kuma farinjinin yarona ko bai nema ba mace za
ta neme shi da kanta. Kada kina bin bayanta ta zagaye ba tare da kin sani ba ta gane mijinta."
Dariya suka saka gabaɗaya, yayin da Ade ta bar wurin tana faɗin, "Bari na kawo miki abin
kari. Ga shi an manta yarona ya tafi ba tare da ya karya ba."
Hajiya tana dariya ta ce, "Shi ya sani Ade, ya je can ya ƙarata, don zamansa ma saka mutum
magana kawai zai yi."
***
Ƙarfe goma da rabi na safiya a gidan mai lallen ta buga wa Minal. Aka shiga tsefe mata kai
bayan an manna mata lalle. Wanda ta zaɓa da kanta a cikin waya, don tun kafin a shafa jan
lallen tsarin jeren salatif ɗin ya fito da ƙafarta fes. Duk da take baƙar mace amma baƙin nata bai
hana jan lallen da zanen baƙin lalle mai fulawowi fitowa ya yi kyau a ƙafarta ba. Haka ma
fuskarta ta washe, saboda tana da cikar gashi tsawo ne babu, wannan ya ba da damar da aka
tsara mata kitso da gashin attach, wanda ta nuna style ɗin da take so. Don da ma can da shi ta
fi auki a koyaushe kitsonta ba ya tsallake na ƙari matuƙar za ta yi fitar kunya. Kuna sosai kitson
ya yi mata kyau kasancewar ƙwararriya ce ta yi aikin, musamman da aka haɗa mata da na
gaba ta ƙara zama 'yar ɗagwas.
Zuciyarta cike da jin daɗi ta cashe kuɗin da aka faɗa babu wata gardama, saboda Hajiya ta
ba ta wadataccin kuɗi har da saka wa kanta kati a waya, don ita ma an gama burge ta. Ranta
fes ta kira Hajiyar ta sanar da ita an gama komai direba ya dawo ya ɗauke ta. Misalin ƙarfe
shida na yamma, Jamal ya faka motarsa a ƙofar gidan lallen sannan ya kira ta a waya ya ce ta
fito.
Ƙirjinta ne ya buga dam tun daga ganin kiransa har zuwa saƙon da ya fesar mata kafin ya
datse kiran ba tare da ya jira cewarta ba. Jiki babu kuzari tana haɗe rai ta fito gidan, tare da
rakiyar wasu matan da ta ƙulla ƙawance da su a wurin lallen, har da musayar lamba. Bakin
motar suka ja suka tsaya suna yi mata Allah Ya tsare, yayin da Minal ta buɗe gaba ta zauna
tana dariyar yaƙe suka yi sallama, ganin irin kallon ƙurullar da wata daga cikin su take yi wa
Jamal, sosai hakan ya ƙona mata rai. Shi kam bai ma san tana yi ba, don ita kanta Minal bai
sake kallon ta ba har ya hau kan babban titin da zai kai su gida, bayan ya bar ƙofar gidan.
Ƙirr! Wayarta ta shiga ƙara, cikin sauri ta duba mai kiran, ganin sunan Zulaiha gidan kitso ta
ɗauka cike da mamakin dalilin kiran.
"Ammm...na ce ba ƙawata.." Zulaiha ta yi magana cikin fargaba. Kafin Minal ta amsa a ƙagauce.
"Kika ce me?"
Ta yi maganar a taƙaice cike da zaƙuwar son jin abin da za ta faɗa, "Don Allah wannan gayen
da ya ɗauke ki yayanki ne ko saurayinki?"
"Me ya faru?"
Minal ta jefa mata tambayar cikin gatsali tana yamutsa fuska. "Ya burge ni sosai wallahi, kuma
idan har ba saurayinki ba ne ni ina ciki. Don Allah ki fara kama mini ƙafa kafin na gabatar da
kaina idan kin ba ni lambars...."
"Ke wace irin shashasha ce? Sannu Gantalalliya 'yar iska!"
Minal jikinta yana tsuma ta yi maganar saboda wani tsinin mashin baƙin kishin Jamal da aka
caka mata a tsakiyar zuciya. "Subhanallahi! Ƙawata me ya yi zafi ne daga tambay..."
"Ki je ki tambayi ubanki wataƙila shi ya san amsoshin da zan ba ki!"
Ƙitt! A zafafe ta datse kiran tare da danna mata block. Sannan jikinta yana rawa ta sake nemo
lambar ɗayar ƙawar lallen ta danna mata blocking ita ma. Tana huci fuskarta a cure ta yi
magana cikin fitar hayyaci numfashinta yana fisga ta ce,
"Da na ba ki lambarsa gara na hango gawarki a kwance ana jana'izark..."
Wata mahaukaciyar dariya ce ta suɓuce wa Jamal babu shiri, saboda duk abin da suka
tattauna yana ji, kuma tun farkon kiran ya kai kallonsa gare ta cike da son sanin wace ce mai
kiran. Fahimtar ƙawance ya koma rigima ya shiga ɓaɓɓaka mata dariya babu ƙaƙƙautawa. Don
tun kallon farko da ya yi wa ƙawayen nata ya ɗauke kai, cike da mamakin ina ta san su. Amma
da yake bai san komai a kanta ba kafin lokacin, hakan ya sa ya yi tunanin wataƙila da ma can
sun san juna. Sai dai fahimtar inda gizon ya yi saƙar ya saka ta gaba da dariya har sai da ta
fashe da kuka babu shiri, tsabar haushin Zulaiha da takaicin dariyar da yake yi mata.
"Aaa'a fa! Ba za ki cika mini mota da kuka ba, idan kika matsa sai na sauke ki ki nemi abin
hawa, don ba na ciki da kayan ihu."
Minal ta ƙara sautin kukanta tare da yage baki iya ƙarfinta tamkar wadda aka yi wa mugun
duka. Rage gudun motar ya yi, kafin a hankali ya gangara zuwa gefen titi ya tsaya. Tsawon
minti biyar yana danna wayarsa tare da sauraron kukan da take yi ba tare da ya ce da ita ƙanzil
ba. Fahimtar za ta ɓata masa lokaci Hajiya ta tuhume shi ya kai kallonsa gare ta yana faɗin,
"Wai duk zafin kitso da lallen ne kike yi wa kuka haka?"
Banza ta yi da shi yayin da ta rage kukanta tana kallon gefe zuciyarta a cunkushe ta dinga
jan majinar kuka tana goge hawayen fuskarta da bayan hannunta.
"Ko na mayar da ke gidan lallen idan kin kammala da ƙawayen naki na koma na ɗauko ki?"
Wani kallo ta yi masa hawaye yana bi fuskarta shaa sannan ta kawar da kanta gefe tana
faɗin, "Wallahi duk na sake yin ido biyu da ita sai na nuna mata kuskurent..."
"Me za ki yi mata?"
Ya yi maganar tare da fashewa da wata sabuwar dariya, a ƙufule ta mayar masa da amsa
kai-tsaye da cewa, "Ka rabu da ni Malam! Babu ruwanka da ni."
"Haka ne kuma."
Ya yi maganar cikin ko-in-kula yana mayar da wayarsa caji fuskarsa a haɗe ya tayar da motar
sannan ya sake hawa kan titin. Kallon sa ta yi ta gefen ido kafin ta sake goge ƙwalla tana kallon
lallen 'yan yatsunta, zuciyarta cike da jin haushin kanta. Ganin kishi ya sa ta bayar da kanta a
gabansa, sai dai dole ta yi wa kanta uzuri don ita kaɗai ta san kalar zafin kishinsa da ke kartar
zuciyarta.
Har suka isa gidan Hajiya babu wanda ya sake magana, yana parking a harabar gidan ta
ɓalle murfin motar ta fice cikin sauri. Kallo ya bi bayanta da shi kafin ya yi hanzarin dafe jijiyarsa
da ke harbawa tsabar ta fara tayar masa da jaraba.
"Ohh Allah! Wannan yarinya kamar ibilishiya komai ta yi sai ta tsokano ni."
Ya jima a cikin motar yana nazarin kishin da ta nuna tare da zaucewar da ta yi a lokaci ɗaya
saboda wata ta ce tana son shi. 'Kenan so na take yi ko me?'
Ya yi zancen riƙe da haɓa don sosai abin ya ba shi mamaki. Saboda ganin babu wata
shaƙuwa ko fahimtar juna ballantana ita kanta soyayyar a tsakaninsu. "Amma me zai sa ta
shiga halin da ta shiga don kawai wata ta ce tana so na?"
Ya yi wa kansa tambayar a fili kafin ya ɗaga kafaɗa alamun ko a jikinsa ya fice zuciyarsa cike
da tunanin Nur da kewar ta a ransa. Saboda babu wani motsin da zai yi ba tare da ya tuno da
ita ba, sai dai kawai ya dinga basarwa don shi ma ya gama tsayar da zuciyarsa wuri ɗaya. A
kan cewa Nur yaudarar sa kawai ta yi amma babu wani son da ta yi masa shi ne ya ɓata
lokacinsa a banza.
Bai shiga cikin gidan ba sai da aka yi sallar magrib, sannan ya isa ciki. Faɗan Hajiya ya tarbe
shi tun kafin ya ƙarasa, da guntuwar sallamarsa a baki ya samu doguwar kujera ya kwanta tare
da dunƙulewa wuri ɗaya tamkar mai jin sanyi. Sosai ya karya wa Hajiya zuciya ta sassauta
faɗan da take yi ganin yanayin da ya shigo falon. Saboda fuskar kukan da ta gani ga Minal
zuciyarta ta tabbatar mata shi ne ya yi abin da ya saba. Duk da ta tambaye ta dalilin kukan
amma ta ce mata babu komai, kuma shi ma bai yi mata komai ba.
"Lafiya kake kuwa?"
Hajiya ta yi maganar zuciyarta a tsinke tare da isa inda yake tana taɓa wuyansa. "Jikinka dai
babu zafi, ko dai ni ce kake yi wa dabara don kana son na daina yi maka faɗa a kan abin da ba
za ka daina ba ko na ce ka bari? To ba zan fasa nuna maka ka yi kuskure ba. Amina ko baiwa
ce ya kamata a ce ka daina yin abin da zai ɓata mata rai, idan har ka sa girman haƙƙin da ke
rataye a wuyank..."
"Ni fa Hajiya ban yi mata komai ba! Ita ma idan za ta faɗi tsakaninta da Allah ta san babu
abin da na yi mata. Kuma ina zaune kika ce na je na ɗauko ta, sai da na nuna miki a nemi Isah
ya ɗauko ta saboda ba na son ki ga laifina. Amma kika ce dole sai na je. Shikenan ni kullum sai
kin ga laifina a kanta, salon ta raina ni a banza. Komai na yi laifi ne bayan ita ma har yanzu ba
ta san darajar auren ba ballantana ta san darajat..."
"Dake ni ubana!"
Hajiya ta yi maganar cikin sanyin murya saboda sosai kalamansa sun shiga zuciyarta. Sanin
halinsa ya sa ba ta son ya fahimci ta yi laushin da zai ƙara kawo mata wani sabon rashin ji.
"Kaina ciwo yake yi Hajiya."
Ba ta ce da shi komai ba ta nufi ɗaki ta ɗauko masa paracetamol da ruwa ta zauna bakin
kujerar da yake kai ta ɓallo maganin tana faɗin,
"Tashi ka sha, kuma idan akwai sauran magungunanka idan ka koma gida ka sha kafin ka yi
barci."
Ya tashi babu musu ya karɓi kofin ruwan ya sha maganin sannan ya koma ya kwanta idonsa
a rufe. Zuciyarsa cike da tunanin abin da Nur ta yi masa, a gefe ɗaya kuma a matse yake da
son kusantar Minal. Wannan dalilin ya sa ya yi barcin ƙarya saboda ba ya son Hajiya ta kora shi
gidansa.
Minal kuma a ɗakin ma kuka ta sha sosai, saboda takaicin Zulaiha da dariyar da Jamal ya yi
mata. Ƙarin abin haushi kuma tana buɗe data saƙonni suka fara shigowa ta hango sunan
Zulaiha yana yawo a saman notification. Ƙirjinta ya buga dam-dam, saboda ba ta yi ƙasa a
gwiwa ba wurin buɗe saƙon ta danna mata ashar. Duba da kalar saƙon da ta turo mata mai cike
da rainin hankali da barazana.
_"Ko ki so, ko kada ki so, sai na yi soyayya da shi tun da na gan shi na ji ina son sa. Saboda
ni babu ɗa namijin da zan yi ido biyu da shi na ji ya kwanta mini ba tare da na farauto shi ta
ƙarfin tsiya ba. Ban san ki ba sai a yau, amma zan nemo wace ce ke a cikin kwana uku, sannan
ko mijinki ne tun da kika zage ni a kansa sai na nuna miki na fi ki zama kalar 'yan hau. Don
haka ki shirya zuwan ranar da za ki gan ni da shi a matsayin mata ko budurwarsa."_
Wata sabuwa
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.
DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. A turo shaidar biya ta nan; 08022014771.
10 February zan sake shi da yardar Allah.
D. AUTA CE✍
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA ƊAYA.*
Wurgar da wayar Minal ta yi a kan gado cikin ƙunar zuciya. Kafin ta shiga zarya a tsakiyar
ɗakin tana cizon yatsa.
"Ba ki isa ba! Wallahi ba ki isa ki mayar mini da hannun agogo baya ba! Ƙarya kike yi, ba
Zulaiha kike ba ko ke kika koya wa shaiɗan shaiɗanci sai na nuna miki na fi ki tashanci. Don
babu macen da ita ta raɓu jikin Jamal idan ba ni b..."
Boyis ɗin da ta yi kenan bayan ta rarumo wayar ta tura mata saƙon, ƙirjinta yana bugawa
babu ƙaƙƙautawa. Kafin zuciyarta ta shiga aika mata tambayar da ta saka jikinta yin sanyi
laƙwas.
'Ta ya ya za ki yi masa iyaka da mata bayan ke ma har yanzu ba ki gama samun mazaunin
dindindin ba?'
Hannu ta ɗora a ka tamkar ta fasa ihu, tsabar firgicin da ta shiga ya saka ta ɗimuwa. Da
hanzari ta bi umurnin wata zuciyarta mai nuna mata ta sake fesar da abin da ke cikin ranta da
gaggawa. Ta sake mayar wa da Zulaiha wanu raddi jikinta yana rawa ta ce.
"Idan ke 'yar halas ce ba shegiya ba, ki yi mini kwatancen inda kike a yanzun nan na zo mu yi
gaba da gaba da ke, don ina so ki maimaita abin da kika faɗa a gaban idona."
Ta saki typing ɗin jikinta yana tsuma idonta a kan rubutun tsabar masifar kishin da ke cin
zuciyarta. Ganin shiru minti uku a tsakani Zulaiha ba ta yi mata reply ba ta danna mata kira ta
WhatsApp call. A nan ma ta yi banza ba ta ɗaga ba, duk da alamu ya nuna tana online ɗin.
Hakan ya sa Minal ba ta haƙura ba ta sake danna mata wani kiran, ringing ɗaya a na biyu
Zulaiha ta ɗauka. Kafin ta yi magana Minal ta riga ta da cewa,
"Ashe matsoraciya ce ke ban sani ba? Amma kuma kike taƙama da rashin mutunci!"
Wata kalar dariya Zulaiha ta yi kafin ta ce, "Allah Sarki, shirun da kika ga na yi miki ba tsoro
ba ne matar Jamal. Saboda ja baya ga kowa ya sani shirin faɗa ne. Don haka ki rubuta ki ajiye,
in dai da gaske ni Zulaiha ɗiyar sunnah ce cikin uwa da uba, sai na farauto zuciyar Jamal ya bi
ni tamkar bawa da uwagijiyars..."
"Ƙarya kike yi baƙar 'yar iska! Jamal ya fi ƙarfinki don kakan ubank..."
Zulaiha ta sheƙe da wata mahaukaciyar dariya kafin ta sake cewa, "Allah Sarki Minal, ni fa
tausayi kike ba ni. Yanzun nan na gama jin labarin ashe ke ma ɗin ba wani sonki yake yi
ba...amma me ya sa za ki dinga hauka a kan wanda bai wani damu da ke ba? Shi fa namiji ba a
cin alwashi da shi ko da kina da madafun ikonsa a hannunki. Don haka matuƙar ba ki iya allonki
ba, to ki daina kishi a kan wanda ba ki da ikon saka shi ko ki hana shi. Na ba ki shawara ne
saboda ƙawancenmu na farko, abin da zai haɗa mu na biyu kuma mu zuba ni da ke mu ga wa
zai yi nasara Saboda ina kan bakana, ni da ke wanda ya fi iyawa ya ja igiyar faɗan daidai da
ƙarfinsa."
Ƙitt! Zulaiha ta katse kiran ta bar Minal riƙe da wayar a kunne tamkar wadda aka zare wa
lakar jiki. Saboda gwiwowinta sun yi sanyi tun a lokacin da Zulaiha ta ce ta san Jamal ba wani
son ta yake yi
ba. Wani hawaye mai zafi ya shiga bin fuskarta, saboda takaici da baƙincikin kalaman Zulaiha.
'Ban san me ya sa na biye ta ta faɗa mini abin da ya ɓata raina a banza ba. Amma kuma to
wa ya sanar da ita ba ya so na? Ko dai gidan