Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
da ta kawo masa farmakin gaggawa. Saboda ganin
tudun bom-bom ɗin ta da shafe ɗin doguwar rigar da ke jikinta ya tona asirin albarkatun
ƙugunta.
"Wai ke ba ki iya gaisuwa ba ne? Ina ta magana kin yi wa mutane shiru!"
Ya Yi maganar a daidai lokacin da ya kasa nutsuwa har sai da ya haɗa jikinsa da nata, yayin
da ya rungumota ta baya ya shiga goga mata jijiyarsa da ke miƙe saman bom-bom yana sauke
numfashi ɗaya bayan ɗaya.
"Innalillahi!"
Abin da ta faɗa kenan cikin hanzarin tare da zabura saboda abin da ta ji tamkar almara. Ta ja
gefe fuskarta a cure tana nuna shi da hannu ta ce,
"Idan maitarka ta tashi ka dinga tsayawa ga iya matan barikin da ka saba bi, saboda ka fi
kowa sanin ni ba 'yar iska ba c..."
"Amina! Fito ki bar masa kitchen ɗin idan ya gama abin da ya kai shi sai ki ci gaba da naki
aikin!"
Muryar Hajiya suka jiyo a sama, wadda ta katse mata magana babu shiri. Saboda jikin
Hajiyar ya ba ta matuƙar Minal tana cikin kitchen ɗin sai ya samu abin da ya yi mata mara daɗi.
Ƙwafa kawai Minal ta yi bayan ta amsa kiran Hajiyar da faɗin 'To' a kan umurnin barin kitchen
ɗin. Sannan ta raɓa ta gefensa tana ƙoƙarin ficewa ya damƙo hannunta ta baya fuskarsa a haɗe
duk da yanayinsa gabaɗaya ya gama sauyawa.
"Ba ki isa ki mini fitsara ba! Idan kuma kika kawo mini tsageranci zan nuna miki na fi ɗanyen
kai. Saboda haka ki bi ni a hankali don ba zan juri rashin mutuncinki ba."
Kanta ta juya gefe riƙe da ƙugu tana girgizar jiki ba tare da ta ce da shi ƙanzil ba. Ƙirjinta ya
shiga bugawa tsabar tsoron sa duk da tana ƙoƙarin nuna jarumtarta a fili. Don maganganunsa
sosai suka kama mata zuciya. Amma sai da Hajiyar ta sake ƙwala mata wani kiran sannan ta
shiga kiciniyar ƙwatar hannunta daga riƙon da ya yi mata, ta kasa. A ƙarshe ma fisgo ta ya yi
gabaɗaya ta faɗa jikinsa ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya ɗaya bayan ɗaya. Ta shiga
ture shi zuciyarta cike da fargabar kada Hajiyar ta shigo ta gan su a yadda suke. Babu shiri ta
ƙwala wa Hajiyar kira saboda jin hannunsa ɗaya ya cafko mata bom-bom tare da zabura a
lokaci ɗaya.
Sautin takun Hajiyar da faɗan da take yi tana nufo kitchen ɗin, hakan ya saka fargaba ta shige
shi ya yi saurin sakin ta tare da kai wa ƙafarta taki cike da haushin kwarantun kiran Hajiyar da ta
yi don ta tona masa asiri. Sannan ya juya bayansa yana ƙoƙarin saita kansa da nutsuwarsa ta
ƙarfi gudun Hajiyar ta gano halin da yake ciki. Cikin ruɗewa ya shiga mayar da niƙaƙƙun kayan
miyan a cikin bulanda da niyyar sake niƙawa.
Minal kuma ta durƙushe ƙasa riƙe da ƙafarta tana yarfa hannu daidai lokacin da Hajiyar ta iso
kitchen ɗin a fusace. Idonta a kan Minal tana salati yayin da ta isa wurin kwandon kwanoni ta
fisgo ludayin miya ta yi kansa da duka. Da gudu ya fice yana dariyar ƙarfin hali yana gaba tana
bayansa har ta kora shi harabar gidan ta rufe ƙofar falon, bayan ta gama yi masa kashe da
babbar murya tana faɗin,
"Kada ka sake zuwa gidan nan daga yau! Kuma idan na sake ganin ka dawo sai na kakkarya
maka ƙafafuwa. Tun da kai ba za ka bar bakin mutum ya huta ba kullum sai ka yi abin magana
kake jin daɗi."
Motarsa kawai ya faɗa zuciyarsa a ƙuntace ya fice gidan cikin fushi tamkar ya tashi sama.
Saboda takaicin Hajiya ta hana shi rage zafi a inda aka tsokano masa sha'awarsa. Da hakan ya
shiga tunanin hanyoyin da zai bi ya yi wa Hajiyar wayo ta bar shi ya dawo gidan da zama. Ita
kuma Minal ya yi mata dabarar da zai samo kanta cikin sirri ya kwashi ganima ba tare da
Hajiyar ta sani ba. Don da ma can amfaninta gare shi kenan tun da har zuwa lokacin bai gama
gamsuwa da ingancin aurensu ba. Kuma zuciyarsa ba ta nutsu da karɓar ta a matsayin matarsa
ta dindindin ba.
A cikin gidan kuma Hajiya ta shiga rarrashin Minal, tare da nuna mata ta daina yi masa kuka,
kuma ta bar barin yana cin zalinta a banza ita ma ta dinga ramawa. Umma Ade tana murmushin
ta yi magana cikin sigar kwantar da fushin Hajiyar ta ce,
"Yaran zamani ne Hajiya. Tasu kalar soyayyar kenan ki bar shiga tsakaninsu."
"Babu wata soyayya sai baƙar mugunta Ade. Ana soyayyar zai kasa cin abincinta ya koma
ƙoƙarin dafawa da kansa?"
Hajiya ta yi maganar cikin ɗaga murya, Umma Ade ma ta sake cewa, "Abincin ne kawai ba ya
ra'ayin ci, amma ko a ido ana gano yarona ba ƙaramin so yake yi wa matarsa ba. Don haka a yi
masa haƙuri Hajiya zai daina in sha Allah. Saboda shi tasa salon soyayyar kenan sai an dinga
yi ana nuna masa hanya."
"Ba hanya ba hanyo Ade! Wace irin hanya ce ban nuna wa Jamal ya kasa bi tun tana gidansa
ba? Kuma yanzun ma da na kawo ta gabana ya ce ba zai ɗaga mata ƙafa ba? To ƙaryarsa ta
sha ƙarya Ade! Matuƙar ya ce zai ɓata mata rai a cikin gidan nan ni kuma wallahi ba za mu taɓa
shiryawa da shi ba. Abincin gidan nan ma daga yau ya daina ci, sai dai ya je can inda babu
mayu su dinga ba shi yana ci...ai Amina ba baiwa ba ce ballantana ya dinga yi mata abin da duk
ya ga dama."
Umma Ade ta yi shiru saboda ganin Hajiyar ta hau sama sosai. Minal ma shirun kawai ta yi
amma zuciyarta ko kaɗan ba ta jin daɗin ganin yana samun matsala da mahaifiyarsa a kanta.
Sai dai dole ta ja bakinta ta yi gum saboda 'yancinta ne take ƙoƙarin ƙwatar mata daga
hannunsa. Jiki babu kuzari ta koma kitchen ɗin, don gabaɗaya Jamal ya gama raunata mata zuciya.
Musamman abin da ya yi mata duk wani motsi abin take ta gani a cikin idanuwanta kamar
almara.
Da marece sakaliya Umma Ade tana shirin komawa gida Hajiya ta kira ta har cikin ɗakinta
suka zauna. Cike da damuwa ta yi magana saboda abin da yake cizon ranta kuma tana ganin
Aden za ta iya taimakon ta tun da ta san komai da abin da ke faruwa.
"Ade, ku ne idon duniya, ina za ki samo mini sahihin maganin mata gangariya? Saboda ina
so na yi maganin matsalolin Jamal a kan yarinyar nan! Duba da yadda aka yi auren babu wani
kyakykyawan shirin da iyayenta suka yi mata. "
"Hmmmmm!" Ajiyar zuciya Umma Ade ta sauke mai ƙarfi kafin ta ce, "Tabbas wannan
shawara ce mai kyau Hajiya. Don wataƙila har da rashin gyaran ya ƙara rura rashin jituwa a
tsakaninsu. Amma idan har wannan ce matsalar, in sha Allahu daga wannan karon an zo
ƙarshe. Saboda akwai wata baiwar Allah maƙociyarmu ce, Ubangiji Ya lamunce mata nan
ɓangaren. Don alamu ya nuna magungunanta suna aiki sosai duba da yadda matan masu kuɗi
suke ta zarya a gidanta koyaushe. Idan kina so zan iya kai ki har gidanta ku tattauna ta yadda
za a shawo kan matsalar cikin sauƙi."
"Yawwa Ade, na gode miki sosai Ubangiji ya saka ki cikin masu kaso a ladar ke ma. Ki karɓo
mini lambarta gobe idan kin zo, sai mu fara yin magana na ji waɗanne iri za mu fara saya mu
gwada. Don ina son ta mallake shi gabaɗaya ta yadda kallo ma ba zai ƙara yi wa kowace mace
ba da sunan shashanci. Ina so ya tsayar da hankalinsa wuri ɗaya saboda gudun ya kwaso wa
kansa ciwon zamani ya bar mu da tashin hankali."
"In sha Allahu hakan ba za ta faru ba Hajiya. Allah zai kare shi babu abin da zai faru da shi
sai alheri."
"Muna fatar haka Ade don ni ma ba na masa fatar hakan, amma mace ko namiji duk wanda
bai tsaya inda Allah Ya ajiye shi ba zai haɗu da ɓacin rai watarana, matuƙar ba a kiyaye dokokin
Allah aka watsar da ƙyale-ƙyalen zuciya ba."
Ade ta muskuta tana faɗin, "Allah Ya ƙara tsarewa Hajiya."
Daga haka suka rabu, a kan Ade za ta karɓo lambar mai kayan matan da safe idan ta dawo ta
kawo mata. Bayan tafiyar Ade Hajiyar ta kira Amina da ke kallo a falo ta shigo ƙirjinta yana
bugawa. Saboda kwarjini sosai Hajiyar take yi mata, ba ta samun nutsuwa idan tana ga wuri har
ta ɗaga. Wuri ta samu a ƙasa ɗan nesa da Hajiyar ta zauna a ɗarare bayan ta yi sallama cikin muryar
ladabi. Cike da tausayin ta a ran Hajiyar ta ja numfashi ta sauke kafin ta ce,
"A cikin kayan da kika zo da su akwai sababbi?" Ta jefo mata tambayar kafin ta ƙarasa furzar
da abin da ke ranta.
"Babu." Ta amsa cikin fargaba saboda ba ta san dalilin da ya kawo tambayar ba. Hajiya ta sake
jefa mata wata tambayar da cewa,
"Me ya sa ba ki zo da su ba?"
Minal ta yi shiru kawai kanta a duƙe tana wasa da yatsunta. Fahimtar akwai abin da ke ranta
wanda ba ta son faɗa Hajiyar ta sake cewa,
"Dole ne ki yakice duk wani abu da ke nisanta ki da mijinki. Sannan ki iya ɗaukar wankan da
zai dinga jan hankalinsa gare ki. Don ba zai yiwu ki zauna a haka babu wani gyara ko kissa irin
ta mata ba. Ki koyi abubuwan da za ki shawo kan mijinki da su a cikin ruwan sanyi ba tare da
kowa ya sani ba. Saboda na san wane ne Jamal yana, yana son mace wayayyiya. Wataƙila har
da hakan ya taka muhimmiyar rawa wurin nisanta ki da shi. Don haka ki bi matakan gyara kanki
ta hanyar da za ki farauto zuciyar mijinki daga matan banzan da ke ƙoƙarin janye miki shi.
Saboda ni uwa ce, kuma yadda ba na son abin da zai samu 'ya'yana haka ba na son abin da
duk zai same ki mara daɗi."
"Na gode Hajiya." Zancen Minal kenan cikin wata murya bayan Hajiya ta tsahirta da bayani.
Minal ta shiga share ƙwallar da ta wanke mata fuska cike da tausayin kanta ta ɗan muskuta ta
gyara zamanta sannan ta ce,
"Jikina yana ba ni koyaushe Nur za ta iya dawowa ga mijinta. Shi ya sa ba na son amfani da
komai a cikin kayan lefenta."
Kallon mamaki Hajiya ta dinga yi mata tsawon mintuna kafin ta ce, "Daga yau zancen A'isha
za ta dawo ga Jamal ya fita daga cikin zuciyarki. Saboda matuƙar ina numfashi ba zan taɓa bari
ya yi zaman aure da ita ba. Kaya kuma naki ne halak malak tun daga ranar da aka ɗaura
aurenki da Jamal. Don haka komai na lefen naki ne ki yi amfani da duk abin da kike so."
"To Hajiya."
Minal ta yi maganar tana ƙoƙarin share hawayenta, zuciyarta cike da farincikin jin tabbaci daga
bakin Hajiyar, bayan ƙwarin gwiwar da ta cusa wa zuciyarta ya faranta mata rai sosai.
A gabanta Hajiyar ta kira Jamal tare da sanar da shi ya haɗa kan lefen duka direbanta zai zo
ya karɓa. Sannan tana sauke wayar ta kalli Minal ta ce,
"In sha Allah gobe zan sa a kai ki wurin lalle da kitso. idan lokaci ya bayar har wurin masu
gyaran jiki duka za ki je a yi miki duk abin da ya dace. Saboda ina so ki yi amfani da wannan
damar ta zamanki cikin gidan nan ki ƙwato darajarki wurin mijinki."
"Na gode Hajiya. Allah Ya ƙara lafiya da nisan kwana."
Daga haka ta ce, "Ta shi ki je, kuma ki tabbatar kin saki jiki kin cire tunanin A'isha a cikin
ranki."
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.
DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta
nan 08022014771.
10 February zan sake shi da yardar Allah.
D. AUTA CE✍
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA TAKWAS.*
Minal ta fito daga ɗakin zuciyarta wasai tamkar an sauke mata wani ƙaton dutsen da ke
saman kanta. Ta kasa zama falon ta yi ɗakin Amna jikinta yana rawa ta danna wa Innarmu
fulashin. Saboda ta gwada kiran ta ji ashe babu ko ficika a cikin wayar.
Minti biyu tsakanin fulashin ɗin ta sai ga kiran Innarmu ya biyo baya. Da zumuɗi ta ɗauki wayar
tun kafin su gaisa ta ce,
"Innarmu Hajiya ta ce ko Nur ta dawo ba za ta bari Jamal ya aure ta ba. Kuma..."
"Ke wai ba ki da wani zance a duniya a yanzu sai na Aisha ne? Tsoron me kike ji bayan ke ce
da komai yanzu sai yadda kika ga dama za ki yi? To karkaɗe kunnuwanki ki ji; Aisha ko ni na
haife da cikina kika samu irin wannan damar ban ce ki yi wasa da ita ba. Ballantana wadda
daga ni har ke ba mu san haƙiƙanin danginta ba....ko kin taɓa ganin uwarta ko dangin Babanta
sun zo gidanmu?"
Minal ta yi hanzarin girgiza kanta tamkar tana gabanta suna kallon juna. Shirun da Innarmu ta ji
ta yi ya sa ta sake cewa, "To ki kiyaye ni Amina! Zancen Aisha ya fita daga bakinki, don ba uwar
mijinki ba ko ni nan ba zan taɓa bari ki yi kishi da Aisha a gidan aurenki ba. Saboda ita ce ta bar
ki shi da kanta babu wanda ya yi mata dole, kuma yanzu ba ta isa ta dawo ta ce za ta hargitsa
mana farinciki b..."
"Innarmu ina gidan su Jamal tun jiya Hajiya ta ce na dawo gabanta na zauna."
"Ki zauna kamar ya ya? Me kika je yi a gidan nasu har da kwana?"
Innarmu ta yi hanzarin yi mata tambayar cikin wata kalar murya alamun ranta ya ɓace kuma
ƙiris take jira ta dira kanta da masifa. Fahimtar hakan ya sa Minal ta sauya zancen da cewa,
"Tafiya ya yi shi ne ta ce na zauna kafin ya dawo."
"To..tooo..da sauƙi har na ji sanyi. Amma farko har hankalina ya tashi na ɗauka ko wani laifi
kika yi wa mijin ya ce ki bar masa gida kika koma can. Amma don dai tafiya Allah Ya tsare
hanya ya dawo lafiya ki koma gidanki ki ci gaba da bautar aure. Kuma wallahi kin ji na rantse ko
da wasa kada ki bari ki masa laifin da zai kawo ƙarar ki gidan nan! Kina gani ni ma haƙuri nake
yi da Babanku sama da shekaru na kafe sai mutuwa. Don haka ke ma babu fushi babu yaji
ballantana kawo ƙarar miji a gida. Duk tsanani ki zauna sai mun ga abin da ya ture wa buzu
naɗi har zuwa lokacin da ki ci moriyar haƙurinki. Amma a ce kina cikin wannan kafcecen gida
tsawon wata da kwanaki ko katin kira na ba ki mallaka ba, a ce ba ki da sai yi wa mutane
fulashi...?"
"Innarmu yau kaɗai ne fa!"
Ta yi maganar cikin wata murya tare da turo baki alamun ta ji haushin maganar. "Kin dai yi ko?
Kuma ko ba ki taɓa ba yau kin fara...ki dai kwantar da hankalinki daga mu har ke a gaba Za mu
ji daɗin auren nan. Burina ɗaya ne a yanzu ki samu ciki ki fara ajiye 'ya'ya a cikin gidan."
Minal ta yi hanzarin rufe bakinta cike da jin nauyin maganar tana 'yar dariya ta ce, "Cikin lafiya
Innarmu?"
"A'a cikin ciwo!"
Ta amsa mata a fusace sannan ta katse kiran. Minal ta sauke wayar daga kunnenta tare da
sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce,
"Innarmu-Innarmu! Ke komai sai kin mayar da shi faɗa...wai Allah wai ni ce zan yi ciki...ko ya
zan yi idan na samu cikin?"
Ta ƙare maganar tana shafa cikinta tana dariya saboda hango ta da ƙatoton ciki a gaba taku
da ƙyar tana tafiya. Ta jima a ɗakin kwance saman gadon Amna tana juya zancen Innarmu,
kuma zuciyarta cike da kewar Jamal da tunanin abin da ya yi mata kitchen. Nan take ta tsinci
kanta cikin shauƙi, kuma karo na farko kenan da ta ji a ranta tana sha'awar ya kasance ta.