Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
dafa mata ɗin kawai."
Ya yi maganar da murya biyu, ɗaya ta Zee cikin tattausa harshe. Yayin da ɗayar ta Minal ya
sauya ta zuwa kakkausa cikin tsare gida. Minal ta saki ƙofar ta fito tana taku a hankali daga ita
sai towel ɗin da ke jikinta iya cinya. Fuskarta babu babu fallasa ta nufi kitchen bom-bom suna
juyawa, kasanacewar Allah Ya albarkace ta da lafiyayyen ƙugu da cikar ƙirji daidai jikinta. Hakan
ya sa Jamal ya bi bayanta da kallo cike da mamakin ganin halittarta. Abin da ya saka shi kasa
ɗauke ido a kanta don bai taɓa hangen surarta a fili ba sai a ranar.
Zee ta fasa ihu saboda ita ma ganin halittar Minal ta raina tata halitta. Da rera waƙar kuka ta isa
gare shi ta faɗa jikinsa tana faɗin,
"Babe ni ba son indomin idan ba ta je ta saka kayanta ba."
"Ki bar ta a haka mene ne damuwarki?"
Ya Yi maganar cikin sanyin murya, saboda jikinsa ya mutu murus kuma ya shiga yanayin da
komai ya Zmzo masa a gaɓa.
"Warin hamata Babe, don Allah ka ce ta saka kayanta ni dai...uhum-uhumm Babe zan yi
kuk.."
Jamal ya miƙe ya nufi kitchen ɗin cikin wani yanayi, don shi ma yana buƙatar sake ido biyu
da Minal a yadda take. Zee ta bi shi da kallo tana kumbura fuska cike da mugun jin haushinsa.
Don kishin da take yi masa ya sa ba ta so kowa ya raɓe sa sai ita, hakan ya sa ta dunƙule tana
faɗin,
"Babe kada ka je ka dawo don Allah."
Ya juyo idonsa a lumshe ya yi mata wani kallo yana faɗin, "Ba kya so ta saka kayan ne?"
Zee ta sake magana cikin shagwaɓa ta ce, "Kawai ba na so ka gan ta ne Babe..plss ka zo ni
zan yi mata magana da kaina."
"Ok!"
Jamal ya yi maganar cikin murya ya dawo ya zauna yana shafa kansa ya rungumo ta jikinsa
cikin sabon yanayin da ya fara shiga jikinsa. Zee ta miƙe cikin sauri ta riƙo hannuwansa duka
biyu ta jawo shi ya miƙe. Sannan ta kwanta a ƙirjinsa tana faɗin,
"Ina son ka."
Kanta ya fara shafawa yana leƙen fuskarta ya ce, "Kin faye kishi, na faɗa miki ba matata ba ce,
kuma babu komai a tsakanina da ita. Yanzun ma don kin ce na je da ba zan so sake ganin
fuskarta b..."
"Ba fuskarta ne ba na so ka gani b..."
Ta yi maganar cikin sauri tana turo baki, shi ma ya katse ta da cewa, "To mene ne?" Ya yi
tambayar yana hango bombom ɗin Minal a cikin idonsa.
"Bar Shi kawai tun da ba ka ga komai ba. Zo mu je ɗakinka na ma fasa Cmcin komai."
Ta ƙare maganar tana jan shi yana 'yar dariya ya bi ta suka shige ɗakin. Minal kam tsam ta yi
da ranta tana kallon indomin da ke tafasa siraci yana fita a cikin tuunyar ƙamshi yana tashi.
Rungume da hannuwa a ƙirji take tana cizon leɓenta, saboda duk abin da suka faɗa a kunnenta
tana ji. Hakan ya saka ta ƙara samun wani sabon darasin da ba a koya mata a gida ko
makaranta ba.
Da murmushi a fuskarta ta nemo plate ta juye indomin ta rufe da wani plate tare da cokali mai
yatsu a sama, bayan ta soya mata faifai ɗaya na wainar ƙwai ƙwara biyu. Zuciyarta wasai ta fito
daga kitchen ɗin ta ajiye musu indomin saman dinning table. Sautinsu da ke tashi daga cikin
ɗakinsa ya saka ta jin bugun zuciya, cikin sauri ta koma ɗakinta hawaye yana zarya a kan
fuskarta.
Ta ci kuka daren ranar kamar hawayenta ba za su kai safiya ba. Sannan ta kwana tana faɗa
wa Allah damuwarta da abin da take buƙata a wurin sa. Ruwan addu'o'in da ta zuba ta samu
ƙarfin gwiwar ƙarfafa kanta da zuciyarta a kan cewa Allah ya karɓa mata su duka. Baccin da ya
ƙi zuwa idanuwanta ma tana tuno ɗaya daga cikin ilmukan da Gwaggo Salame take ba ta tana
yi ta samu nannayan barci mai daɗi.
'A duk lokacin da bacci ya ƙaurace wa idonki; ki karanta suratul Falaƙ uku, Nas uku da
ƙulhuwallahu Ahad ita ma sau uku. Da yardar Allah ba za ki kammala su ba ki fara jin barci ba.
Wannan wani sirri ne da na riƙe ina aiwatarwa a duk lokacin da damuwa ta aure ni. Ke ma ki
riƙe duk tsananin damuwa matuƙar kika yi a yadda na sanar da ke za ki yi barci har da
minshari.'
"Tabbas na ga amfanin hakan gwaggo. Don ba don na yi ba da ba na jin takaicin abin da na
gani da wanda nake ji da kunnena yana faruwa su bar ni na runtsa."
Furucin Minal kenan a lokacin da ta farka sallar asuba. Domin kamar da gayya tana farkawa
zuciyarta ta hango mata Jamal da Zee rungume da juna. Ta jima bakin gadon zaune ɗauke da
tagumi tana nazari kafin ta miƙe ta yi sallah. A nan ma ta kai kukanta ga Allah kuma ta yi
laziminta tsaf tare Ya wadudu ƙafa arba'in. Sannan ta tashi cikin kuzari ta shiga gyaran ɗakinta
har zuwa falo, bayan ta gama ta koma ta kwanta da carbi a hannunta tana ja wani sabon barcin
ya kwashe ta.
Misalin ƙarfe tara na safiya ƙwanƙwasar ƙofa ya tayar da ita. Cikin sauri ta sauko gadon tana
ƙarfafa zuciyarta a kan haƙuri har ta buɗe ɗakin. Ido cikin ido suka kalli juna kafin ya shiga
shafa kansa cikin haɗe rai ya ce,
"Baƙuwata tana jiran breakfast. Ta ce indomin jiya ta yi mata daɗi yanzu ma abincinki take son
ci."
Cike da jarumta Minal ta gayyato murmushin ƙarfin hali ta ce, "Ayya! Ka ce ta jira ni kaɗan
zan yi wanka na fito."
Ta ƙare maganar har da 'yar dariya tamkar babu komai a cikin ranta. Jamal ya yi tsayar da
kallonsa a tsakiyar idanuwanta cike da mamaki, yana so ya yi wata magana amma ya kasa.
Saboda girar da Minal ta ɗaga masa tare faɗin,
"Ummm!" Alamun tabbatarwa ga zancenta. Ya juya yana waigen ta ba tare da ta sake cewa
komai ba ta juya ko rufe ɗakin ta kasa yi. Sai da ta sha kukanta a toilet sannan ta yi wankan a
gurguje ta fito.
'Za ku ga tsiya.'
Abin da ta furta kenan a lokacin da ta shiga buɗe kayan lefen Nur tana zaɓen wasu ƙananun
kaya cikin sauri. Can ta hango wani mini siket baƙi iya gwiwa da wata jar riga half vest, wadda
ake ɗaure ta gaba a saki jelar a saman ciki. Cikin sauri ta shirya a cikin kayan babu shiri dariya
ta ƙwace mata. Musamman a lokacin da ta ga kanta jikin madubi tamkar wata Ingozi, duk da
kayan sun hau jikinta ta yi mugun kyau. Saboda tun da take a duniya ba ta taɓa shiga irin
wannan ba. Asali ma ƙananun kaya ba su taɓa burge ta ba. Ko kayan lefen da aka kawo wa
Nur duk ta ɗaga kayan sai dariya ta zo mata a ranar da aka kawo lefen. Saboda tunanin ta ya
ya ita za ta iya saka su a jikinta, don har kullum tana jinjina wa Nur a kan yadda ba ta jin nauyin
shiga duk yadda ta ga dama, kuma ko a gaban waye ita babu ruwanta da ɓoye jikinta. Saɓanin
ita Minal da ba ta saba da hakan ba, kuma ba ta tashi ta ga ana yi a cikin unguwarsu ma
ballantana a gidansu. Har ganin take yi babu ranar da za ta iya shigar 'yan bariki a cewarta
koyaushe.
"Ashe akwai ranar."
Zancen da ta yi kenan tana juya jikinta gaban madubin bayan ta saka wata hula mai kama da
pesin cap mahaɗin siket ɗin. Ƙwanƙwasa mata ƙofar da aka sake yi ta yi hanzarin fesa turaren
Nur a jikinta har saman hula, sannan ta maƙala passion ɗin ɗan kunne ja da baƙin agogo a
tsintsiyar hannunta. Ta nufi ƙofar da sassarfa ta buɗe fuskarta a sake tamkar wadda ke cikin
matsanancin farinciki.
"Babe!"
Zee ta ƙwala wa Jamal kira saboda ganin Minal a yadda take ba ƙaramin firgita ta yi ba. A ruɗe
ya iso wurin yana ƙoƙarin tambayar lafiya ta faɗa jikinsa tana dukan ƙirjinsa a haukace tana
faɗin,
"Zan mutu Babe idan ina ganin matar nan."
Haka ta dinga ɓarin sambatun da Jamal bai ma san tana yi ba, saboda hankalinsa da
tunaninsa gabaɗaya suna kan Minal. Tsabar mamaki da tashin hankalin da ya Yi masa dirar
mikiya a saman ka. Saboda ƙamshin turaren Nur da Minal ta saka zuciyarsa ta shiga birbration.
Nan take ya tsinci kansa a cikin wani yanayi mara misali, don Minal ba ta bar shi da iya turaren
da shigar ba, sai da ta haɗa masa da kanne ido ɗaya tare da fari da ido tana cizon leɓenta kafin
ta koma yi masa wani kallon ƙasan ido tana jingine jikin ƙofar rungume da hannuwanta a ƙirji.
Da ma ta ga halin da yake ciki ta ƙara masa da juyi a gabansa tamkar tarwaɗa, tana shafa
jikinta da lasar baki cike da ƙwarewa a kan zama gogaggiyar 'yar duniya.
Ƙaƙƙarfan dukan da Zee ta kai masa a ƙirji hannuwa biyu ta tura shi, hakan ya saka shi yin
baya ya faɗi ƙasa daɓas babu shiri. Amma hakan bai saka shi ɗauke kallon sa a kan Minal ba,
tamkar wani sakarai ya saka hannu ya janye Zee da ke gabansa tana masifa, tsabar kishi ya
saka ta ƙaramar hauka.
Miƙewa ya Yi jikinsa yana rawa ya isa gaban Minal yana muzurai tare da saita kansa cikin
ƙarfin hali ya ce,
"Je ki sauya kayan jikinki ba na buƙatar sake ganin ki da su."
Sai a lokacin Zee ta daina surutai da kukan da ta ja gefe tana yi. Saboda jin daɗin zai rama
mata wulaƙanci da cin zarafin da Minal take son yi mata a fakaice. Don surar jikinta ko ita da
take mace ta ƙyasa ballantana shi a matsayinsa na namiji mabuƙaci.
Minal ko wani kallon 'yan duniya ta yi masa tana 'yar dariya ta ɗaga hannu sama alamun sara
masa ta ce, "Ok sir!" Sannan ta juya ta shige ɗaki .
Sai a lokacin Zee ta samu kuzarin zuwa inda yake ta faɗa jikinsa tana rera waƙoƙin kuka
kala-kala. Ya ja ta jikinta ya rungume tsantsan sannan ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya mai
sauti. Haƙuri ya shiga ba ta bayan sun isa kan kujera sun zauna, tare da yi mata alƙawarin ba
zai taɓa son Minal ba.
Mintuna a tsakani bayan Jamal ya shawo kan Zee ta daina kukan tana masa shagwaɓa Minal
ta fito cikin wata sabuwar shigar ƙananun kayan. Inda ta saka riga mai hannun best iya cibiya
da dogon wandon da ya ƙara fitar da halittar jikinta, don ko bra cirewa ta yi ta bar kan nipples
ɗin ta suna maraba da mai kallo. Sannan ta saka wata kwantacciyar hula kamar ta 'yansanda ta
saki jelar kitson burazil da ƙanwarta ta yi mata a gida, wanda ya saje da gashin kanta kuma ya
sauka gadon bayanta yayin da ta zubo wasu a gaban fuskarta. Da takalmi mai mugun tsini a
ƙafarta ta fara taku cikin nutsuwa har ta iso gabansu. Sannan ta shiga fareti tana juyawa tare
da buga ƙafa bombom da ƙirjinta suna ta aikinsu na rangaji.
Ganin abin da take yi ya ja hankalin Jamal Zee ta fashe da wani sabon kuka tana kai masa
duka tare da kiran sunansa. Minal kam ko kaɗan hargowar Zee ba ta saka ta daina abin da take
yi ba, sai da ta gama iya juyin da take so sannan ta ƙame ƙam a gabansu ta ƙara sara wa
Jamal ta ce,
"Me za a dafa mata 'yar laɓai?"
Takun ƙaniya
*SANARWAR!*
*INA SO KU NUNA MINI KARA RIN WADDA ZAN TABBATAR KUNA JIN DAƊIN BIYA TA A
CIKIN LITTAFIN FANSAR ƘAUNA. MUTUM 50 KACAL NAKE SO MASU SAYEN lLITTAFIN
DAKAN ƊAKA.. COMPLETE BOOK 1-2 PRIZE 1K GA MAI BUƘATA YA TURO KUƊINSA TA
NAN; 9032685442 OPAY. SHAIDAR BIYA TA NAN 08022014771. ZAN SAKE SHI A RANAR 3
GA WATAN FEBRUARY. LABARI NE MAI ƊAUKE DA RIKICI, HARGITSI, TASHIN HANKALIN
DA RIKITA-RIKITA BAYAN ZALLAR TSAGWARON SOYAYYA MAI ABIN MAMAKI. NI CE DAI
MARUBUCIYAR ABOKIN AIKINA. KUN SAN KALAR ALƘALAMINA BA NA RUBUTA ABIN DA
BA ZAI DAMƘO ZUCIYA BA*
*SAURA KWANA HUƊU KACAL YA RAGE GA MASU BUƘATAR SHIGA CIKIN WANNAN
TSARI. GA WAƊANDA SUKA SAYA SUNA DA KYAUTAR LITTAFAINA BIYU. RUWA DA
ƘANƘARA DA BAKAN GIZO.*
SAI KUN ZO.
D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA BIYAR.*
Ƙaƙƙarfan tsaki Zee ta ja sannan ta zame daga jikin Jamal ta miƙe a fusace ta nufi ɗakinsa,
tana goge hawayen da ke malala a kan fuskarta.
Kallo Jamal ya bi ta da shi, hakan ya sa Minal da ke tsaye gabansa rungume da hannu ta ce,
"Ka tambayo ta mu ji abin da take so na je na dafa mata lokacin breakfast yana ta ƙurewa.
Ina so na gama da wuri sai na ɗora mata girkin rana kafin na dare ya zo shi ma."
Wani sakaran kallo Jamal ya bi ta da shi cike da mamakin da ta ƙara jefa shi a ciki. A gefe
ɗaya kuma kukan Zee yana shiga kunnuwansa, gabaɗaya zuciyarsa ta hautsine. Zumbur ya
miƙe ba tare da ya tsaya ba ta amsa ba, cikin sauri ya nufi ƙofar ɗakinsa saboda hango Zee da
jakar kayanta tana ƙoƙarin fitowa daga ciki.
"Ina za ki je kuma? Ba sati ɗaya za ki yi mini ba?"
Ya furta maganar bakinsa yana rawa tsabar ya gama ruɗewa, kuma yana hangen Minal ta
lalata masa duk wani tsari.
"Ba zan iya zaman b...zuciyata za ta iya fashew.."
Ta yi maganar tana murza idanuwanta cikin shesshekan kukan da ta yi har idanuwanta suka
sauya. Cikin sanyin jiki ya isa daf da ita ya riƙo jakarta yana faɗin,
"Ki yi haƙuri zan ɗauki mataki a kan duk abin da ta aikata miki. Amma ki sani babu inda za ki
je har sai kin gama mini kwanakin da muka tsar...."
"Tun farko ban san da wata a cikin gidan ba da ban yarda na amince da zuwan ba. Amma tun
da idanuwana sun ga komai ba zan yarda a fasa mini zuciyata a banza ba...sakar mini jaka ni
ba zan zauna ba.."
Ta ƙare maganar tare da fisge jakarta ta yi gaba. Ya bi bayanta yana magiyar ta yi haƙuri ta
zauna har suna ƙoƙarin ficewa daga falon, daidai lokacin da suka ji Minal tana faɗin,
" Ke! Hajiya kwartuwa, ga shi har za ki tafi ba ki faɗa mini abin da zan girka miki ba."
Daga Zee har Jamal kallon mamaki suka bi ta da shi, saboda sunan da ta kira kuma ta bi da
zance kamar wadda ta yi abin arziƙi. Babu shiri Zee ta ƙara fashewa da wani sabon kuka tana
nuna ta tare da kallon Jamal ta sake cewa,
"Babe, kana jin me take faɗa kuma ba ka ɗauki matakin komai b...to na rantse da Allah ni
kuma ba zan ƙyale ta b..."
Ta yi maganar cikin hargowa tare da sakin jakar ta nufi kitchen da gudu tamkar wata
mahaukaciya. Minal da ke tsakiyar falon a tsaye rungume da hannuwa a ƙirji, babu shiri ta fashe
da wata mahaukaciyar dariya. Saboda kalar gudun da Zee ta yi ga ta ɗunɗumemiya kamar ta
kifa ta faɗa zuwa kitchen. Hakan ya saka Minal dariya sannan da farincikin Zee ta ji haushin
sunan da ta kira ta da shi. Ta ƙara sakaws ranta kaɗan ta gani kuma sai ta koya mata hankali.
Zee da ke kitchen kamar wata mahaukaciya ta shiga neman wuƙa ta dinga ɓarin kaya, amma
duk neman ta ba ta samu ko ɗaya ba. Saboda tun lokacin da Jamal ya kwashe su ya ɓoye a
ɗakinsa bai dawo da ko ɗaya ba. Ita ma Minal da dubara take amfani da cokali mai yatsu har ta
yanka abin da take so. Ganin babu wuƙar da gaske kuma neman zai ɓata mata lokaci, ta fisgo cakali mai yatsu ta
fito a haukace tana ƙoƙarin isa kan Minal idonta rufe. Cikin sauri Jamal ya sha gabanta tare da
riƙe ta yana ƙoƙarin hana ta abin da zuciya ke ingiza ta, ita kuma tana ƙoƙarin kufce wa riƙonsa
don ta yi kan Minal da nufin ƙaddamar mata, ta huta da