Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   3 / 26

6K to 9K   out of 77.3K words

kuma ki riƙe sirrin mijink..."

Kiran da Innarmu ta sake bugo mata ya sa ta fice da sassarfa ta bar Minal a daskare bakin
gadon, don ta kasa motsa laɓɓanta ta yi mata sai anjima ballantana ta raka ta. Bayan idon da ta
bi ƙofa da kallo tsawon mintuna da fitarta ba tare da ta ɗauke kanta ba.

***
Jamal kuwa, tun da ya fice daga ɗakin bayan ya gama jaddada wa Hajiya ba ya son Minal.
Cikin ƙunar rai ya buga motarsa jikinsa yana rawa ya nufi gidansu. Sai dai kuma Allah ne ya kai
shi gida lafiya, saboda mahaukacin gudun da yake yi tamkar an koro shi ko kaɗan ba ya cikin
nutsuwarsa. Uban horn ɗin da ya dinga bugawa babu ƙaƙƙautawa; ya sa Baba maigadin
gidansu ruɗewa jikinsa yana rawa ya buɗe gidan bayan ya tabbatar shi ne ba gizo ya yi masa
ba. Amma zuciyarsa cike da mamakin dawowarsa cikin gidan a daidai lokacin, wanda ya dace a
ce yana tare da amaryarsa a matsayinsa na sabon ango mai zumuɗi da daren farkonsa.
Da ido Baban ya bi shi baki buɗe har Jamal ya shige sashen da ɗaƙinsa yake ba tare da ya
bi ta kan motar da ya bari a kunne ba, ballantana ya rufe murfi bayan fitarsa. Saboda
idanuwansa ko gani ba sa yi daidai ya faɗa ɗakinsa ya datse ƙofa, a sukwane ya isa bayi ya
dinga zuba wa kansa ruwan shawa ba tare da ya cire komai na jikinsa ba. Ya ɗauki tsawon minti
talatin idanuwansa rufe ba tare da ya yi dogon motsi ba. Zuciyarsa danƙare da ƙuncin da yake
haddasa mata bugawa da ƙarfi tamkar ta ɓalle daga mazauninta ta fito ƙirjinsa.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi, kafin ya fara atishawa wata bayan wata
kuma har lokacin ruwan yana sauka kansa zuwa jikinsa. Da lalube ya rufe shawar amma ya
kasa ɗagawa daga wurin tsawon mintuna. Saboda zuciyarsa ta ci gaba da hasko masa fuskar
Nur tana feshin tsadadden murmushinta har dimple ɗin ta biyu suna lotsawa. Hoton zuciyarsa
ya hasko masa ita ne a wani lokacin da suka je yawon shaƙatawa, inda ya ba ta cake a baki

tana tauna tana yi masa wani kalar kallon da ya saukar masa da kasala.

"Ya Allah!"

Furucinsa kenan a lokacin da kansa ya ƙara sarawa tamkar an kwaɗa masa guduma. Dafe da
kan ya fito yana layi saboda jirin da ke kwasar sa har ya zube kan gado riƙe da kansa yana
faɗar kalmar Innalillahi fili da zuciyarsa. Nan take ya fara rawar sanyi jikinsa ya hau fisga babu
ƙaƙƙautawa, cikin mintuna kaɗan numfashinsa ya fara sarƙewa, kafin ya yi luf bayan ya gama
tari sama-sama yana dafe da zuciyarsa, saboda idauwansa sun gama kafewa numfashinsa ya
tsaya cak.

Ya kwashe tsawon lokaci a halin da yake ciki kafin dawowar Hajiya, bayan ta gama neman sa
a waya ba ta samu ba. Kuma maigadin gidansa ya tabbatar mata da lalle ya fita. Cikin tashin
hankali ta kira maigadinsu sannan ta samu nutsuwar faɗawa mota direban da ya kawo ta ya
juya da su zuwa gida. Saboda jin Jamal yana gidan ya rage mata kaso bakwai a cikin goman
tashin hankalin da ta afka. Don zuciyarta ta gama tsinkewa cike da tsoron faruwar abubuwa
biyu, na farko kada ɓacin rai ya saka shi barin garin ba tare da ta sani ba. Na biyu tsoron kada
ya yi tsautsayi ya ja shi ya yi haɗari, don a halin da yake ciki bai dace ya yi tuƙi ba.
Makullin motarsa da maigadinsu ya ba ta tare da yi mata bayanin yanayin da ya shigo gidan;
jikinta ya yi sanyi ƙalau, amma hakan bai hana ta isa ƙofar ɗakinsa da sassarfa ba. Amna biye
da ita a cikin firgicin suka shiga bugun ƙofarsa tare da kiran sunansa a lokaci ɗaya. Ganin babu
motsinsa ballantana alamun zai buɗe ƙofar, ga tagoginsa duka a rufe. Hakan ya sa Hajiya ta sa
Baba maigadi ya ɓalle ƙofar iya ƙarfinsa.

Hajiya Mummy da Amna ihu mai ƙarfi suka fasa yayin da suka yi ido biyu da Jamal a kan
gado. Baba maigadi ya hau salati saboda alamunsa ya nuna babu numfashi a tattare da shi.
Hajiya Mummy ta faɗi ƙasa tana kuka bakinta ɗauke da kalolin salati saboda idanuwanta sun
gama tabbatar mata da Jamal ya jima da barin duniya. Amna kuma jikinsa ta haye tana ihu tare
da faman jijjigarsa a kan ya tashi cikin ƙaraji da zaucewa, bayan kururuwar da take yi a kan don
Allah a kawo musu agaji.




Hmmm!�




D. AUTA CE✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*Masu neman littafaina akwai free akwai na kuɗi sai wanda kuke so.*
*ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI.*
*JIKI DA JINI (A'ISHA), AMFANIN FITILA.* *MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA.*
*RUWA DA ƘANƘARA, GIDAN AURE.* *BAKAN GIZO, ZUBAR HAWAYENA.*
*DAKAN ƊAKA.., MUSAYAR ZUCIYA.* *TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran su.'Yan
kasuwa masu neman a tallata musu hajarsu ƙofa a buɗe take. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni ta
wannan lambar; 08022014771.*


*LAMBA TA HUƊU.*

"Ba..ba..bai mutu ba!"

Zancen direban Hajiya kenan a lokacin da ya taɓa gefen idon Jamal, waton tsakanin ƙwayar
idonsa da kunnensa, inda ya danne wurin ya ji jijiyarsa tana harbawa ɓal-ɓal. Hakan ya sa
gumin tashin hankali karyo masa ya yi maganar a rikice bakinsa yana rawa. Shi ma Baba
maigadin yana taɓa wurin ya yi gaggawar nanata zancen cike da jaddadawa ya ce,
"Da sauran numfashinsa Hajiya! A gaggauta kai shi asibit..."

Kallon da Hajiyar ke yi wa Jamal ya ƙara tabbatar mata da gaske ne. Saboda kallon da take yi
musu ya nuna zuciyarta ta gama sarewa a kan sun yi rashin Jamal, rashi na har abada. Amma
maganar Baban bayan direban ya gano da sauran ransa sa; sun ƙarfafa mata gwiwa matuƙa,
duk a ranta ba ta gasgata abin da suka faɗa ba gaskiya ne ba, duba da abin da idanuwanta
suka ganar mata zahiri.

Zumbur ta zabura saboda ganin Baban da direban kowa yana bakin ƙoƙarinsa a kan farfaɗo
da shi. Cikin sa'a numfashinsa ya dawo, ya yi wani irin ƙugi sannan ya fara tari ɗaya bayan
ɗaya a hankali.
Jikinsu yana rawa suka yi gaggawar saka shi mota, direba ya fice aguje Baba da sauran
baƙin 'yan bikin da suka hankalta da abin da ya faru; suka bi su da addu'ar nasara har suka isa
wata asibiti mafi kusa da gidan. Daga Hajiya mummy har direbanta a tsaye suka kwana tamkar
haƙori. Sai faman zarya suke yi a baranda, tsakanin ɗakin bayar da agajin gaggawar da aka
kwantar da Jamal ɗin, zuwa kujerun da suka zauna suna dakon fitowar likitan da ke ƙoƙarin
ceto rayuwarsa. Bacci ko kaɗan bai zo idanuwansu ba tun daga daren har aka yi sallar asuba.
Tsabar tashin hankalin da suka shiga baccin da kansa ya kori kansa a cikin idanuwansu. Har
gara Amna ta ɗan runtsa a lokacin da hajiya ta matsa mata ta yi baccinta saboda ganin tana
zuba hamma wata bayan wata da tangaɗi tamkar 'yar maye. Safayar gadon maralafiya aka kai
ta daga gyangyaɗi ta ɗan kishingiɗa sai nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.

Bayan an kammala sallar asuba a cikin masallacin da ke asibitin; Likitan da ya tsayu a kan
Jamal ya kira Hajiya zuwa ofishinsa. A gurguje ta shafa addu'ar neman lafiya ga Jamal hawaye

yana fareti a kan fuskarta ta bi shi cikin sassarfa tamkar ta kifa. Amma idanuwanta a kan ɗakin
ceton gaggawar zuciyarta cike da ƙosawa a kan tsaikon zuwa ganin Jamal da likitan ya yi musu.
Saboda tun fitowarsa daga ɗakin ta isa gabansa tana jera masa tambayoyi a kan ya faɗa mata
a wane hali Jamal ɗin yake ciki, har da magiya tana hawayen ya bar ta shiga ɗakin ta yi masa
ganin bankwana. Amma fafur ya ƙi barin ta gan sa, ya ce ta je ta yi sallah idan aka kammala
komai za su yi magana. A haka ya bar ta tsaye fuskarsa babu yabo babu fallasa ya wuce ya bar
ta da fargaba, saboda ta kasa tantance halin da Jamal yake ciki daga yanayin fuskar likitan.

Shiru ya ratsa a cikin ofishin, bayan Hajiya ta samu wuri ta zauna ƙirjinta yana bugawa. Sai
da likitan ya gama 'yan rubuce-rubucensa biro a hannunsa yana jujjuya shi sannan ya yi
magana.

"Hajiya mene ne damuwar yaronki?" Bai tsaya jiran amsarta ba ya ɗora da cewa,

"A binciken da na yi masa, na gano yana ɗauke da ciwon kai na damuwa, wanda a likitance
muna kiran sa da Tention Headed."

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"

Hajiya ta yi hanzarin yin salati tare da ɗora hannuwanta a ka bayan ta miƙe daga kan kujerar
jikinta yana kyarma. Cikin fuskar tausayi likitan ya yi magana cikin sauri ya ce,

"Ba wani ciwo ba ne ki kwantar da hankalinki. Saboda a yanzu bai zama matsalar da za ta iya
jawo masa manyan cutukan da suka danganci ciwon ba. Sannan abu mai sauƙi ne a shawo kan
ciwon matuƙar aka bi shawarar likitoc..."

"A ba mu maganin ciwon kawai likita, wanda idan ya sha zai warke nan take."

Furucin Hajiyar kenan bayan ta koma zaune kamar yadda ya yi mata nuni da hannunsa, tana
haɗa gumi tare da haɗiye wani dunƙulallen yawun da ya tsaya a maƙogwaronta. Murmushin
ƙarfafa gwiwa likitan ya yi kafin ya sake cewa,

"Magana ta gaskiya babu maganin ciwonsa a hannunmu Hajiya..."

"To ai ka faɗa mana inda za mu samo masa maganin..."

"Ki nutsu Hajiya a hankali zan warware miki komai. Saboda maganin ciwonsa yana hannunsa
idan ya so zai wartsake a cikin kwanaki kaɗan har ma ya rabu da ciwon gabaɗaya."

Hajiya ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da sake jefa masa wata tambayar, "Ta ya ya zai
warkar da kansa a irin mawuyacin halin da yake ciki, bayan ko inda kansa yake a bai sani ba?
Kai-tsaye ya ba ta amsa da cewa,

"Ta hanyar sanya haƙuri a kan abin da yake damun sa, sannan ya mayar da lamuransa ga
Allah. Da cusa wa ransa komai zai wuce idan aka mayar da shi ba komai ba."

"Alhamdulillah!"

Hajiya ta furta hamdalar tare da ɗaga hannu ta shafa saman fuskarta. Likitan ya yi 'yar dariya
sannan ya sake gyara zamansa yana cewa,

"Inda matsalar take idan ya ƙi bin abubuwan nan da na lissafo..."

"Ba ma za a samu matsala ba."

Ta yi hanzarin faɗar maganar tana wara hijabinta tare da ƙara naɗe shi cikin jikinta. Likitan ya ci
gaba da bayaninsa, wanda kusan shi ne gundarin abin da yake son faɗa tana shan gabansa da
zance.

"Ciwon zai iya tashi har ma ya faɗaɗa idan ya kasa saka wa zuciyarsa haƙuri da dangana a
kan ko ma mene ne yake damun sa. Kuma idan ya dawo zai iya haddasa masa cutar bugun
zuciya, wanda nan take zuciyarsa za ta iya bugawa ya yi mutuwar fuji'a."

Hannuwan da ta ɗora a ka tana salati bai hana shi ci gaba da bayaninsa ba tiryan-tiryan ba.
"Ko kuma jijiyar ƙwaƙwalwarsa ta tsinke ya samu cutar shanyewar ɓarin jiki da sauran
cututtukan da ba a fata. Don haka tun kafin a je fagen da ba a so ya taimaki kansa ya rabu da
ciwon tun yana ƙarami kafin ya kai babban mataki."

Shiru Hajiya ta yi saboda luguden uku-ukun da ƙirjinta yake yi, idanuwanta a kan likitan ta
kasa daina kallon sa kuma ta kasa furta ko kalma ɗaya daga bakinta.

"Na san zancen ba zai yi miki daɗi ba, amma ki yi haƙuri, sanar da ku dole ne saboda ku taro
kan matsalar tun tana farko kafin ta yi nisan da abin zai damu kowa. Sannan na sanar da ke ne
a matsayinki na uwa ko akwai wata gudunmawar da za ki iya bayarwa wurin ceton lafiyarsa da
ransa gabaɗaya. Shi ma idan muka samu ya warware za mu zauna da shi mu yi masa irin
bayanin da na yi miki saboda fitar haƙƙi. Da ma aikinmu shi ne gano cuta da neman hanyar
waraka. Kuma idan an bi ƙa'idojin asibiti sau da ƙafa za a dace da yardar Allah."

"Hmmmmm! To Ubangiji ya shiga cikin lamarinsa da namu bakiɗaya. Kuma in sha Allahu
zuciyar Jamal ba za ta buga ba, kuma zai rabu da ciwon lafiya ya ci gaba da rayuwarsa kamar
kowa."

Ta miƙe har za ta fice ranta a jagule ta waigo, tana tambayarsa za ta iya ganin sa a daidai
lokacin. Likitan ya nufi hanyar fita ofishin yana cewa ta biyo shi.
Jugum Hajiya Mama ta yi a lokacin da ta yi ido biyu da Jamal, saboda likitan ya yi mata jagora
har gaban gadonsa, cike da sharaɗin kada ta yi dogon motsin da zai damar da marasa lafiyarsu

da ke cikin ɗakin. Hawaye ta shiga sharewa da gefen hijabinta, saboda ganin yadda ya rame a
dare ɗaya tamkar wanda ya yi kwanaki yana jinya. A ranta tana tuno kalaman likitan da suka
gama tsinke mata jijiyon jiki da na zuciya.

Ƙarfen gadon ta riƙe daidai kansa tana tofa masa addu'o'i tana hawaye, kafin likitan ya gama
zagayen marasa lafiyar da yake dubawa. Fahimtar ta shiga yanayi mara daɗi ya dawo kanta da
kalaman kwantar da hankali a kan Jamal zai farfaɗo cikin lafiyarsa da sabon kuzari. Da ma
ƙarin ruruwar wutar ciwon nasa har da zazzafan zazzaɓi. Don haka ta kwantar da hankalinta
babu abin da zai sake samun sa.
Hakan ya ƙara mata juriya ta fito daga ɗakin zuciyarta cike da gamsuwa da maganganun
likitan. Kiciɓis ta yi da Amna a bakin ƙofar shiga a hargitse, raɓa gefenta ta yi ta faɗa tana wara
idanuwanta a kan gadajen masu jinyar da ke jere har ta hango shi a kan gadon ƙarshe.
Bakin gadon ta ja ta tsaya tana rufe bakinta saboda sabon kukan da ya zo mata babu shiri.
Hannunsa ta yi hanzarin kamawa ta ɗora kanta a saman hannun tana kuka mai sauti cike da
tausayin sa a ranta. Sanyin hawayenta da ya ji a hannunsa ya ɗan motsa tare da buɗe
idanuwansa kaɗan, sannan sake rufewa tare hanzarin dafe kansa yana faɗin,
"Nur, ki matso kusa da ni."

Amna ta saki hannunsa tana murmushin farinciki hawaye yana zuba a kan fuskarta ta ce,

"Auncle J Amna ce.."

Juyo kansa ya yi saiti da fuskarta yana kallon ta kamar zai yi magana kuma ya ja bakinsa ya yi
shiru bai ce komai ba. Amna ta fice da sassarfa cike da jin daɗi ta sanar da Hajiya ta zo ya
tashi. Tare suka dawo har direbanta suna murnar ganin sa a raye kuma ya farfaɗo a cikin
hayyacinsa. Da ido kawai yake bin su ɗaya bayan ɗaya kafin ya yi ƙarfin halin furta abin da ke
cizon ransa.

"Hajiya, har yanzu Nur ba ta dawo ba ko?"





Uhum





D. AUTA CE✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA IBRAHIM D. AUTA*

*LAMBA TA BIYAR.*

Shiru Hajiya mummy ta yi masa, saboda babu wata amsar da za ta iya ba shi a daidai
lokacin. Hakan ya sa ta kawar da kanta gefe kawai tana share hawayen da ke bin fuskarta,
zuciyarta cike takaicin abin da ya faru, wanda ya yi silar ciwon da ke barazana ga lafiyarsa.
Amna ta matsa jikin gadon tare da dafa hannunsa ta yi magana cikin sigar rarrashi ta ce
masa,
"Ka yi hakuri Uncle J, ni na sani Nur za ta dawo maka, saboda ita ma tana son ka. Kuma
abu ne wanda kowa ya san da hakan ba za ta iya rayuwar da babu kai a cikin ta ba. Don haka
don Allah ka taimake mu ka taimaki rayuwarka Uncle J, ka kuma ƙarfafa kanka da zuciyarka ka
yi ƙoƙarin cire damuwar komai a ranka Allah yana sane da komai da ya far..."
"Laifin me na yi mata za ta guje ni?"

Ya wurgo mata tambayar cikin sauri saboda ya kasa shanye takaicin, kuma tambayar da ke
ransa kenan tana yawo a ƙwaƙwalwarsa.

"Ka bar zancen nan Jamal. Za a yi shi daga baya idan ka samu lafiyarka."

Maganar Hajiya kenan cikin kakkausar murya, duk da take ƙoƙarin danne da abin da ke cikin
zuciyarta. Saboda ko kaɗan ba ta fatar ta yi asararsa kamar yadda likita ya yi mata mummunan
albishir. Daga hakan Jamal bai sake cewa komai ba, sai kawar da kansa da ya yi gefe tare da
runtse ido ƙirjinsa yana bugawa da sauri da sauri. Bacci mai nauyi ya ɗauke sa,

3 / 26