Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   5 / 51

12K to 15K   out of 151.9K words

Allah kawai yake a san yadda za a yi a kai innar tasu asibiti, dan jikin nata ya tsorata kowa!
Babba da Yaro.

Suna fita Manubiya ta mi?e ta cire hijabin Jikinta.
Daga haka ta ?arasa inda su Innar su ke, (ita da jidda).
Sai da ta tabbatar innar bacci ta ke yi tukunna ta kalli Jiddan ta ce
  Mai ya faru Wazu da kika je gidan?
kin gan shi?  .

A hankali Jidda ta share hawayen da su ka zubo mata.

Kafin ta shiga koro mata bayanin
yadda su ka yi& .
Da yadda Ya Musbah ya ce kawai ta zo gida, su jira shi.
Gashi kuma har yanzun bai zo ba.

Shiruuuuu, duk su biyun su ka yi!
Ko wacce zuciyarta babu daWi.
Suna kuma tunanin a ina za su je su samo kuWi!
Dan sun san tunda Ya Musbah ya fara wasar ?ar Suya da su
tou shima bashi da yadda zai yi ne.
A take zuciyar Manubiya ta fara bata shawarar ta cire kunya kawai ta gayawa Abbakar gaskiya, ta san zai taimake su.
& & &
A ?ofar gidansa su Baba su ka hango shi.
Kamar wani saurayi haka yanayi da jikinsa ya ke, sam bai yi kama da magidanci ba.
Fari ne sol kyakkyawan gaske, bai cika tsayi ba amman yana da faWin ?ashi.
Cikin sanyin jiki Baba da Muhsin su ka ?arasa inda Ya Musbahn ya ke
alwallar sallar Maghrib Win da ta gabato, shi da wani ma?wafci kuma Abokinsa mai suna  Nafi u .

Cike da girmamawa
shi da Abokin nasa
su ka gaida Baba.
Kafin Abokin ya cewa Ya Musbah
  Bara in wuce.
In fara karatu kafin ku kammala. 
Jinjina kai kawai Ya Musbah ya yi, dan gaba Waya hankalinsa a mugun tashe ya ke, ga shi ya ga Baban sai wani irin kallo ya ke ta yi ma sa
wanda ya kasa gane ma anarsa.

Rashin sanin abun yi da kame-kame ne su ka sanya shi cewa
  Bismillah Baba
Mu shiga daga ciki ko? 

Sai da Baban ya sau?e ajiyar zuciya tukunna ya ce
  Naa shiga kuwa? 

A hankali Ya Musbah ya ce
  to ko soro ne ka shiga dan Allah.
Akwai bayanin da na ke so in yi maka ne.

Ba dan Baba ya so ba!
Ya Kama Hannun Muhsin su ka bi bayan Ya Musbah.

Anan soron kuwa ya shimfiWe musu tabarma& ..
Dan a wannan lokacin bai isa shigar da su cikin gidan ba!
Daff da zuwan su Baban
Nafi u ya gama yi musu shari ah shi da Baraka!
Saboda kawai Jidda ta zo Wazu, shikenan tunda Yarinyar ta zo ta tafi Baraka ta ke ta bambami
 Wai ta zo har gida ta yi mata rashin kunya!!!!
Kuma sarai ya san ?arya ta ke yi!
Kawai ta na neman hanyar da za ta bi ta datse zuwan ?an uwan nasa gidansa ne!
Gaba Waya.
Bayan a yanzu kamata ya yi ma ace shi ya ke ri?e da Jidda ko Manubiya& ..

  Tunanin mai ka ke yi??? 
Muryar Baba ta Katse ma sa tunani.
A hankali ya sau?e ajiyar zuciya!
Ya na shirin yin magana Baban ya sake katseshi ta hanyar cewa
  Innar ku har yanzu ta na kwance,
babu kuWin magani, babu na zuwa asibiti.
Musbahu!
Kai ne ka hanani aikin ?arfi,
Sannan kai ne ka ce ?annen ka Mata ba za su yi Aikatau ba wanda ba daban hakan ba na san da yanzu mun san yadda mu ka yi
aka kai ta asibiti.
Tun shekaran jiya mu ke ta tsammanin ka!
Ka kashe wayarka kuma
ka ?i ka yarda ka zo inda muke.
Wanda in m kuWaWen ne ba su samu ba a gani na dai a ya kamata ace ka zo ka duba Mahaifiyar ka dai ko? 

Cikin yin ?asa da murya sannan a hankali Ya Musbah ya ce
  Baba, kalli fa ?afar ka. Ba za ka iya aikin ?arfi da ita ba!
Ina tsoron ka saka mata nauyi da yawa haka nan mu je Itama ?waya Wayar wadda ta rage maka ya zamana itama ta samu matsala.
Su Manubiya kuma
ba wai girman kai bane ya sanya na ce ba za su yi aikatau ba!
Kawai a ganina bai kamata ace ina raye muna zaune a unguwa Waya
amman ace ?anne na Mata su ne za su na kula da iyayena, ba.
Dan Allah Baba ka yi ha?uri,
ka bar maganar dakon da ka ke so ka yi, da duk ma wani aikin ?arfi.
In sha Allahu zan yi ?o?ari in san yadda za a yi.
InshaaAllah zan iya kula da kowa.
KuWin asibitin ma na nemo, ba wai ban nemo ba!
Amman sai jikin Baba ?arami ya Wan mot& &  
Shiru ya yi kafin ya ci gaba da cewa
  Amman karka damu
Nafi u ya yi wa Wan uwansa magana kuma Wan uwan ya ce
za a san yadda za ayi&
Mu jira shi zai kawo kuWin. Shiyasa ma ka ga ban zo ba saboda
bana so in zo muku ba tare da kuWin ba. Shi nake ta jira na fi so in ya zo ya bani ni kuma sai in zo
a kaita asibitin  .

Sai a sannan
Baraka wadda ta laSe musu tun Wazu ta shigo cikin soron.
A hankali ta ?arasa inda su ke ta zauna!
Cikin ladabi ta gaida Baba. Inda ya
amsa mata da Kulawa ya na mai tambayarta  Ina takwaran sa ta ce
masa  yana ciki yana barci.
Da ladabi Muhsin ya gaida ita
ta amsa daga nan soron ya Wauki shiruuuuu,
kafin a hankali sautin kukan Baraka ya soma tashi.

Da sauri Baba ya ce
  Subahanallah,
Baraka lafiya?
Mai ya faru? .

Cikin kukan da kyar ta Wan tsagaita sannan ta ce
  Ba komai Baba, ba komai. Ku yi ha?uri, suSuce mini ya yi. 
Tana gama faWin haka ta fara ?o?arin mi?ewa.

Cikin Wan tsare gida Baba ya ce
  Koma, koma
Baraka.
Koma ki zauna  .
Ya bata umarni
ransa duk babu daWi.
A hankali ta koma ta zauna ta na Wan satar kallon Ya Musbah wanda ya haWe rai!
Yana ji kamar ya rufe ta da shegen duka.

Cikin kulawa Baba ya shiga rarrashin ta& .
Har sai da ta yi shiru tukunna ya nemi ta ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?faWa masa me ke faruwa.


Cikin yin ?asa da murya ta fara zaiyyane masa cewa
 dama kwanakin baya ne Ya Musbah ya karSi kuWinta, kuma itama kuWin ba nata bane ba
na wata ?awar Mamanta ne
To a halin da ake ci
Maman tata ta biya rabi, amma ta kasa biyan rabi shine ?awar ita Mahaifiyar tata ta ce  za ta je da ?an sanda ta tafi da Mahaifiyar tata .
Tun jiya ta ke bin Ya Musbah akan ya bata kuWin shi kuma ya ?i ya bata,
yanzu gashi ?an sandan sun je za a tafi da Mahaifiyarta.& .

Shiruuu Baba ya yi,
da jin batun Baraka.
Kafin ya mi?e tsaye ya kama Hannun Muhsin.
A hankali ya kalli Ya Musbah ya ce
  Musbahu, idan an kawo kuWin da akayi maka al?awari ka bata. 

Da sauri Ya Musbah ya ce
  Amman fa Baba.. 

Cikin katse sa ya ce
  Bana son musu!
Sannan bana son ja-in-ja!
Ka bata kawai.
Kar ka damu, zan san abun yi   .

Tukunna ya kalli Baraka
wadda ta yi kalar tausayi ya ce
  Kar ki damu, ba za a tafi da Mahaifiyarki ki ba.
Inada mara lafiya a gida, shiyasa ba zan iya bin ki mu je in ga komai ya lafa ba.
Yanzu ki yi sauri ki je wajen ta, Musbahu zai biyo ki da kuWin
InshaaAllah.
In basu cika ba ma
In na san yadda nayi na haWa kan ?an kuWaWe na kashe wutar gaba na&
Ki yi mini magana sai in cika miki   .
Yana gama faWin haka ya jaa Hannun muhsin su ka fice daga soron.

Cikin Sacin rai Ya Musbah ya kalle ta kamar zai ce wani abun
sai kuma kawai ya mi?e shima ya fice!
Ya bi bayan Baba ranshi a mugun Sace!.

Yaso ya fahimtar da Baba
a samu
ya yi ha?uri ya karSa kuWin ya bar batun Baraka!
Amman furr Baba ya ?i sauraron sa, karshe ma faWa ya rufe sa da shi!
Sannan ya ce  ya koma kar wanda zai kawo masa kuWin ya zo bai same shi ba,
kuma Wallahi idan ya sake karSarwa Baraka kuWinta sanna ya hana ta tabbas ransa sai ya yi mugun Saci.


Ganin yadda ran Baba ya Saci sosai ne ya sanya kawai Ya Musbah ya ha?ura& .
Sannan ya ba shi ha?uri, daga nan ya juya ya nufi hanyar gidansa.
Bai shiga ba!
direct masallaci ya wuce,
ana idar da sallar Wan uwan Nafi u ya kawo kuWin kamar yadda ya al?awaranta.

Ya Musbah, ji ya yi kamar ya cewa
Wan uwan Nafi un kawai ya bar kuWin ya fasa ranta& .
Dan ya san idan ya sa Hannu ya karSa kuWin
ya baiwa Baraka
To fa
bai san ranar biya ba,
gashi yana tsananin jin kunyar Nafi u wanda ya ke bin sa bashin kusan dubu Wari kuma bai san ranar biya ba& ..
Gashi yanzu na Wan uwansa shima ya fara hawa kan shi.
Dama saboda ya ga na asibitin Mahaifiyar sa ne Shiyasa kawai ya rufe ido zai karSa& &

Kamar Nafi un ya san me Ya Musbah ya ke tunani.
A hankali ya dafa Abokin nasa wanda suka taso tare tun ?uruciya ya ce
  Ka kwantar da hankalinka.
Kar ka damu!
Ko yaushe ne in ka samu kana iya biya.

Sai da ya Wan sau?e ajiyar zuciya
tukunna a hankali ya sa Hannu ya karSi kuWaWen, waenda ko bai ?irga su ba ya san ba su fi naira dubu goma ba!
Ya so ace sun Wan fi haka
da sai ya bawa Baraka dubunta goma ragowar kuma a yi hidimar asibiti da shi&

Godiya Sosai ya yi har sai da ya bawa Wan uwan Nafi un kunya ma.
Daganan Mutumin ya yi musu sallama ya burga mashin Win sa ya wuce, ya barsu anan tsaye.
Kafin suma su ka juya a tare su ka nufi ?ofofin gidajen su& .
Har su ka ?arasa ?ofar Gidanjen nasu guda biyu..
Ya Musbah tunani kawai ya ke ta yi&
Tausayin sa Nafi u ya ke ji sosai dan ya san in ba matsalar Baraka ba tou matsalar rashin lafiyar Mahaifiyar su ce ta sanya shi a damuwa haka.

Yana shirin yi masa magana ya ji Ya Musbah ya ce
 Nafi u kuWin nan fa Baraka zan bawa  .
A Wan fusace Nafi un ya ce
  Saboda ka zama Mijin ta ce? 

Ya Musbah, bai Soyewa Abokin nasa komai ba haka ya zaiyyane masa abunda ya faru&
Sannan ya ?ara da cewa
  Ba wata maganar ?an sanda,
Biki ne take da shi!
tsabar bala i wai ankon super za su yi!
Me sunan Baba kan sa ta yi masa kaya masu kyau da tsada sama da kala uku!
Amman saboda
Allah ace wai Mahaifiyata bata da lafiya amma sam Baraka ta kasa mini kara, kwata-kwata ba ta damu ba& . 
Ya ?arashe maganar hawaye su na silalo masa.

Da kyar Nafi u ya iya danne fushin sa, gudun kar ya sake tunzura Abokin nasa.
Sai da ya Wan daidaita kan sa
daga takaicin Baraka, tukunna a hankali ya dafa shi sannan ya ce
Ka yi ha?uri Musbah!
Komai in ya yi zafi to maganin sa Allah.
Tunda ta yi maka haka kuma Baba ya ce a bata to kawai a bata Win.
Ita ta sani, in dai duniya ce, dai dai ta ke da ita.
Kawai yanzu matsalar ita ce inda za mu nemo wasu kuWin.
Saboda nima Wallahi babu a waje na, da ace ina da shi da na baka.
Ka san lokacin biyan kuWin gida ya yi,
Mutumin nan sam ni baya taSa Waga min ?afa,
har gara kai ma ya ce
ai ya san baka aiki& .
Gashi wannan term Win Khairat ta shiga makaranta
shiyasa nima duk na zama a matse, ba ni da shi.
Shiru ya Wan yi kamar me tunani kafin ya ci gaba da cewa
  kuma kaga yaya na guda Waya tak a duniya na tambaya maka shi shima
amma bara muga ko akwai& . 

Da sauri Ya Musbah ya katse shi ta hanyar cewa
 Nafi u kar ka damu.
Na gode wallahi ban san da wanne Baki zan yi maka godiya ba.
Ba na jin akwai Aboki irinka har yanzu
a duniyar nan in har kuma akwai
tou tabbas ba ku da yawa.
Nagode nagode.
ka kwantar da hankalinka,
bara inje in bata kuWin.
dole haka zan ha?ura in le?a Innar babu ko sisi!
Idam na je Win sai a san yadda za a yi  .

  Ok 
Nafi un ya ce, cikin
rashin Jin daWi.
Kafin ya sake cewa
  Nima bara in duba gida,
Idan komai normal sai mu tafi wajen Innar tare& ..


BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*04*

Ba kunya ba tsoron Allah haka Baraka ta sanya Hannu ta amshe kuWaWen nan, duk da kuwa ragowar kwallar da ta gani a Idanun Mai Gidan nata wanda hakan ya tabbbatar mata da kuka ya yi!
Dan hatta ga jijiyoyin gaban Kansa sun fito raWau! Ga kuma farar Fuskarsa itama ta yi jajawur gaba Wayanta. Ka na ganinsa ka san
yana cikin tsananin tashin hankali.
& &
Tana amshe kuWaWen ta shige cikin parlournsu mai Wauke da Wakuna biyu, dama fitowarta daga banWaki kenan ta ganshi tsaye da kuWaWen yana jiran ta.

Ya daWe tsaye a wajen, kafin ya samu ya iya jan
?afafuwansa ya juya ya fice daga cikin gidan, gabaWaya.

Sai a sannan ta bar bakin windown inda ta laSe tana kallon sa tana mai taSe Baki! A fili ta ce
  Haka kurum in bada kuWaWena a kai uwar wani ba tawa ba asibiti, bayan ga biki a gabana& .
Idan na biye maka Musbahu naga alamun sai na gagara shiga cikin ?awayena watarana wallahi.

Da mutunci na da kyalli na ka auro ni
amma iyakar inda ka ajjiye ni da suturun da ka jere mini a lefe ya sanya yanzu ko hamsha?iin taro idan za a yi ?awayena basa gaiyyata ta! Yo ina dalili fisabilillahu. 
Hakanan tayi ta mita ita kaWai daga ?arshe ta shiga kasafta mai da me zata siya da kuWaWen& &



Tun lokacin da suka rabu da Ya Musbah,  Baba ya ke tunanin ta Ina zai samo kuWi , duk inda ya duba ya zaga ya zagayo babu hanya!
Hakan ya sanya gaba Waya hankalinsa ya sake tashi!!!

A haka suka yi alwallah su ka yi salla shi da Muhsin daganan suka fito daga masallacin suka zauna akan Wan dakalin ?ofar gidan.

Yana cikin tunani ya ji wasu zafafan hawaye suna zuba akan kyakkyawar tsohuwar Fuskarsa&
Sai da ya faki idon Muhsin wanda ya yi shiruu shima ya sunkuyar da Kansa ?asa tun Wazun da su ka zauna
tukunna ya sanya Hannu ya share Hawayen nasa kafin a hankali ya faWa duniyar wani tunanin na daban ..
<<<<
Yanzu haka, a tsakiyar ?an uwansa yake!
Babban yayansu
BABA HABU da Matansa guda biyu
Umma DIJE da Umma KULUWA
Umma dije ?a?anta mata uku
Zainab, Hauwa sai Maryam,
gaba d ayan su sun yi aure.
Sai Umma Kuluwa
tana da Yaro Waya Namiji
 Ya Yusuf wanda ya girmi Ya Musbah da shekara Waya amma shi bai yi aureba.

Sai Wayan Yayan nasa
UTHMAN
Wanda kowa yake kiran sa da
UNCLE
Uncle yanada mata uku
Kasancewar yana aiki a banki ya sanya duk ya Wan fi su rufin asiri
Matarshi ta farko FATIMA
Umma Fati
Yaro Waya tak ta Haifa
Ya iliya (yayi aure)daganan ta samu matsala bata sake haihuwa ba
ta biyun sunanta Khadija
Ita kam ko Satan wata ma bata taSa yi ba.
Sai ta ukun Anty RUMASATU
(Anty amarya)
tanada ?a?a biyu mata twins
Shamsiyya da Salaha masu shekaru goma a duniya.

Sai Yayarsa
Anty Umma (Binta), wadda Mijinta ya rasu ta komo gidan da zama
?a?anta biyu Mata ta farkon sunan ta Fiddausi tana aure a illorin sai autar ta wadda ta ke tare da ita  Siyama
Siyama ta girmi Jidda Manubiya kuma ta bata shekara Waya.

Sai shi Baba (MUSA)
Matarshi Waya Aminatu (Inna)
Da ?a?ansa huWu!

Na farko Musbahu mai shekaru 27
Sai
Manubiya mai shekaru 22
Sai
Maijiddah mai shekaru sha bakwai
Da auta Muhsin wanda bai ?arasa rufe shekaru sha Waya ba.

Duk a cikin ?an uwan nan nasa(Baban) da suke zaune tare a gida Waya babu wanda zai tambaya kwandala a cikinsu yau ace ya Wauuka ya basa!

Idan ana maganar asalin rashin haWin kai
Tou shine definition(ma anar) rayuwar Baba da ?an uwansa!.
Babu hassada babu faWa babu hayaniya a tsakaninsu amma fa kowa na sa kawai ya sani, hatta Anty Umma, kaff cikin yayun nasu Maza babu mai ciyar da ita kuma sunada rufin asiri ba wai babu ba amma sai dai ta ci da kanta ta ci da ?arta (Siyama)
Da taimakon ?ar sana ar siye da siyarwar da take yi, sai kuma Yayar Siyaman itama tana taimakawa ba laifi.


A ta?aice dai kowa ta kansa yake yi a gidan& kowa nasa kawai ya sani, sannan babu ruwan kowa da kowa. Yanayin zaman sam babu daWi. Ga baki ga hanci..compound Waya amma idan ba su Manubiyan ba babu me le?awa ya ga Wan uwansa idan wani abun ya faru domin a ji ko a ga halin da yake ciki.

Mai ?ananun maganganu, rigima da son haWa faWa a gidan Mutum Waya ne
 Kaka Malan
Wani Wan uwan Mahaifinsu da Allah bai ba shi haihuwa ba
suka Wauko suka bashi Waki mai banWaki a cikin compound Win nasu.
Wanda shima sai ya yi da gaske tukunna ake kula shi ake zuba masa abinci, dan Kaka Mallan irin tsoffin nanne masu tijara, gulmace-gulmace, shishshigi da zalama.

Su kam ragowar

5 / 51