Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   11 / 51

30K to 33K   out of 151.9K words

baki handouts d in da ya fitar a jiya, ya ce gobe zai kuma yin open test shima part of CA Winmu ne  .

  Okay  ta ce, tana mai mik ewa
sannan ta k ara da cewa
  Mutumin nan d an wahala ne Wallahi
Da shi da test 5&6  .

Dariya ya yi daga nan suka saka kai suka fita a tare.


A bakin ward d in ta hango Ya Musbah shi da Baraka a tsaye!
Kallo Waya za a yi wa Fuskokinsu kai tsaye a fahimci fad a su ke yi.
Baraka ce take facing d in ta dan haka tana ganin tahowar ta ta yi shiru, har suka zo suka wuce.

A cikin garden ta chan gefe ta hango su Muhsin da Baba a zaune& &


Allah sarki Abbakar&
Duk wasu handouts d in da aka fitar na course d in da suke yi sai da ya siya mata, daman exams ta taho!
Duk haka ya had a ya bata
sannan ya sake tabbatar mata
Da
 ta zo gobe.

Ta san saboda mamansa ne ya sanya ya ce  iya na sir Najeeb ya siyo mata dan ta lura da yadda suka yi a lokacin da ya ce  yayi mata test d in ma.

Shiyasa itama da ta karb i jakar ta yi godiya ta goya a bayanta,
ta ci alwashin b oyewa& &


Har ta karya kwana ta nufi inda su Ya Musbah suke sam ba su lura da ita ba!
Ranshi a tsananin b ace yake ita kuma Baraka ta bata baya
shiiyasa duk basu lura da ita ba.
Tun kafin ta k arasa kusa da su
ta ji Ya Musbah yana cewa
  Yanzu Baraka ya kike so in yi?
Ko sata kike so in je in yo?
Na fad a miki wallahi babu kud i a Hannuna 

Cikin tsiwa ta ce
 Eh kam babu kud i a Hannunka ga alama nan ai na gani!
Rashin kud in naka ne ya sanya Innar ka take kwance a aminity
d aki cike da kaji da lemuka!!
Ko y an uwanku ne suka kawo?   .

A zuciye ya ce
  Ba na son cin fuska kuma.!
Na ce miki ba ni da kud i
hidima kuma da kika gani ba ni nake yi ba!
Ki yarda ko kar ki yarda wannan ba matsala ta bace ba.
Akwai kud i a hannun ki na sani ba wai babu ba dan haka idan za ki yi hidimar gida dasu Bismillah&
Duk ranar da na samu zan maida miki,
Idan kuma za ki iya barin Wan da kika haifa a cikin ki da yunwa saboda rashin sanin ciwon kai to shima Bismillah&
Sannan idan kinga ba zaki iya ci gaba da zaman ba
nan ma kin san mai za ki ce min inyi
ni kuma in sha Allahu zan yi miki yadda kike so 

Cikin tsananin b acin rai
ta ce
  Eh lalle Musbahu ka yi arzi?i, ga alama nan na gani& ai dama ku Maza haka kuke, wato kud i sun fara zama maka shine ni Baraka yau nice abar wulakantawa ko?
Ka barmu da yunwa ni da d anka
ka dauko Babarka ka kawo aminity kuma na yi magana ka ce za ka sakeni
Saboda yanzu ka san kana da kud in da za ka yi wani auren idan na tafi ko &  


Cikin katse ta ya ce
  Ba wai cewa na yi zan sake ki ba, cewa na yi idan kinga ba zaki iya zama ba to ki fad i abun da yake ranki ni kuma in aiwatar.
Magana ta ta ?arshe anan  ki yarda ko kar ki yarda
Ba nine nake hidimar asibitin nan ba, saboda bani da shi.
Dan haka idan zan baki shawara ki d auka to,
ki je ki siyo kayan abinci ku ci da ke da mai sunan Baba
kar ki damu da cikina
In sha Allah zan samu abun da zan ci, kuma duk lokacin da Allah ya bani kud i zan mayar miki &  
Yana gama fad in haka ya juya ya wuce ciki! Yana adduar Allah yasa Manubiya ba ta ji conversation d in nasu ba dan shi sai yanzun ne ya lura da ita.

Takaici kamar ya kar Manubiya, sam bata yi niyyar kula Baraka ba, dan haka ta zo za ta wuceta da sauri ta na jin wani takaicin ta na musamman yana rufe ta!.
Ita kuma Baraka dai-dai ta juya dan haka suka yi kiciSus!!!&

Wani tsaki Baraka ta jaaa!
Kafin ta ce
  Ni kam wannan aure,
a cuce ka kuma ka yi magana aji haushi!
Sannan ga ido ta ko ina&  

Har Manubiya ta Wan yi gaba
sai kuma ta juyo ta dawo ta sha gaban Baraka, ta tsaya.

Gyara tsayuwa kawai Baraka ta yi itama ta shiga watsa mata kallon wula?anci.

Cikin takaici Manubiya ta ce
  Wallahi kin bada Mata, ai ko kishi da rashin hankalin ma yanzu an daina yayin irin wannan.
Duk abubuwan da kike yi zuba miki ido kawai muka yi ba wai dan bamu san me kike yi ba ne
sai dan
a kullum adduar mu itace ki shiryu.
Haba Baraka
Mahaifiya fa?
Itace abar kishi?
Inda ace ma lafiyar ta ?alau tou da da sauk i
amman bata fa da lafiya, a kwance take, a gani na idan baki taimako ba to bai kamata ki d agawa kowa hankali ba.
Kaico!!Wallahi Ya Musbah bai yi sa ar Mace ba. 

Yadda Baraka ta zazzaro Idanuwa waje duk wanda yagansu a wajen zai yi zaton daddanawa Iyayenta zagi Manubiya ta yi&

Ta san dama Manubiya bata da hak uri amman bata tab a tunanin zata iya gaggaya mata magana har haka ba.
Tijara da Zuciya da suka ciyota ne suka sanyata ta figo Hannun Manubiya da dukkannin k arfin da Allah ya bata suka yi ciki tare.

Tun daga bakin k ofa ake kallon su, ga security ya biyo su yanata faman yi wa Baraka magana
Yana cewa  ta sakar mata Hannu
amman sam Baraka bata da niyyar sauraren sa,
ita kuma Manubiya taso yin tirjiya ko kuma ta fisge Hannun nata amman kuma a ranta sai ta ce  bara kawai ta barta gudun kar su yi kokawa ta sake tada wani case d in a tsakiyar asibitin..
Ta fahimci d akin da Inna take take shirin kaita shiyasa ta gama rayawa a ranta  suna shiga d akin in ta cika ta ita kuma zata fice ta barta dan ta lura burin Baraka tabbas bai wuce ta ga gawar Inna ba&

Da k arfi ta tura k ofar suka shiga tare ita da Manubiyan.
Da sauri su Jidda su ka mik e tsaye saboda a yadda Baraka ta shigo kamar wata mahaukaciya sun yi zaton wani gagarumin abu ne ya faru.
Duk yadda Manubiya ta so ta cika mata Hannun sai ta kiya,
ta rik eta gam!
Sai a sannan Manubiya ta yi dana sanin k in kwace Hannunta tun a waje su yi ta ta k are dan tana shigowa d akin da Inna ta fara tozali ta bud e idanuwanta sab anin Wazu da ta barta tana bacci.

Da kyar Ya Musbah ya samu ya had iye wani k ululun takaici wanda ya tokare masa ma?oshi tukunna ya k arasa wajen su.
Ba tare da ya kalli Baraka ba ya cewa Manubiya
  D auki jakarki ki wuce gida 
Dan ya fahimci akan maganar da Manubiyan ta ji suna yi ne shi da Baraka, ta yi wa
Barakan magana
shine ita kuma ta janyo ta nan domin ta d agawa Inna hankali.

Cikin d aga murya, hargowa da hayagaga Baraka ta ce
  Ka san me ta yi mini ne
da za ka ce ta tafi haka kawai,
wato ta zagi banza ma kenan ko?.

Allah na tuba in banda k addarar aure da ta kanainaye ni a gidanka
Manubiya ta isa ta taka inda na taka?
Ballantana har ta kalle ni ta fad a min maganar banza?

A hankali Ya Musbah ya lumshe Idanuwansa waenda su ka yi jazirrr!! Kafin ya bud e su ya zubawa Baraka ya ce
  Baraka saki Hannun Manubiya ta wuce gida.
Zan yi mata magana. 

Cikin gurb atacciyar Hausa security d in da ya biyosu shima ya matso ya ce
  Madam, cika mishi Hannu, ki bar fad a, ba a hayaniya, kalle patient fa
Ya yi maganar yana nuna Inna wadda ta kafesu da Idanuwa.

A hankali Ya Musbah wanda ya ke ji kamar ya nutse a cikin ?asa ya Wan waiga ya kalli Innar
kafin ya juya da Wan zafi ya ce
  Baraka ki sake ta, ta wuce nace, ko? 


Cikin tsananin tsiwa rashin kunya sannan da ?arfi ta ce
  Kaga rufe Bakinka, tunda ba za ka yi adalci ba!
?anwarka ta zage ta zuba mini rashin kunya sannan ko bin ba asi ma baka yi ba kace kawai in cika ta ta tafi?
wato ban isa bama kenan ko?
To Bari ka ji
bayan cin kashin da kake yi mini da azabtar dani Win da kake yi wallahi ban shirya sake d aukar rashin kunyar k annenka ba, dan haka ba zan cika ta ba kuma sai ta bani hak uri yanzu ba sai anjima ba sannan ka kora mata zazzafan warning idan kuma ba haka ba to wallahi sai mun kwashi y an kallo ni da ita 

Da mamaki Manubiya ta ke kallon Baraka&
ba abunda ya fi bata mamaki irin yadda Barakar ta ke ihu bayan ga Inna a kwance sannan ta bi ta wani dage akan wai an yi mata rashin kunya
bayan ita Manubiyan ta bata wata biyu a duniya!
Yanzu haka ita ta cika shekaru ashirin da biyu
ita kuma Barakar sai watan gobe& .

Security ya yunk uro kenan zai yi magana
Maman Abbakar ta mik e ta ce masa
  Yi hak uri, je ka.
Za su yi shiru, bara in yi musu magana 

Ba dan ya so ba ya juya ya fita dan ya k ule sosai da Baraka.

Yana fita Baba yana shigowa rik e da Hannun takwaransa, Muhsin na biye a bayan su.
Dama tun kafin ya k arasa ya ke jiyo hayaniya gashi kuma ya tadda su cirko-cirko
dan haka ya hau tambayar su ko lafiya& .

Maman Abbakar ce ta ce
  Tou Baba Musa, ka san dai Manu da Baki da kuma rashin kunya!
To inaga yau abun nata ya biyo ta kan yayar tata ne,
dan gashi har janyo ta ta yi ta kawo k ara shi kuma Musbahu ya ma k i ya bari a yi maganar, sai cewa yake ta yi Manubiya ta wuce ta tafi kawai zai yi mata magana  .

A cikin ransa Baba ya shiga karanto sunayen Allah.

Tsit haka d akin ya d auka.

Sai da Baba ya ji ya d an dedeta tukunna
Ya ce
  Musbahu ya ce Manubiya ta tafi za su yi magana saboda nan d in d akin mai jinya ne wadda take fama da kumburin zuciya, hawan jin, k oda da kuma mutuwar b arin jiki.
Ina fatan kun fahimci dalilin da ya sanya ba ya so a yi wata rigimar a gaban Idanunta kar ku yi masa mummunar fahimta,
ba wai son kai yake shirin gwadawa ba & . 
A hankali
ya juya ya kalli Baraka tukunna ya ce
  Me kike so Manubiya ta yi miki yanzu? 


A hankali ta sunkuyar da kanta ta cika Hannun Manubiya tukunna ta ce
  Baba ta bani hak uri, karta sake kuma 

  InshaaAllah Baban ya ce
Sannan ya juya ga Manubiya har
Idanuwansa sun yi jajir suna kyalli tsabar Sacin rai,
zai yi magana da sauri Manubiyan ta ce
  Ki yi hak uri, sharrin Zuciya ne, ba zan sake ba, inshaaAllah 

Ajiyar zuciya Maman Baraka ta sauk e sannan ta mik e,
Baba kawai ta cewa
  Allah ya k ara sauk i  daganan ta taho kamar zata bangaje Manubiya
ganin haka yasa tayi sauri ta matsa
Itakuma ta bud e k ofar ta fice.
Baraka ma Hannun Baba k arami kawai ta kama suka fita bata cewa kowa uffan ba.
Maman Abbakar ce ta d an tsaya ta yi musu sallama daga nan ta saka kai ta fice
Jidda da Baba suna masu ce mata sun gode.

A hankali Baba ya ga wasu hawaye suna tsilalalowa Inna ta ido d aya

da sauri ya k arasa ya sunkuya dai dai fuskarta ya shiga share mata hawayen nata yana girgiza mata kai alamun ta yi shiru& .
Sun jima a haka kafin
ba tare da ya juyo ba
ya ce
  Manubiya ki kwashi duk Kayanki da suke anan,
Ki wuce gida. 

Fashewa ta yi da kuka
Cikin kukan ta ce
  Baba dan Allah ka yi hak uri,
wallahi ban yi tunanin Baraka za ta yi haka ba 

Still bai d ago ya kalle ta ba
ya ce
  Ni kuma ban yi tunanin har yanzu ba ki yi hankali ba, ban yi tunanin har yanzu ba za ki iya barin abu d an k ank ani ya wuce ba tare da kin yi magana ba 

Cikin fushi Ya Musbah ya ce
  Ko ma menene ki ka ji tsakanina ne ni da ita!
Dan mai yasa za ki shiga ciki har ki yi mata magana?

A hankali tana kuka ta ce
  ku yi hak uri 

Ya d an jima yana kallon ta kafin ya ce
  Ki kwashe Kayanki ki wuce gida, ki je ki fara karatu
Jidda za ta ci gaba da zama anan,
Ke kuma kya dinga yin girki daga gida. 

Za ta yi magana
ya ce
  Manubiya ki je a ka ce ko? 

A hankali ta d aga kanta alamun  to tukunna ta k arasa ta je ta shiga had a kayanta, har ta gama bata yarda ta d ago sun had a ido da Inna ba
dan ta san ita take kallo,
sai da ta zo tafiya tukunna ta je ta rungumeta ta ce  Inna Allah ya baki lafiya 
Still bata yarda ta kalle ta ba.
Daganan ta yi wa su Jidda sallama, Baba ya bata kudi n mota ta sa kai ta fita.

Ya Musbah ji yake kamar ya fashe da kuka, tabbas Baraka ta kai shi bango!!! k iri-k iri duba fa yadda ta disga shi ta wulak anta shi a gaban jama a harda wani cewa  k addarar aure !!
babban takaicin sa shine idan ya d au mataki a wannan gaSar ya san sai ya had u da fushin Baba saboda cewa zai yi dan mai yasa zai biye mata a case d in da ya had a da su Manubiya, tunda wani abun yana faruwa kowa cewa zai yi ya bi bayan k anwarsa sam baza a duba rashin d a  a da furucin da ta yi a gaban iyayensa ba& & & .
&
Chaaan yamma.
Jidda na zaune ita kad ai gashi lokacin zuwan Al ameen ya yi
ta rasa yadda za ta yi ta fita.
Sai da Innar ta yi bacci tukunna ta samu ta fita, tana ta sauri.

A cikin mota ta same shi yana ta jiran ta

Ba tare da b ata lokaci ba ta ce   ya zo su je d akin,
Adda Manu bata nan yau, ta bar Inna ita kad ai 

Murmushi yayi
Daganan ya fito suka jera suka nufi d akin gwanin ban sha awa.

Sun jima kuwa suna hira,
tukunna ya yi mata sallama ya wuce.

Allah da ya taimaki Jidda sam Ya Yusuf bai had u da Al ameen ba dan tana dawowa daga raka Al ameen d in ta tarar da shi a d akin,
ko waye ma yayi masa kwatance, sai Allah .

Tunda ta shigo ta gan sa sai ta tamke fuska, daga gaisuwa bata yarda sun yi wata hirar kirki ba.

Ita sai da ya fad a mata ma tukunna ta gane wai ashe fushi ya yi tun ranar da ta gudu
shiyasa shi kuma ya ?i zuwa ya duba Innar sai yanzu& .

Ganin dai duk yadda ya yi fad a, fushi da rarrashi sam ya gagara samun fuska a wajen Jiddan ne ya sanya kawai ya tashi ya tafi dan ya riga ya gama tsara yadda zai yi da ita next tunda ya lura bata san a bita ta sauk i ba.
Katamau!! Haka shima ya wani tamke fuskar nan tukunna ya fice bayan ya ajjiye musu dubu d aya akan gadon, wai su sayi abun da basu da shi& ..

BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*10*

Ko da Baba ya koma gida da daddare sai da Manubiya ta sake ro?on sa akan  ya barta ta je asibitin washegari amman furr ya
?i amincewa illa ya ce mata  ta yi karatu ta dinga zuwa makaranta akai-akai kawai.

Da asubah ta tashi ta shirya musu breakfast, har lunch, ta cewa Muhsin  ya d umama miyar idan an zo kaiwa daganan ta wuce makaranta saboda tana so su yi karatu da Abbakar yau sosai, gashi lecture Win Sir Najeeb gare su da sassafe shiyasa take ta sauri saboda ta san baya bari a shiga muddin ya riga ya shiga.

Duk saurinta kuwa sai da ta yi
rashin sa a, dan ta na karya kwanar inda k ofar tafkeken hall d in ya ke ta hangoshi yana shiga dan haka ta k ara sauri amma dukda hakan kafin ma ta k arasa bakin k ofar har ya rufe.
Haka nan ita da ragowar d aliban da suka yi letti suka ja suka tsaya a bakin k ofar hall d in dan waatak ila idan sun ci sa ar shi
In ya fito ya karb a sunayen su da Matrc number Winsu ya raba musu ko da half half maki ne.

3 hours ne

11 / 51