Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   13 / 51

36K to 39K   out of 151.9K words

ki zo ki yi reporting  .

Da sauri suka had a Baki suka ce
  In sha Allah, mun gode Sir,
Sosai. 

A hankali ya jawo computersa ya fara latsawa
kafin ya ce
  U can leave 
Ba tare da ya kalle su ba.
& & & & & & & & &
BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*12*

Tun lokacin da Yashjub ya baro office d in Najeeb, gaba Waya ya rasa nutsuwar sa. Har ya k arasa gida ya yi wanka ya yi sallah ya nufi side d in Mommy domin ya Isar mata da sak on Daddy gaba d aya hankalinsa yana kan Yarinyar da ya gani Wazu a office d in Najeeb.

Sai da ya yi addu a sosai tukunna ya samu tunanin ta ya bar shi ya yi sallah a nutse.

Bai samu Mommy a parlour Winta ba dan haka ya wuce d aki sai dai nan Win ma bata nan& .

Har ga Allah Kansa har ya fara ciwo shiyasa ya bi gadonta ya kwanta shi kad ai ya yi shiruu.
So yake ya lumshe idanuwansa ya d an huta amma ba ya son yin hakan saboda ya san yana lumshe su idanuwan wannan Yarinyar zai ke gani.

Abun takaicin shine ko sunanta bai sani ba sannan ya san idan za a jere masa mata blindfolded(a rufe musu Idanuwa da kyalle) ace masa ya nuna ta a cikin su sam ba zai iya gano ta ba.
Ya san
bashi da wata alak a da ita amman kuma sam muryarta da idanuwanta sun addabi zaman lafiyar sa ya rasa nutsuwa ya kasa yakiceta sam ya rasa sukuni, tun Wazu da ya ganta har kawo yanzu babu da?i?ar da ta wuce wadda bai yi tunaninta ba.
Sai da ya yi da gaske ya had a da addu o i tukunna Wazu ta Wan lafa a ransa ya samu ya yi sallah cikin nutsuwa& ..


Wani bahagon tsaki ya jaa ya mi?e ya zauna a kan gadon,
kafin ya zaro waya ya danna kiran Najeeb& .

Sai da ta katse ya sake kira nan ma ta kusan katsewa tukunna ya d auka da sallama&
A hankali Yashjub ya amsa,
tun kafin ya yi k orafi Najeeb ya ce
  Sorry, ina wanka ne, yanzun nan fitowa ta na ga wayar tana haske 
Ya k arashe maganar yana mai shirin ajjiye wayar dan ya san tunda Yashjub d in ya ji haka zai ce  ok,
Idan ya shirya ya kira sa kawai.
Har ya maida wayar kan side drawer sai kuma ya ga still ba a kashe ba, shiruuu ya d an yi kafin ya sunkuya ya d auki wayar ya mayar ya kara a kunnensa, a ransa
yana tunanin  shin me yake damun Yashjub haka, ko dai family matter ne? tunda dama ya ga Daddy ya kira shi d azun, kuma tunda ya fita ko sallama bai dawo yayi masa ba kiran sa kawai yayi ya ce masa ya wuce!.
It s very unlike him& . .

Yana cikin wannan lissafin a hankali ya ji Yashjub d in ya ce
  Am..Najeeb, Yaran d azu ya sunansu?
I mean, ya sunanta? 

Shiruuuu Najeeb d in ya yi ya zaro wayar daga kunnensa ya kalli sunan da kyau ya tabbatar Yashjub d in ne tukunna ya mayar ya d an tab e Baki ya d aga gira yana murmushi kad an -kad an yana jinjina Kai alamun  yes tukunna ya ce
  Okay!!&  
sai kuma ya kwashe da dariya.

Da sauri Yashjub wanda dama
tunda ya yi masa tambayar a take ya fara jin inama he can take it back(inama bai yi ba), ya ce
  ka ji matsalar ka, ko?
Ba abun da kake tunani bane ba tou, she just looks like someone (ta yi min kama da wata) shiyasa nake so in yi confirming (in tabbatar)
Ita d in ce ko ba ita bace ba, that s all.

Cikin son k ok arin danne dariyar tasa dan ya lura mutumin nasa har ya dan k ule, Sir Najeeb Win ya ce
  Maybe ita ce, a ina ka san wacchar d in? 

Cikin rashin gaskiya Yash ya ce   A uk, neighbor d in mu ce, amma gidan nasu gaba d aya sun dawo Nigeria, har ita.
Last year 

  Girlfriend?? 
Najeeb ya sake jeho masa tambayar yana mamakin yadda Yash d in ya k irk iro k arya haka tashi guda ya zabga masa.


Cikin d an d aga murya
Yashjub ya ce
 I said neighbor!!(ma?ociya fa na ce maka)
Ko ife-ifen d alibai ya kurmantar da kai ne ban sani ba?.
Ma?ociya ce kawai.
ka fad a min sunan ta kawai mu wuce gurin 
Ya k arashe maganar tasa a k age, dan ji yake yi kamar ya shiga ta waya ya zak ulo sunan nata daga cikin bakin Najeeb d in.

A hankali Najeeb ya ce
  Gaskiya ba ita bace ba!..
Yarinyar da ka gani Wazu I don t think ta san ko hanyar airport ma.
ko last time da kyar ta yi registration fa, har aka fara exams tana cike crf, da farko ma k in yi mata signing mukayi
sai da hod ya ce  mu yi mata tana da d an issue
tukunna 

Zuwa wannan lokacin Yashjub ya fara ji kamar ya shiga ta waya ya shak o Najeeb!
Dukda tashi d aya ya ji damuwa daga jin labarin nata
amman kuma jan ran da Najeeb yake ta yi masa ya gama k ular da shi dan haka ya kira sunansa da dakakkiyar murya, ya ce
  Najeeb! 

  Na am,Yash. 
Najeeb d in ya amsa

Ya sunan Yarinyar da na gani Wazu a office d inka? 


Sarai dama Najeeb ya gano shi, ya fahimci inda ya nufa..
Kwana-kwanar da ya tsaya yi masa ce ta sanya shima ya so ya ja masa rai amma jin yanayisa ya sanya kawai ya hak ura!
Ya san zai dawo gareshi, soon.
Dan haka kawai sai ya ce masa
  Manubiya Musa 

Ajiyar zuciyar da Yash ya sauk e saida Najeeb d in ya ji,
dan haka kawai ya yi murmushi a ransa
Ya na adduar  Allah ya sa su daidaita
dan ya san idan
Yashjub ya samu ya auri wadda yake so to zai fita daga wannan k uncin da ya d aurawa kansa k arfi da yaji ta dalilin miskilanci&
Yo miskilanci mana, saboda in ba
hakan ba
Mutum successful kamar Yashjub ace wai ba shi da aiki sai yamutse fuska da fushi da rashin hira da dariya da walwala, kullum& & & &


Yashjub yana gama jin sunan Manubiya ya yi sallama da Najeeb. ko komawa bai yi ya kwanta ba
Ya hau instagram ya shiga searching  Manubiya Musa
dan ya san idan ya samu ya ga pictures Winta complete maybe zai samu ya W an rage damuwa
ya samu ta daina yi masa yawo a ido da kunne& .
Sai dai kuma sam bai samu ba!
Shine twitter!!
Shine Facebook!!!
Ko ina sai da ya duba amman sam bai samu ba
Dan ko da ace bai santa ba idanuwan waenda ya ke gani masu irin sunan ta sam ba irin nata bane ba&
Dan haka tashi d aya yake fahimtar ba ita d in bace ba.

Tunani yayi  ko dai ya sake kiran Najeeb ya tambaye sa ko tana da wani nick name sai kuma ya ga in ya yi hakan Najeeb Win zai ga zak ewar sa,
kuma ya san yana tambayar sa ma shikenan
zai fara judging d in sa, dan haka sai kawai ya hak ura ya koma ya shiga searching  Manubiya eyes
A tunaninsa maybe friends d inta da hakan suke kiran ta!
Tunda shakka babu Idanuwanta are one in a million.
Ya jima yana Abu d aya kafin chaaan kuma ya yi shiruuuuu!
Ya fara tunani da auna wawtar sa.

Shiruu yayi shi kaWai!
Yana mamakin yadda ya haukace tashi d aya, dan shakka babu wannan d an k aramin haukane yake yi&
A hankali ya ajjiye wayar ya dafe goshin sa, sai da ya d an nutsu tukunna ya ja ya kwanta ya shiga sauk e ajiyar zuciya a jejjere.

Yana kwanciya tashi d aya
tunaninta ya dawo masa&
Me yake damun ta?!
Me ya ke saka ta saurin kuka?!
Me yake saurin breaking d inta!!!
Ya akayi bata samun kud in registration da wuri??!& .
Runtse idanunsa ya yi da k arfi
cikin b acin rai ya yi tsaki!!!
kafin a fili ya ce
  Yau ni kam na had u da aljana  .

  Wacece aljanar?? 
Muryar Mommy wadda ta shigo yanzu ta daki dodon kunnuwansa.

Sarai, ya ji ta.
Sai dai bai bud e idanunsa ba ma
ballantana ta yi tunanin samun amsa daga gare shi.

Wani maWaukakin tashin hankali ta danne da kyar, kafin ta k araso ta tsaya a kansa tukunna ta sake cewa
  Wacece aljanah?? 

Sai da ya d an d auki lokaci
tukunna ya bud e Idanuwansa ya kalle ta sannan ya ce
  Daddy ya ce gobe zai zo, da daddare. Yana buk atar ganin kowa.
Sannan kin gayawa Yasir da Bakinki yadda kukayi da shi? .

Cikin inda inda ta ce
  Shi Daddyn me ya ce maka mun yi da shi??
Me yace maka na ce?  .
Ta yi maganar ta na mai zama a Bakin gadon wajen ?afafunsa.

Sai da ya d an yi murmushi kafin ya ce
  Nothing.
Ya ce dai kawai ki san yadda za ki yi da Yasir kafin ya zo, dan idan ya zo a goben baya son jin wata magana game da komai kuma,
akwai important abun da zai kawo shi!
So kar a zo ku bashi kunya  .
Yana gama fad in haka ya mik e ya ce   sai anjima 
daga haka ya nufi k ofa.

Da sauri ta mik e ta ce
  Yash.
Wacece aljanah? 

Juyowa kawai ya yi ya kalleta,
kamar zai ce wani abun!
Sai kuma kawai ya sauk e wata nannuyar ajiyar Zuciya
daga nan ya sa Kai ya fice ya barta nan a tsaye& &


Gaba d aya Kan Mommy d aurewa ya yi, ta rasa mafita game da lamarin Daddy da kuma Yashjub, da su da maganganun su duk sun taru
sun d aure mata Kai kwarai.
& & .
Kamar yanda Daddy ya fad a, washegari da daddare
bayan sallar isha a,ya zo.
Tare suka shigo da Yashjub wanda dawowar sa daga masallaci kenan ya had u da su suna parking dan haka ya jira suka shigo tare.

Suma gama zama ya haura sama domin yana son magana da Mommy kafin ta sauk o saboda kar ta ga bambarakwai.


BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*13*

Waya ya same ta tana yi, da alama da Uncle d intane
(yayan Abban ta& .)
Yanayin maganan nata ya sa ya yi tunanin maybe ko k ara ta kai.

A hankali ya nemi guri ya zauna yana mai lumshe idanuwansa a ransa ya ce
  In ban da abun Mommy, ta bar Abb oi ya huta mana, Mutum ko gani bayayi sosai shekaru sun ja amman tana d aga masa hankali, tabbas shiyasa bata shiri da ya yan da jikokinsa
dan sun lura kashe musu shi take k ok arin yi da tension d in matsalolin ta& & 

  Yash! 
Muryarta ta katse masa tunani.
A hankali ya bud e idanuwansa
kafin ya mik e ya k arasa bakin gadon ya zauna ya ruk o Hannayenta.

Tunda ta ga yayi mata haka
ta fahimci abu mai matuk ar mahimmanci zai fad a mata,
dan haka ta tarkata ilahirin hankalinta zuwa gare sa,
kirjinta yana mai dukan uku-uku.

Gaba d aya tashi d aya sai tausayin ta ya lullub e sa, dan haka ya sake runtse Hannuwanta a nasa tukunna ya fara magana
  Mommy dan Allah ki yi hak uri,
duk abun da zan fad a miki yanzu inaso ki danne Zuciyarki, ki yi
hak uri, ki fahimce ni  .

Zuwa wannan lokacin gaba Waya hankalin Mommy ya gama tashi, da kyar ta samu ta iya ce masa
  in shaa Allah, Yash  .

A hankali ya ce   Su Daddy sun zo, suna k asa shi da bak uwa,
mun samu k arin member a family d in nan, jiya& & .
Inaso ki fahimci ba wai saboda kun samu matsala ne shiyasa ya yi miki kishiya ba, dama chan akwai plan d in b oyewa yayi.
Nima ban sani ba sai last week
But I think an d an matso da d aurin auren kusa saboda a yadda na sani kamata yayi ace yanzu saura two weeks.
Mommy dan Allah ki yi hak uri
na san dole za ki ji babu dad i, ni kaina ina jiye miki, kinga dai bani da ko budurwa
amman ko tunani na yi
 For instance (misali)ace
Inada budurwa, ta je tana kula wani to bansan ya zanyi ba!!!
Ballantana kuma ku da ku ke ma aurata.
Ki yi hak uri, na san babu dad i
amman a yadda Daddy yake a yanzu
Idan kika b ata masa rai tabbas ban san kuma mai zai yi ba!.
Ki yi hak uri Mommy na san kina hak uri da Daddy amma dan Allah ki ?ara ki sake hak uri!!!
For us & . 

Tunda ya fara magana ta kafe shi da idanuwa ta kasa motsi, sai da ya sake runtse Hannunta dake cikin nasa
tukunna ta yi fir-gi-git!!!
Tabbas they saw it coming(dama sun gani), amman ba su yi tunanin kwana kusa ba!
 Innalillahiwainnailaihirrajiun
Ta shiga ambatowa a k asan ranta..
Ta manta rabon da ta shiga tashin hankali Irin wannan a rayuwarta, sam ta manta!!

Ta ma kasa kuka& ..ji take yi kamar an tsunduma Zuciyarta a cikin talge! Saboda tsabar azabar da tsananin tashin hanakalin
ya tsunduma Zuciyar tata a ciki.
  Mommy! 
Yashjub ya sake kiran sunanta.

A hankali sannan da kyar ta k ak alo wani murmushi wanda ya fi kuka da ife-ife ciwo!
Tabbas wannan babban tashin hankali ne da aiki ya same ta, amma
ta wata fuskar kuma dama ce ta samu na gyara tsakaninta da Yash, dan yadda ta hango tsantsar tausayinta da kulawa a gareta
A idanuwan Yashjub yau
wataki ila wannan auren da Daddy yayi ya janyo mata kulawa da sha?uwa a wajen d annata. Ta lura kamar yadda kishi yake weakness d in Daddy haka Yashjub shima&

A hankali ta ce
  Zan sak k o Yashjub, ka je k asa kawai, zan taho.
I need some time alone(ina bu?atar kasancewa ni kaWai, yanzun.

Har zai mik e sai kuma ya janyota zuwa jikinsa ya yi hugging nata ya shiga bubbuga mata baya alamun rarrashi&
kafin ahankali ya ce
  Ki yi hak uri Mommy, Allah zai baki lada 
Daganan ya cikata ya mik e ya fita.

A bakin k ofar d akin suka yi kiciSis shi da Baaba Larai alamun shiga take shirin yi shi kuma ya fito.
Murmushi kawai ta yi masa daga nan ya nufi k asa inda su Daddy suka jiran su, ita kuma ta shige.
*Baaba Larai* cousin d in Mommy ce, kamar yadda Mahaifiyar Mommy ta haifesu su biyu kawai (ita da Ammin kausar)
Haka itama kakarta ta haifi maman ta da maman Baaba Larai kawai, sai dai ita Baaba Larai ita kad ai aka haifa sannan har gobe Allah bai bata Mijin aure ba!!
Tun tana budurwa dama bata da samari& .
Idan k awayenta suka yi aure
sai ta koma wajen k annen su da k awance!!
Hatta da niece d in k awarta Baaba Larai ta tab a yin k awance.
A lokacin da ta kai shekaru talatin a duniya sai y an k auyansu suka fara d aura mata sharrin *Maita!* wata?ila ko dan sun ganta fara sol ga gashi sannan kyakkyawa amman babu Miji ne, oho.
A lokacin Mahaifiyarta ta jima da rasuwa,
shiyasa Mahaifiyar Mommy ta d aukota daga gaban Mahaifinta da Matarsa ta ce za ta ci gaba da rik eta, dan sharrin dama ya samo asali ne daga bakin Matar uban.
A yanzu kuwa iyayennasu duk sun rasu shiyasa suka rungumi juna su uku
Ita(Mommy), Baaba Larai da kuma y arsu Kausar.

Badaban shi Kansa Yashjub ya san Yahanasu y ar kishiyar Mommy ce ba to da sai ya ce
 Maybe a wajen Baaba Larai ta gado rashin auren
amma dukda haka a kullum adduarsa itace  Allah ya sa kar y ar uwar tasa ta k are kamar Baaba Larai 
Dukda kuwa cewa
 ita Yahanasu tanada samarin
kawai idan an zo maganar aure ne ganga-ganga da ikon Allah sai wani abun ya zo ya tarwatsa& & .
Amma still yana yi mata adduar kar ta ?are kamar Baaba Larai, a kullum da ko da yaushe& .

  Tana Ina? 
Muryar Daddy ta katsewa Yashjub tunani.

  Tana sauk owa  ya basa amsa yana me k arasawa cikin parlourn sannan ya nemi waje ya zauna suka sake gaisawa da Anty Amarya. Dama shi ya riga ya santa dan employee d insu ce, kawai dai bai san akwai abu tsakaninta da Mahaifin nasa ba sai yau da ya ganta a matsayin Matar ubansa.

Kafin su Mommy su sauk o, Daddy ya kira Yadira ya ce mata ta kirawo mada kowa hatta drivers da masu gadi da Kausar& .
Yassir ne kawai bai hallara a wajen ba saboda har zuwa wannan lokacin bayan sati biyun da ya shafe baya gidan bai kai ga kenan dawowa ba, ya ma kashe wayar da ya tafi da ita gaba d aya.

Mommy bata wani b ata lokaci ba suka sauk o itama tare da Baaba Larai!
She looks calm amman fa ana

13 / 51