Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   36 / 51

105K to 108K   out of 151.9K words

yana zuwa suka saka inna a motarshi suka kaita gidan Ya Musbah, kana ganinsu ka san suna cikin tsananin tashin hankali Jidda kam in banda hawaye ba abunda takeyi, ya Musbah ma da kyar ya ke iya rik e kwallarsa, dan basu da tabbacin dawowar tasu&

Baraka tana kitchen ya lek a ya ce mata   za su je wani waje, ga inna nan a d akin bak i. 
Bata ko kalle sa ba ballantana
yayi tunanin zata amsa shi.
Hakanan ya juya ya bar mata kitchen d in, ya samu Muhsin yace masa  in yana buk atar
wani abu ya je ya kira anty Aisha
daga haka ya kama hanya ya fito ransa duk ba dad i.

Yana zama a cikin motar, Nafi u ya lura da yanayin shi dan haka ya ce   in ba zata yarda ba Musbahu kawai mu kai Inna wajen Aisha, tun d azu da ka kirani dama na kira ta na gaya mata, dan da ni da ita duk mun d auka a gidana ma za a ajjiye innar a wajenta& shiyasa ma har ta gyara mata d ayan d akin bak in dake a tsakar gida. 

Girgiza kai kawai ya Musbah ya yi kafin yace  karka damu Nafi u.
ba zai yiu ace ni da
gidana amma mahaifiyata ba zata shiga ba! ba zai yiu ba!.

Ka bar batun Baraka kawai, dan bata da lissafi da ishashshen hankali, mu yi sauri mu yi abunda yake a gaban mu kar mutanen nan su fara shirme. 


A bakin titi suka tsaya suka d auki Manubiya tukunna suka kama hanyar Bankin&

cikin d aurewar Kai Ya Nafi u
Ya ce
  Ni fa duk ban gane komai ba, wanne irin banki ne za su ranta kud i iya na kwana uku
kuma su ce za su kama Mutum tashi d aya?

Sannan na ji kace Baban ya ce maka da kansa ya je bankin to ya akayi kuma suka kamashi???? 

Ajiyar zuciya Ya Musbah ya sauk e kafin ya ce   wallahi nima kaina a d aure yake da lamarin nan, na dai san sharrin Yusuf ne bani da tantama shi ne ya had a komai.
Shi kuma Baba ya yarda da shi,
kuma ka san shi da b oye b oye,
sannan ya ?i yin shawara da kowa har ta chab e.
Bara dai mu je d in, sai mu ji komai, Allah ya shige mana gaba. 

  Ameeen 
gaba d ayansu suka ce, daga haka motar ta d au shiruuu kowa yana tunani da fargaba, dan haka suka shiga jero addu o i a cikin ransu.


Aikuwa da suka je abun da suka yi zato d in ne, dan ko cikin bankin ma ba su shiga ba a waje ake case d in, saboda babu bashin banki tsakanin Baba da banki.
Bashi!
a tsakanin Baba da wani mai kud i ne wai shi  Black Snake
wanda k asa take zarginsa dan a file d in nashi ma har da case da efcc suna kan yi& .

A jikin takardar
& .Baba ya tambayi Mutumin aron miliyan d aya, akan yana buk ata urgent kud insa sun d an mak ale amma suna fitowa nan da 2 days zai maida masa har da interest!.
Idan bai maida ba kuma to ya yarda Mutumin ya yi masa
duk abunda ya ga dama&

Su ya Yusuf su suka yi shaida suka tsaya a tsakani da shi da
wasu Abokan shi guda biyu.

Babban abun takaicin
shine yadda Mutumin ya ?i baiyyana su gansa balle su samu su yi mishi magana!!!
an ma ce musu baya ma k asar gaba d aya&
Wasu mutane ya aiko su biyu
bak ak e murd ad d u, waenda ana ganinsu kallo Waya an san babu d igon Imani a tare da su.

Ana cikin haka aka ce   ai case ya tashi anan, awa uku da aka bada ta cika dan haka yanzu sai dai a tafi da shi
Police station.
Kamar wani shahararren b arawo haka aka datsa masa ankwa, aka saka shi a mota.

Gaba Wayansu Yaran suna kuka haka aka tafi da shi.

Ba tare da b aata lokaci ba suka bishi a motar ya Nafi u.

Suna zuwa suka tarar da wani sabon tashin hankali  Wai an bada order, a yi masa horo mai tsanani,

Gashi an k i a basu bail d in shi.


D ayan police d in ma ce musu yayi  su gudu.
Saboda wai black snake d in tun d azu ya bada order a kama har family d in Baban a had asu waje d aya..

Suna tsaye a reception suka fara jiyo ihu, babu yadda ba su yi ba amma aka hana su shiga& .

d ayan police d in ne ya d an kwantar musu da hankali ta hanyar ce musu  ai ba ihun Baba baneba sannan ya basu shawarar  su je su nemo kud in, tun kafin abun ya fi haka lalacewa

Da kyar dai aka samu suka hak ura suka yi waje a gigice masu hawaye suna yi
masu kuka sunayi.
suna fita
Ya musbah da ya Nafi u
kowannensu ya d au waya suka shiga neman mafita a rikice.

Sun shafe sama da awa d aya
suna tambayar jam ar da suka sani bashi amma daga Ya Musbah har Ya Nafi un kwata-kwata dubu ashirin suka had a& .

Uncle kanshi dubu uku ya turo ta acc d in ya Nafi u ya ce
 su jira sa, in ya tashi a aiki zai zo ya duba Baban.


Gefe Jidda ta koma ta fashe da wani sabon kuka, ji take kamar ta gudu& ..
Saboda ita Manubiya ta yi aikatau a gidan Ammi!
sannan yanzu ma gashi saboda ita aka kama Baba!
in ba dakyar ba kuma ta san Ya Yusuf ne ya ce ayi masa horo mai tsanani, so yake ya rama dukan da suka yi mishi.

Kuka gaba d ayansu suke yi daga ita har Manubiya&
Su ya Musbah kuma in banda waya ba abunda suke yi dan kaff
d an kud in hannunsu ma duk ya k are a siyen kati.


Suna tsaye a harabar police station d in sukaga wasu polisawa sun fito da tray da almakashi da wasu k arafuna akai duk jini,
sun nufi fanfo suna ?arasawa su ka hau wankewa& .

Tun kafin kwakwalwar Manubiya ta gama d aukar charjin  watakil jinin Baba ne wannan& 

ta kwasa a guje ta yi cikin police station d in, da kyar ta iya tsayawa ta shiga tambayar police d in da ya biyota da niyyar taro ta. Tana kuka ta ce  ka bar ni in ga Baba, saboda Allah da Annabi.
Tausayi ta bashi dan haka ya nuna mata k ofar inda Baban yake, ya juya kawai, a ransa yana mamakin  mai ya had a waennan kamilallun mutanen da Black snake.

Juyawa ta yi zata koma dan ta baro d akin a baya, suka yi ido huWu da su Ya Musbah, ashe sun biyota a baya suma, duk a gigice.

sai da suka je bakin k ofar d akin kuma duk sai suka kasa shiga,kowa yana jin tsoron abunda zai shiga ya tarar.

Da kyar Ya Musbah ya yi ta maza ya tura k ofar ya shige!
daga haka suma suka samu kwarin guiwar mara masa baya.


Turuss! ya Musbah da ya Nafi u suka ja suka tsaya& .
Su manubiya kuma suka saki wani irin kuka.

A kwance suka sameshi daga shi sai vest da dogon wando&
In banda karkarwa babu abunda jikinsa yake yi, da alamun bai ma san waye a kansa ba, ga jini a zuzzube a k asa!
Sai da suka matsa kusa dashi sosai, dakyar, tukunna suka lura ashe har da faratunsa na k afa d aya guda d aya da na Hannu yatsu biyu suka fara zarewa.
Da sauri suka zauna a gabanshi Jidda ta d aura k afafun shi akan cinyar ta Manubiya ta shiga goge masa gumi tana yi masa fifita, suna yi suna kuka a rikice.

A zuciye ya Nafi u ya mik e cikin fushi ya ce
  Wanne irin rashin imanine da dak ik anci wannan?
A haka zai fito musu da kud in nasu? 
Sai kuma ya nufi hanyar waje.

Da sauri Ya Musbah ya sha gabansa ya tare sa.

Cikin fushi ya Nafi u yace   matsa,matsamin in je in samesu

Cikin son fahimtar da shi ya Musbah ya ce   Nafi u idan rai ya b aci hankali ba ya gushewa&

ka je ka samesu ka ce musu me?

kud i fa aka basu aka basu order kaga kuwa dole su yi abunda aka ce, kuma baka karanta takardar bane?
mutum bai saka hannu bama ya aka k are ballantana an saka hannu?

Dole su yi abunda aka ce!

Kuma ko Ina za mu je babu wanda zai tsaya mana, idan ka yi fad a ko kuma ka ce zaka tada rikici yanzu sai a had a da kai saboda baka da kud i nima bani da kud i shima Baba bashi da kud i.

Ka tsaya yanzu mu nutsu mu San abunyi mu ceto Baba, dan hayaniya da rikici ba namu bane ba. 

Da kyar dai ya Musbah ya samu ya d an kwantarwa da ya Nafi u hankali aka samu ya nutsu kaWan.

Yana huci ya ce   na ji, ka fi ni gaskiya, ba zan je in same su ba amma wallahi tallahi
duk wanda ya shigo da niyyar sake yin wani hauka anan wajen sai na illatashi.
Ina nan ba inda zan je  .

Lumshe ido kawai ya Musbah ya yi ya bud e ya ce   ba za su sake ba, in ma bamu samu mun had a kan kud ad en ba, ba komai ni sai in fanshe sa  .

daidai nan Abbakar ya shigo wajen shima a rikice. Yana ganin Manubiya da yanayin kukan da take yi hankalinshi ya sake tashi..hankalin nashi bai gama tashi ba sai da idanuwansa suka kai ga Baba.
Da sauri ya k arasa ya na salati
sai kuma ya kalli Manubiya, kamar jira take yi kuwa a take ta sake fashewa da wani sabon kukan.Ji yayi kamar shima ya sa kuka, da kyar ya samu ya tsugunna inda take a ahankali
ya d aga hannu kamar zai shafa fuskarta sai kuma
ya sauk e hannun jiki a sanyaye kafin ya runtse idonshi da k arfi ya bud e tukunna a hankali ya ce
  Ki yi hak uri Manu, za mu san yadda za a yi inshaaAllah..
d azu
ya Musbah ya kirani yake gaya min,
3k ne kawai a acc d ina na tura mishi yanzu kuma ga 20 na sake nemowa& ki kwantar da hankalinki za a samo, kin ji, dan Allah ki daina kuka 

Da kyar ta samu ta ce
  Abbakar kafin nan mukasan mai za su sake yi masa? kall & ..


K arar bundugun da suka ji ba k ak k autawa tare da hayaniya da k arar motoci ne ya sanya duk suka yi tsit.

Basu gama tunanin mai ya faru ba suka ji an banko k ofar da mahaukacin k arfi an shigo da gudu&
*MANNUBIYA*
*36*

K arar bundugun da suka ji ba k ak k autawa tare da hayaniya da k arar motoci ne ya sanya duk suka yi tsit.

Basu gama tunanin mai ya faru ba suka ji an banko k ofar da mahaukacin k arfi an shigo da gudu&

Body guards ne bak ak e k irin da su sanye da bak ak en kaya da bak in glass&
biyu na farkon suna rik e da manya manyan bindigu, ragowar na bayansu kuma k anana ne a sak ale a gefen k ugun ko wannensu.


Yanayin wajen suka kalla dan haka d aya a cikin su ya juya ya fita da gudu, ya je ya kawo kujera ya ajjiye, kafin ya koma ya shiga cikin layi biyun da suka yi a jere tundaga bakin k ofar har izuwa inda suka ajjiye kujerar a gaban Baba.

Tsayawa kawai su Manubiya suka yi gaba d ayansu suna kallonsu..

Basu kai ga gama tunani da lissafin abun ba, tashi Waya suka fara jiyo wata iriyar dariya ana yinta cikin
wani kalar sauti da kuma murya marar dad in sauraro& .

Yadda ake dariyar ne zai sanya tashi d aya a
fahimci rashin kamala da rashin sanin ciwon kan mamallakin muryar& Yana magana da turanci yana dariya sosai kamar wani tab abb e!.

Yadda su ke jiyo muryar tana matsosu ne ya sanya suka fahimci Mutumin nan cikin d akin zai shigo..


Ta tsakiyar body guards d in nashi waenda suka hau layi ya bi ya shigo&
?ato ne sosai, dogo, lukuti, fari sosai..farin nasa irin jaaa!! ?innan.
Babu gashi ko
guda d aya tun daga scarf d insa (fatar kansa) har gemun sa da gashin baki duk babu gashi!
Iya kar girar sa da gashin idanunsa ne kawai masu gashi a kaf ilahirin kansa zuwa fuskarshi wanda hakan ne ya basu damar ganin asalin yanayin fuskartashi
wadda take d auke da
k ananan Idanu jajaye, da Wan
guntun Hanci, yayinda Bakinsa ya kasance madaidaici.

Yadda dpo yake binsa yana russuna masa yana yi masa magana kamar zai kwanta
abun dole ya k ular da jama a&

dariyarsa kawai yake ta yi shi kam at the same time yana bawa dpo amsa, har ya iso inda Baba ya ke!.

Shiruu ya yi ya tsayar da dariyar tasa kafin ya kalli dpo tukunna ya ce   ku ka ce yana kan karb an punishment (hukunci)
But (amma
nagani he s still conscious,Y(har yanzu yana cikin haiyyacinsa, mai yasa?)?  .
Yayi tambayar yana mai zubawa dpo jajaye idanuwansa.

A take dpo d in ya rikice ya fara kame-kame ya shiga
karanto addu o i daban-daban a k asan ransa yana mai neman tsari daga sharrin  Black Snake !
Dan kasancewar yanzunnan ya gama raha da dariya da shi
ba shi zai hana shi sauya masa kamanni a take a wurin ba!..

kamar kuwa ya sani dan tashi d aya black snake ya gama rayawa a ransa  zai sanya body guards d in shi su yi wa dpo asalin horo, a yanzu a gaban kowa, ta yadda next time zai fahimci mai ake nufi da horo!!
dan haka ya d an d ago kansa da niyyar juyawa ya kira biyu a cikin body guards d in shi amma sai
Idanuwanshi suka sauk a akan Manubiya
wadda gaba d aya tashi d aya ta rikice sannan tsoro ya lullube ta daga ganinsa!
Ba abunda ya fi d aga mata hankali irin zanen bak in macijin da ya fito tarr!!
wanda yake nan a kwance a hannunsa na dama& tun daga kwanjinshi har kan bayan tafin hannunshi
kamar na gaske
ga wasu uban sark ok i a jikinsa wuya da hannu da wani burgujejen wando shima mai sark ok i a jiki amma kuma rigar jikinsa armless(marar Hannu).

Wata mahaukaciyar dariya ta ga ya kwashe da, ga mamakinta kawai sai ta ga ya nufota aikuwa kafin ya k araso tuni ta shige bayan Ya Musbah ta b uya.

Da mamaki ya kalleta ya juya ya kalli Jidda sai kuma ya juya ya kalli d aya daga cikin bodyguards d in nasa ya ce
  John!dama ita biyu ce? 

  A a ai dama Kabir d in ya ce tanada sister, remember(ka tuna)? 

Dariya ya yi kafin ya juya ya shiga yi wa Manubiya wadda ta b uya a bayan ya Musbah
wani irin kallo har da lek awa yake yi yana sakewa saboda a yadda Abokin Ya Yusuf ya yi masa bayani tabbas Yarinyar ta fi haka kyau a fili..

Ya Musbah ya kalla ya kalleta
kafin ya yi wani kalar murmushi..

Ba su gama fahimtar ma anar murmushin nashi ba suka ga ya yi fito!.
Da sauri Waya a cikin body guards d inshi ya zo ya hankad e Ya Musbah ya fisgo Hannun Manubiya ya dawo da ita gaban black snake ya tsayar, tukunna ya juya ya koma ya je ya tsaya a wajen tsayuwarshi.


Cikin d an d aga murya ya Nafi u ya ce
  Me ye haka wai? 

Ba wanda ya ko kalle sa balle su bashi amsa, a hankali black snake d in ya sa Hannu ya d an kamo hab ar Manubiya ya d ago yana mai k are mata kallo.

Da sauri ta kawar da kanta gefe, tana wani irin kuka& dan gaba d aya a tsorace take
ga tashin hankalin da take a ciki tun farko dama ga kuma zuwan wannan abun tsoron
shiyasa duk ta bi ta sake duburcewa,
in banda karkarwa babu abunda jikinta yake yi.

  Mallan kana haukane! 
Ya Musbah wanda ya taso yanzu ya fad a a Zuciye yana shirin yin kan black snake d in&

A take wani a cikin bodyguards d in nashi ya saita masa bindiga..

Da sauri Baba ya ce   dan Allah kar ku yi musu komai, dan Allah
sai kuma ya fashe da Kuka.

Shi kam black snake gaba d aya hankalinshi ya tashi
da ganin Manubiya!..
Babu k asar da bai je ba a rayuwarshi sai dai in da ba a rasaba, amman ba zai yi k arya ba duk yawonsa da gane ganensa bai tab a ganin Mace mai kyawu sannan Macen da ta d auke hankalinshi lokaci guda kamar Manu ba.
Kallonta kawai yake yana sakewa
kamar ya samu television& .
Sai da ya lashe Bakinshi tukunna ya kamo hijabinta ta k asa bata yi auni ba kawai ta ji ya d ago shi ya zare ya yar a gefe&

Tabbas ba k aramin zafin tozarcin da ya aikata mata ta ji ba, dukda kuwa doguwar riga ta Abaya ce a jikinta amma ji ta yi kamar ta kurma ihu.
Tashi d aya ta ji wani irin bak in ciki
ya lullub eta, bata san lokacin da ta d aga Hannu za ta kifa mishi mari ba.
Ya Musbah da Ya Nafi u ma duk nufar sa

36 / 51