Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   27 / 51

78K to 81K   out of 151.9K words

bakin k ofar shiga parlourn
suka had u da Yasmin, tana shiga Yasmeen d in kuma tana fitowa..ko kallon ta bata yi ba
Itama Ummin bata kulata ba.

Da sallama ta shiga, ba ta same shi a parlournsa ba sai a chan cikin d akinsa a zaune a kan gado,
Ya yi shiruu alamun tunani yake yi.

A kusa da shi ta je ta nemi guri ta zauna kafin a hankali ta ce
  Barka da dawowa Daddy, ya
meeting d in?  .

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce
  Alhamdulillah 
Daga nan ya mik e ya fad a toilet.

Har ya fito tana nan a zaune,
ta yi zurfi a tunani..

Sai da ya gama shirin bacci tukunna ta ce
  Bara in kawo maka abinci 
Ta fad i hakan tana shirin mik ewa.

Cikin dakatar da ita yace   don t bother, a k oshe na ke. 

Cikin kwantar da murya tace
  Daddy, ka d an ci ko kad an ne m& . 

  Wai Saddik a ni k aramin Yaro ne?d ura zaki yi min ko me?
Na ce miki a k oshe nake amma kin bi kin ishe ni&
daga meeting na dawo Ina buk atar hutu shin baki da fahimta ne????

A hankali ta ce   ka yi hak uri,
Allah ya huci zuciyarka  &

Har zai kwanta sai kuma ya ce
  Ki koma parlour ko kuma ki zab i wani bedroom d in ki kwana,
ban ce ki fita a side d ina ba& kawai ki nemi wani bedroom d in a parlourn.. 
Sai da ya sake cewa  bakya ji na ne? 
Tukunna da kyar Ummi ta ce   to Daddy, sai da safe. 

Washegari da sassafe ta tashi, tunda ta yi sallar asuba ba ta koma ba, dama tun a daren jiyan ta fitar da abincin da ya ce ba zai ci ba ta saka a fridge dan a lokacin hatta gwaggo ta riga ta tafi side d insu na masu aiki.

Had add en breakfast mai rai da lafiya yau ma Ummi ta shiga had awa Daddy&
tana cikin yi su gwaggo suka shigo dan haka ta shiga akayi har na gaba d aya gidan tare da ita.

K arfe bakwai da kwata suka kammala, dan haka ta d auki na Daddy ta nufi sama da shi cike da sassarfa.

A bakin k ofar d akinshi ta same sa yana gyara zaman necktie d insa, tun kafin ta gaida shi ya ce   koma da abincinki yanzu ma, na k oshi 

A hankali ta nufe sa da tray d in a hannunta da niyyar idan ta je ta durk usa ta bashi hak uri, amma tana zuwa kusa da shi tun kafin ta durk usa ya yi wani irin fatali da abincin wanda ta sanadiyyar hakan gaba d aya parlourn, kayan jikinsa da kayan jikinta suka b aci& .

Cikin fushi ya juya ya koma d aki ya bar ta nan a tsaye cikin tsananin tashin hankali da mamaki, bata san lokacin da wasu hawaye masu zafi suka shiga tsilalo mata ba.

Da kyar ta samu ta goge wajen tana yi tana kuka haka nan ta je ta chanja kayan jikinta tukunna ta dawo ta tattare kwanukan ta nufi k asa.

A hanyar stairs ta tsaya ta goge hawayenta tukunna ta k arasa sauk a ta nufi kitchen.
A kitchen d in ta tarar da Yasira Kausar Yasmeen da Ya isha,
da alamun kowa fita zata yi kuma masu aikin ba su gama jerawa a kan dining d in ba shine suka zo suke d iba anan d in&
a cikin su ba wanda ya ce mata ci kan ki haka ta wuce ta ajjiye kwanukan ta shiga wanke Hannunta&
Cikin rashin mutunci ta ji Ya isha na cewa
  Dad ina da talaka bai iya samun guri ba, a yi employing d inka amma ka nemi zak ewa, na rantse da Allah Asabe duk ranar da kuka sake yin letti ba ku jera mana abinci har kuka ja muka makara ba to
ko wacce shegiya sai ta koma inda ta fito, sai ku dinga yin abu kamar ku kuka haifi Mutum& ..
Mtswwwww 
Ta k arashe maganar tata tana mai jan wani uban tsaki,
daganan ta sa Kai ta fice.

Wata dariya Yasmeen ta yi,
Irin wadda ta yi wa Ummi jiya ciki-ciki.

Dariya sosai Kausar ita kuma ta yi kafin tace
  Kin ga Malama, ki saki Baki ki yi dariyarki dan babu uban wanda ya Isa ya hanaki. 

Ahankali amma yadda ta tabbatar Ummin za ta ji Yasira ta ce
  Tana jin tsoron a shiga tsakanin ta da Daddy ne 

Cikin dariya k asa-k asa ta rainin hankali
Kausar tace   au,haka ne fa 

Daganan duk suka d auka abincin da suka zuzzuba suka fita suka nufi dining table banda Yasmeen wadda ta tsaya haWa tea a cikin kitchen d in.
Har Ummi ta fita sai kuma ta tuna akwai flask d in da ferfesun ciki bai gama zubewa ba dan haka ta juya da niyyar komawa ta cewa gwaggwo su juye mai kyau ne&
a k ofar kitchen d in suka yi kiciSus da Yasmeen wadda ta yi kamar irin ta tare k ofar nan ne..ita ba ta matsawa Ummin ta wuce ba sannan ita bata fito ba..

da mamaki Ummi take kallon yarinyar tana so ta ga iya gudun ruwanta.

A hankali Yasmeen wadda ta hango Daddy yana sauk owa daga bene tace  na ga kin shigo da kwanuka a hargitse
kuma idonki kamar kin yi kuka, gaya min gaskiya dukan ki Daddy ya yi?  ..

Dama tun Wazu da kyar Ummi take danne kanta dan bata so ta kula Yaran amman duk maganganun da suka yi a kitchen d in ta san da ita suke ga kuma takaici da tashin hankalin da Daddy ya tsoma ta a ciki tun jiya shiyasa duk yadda ta so hana kanta ta kasa dan haka ta d aga Hannu ta zabgawa Yasmeen wani irin gigitaccen mari,
dai-dai nan kuma Daddy ya k arasa saukk owa cikin parlourn.

Wani irin kuka Yasmeen ta saka ta durk ushe a wajen ta dafe kunnnenta tana ihun   Wayyo Allah kunnena 

Dai-dai nan Daddy ya k araso wajen a gigice, da k arfi ya ce
  Innalillahi wa inna ilaihirrajiun 
sakamokon ganin jini yana zubowa ta kunnen Yasmeen.

Sai a lokacin Ummi ta ji ashe wai  Yasmeen tana da abu a cikin kunnenta wanda ya ke zuk o mata magana sakamokon rashin aiki da kunnuwan nata basa yi sosai.

kuma ba kunya ba tsoron Allah a take Kausar har da rantsuwa ta yi tsalle ta dire wai  ai sun gayawa Ummin jiya da ta yi yun?urin marin Yasmeen d in amma shine yau sai da ta mare ta, shikenan yanzu in ba da kyar ba ta danna mata abun chan ciki ta lalata mata kunne gaba d aya.

Cikin tsananin gigita Ummi ta ce
  Kausar ki ji tsoron Allah, yaushe& .

Wata rikitacciyar tsawa da Daddy ya buga mata ce ta sanya ta kasa ci gaba da magana& cikin tsananin fushi ya ce   ki b ace min a wajen nan tun kafin na illataki . 

A hankali sannan k afafuwanta suna wani irin karkarwa ta samu da kyar ta juya ta kama hanyar sama zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Yayinda su kuma suka d unguma kai Yasmeen asibiti, gaba d ayan su.
" " " " " "
Sai yau Manubiya ta d auki wayarta a jikin charji daga gidan Ammi,
dan sai da ta bar wayar ta yi awannin da aka rubuta ana buk atar ta yi a jikin charjin. Layinta na jiya da suka yi wa register ta saka, bayan kamar 30 minutes ta d auki wayar ta dudduba daganan ta d auko katin Yashjub cikin nutsuwa ta juye numbersa tukunna ta tura masa sak o kamar
haka
  Good morning Sir(ina kwana sir), yau na kunna wayar tawa daga charji, my mail is empty as for today(yau, mail Win nawa ba komai a ciki)..idan sun turo I ll report everything to you on Friday (zan haWa in sanar maka komai ranar juma a)..
InshaaAllah
Thankyou(na gode)...
Manubiya Musa.. 

Fitowar Yashjub daga wanka kenan dan lokacin 7 dai-dai,itama Ammi ce ta ce mata ta tabbata ta je da wuri fiye da yadda take zuwa kullum, wai tana da bak in da za su zo daga Abuja so akwai aiki sosai..

Yana fitowa ya ga wayarsa ta yi k ara dan haka ya k arasa ya d auka ya shiga duba message d in, dama ya saka a ransa maybe ita d in ce dan tun jiya yake ta jiran ya ga kira ko messge d inta.

Murmushi kawai ya yi, ya sake karanta sak on ya kuma maimaitawa ya sake maimaitawa kafin ya ajjiye wayar da kyar yana mai sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya&
yanzu mene ne abun yi, saboda duk taurin kansa da kauce-kaucen sa ya riga ya sak k o, ya fahimci yana mahaukacin son Manubiya..duk yadda ya yi ta denying yana kaucewa, a iya jiya kad ai ya tabbatar k aunarta yake yi, k auna ba ta wasa ba, amma kuma ta ya zai fad a mata abunda ko Najeeb yana tunanin anya zai iya fad awa kuwa& .
numfashi ya fesar ya nemi guri ya zauna a ransa yace   Yashjub a yadda kake son Manubiya, b oye b oye ba naka bane ba, 
domin
shi kansa ya san yana da buk atar wani abun ya faru soon& a fahimci juna a yi aure tun kafin sonta ya zautar da shi sannan ga wannan cousin d in nata da ya ga take-taken kamar shima sonta yake yi, kasancewar sa na gida ne ya sanya Yashjub yake ganin gara ya d auke Manubiya tun wuri tun kafin iyayenta su yi abunda zai kai sa lahira ta hanyar aura mata Abbakar.
A part from all these (bayaga duk waennan abubuwan ma) a yanda yake jin Manubiya a zuciyarsa da ransa to tabbas
ba ya jin zai iya ci gaba da rayuwa daga nan zuwa watanni hud u ko uku gaba ba tare da ya mallake ta a matsayin matarsa ba& ..

Da wannan tunanin ya shirya ya fice office, ko Daddy bai tsaya jira ba dan yana buk atar ya yi tunani sosai sannan ya san ta inda zai fara Kafin Daddyn ya zo su fara aiki,kuma yana da buk atar lek awa d ayan company d in nasa duk a yau.
& &
Manubiya tana ajjiye wayar ta juya kenan su ka yi ido biyu da Maamaa,
da sauri ta sunkuyar da kanta k asa kafin tace  Maamaa Ina kwana. 
sai kuma ta fara k ok arin fita daga kitchen d in.

Murmushi Mama ta yi sannan ta ce  ni kam Manubiya tsoro na kikeyi ne?
naga kwata kwata kin k i ki yarda ki saki jiki da ni ga shi kuma k addara ta had a mu zama guri d aya,ya kenan? 
Ta k arashe maganar tata da tambaya tana murmushi.


Murmushi Manubiya ta yi
kafin a ranta ta ce
  Tabbas k addara ta had a ni zama guri d aya bama da ke kad ai ba har da wanda nake
gudun ki domin shi. 
A fili kuma sai tace
  Ba komai Maama ba gudun ki nake yi ba kawai dai abubuwan ne suka d an yi min yawa,shiyasa. 

Cikin rashin jin dad i Maama tace  Ayya!na ji Ammi tana cewa mamanki ma ba lafiya ko? 

Ahankali Manubiya ta d aga kanta alamun  eh 

Cikin tsananin jin tausayin ta
maama ta ce
  Allah ya bata lafiya Allah ya sauwwak e, ku yi ta addu a za ta warke inshaaAllah, kin ji ko? 

Ahankali ta jinjina mata kai tukunna tace   nagode Maama 
ta fad a hakan tana mai Jin tsananin k aunar matar na shiga ranta.

Murmushi Mama ta yi, ta matso ta d an shafa fuskar Manubiya
tukunna ta ce
  Allah ya yi miki albarka
daga nan ta wuce ta fita daga kitchen d in..
so gamon jini!!
ita dai haka kurum Ubangiji ya d aura mata k aunar Yarinyar,
tana jinta ne har cikin ranta& & .

BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*28*

Har wajajen 11 shiru babu Daddy ba Yasira a company.
Ba?in da suka yi
ma Yashjub ne ya yi handling d insu shi kad ai, gashi yana ta kiran number Daddy amma baya d auka ita kuma Yasira nambobinta duk ba sa shiga.
Dan haka Ba?in suna tafiya
shima ya kamo hanyar gida.

Sai k arfe 10 tukunna likitocin da su ka karb i Yasmeen suka fito,
cikin son fahimtar dasu
Babban Likitan ya kalle su ya ce
 It s nothing serious(ba wani babban abu bane ba), dan bai tab a komai ba kawai dai d an kurjewa ta yi shiyasa kuka ga jini.
abun nata dama ina so in bata sabo shine kawai muka tsaya aka d an yi dressing wajen na bata sabo na bata drugs da 1 week off ta huta a gida,
Allah ya kare gaba. 

Cikin samun relief dukkan su suka ce   Ameen  sai a lokacin tukunna Yasira ta d au waya ta kira Mommy take gaya mata komai.

Office Yasira ta wuce
Yusra da Ya isha da Yadira kuma school, yayinda Daddy da Kausar suka kama hanya domin maida Yasmeen gida.

Suna shiga Daddy ya cewa Kausar ta kai Yasmeen d akinta shi kuma ya nufi b angaren Ummi& ..
Bai same ta a d akin nata ba ashe ya baro ta a k asa a d akin Yahanasu wadda zazzab i ya rufe tun jiya da daddare ba wanda ya sani.

Munirat ya tarar tana share d akin, cike da girmamawa ta durk usa har k asa ta gaida shi, ba yabo ba fallasa ya amsa
kafin ya ce mata  Ina saddik a? 
A hanakali tace masa
  Tana d akin Adda Yahanasu wadda batada lafiya 

A ranta tana mamakin Allah dai yasa lafiya dan bata tab a ganin shi a dai dai wannan lokacin a gida ba,
kuma a side d in Ummi.

Cikin fushi ya juya da niyyar fita, a bakin k ofa suka yi kicibis da Ummi wadda ta ji shigowar su ta biyo domin ta ji ya jikin Yasmeen d in& .
tunda suka fita ta ke trying numbers d insa, saboda ita shi kuma ya saka wayoyinshi gaba d aya a silent..

Da kyar Daddy ya iya cewa
  Munirat give us a moment
(Munirat bamu waje)
ya fad i hakan idanuwansa a kan Ummi, ba tare da ya kalli Munirat d in ba.

Da sauri ta ajjiye parker da abun sharar ta fice daga d akin, tana tafe tana waiwaye gaba d aya hankalinta a tashe
tana mamakin me ya had a su haka dan ita Ummi bata ce mata komai ba tun Wazu, gashi
ta ga ran Daddy a mugun b ace!!!

ba abunda ya fi d aga mata hankali irin yadda ta ga mood d in nasa, tsoronta kar ta je ya bugi Umminta&
tana tafe tana lissafi tana waiwaye haka ta fice a parlourn, bata yi auni ba kawai ta ji ta afka kan Mutum,
da sauri ta ce   Innalillahi 
sai kuma ta fara k ok arin kwace kanta daga rikon da Yassir ya yi mata.
Tunda ta taho tana kallon baya ya ganta dan lokacin dai-dai shi kuma ya fito daga corridor na side d in Mommy ,
ahankali ya wani lumshe ido ya bud e saboda yauma riga da wando ke jikinta na bacci irin me bin jikin nan, rigar iya cinya wandon kuma har k asa,dan haka a ransa ya ce   lucky me 
Ganin bata gansa ba ne ya sanya shi sake nutsuwa ya ?i motsi gudun kar ya ankarar da ita,ai kuwa da ikon Allah ta afka jikinsa!!!
Without thinking twice shi kuwa ya rungume ta gamgam& .
tana d agowa su ka yi ido biyu da shi, cikin tsananin firgici ta ce   get off me, (ka cika ni) baka da hankali ne 
Ta k arashe maganar cikin tsawa.

Wani irin murmushi ya yi kafin ya ce
  Munirat yo ai ko malaikan mutuwa ne ya zo d aukar raina
to
Sai ya d aga min k afa na gama appreciating moment d innan (godewa lokacin nan)
tukunna .. 

Wani irin kuka ta saka kafin ta fara k ok arin kwace kanta tana magiya tana kai masa duka, ganin tana neman cika masa kunne ne ya sanya ya fara k ok arin kissing d inta& ..
A gigice ta kwala wata mahaukaciyar k ara dai-dai shima Yashjub ya ce
  Yassir 
Cikin tsawa
& & & & .
Achan d aki kuwa, Munirat tana fita
Daddy ya cewa Ummi   Ki had a kayanki, duk wani abunda kika san naki ne, ki tartare, ki bar min gidana 

A hankali Ummi ta ce
  Daddy har me ya yi zafi haka?
Wallahi Kausar k arya take yi, ban san Yasmeen tana da matsala a Kunne ba!
Sannan ya kamata ka tsaya ka ji abunda Yaran nan su ka yi min kafin ka yanke wannan d anyen hukunci hak& . 

Cikin katseta Daddy ya ce
  Na san k arya Kausar ta yi miki, na san basu gaya miki Yasmeen tana da matsala a kunne ba.
Kinsan abu na farko da ya fara had ani da ke?  .
Cikin zubar kwallah Ummi ta girgiza kanta alamun  a a 
Cikin fushi Daddy ya ce
  Ranar da kika zo d akina kika bamu asalin labarin

27 / 51