Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   45 / 51

132K to 135K   out of 151.9K words

nan suka shiga tattaunawa game da lamarin& . 

Yahansu ta san menene so duba da yadda itama ta so first love Winta(saurayinta na farko a duniya) kamar ranta,,saurayin da ya fara yin watsi da ita&
Shiyasa yanzu sam bata ganin laifin Yashjub da ya gigice akan Manubiya& .
Adduarta d aya ita ce  Allah yasa a bashi ita a yi auren kamar yadda suketa tsarawa yanzun, Allah yasa kar su Mommy su kawo cikas d in komai.

Yash yana k aunar y ar uwar tasa sosai..ya lura da yadda su Yasira basa janta a jiki..dukda bai ma san wasu daga ciki hantarar da suke yi mata ba
amman yana yawan tsawatar musu da nuna musu gaskiya,
kawai dai ya san tunda suka riga suka nuna basa sonta to ba lalle ya iya gyara tsakaninsu su dawo su k aunace yadda ya kamata ba. Yanaso ta ji itama ta musamman ce& itama ta ji tanada Wan uwa me kaunarta a ko da yaushe, shiyasa ya ke bata kulawa ta musamman,
kuma har ga Allah yana ji da itan da gasken gaske kuma ita kad aice zai yi shawara da ita ya ji dad i dan sun saba sosai, shiyasa yanzun ma yake ta neman shawarwarin ta&
Ta kuwa ji dad i
tun ba ma da ya ce  itace za ta had a masa lefe ba!
bata san lokacin da ta fashe da kuka ba& .

Yahanasu& .
Ta kan yi kukan rashin jituwa tsakaninta da y an uwanta mata, amma a duk lokacin da ta tuna tana da Yash sai ta ji duk damuwarta ta Kau.

Bata jin a duniya akwai d an uwan da ya ke tsananin k aunar ?ar uwarshi kamar yadda Yash ya ke ?aunarta ya ke ji da ita, ko shawara ce da ita ya ke yi,
ko menene sai ya gaya mata& .
shiyasa har yau har gobe ta kasa yafewa kanta duba da yadda ita ta kasa gaya masa abu mafi mahimmanci na rayuwarsa bayan ta sani, kuma tana da ikon da za ta taimaka mishi wajen samun abunda ta san zai sanya shi farinciki fiye da komai& ..

Ta jima tana kuka har sai da ta
d an fara bawa Yash Win tsoro.

Tukunna ya samu ya rarrasheta da kyar,
ya d an jata da wasa da hira
daga nan suka shiga wata maganar& .
Kafin daga baya ya yi mata sallama, ya tafi bayan ya samu ta hak ura ta karb i number Manubiya kawai
dan da farko cewa ta yi sai ya kira mata ita sun yi video call,,
da kyar ya lallab ata ta hanyar ce mata  Manubiyan ta yi bacci by now. 
daga haka suka yi sallama, ya tafi.



& & ..2 hours before now& & &
& & .awanni biyun da suka shuWe(kafin yanzu)..
Ummi bata wani dad e a wajen su Mommy ba, ta fita ta wuce d akinta.
Bata dad e da fita ba, su Yassira suka shigo, suka taru a d akin har Yasmeen kamar wasu masu meeting.

Mommy ce ta cewa Yasira  ita da Kausar, su je su saka mata ido a k ofar Yahanasu
dan ta san tunda ya ce yana so yayi magana da Yahanasun yau to komin dare sai ya je sun yi, su kuma ta maganar da za su yin ne kawai za su samu haske akan zargin nasu& .


Ba k aramin tashin hankali ta sake shiga ba lokacin da ta kira shi ta ji yana waya, kawai ita ta yadda ta gama amincewa ta bada amanna akan maganar Baaba Larai!!
Shiyasa kwata-kwata kwakwalwarta bata bata cewa  ai waya yake akan business ko wani abun ba!
tashi d aya ta amince kawai da wannan Yarinyar yake ta waya. .


Yassira ce ta samu ta ga Yash d in, dan Kausar ta saman balcony ta tsaya tana jiranshi, ta yadda yana fitowa daga side d inshi ita kuma zata gani daga nan sai ta jira in ya shige d akin Yahanasu ta je ta lab e!!
saboda ta fi kowa k aguwa da son jin menene asalin gaskiyar maganar amma sai Allah bai bata ikon ganin nashi ba dan lokacin dai-dai ya zo zai wuce sai aka yi mata text dan haka bata ga shigar tasa ba.
&
A kitchen Yasira ta jira har ya gama da wajen Daddy ya sauk o ya shiga d akin Yahanasu, tana ganin ya shige ya turo k ofar ita kuma ta fito ta Isa bakin k ofar da sauri ta lab e.


Shiruu Yassirar ta yi tana sauraron su&
Wato dai zargin su ya tabbata kenan, sannan bayaga hakan kuma aure cikin wata d aya ma yake son yi!!!
 Innalillahi wa inna ilaihirrajiun
Ta aiyyana hakan a cikin ranta hankalinta a masifar tashe, ta shiga lissafin& .
 Shin ta ya za su iya
cin nasara akan wannan abunda ya taho musu gadan-gadan haka?.
Babu tausayin wadda ya lullub eta sai Kausar!
Saboda zuwa wannan lokacin idan Kausar Win ta yi wani abun har mamaki take bata, kamar
wata wadda ta fara samun taSin hankali haka so da k aunar Yash suka maida ita, sam bata ji bata gani aduk abunda ya shafeshi & 
Yasira tana cikin wannan tunanin ta ji Yahanasu za ta bud e k ofar
dan haka ta yi sauri ta wuce ta
fad a kitchen.

& Now&
& yanzu..
Sai da Yassira ta ji fitar Yash, tukunna ta fito, tana ji kamar zuciyarta za ta tarwatse,
ta nufi sama.
*MANNUBIYA*
*44*

Kausar na tsaye, ta saman balcony ta hango fitar Yash..
ta yi mamakin rashin ganin shigar shi Win da bata yi ba dan haka ta fito da sauri tana adduar  Allah ya sa Yassira ta samu ikon saurarar su.
Dai dai tana fitowa ta hangi Yassirar ta nufi side d in Mommy a rikice, dan ko lura da fitowar Kausar d in ma bata yi ba.

Da k arfi k irjin Kausar ya buga! yayinda k afafuwanta su ka fara karkarwa&
Da kyar ta samu ta tattaro gaba d aya kuzarinta
ta bi bayan Yassira tana jin kamar zata fad i a k asa dan tabbas wannan rikicewar da ta ga Yassira ta yi tou akwai matsala kenan.



Yassira tana shiga d akin Mommy, duk suka mik e tsaye!.
Dama gaba d ayansu sun taru
Yusra da Yadira ne kawai babu.

Yasmeen ce ta matso kusa da ita ta ce
  Lafiyan ki kuwa? Me ya faru? 

Wani k ululu da ya tokare mata mak oshi Yasira ta hadiye tukunna da kyar ta ce   Ya isha, ku d an fita, Ina son yin magana da Mommy ita kad ai 

Cikin d an b acin rai Baaba Larai ta ce   zancen banza kenan, waye kika gani Bare a cikinmu? 

A hankali Yasira ta lumshe idanunta ta bud e ta na jin tsananin tausayin Kausar har ma da Mommy yana sake lullub eta, kafin ta ce   Ba haka bane Baaba, bana son maganar ta yayatu da yawa ne gudun kar wata a cikin ku ta manta ta yi suSutar Baki a gaban Kausar. 

Dai-dai nan Kausar wadda ta k araso bakin k ofar d akin Mommy ta jaa ta tsaya&
Tabbas a yadda ta ga Yasira d azu da kuma yanda ta ji muryarta a yanzu da abunda ta ji ta fad a, ta san idan ta ganta ba za ta fad a mata komai ba duk runtsi!.
Dan haka kawai sai ta yanke shawarar lab ewa a wajen.

A hanakali Mommy wadda gabanta ya fara fad uwa sosai, ta k arasa inda Yassira take ta ce
  Yi magana Yassira, ko menene ma fad i, za mu iya fuskanta in sha Allah!.
Me ya faru? Wacce maganar ki ka ji Yash suna yi da Yahanasu?  .

Dafe Kai Yassira ta yi, ta matsa gefe ta juya sannan ta d an runtse idanunta ta yi shiru kafin ta bud e ta ce
  Abin ba?in ciki ne sosai!! Ace lokaci guda gaba d aya aikin da ku ka yi tu?uru na shekara da shekaru ya tarwatse, ba tare da mun ci riba ko guda d aya ba  .

Da sauri Mommy ta ruk o ta, ta juyo da ita sannan ta ce
  Yassira, ina son abu na gaba da zai fito daga Bakinki ya tafi kai tsaye zuwa ga ainihin maganar da duk mu ke son ji!
Ki fad a min abunda ya faru tun wuri saboda raina ya fara b aci. 

Kallon ta Yasirar ta yi kafin ta ce   ai ba ki ji b acin rai ba
Mommy sai na ce miki Yash zai yi aure!
Kuma nan da wata Waya na ji ya ce dan haka kinga kuwa an riga an gama komai ma kenan& ba maganar budurwa ake yi ba yanzu, maganar aure ake yi 

Cikata Mommy ta yi da sauri, sai kuma ta k ame, sam ta kasa sake yin motsi.

Cikin takaici Yassira ta ce
  Yes Mommy, Yash zai yi aure
ba tare da kun fahimci juna ke da shi ba, ba tare da mun samu damar amso uban dukiyar da Daddy ya mallaka masa ba, ba tare da ya damu ko ya had a Kai da d aya daga cikinmu ba
Sannan mafi muni Yash zai auri wadda bamu sani ba kuma
ga dukkan alamu yana matuk ar sonta da k aunarta, kinga kuwa zuwa nan da y an shekaru kaWan komai ya zama nata, daga ita sai ya yan su!
mu kuma sai dai kallo! 

Cikin fushi Mommy ta ce
  Yi shiru Yassira, ya Isa haka! 

  Mai yasa? Saboda me zan yi shiru?
Ba kya son ji ne?
Ai gaskiya na fad a, in ba haka ba Mommy ki duba fa ki gani aure ne Yash zai yi ko kuma in ce yake shirin yi nan da wata Waya fa!!! Amman kaff d inmu nan babu wadda ya gayawa, ko kyallin zancen ma babu wadda ta taSa ji saboda tsabar yadda kanmu da nashi yake ba a had e ba!& .
Wannan shegiyar Yahanasun ita kad ai ce ta sani, ita kad ai ya gayamawa, ashe tun farko dama ta san da Yarinyar amman ta yi mana shiru.. 

Cikin fushi Yasmeen ta ce
  Ai ita take cin dunduniyar mu dama, ku gaya min dalilin da zai hanani cin uwar Matar nan yau a cikin gidan nan! 
Ta fad i haka tana shirin fita da niyyar zuwa ta sami Yahanasun.

Da sauri Baba Larai ta sha gabanta, ta rik eta kafin ta ce
  Ba za ki tab a Yahanasu ba Yasmeen, ba za ki ce mata komai ba 

A harzu?e Ya isha ta ce
  Haba Baaaba! Ya za ki ce haka???yanzu inda ace ta gaya mana tun farko ai da mun san abun yi, da tuni ba a kawo ga haka ba, amma yanzu kalli abunda b oyewar da ta yi ya janyo.
saboda Allah idan mu tana ganin bata shiri da mu ai ko ke ko
Mommy ya kamata ace ta gayamawa, tunda na san ta san dole ba a san da zancen ba.

Har ga Allah Yahanasu ta fara wuce iyakarta kwana biyun nan,
Ranar chan fa da ta gaggaya mana magana a parlour
ranar da akayi case d in senator
da Yassira ta je d akinta idan kika ga yadda ta yi wallahi za ki sha mamaki, Yasira tana fad a atake itama take mayar mata k arshema toilet ta shige ta banko mana k ofa.

Kwata-Kwata bata shakkar uban kowa a cikin mu amma dukda haka kuna gani kun yi shiru sannan da ance za a gyara mata zama sai ku hana& .yanzu kalli abunda saken da kukayi ya janyo  .


A hankali Mommy wadda zuwa yanzu tama daina gani sosai tsabar b acin rai ta ce   Ya isha so kuke ku kasheni? Aka ce ku bari tukunna yanzu a fara sanin abun yi in ba hakaba wallahi zan tura ku d akinku kamar Yusra da Yadira tunda kuma Yaran ne&
Ku tsaye ga matsalar da ya kamata ayi magana akai nan amman kun tsaya kuna shirme? 
Mommy ta k arashe maganar tata cikin d an d aga murya da tsananin b acin rai.


Komawa Yasmeen ta yi ta zauna, haka itama Ya isha, ammafa dukda haka a kumbure suke kamar za su fashe..

Shiruu d akin ya d auka kowa ya shiga tunani& .

 To kenan Daddy shima ya sani amma ya b oye mata ko dai ya abun yake ne???
Mommy ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba, a take wata zuciyar ta ce mata  da wuya idan ya sani, kuma ko da ace bai sani d in ba ma ta san wuyarta Yashjub ya ce masa yana son aure! Ko a cikin sati d aya ne ba abunda ya shafesa tsaf zai d aurawa Yash aure, in dai har Hajiya Maama ta amince kuma an yi bincike  &
Sabodahaka ta san yanzu Baaba Larai ce kad ai za ta iya taimakon su, dan haka ta d ago da niyyar yi mata magana kenan Idanuwanta suka sauk a a kan Kausar wadda ta turo k ofar d akin a dai dai lokacin ta shigo.

Lumshe idanu Mommy ta yi ta bud e saboda yadda ta ga hawaye shab e-shab e a fuskar kausar d in ta san ta riga ta gama jin komai.


A hankali ta d an matsa kusa da ita da niyyar yi mata magana amma sai Kausar d in ta yi saurin d aga mata Hannu alamun  stop! Kafin kuma ta juya da
sauri ta bar wajen& &


Da sauri su Ya isha su ka bita
da hanzari, su Mommy suma suka rufa musu baya..duk suka d unguma side d in Kausar inda suka ga ta shige.

Suna zuwa suka tarar har ta shige ta turo k ofar bedroom d inta dan haka suka tura suma, cikin ikon Allah bata rufe ba. Suna shiga suka tarar da ita ta fasa kwalba tana k ok arin yanka jijiyan wrist d in ta(wuyan Hannunta).


Da sauri sannan a tsorace suka je suka rirrik eta Mommy tana cewa   Haba Kausar, ba fa auren aka ce miki an riga an d aura ba 

Inaa! ko jin ta Kausar bata yi ba,
in banda kuka da hauka ba abunda take musu..
Dan haka Mommy ta juyo da ita ta wanka mata wani kalar gigitaccen mari.

Wani sabon kukan Kausar ta sake fashewa da shi kafin ta fad a jikin Mommy ta rungume ta tana kuka sosai kamar za ta shid e ta shiga cewa
  Mommy kawai ki barni in mutu, all my life I ve been unlucky (ni duk tsawon rayuwar da na yi ba ni da sa a)
Ammina ta rasu!
Mahaifina bana jin ma ya san da ni!Daddy shima ya tsaneni!
Sannan tare muka fara karatu da su Yassira su duk har sun gama sun kama aiki
amman ni har yanzu Ina project!&

Dan Allah ku bar ni in mutu,
Idan na zauna Yash ya rayu da wata a matsayin Mata mutuwa zan yi Mommy, gara kawai in mutu& .


A hankali Mommy ta rungumota itama zuwa jikinta sannan ta ce  Na yi miki alk awari, Yashjub ba zai auri kowa ba sai ke.

Cikin katseta ta ce
  Mommy haka kike cewa kullum, gashi yanzu har yayi budurwa yana shirin aurenta bama mu sani ba 

A hankali Mommy ta saka Hannuwanta ta d ago da fuskarKausar ta yi cupping a cikin tafin hannuwan nata kafin ta ce mata   kin yarda da ni??? 
tayi mata tambayar tana kallonta

A hankali kausar wadda duk ta mi?a wuya ta jin jina mata kai alamun yes
Idanuwanta shab e-shab e da hawaye, har ga Allah ta karaya da yadda ta ji maganar ta taho gadan gadan dan ta san tunda akace nan da wata Waya to hatta su Hajiya mama sun sani kuma sun amince, ta riga ta san duk bala i ba a isa a chanjawa hajiya mama ra ayi ba, shiyasa kawai ta zab i ta mutu amma wannan al?awarin da mommy ta yi mata ya sanya ta Wan ga alamun haske dan haka ta zaSi saka rai da dacewa sannan ta zaSi ta yarda da mommyn Wari bisa Wari ko bayaga hakan ma yarda da mommyn dama shine zaSinta mafi sau?i wanda ta ke so Win, dan akan ta mutu ta barwa wata yash Winta gara a fafata su yi nasara ta hanyar raba shi da Yaroinyar, in sha Allah.

Dan haka ta sake cin Wamara, bayan ta Waura gaba Waya yardarta akan abinda mommy ta faWa mata Wari bisa Wari ta kuma aminta da momnyn za ta cika mata burinta.

Sai da Mommy ta sauk e ajiyar zuciya tukunna ta ci gaba da cewa  ki kwantar da hankalinki,
babu wadda ta Isa ta shigo cikin gidan nan a matsayin matarsa, ki zuba ido ki ga ikon Allah 


Ya isha ce ta ce
  Mommy me za a iya yi a cikin sati uku zuwa wata d aya? Wata?ila ma fa an riga an kai komai.

 Ba dai ni nace muku ku zubamin ido ba?& .dan haka bana so in sake jin wata magana game da batun auren Yash a cikin gidan nan 
Sai da ta sake sauk e ajiyar zuciya tukunna ta ce   zan ga ta yadda zai yi auren, zanga ta yadda zai aureta. 

A hankali ta kamo fuskar Kausar ta ce   alfarma d aya nake so daga gareki&  ki kwantar da hankalinki! .
Ki cire komai aranki,

45 / 51