Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   17 / 51

48K to 51K   out of 151.9K words

na ci gaba da zama da ke a k ark ashin inuwa d aya tou nima inaso ki yi mini alfarma d aya tak,ina so  ki fita a harka ta !!!!
Iyaka wannan kawai nake da buk ata daga gare ki.

Case d in Yasir na ce a gaya miki ki yi solving tun kafin mu zo ni da Saddi?a, yanzu kuma da ya ?i dawowa wannan ma matsalarki ce, ke kika san yadda za ki yi ki je ki nemo sa, amma Yasir ba jariri bane ba da zaki fake da case d in sa ki k ulla wata alak a a tsakanin mu,
duk inda ya je idan ya gaji zai dawo in bai gaji ba kuma
Ubangiji ya sada fuskokinmu
A aljannah& .

abu na k arshe da zan ce da ke shine ki tabbata wannan ita ce maganata mai tsayi ta k arshe da ke, in ba haka ba wallahi zan baki mamaki. 

Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Mommy, a hankali yana shirin wucewa ta ce
  Ubangiji ma muna yi masa laifi mu rok i gafara kuma ya yafe mana, na ce ka yi hak uri Daddy!
Ka bani last chance!
I love u, kar ka yi mini haka& .. 
Cikin fushi ya ce
  Ba kya so na ba kya k aunata sam, shiyasa kike turturing d ina(azabtar da ni). ko kin san cewa akan maganar da kika yi mini kad an ya rage in mik a kaina ga hukuma?kuma na san kin san menene hukunci na ko? 

Cikin zubar hawaye Mommy ta ce
  Ka yi hak uri mu bar wannan maganar ta wuce& .. 

  Get out! 
Daddy ya fad a cikin katse ta.

Za ta yi magana ya sake cewa
  ki fita ,na ce. 
Da d an k arfi.

A hankali ta sa Hannu ta share hawayenta ta toshe Bakinta saboda kar sautin kuka ya sake fitowa, sai da ya Wan lafa tukunna cikin tsananin mutuwar jiki ta ce  ka yi hak uri 
daga nan ta juya ta fita tana mai sake toshe Bakinta.


Ya dad e a wajen kafiin da k yar ya samu ya juya ya wuce d akinsa.
& .
A d akinta ta tarar da Kausar da Yasira&
Ta so ta b oye musu damuwar ta amma suna had a idanu da su sai ta karaya bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.
Sai da suka yi da gaske tukunna suka samu suka rarrashe ta, ta yi shiru, Yasira ta d au waya ta kira Baaba Larai, tana zuwa suka shiga tattaunawa.
Ba su suka bar d akin nata ba sai wajajen k arfe d ayan dare bayan sun saka Kausar ta yi musu alk awarin kiran Yasir washegari,
Idan Allah ya kaimu& ..
&
Washegari da sassafe
Kausar ta tashi ta shirya cikin wata dress mai kyau wadda bata k arasa rufe mata k afafunta ba.
Jan jambaki da kwalliya ta rambad a sosai wanda hakan ya sake fito da ainihin kalar farar fatarta&
Hula kawai ta saka a kanta daga nan ta kama hanya ta fice ta nufi side d in su Yashjub tana adduar Allah yasa bai fita ba, dan dukda yau ba aiki ta ji Yasira tana cewa sunada important meeting.

A parlourn ta same shi shirye tsaf cikin suite ga briefcase d insa a gefe yana zaune yana sipping tea.

A hankali ta saki wani lallausan murmushi kafin ta k arasa ciki, cikin takun ta mai tsananin d aukar hankali.
sai da ta je kusa da shi tukunna ta ce
  Salam alaika  .


Tun lokacin da ta turo k ofar ta shigo ya lura da ita dan haka ya sake tamke fuska tamau kamar bai tab a murmushi ba.

A hankali ta nema waje ta zauna a gefen sa, sannan ta ce
  Ya Yash, Ina kwana  .

Ci gaba kawai yayi da sipping tea d in sa yana kallon tv still bai ce mata uffan ba.

Badaban Kausar A ce a fagen tsaurin ido ba to da
a yadda ya tamke fuska kaWai ya Isa yasanya ta tsorata, ta fita.


Duk da tana d an fargaba haka ta daure a karo na uku ta ce   Ya Yash  .

Lumshe kyawawan idanuwansa yayi a hankali ya juyo gare ta sannan ya bud e yana mai kallon ta ido cikin ido
tukunna ya ce
  Duk abun da kike buk ata ki turomin Yadira anjima, tashi ki fita. 
Ganin yadda ta kafe sa da idanuwa ne ya sanya kawai ya mik e ya d au briefcase d insa ba tare da ya sake bi takanta ba ya nufi hanyar fita.

Da sauri ta sha gabansa cikin d an gudu ta ce
  Ya Yash Mommy ce fa ta aiko ni wajen ka 
Ta fad i haka tana k ok arin matsawa jikinsa sosai sannan ta saka Hannu zata kamo briefcase Winsa.

Duk kalar tsaurin idonta sai da ta ji tsoron kalar kallon da yayi mata dan haka ta d an ja baya kad an ta sunkuyar da kanta k asa.

Da kyar Yashjub ya samu ya d an rarrashi kansa, kawai ya wuce ba tare da ya yi mata komai ba ya fice ya barta anan wajen
amma da farko yadda zuciya ta taso masa so yayi ya d an wanke ta da mari watakila zata dawo saiti!!!

Idan akwai abunda ya fi tsana a rayuwar sa bayan cin amana to shine Mace marar kamun kai!
tabbas Kausar y ar uwarsa ce
amman kwata-kwata jininsa bai d auke ta ba tun filazal, gashi yanzun kuma rashin kamun kanta ya sanya ta kuma fita a kansa ko ganin Yarinyar baya son yi,wallahi.

Da wannan tunanin ya k arasa motarsa ya shiga ya zauna ya
lumshe idanuwansa& .
A take idanunta waenda izuwa yanzu abun ya zame masa jiki suka hau yi masa gizo.
A ransa ya ce
  Ga inda ake Mace nan, gaisuwar ta ma tsada ne da ita, sannan ta yi laifi amman tsabar sanin darajar Kai
bata yi gigitar da d ayan Namijin ya yi yana bada hak uri ba& .
Ana ganinta kuma za a fahimci yadda itama take a ruWe amma ta dake sam bata yarda ta zubar da class d inta ba& .
A hankali wani lallausan murmushi ya sub uce masa
A fili ya ce
  Sai shegen kukan shagwab a kamar wata y ar baby  &

Yana nan zaune yanata tunani
kira ya shigo wayarsa&
Ba k aramin fad uwa gabansa yayi ba a lokacin da ya d auko wayar zai amsa idanuwansa suka sauk a akan time,
 Wato zaman sa anan har ya yi 30 minutes kenan??
ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya samu mai basa amsa ba.
Ganin kiran yana shirin tsinkewa ne yasa yayi sauri ya d auka ya kara a kunnensa ahankali ya ce
  Daddy Ina kwana,sorry wani abu ya Wan tsaida ni,gani nan zuwa  .
Yana gama fad in haka ya kashe wayar ya kunna motar ya bata wuta ya wuce& .

A ransa yace
  I really need to see Najeeb.(tabbas dole zan ga Najeeb)
Zuwa yanzu ya fahimci in dai ba son Yarinyar nan yake yi ba
to tabbas akwai dalilin da ya sanya Ubangiji ya turo ta cikin rayuwar sa, ya san ma ba zai you ace yana son ta ba tun da bai san ta ba&
ya kuma yi addu o i dan haka definitely ba aljana ko mayya bace ba tunda gashi har yanzu bai bar tunanin ta ba!
Tun yana k ok arin yakice tunanin nata ma har ta kai ta kawo zuwa yanzu ya daina saboda in yana tunanin nata wani
nutsuwa, annashuwa da farin ciki na musamman ne suke dirar masa wanda har ya kan ji
baya k aunar abun da zai gilma ko ya gifta a tsakanin sa da tunanin nata& .
Dan haka kawai ya gama yankewa akan zai ajjiye b oye-b oye a gefe ya fuskanci Najeeb akan maganarta yau yau d innan inshaaAllah, tun kafin a samu matsala, yana da bu?atar ya santa.


BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*18*

Da wannan tunannin
Ya ?arasa makeken company d in Daddyn nasu.
Sanin da yayi suna da bak i ne yasanya bai wani tsaya ko ya biya ta office d insa ba, kai tsaye kawai ya wuce in da ake meeting d in&

Bai samu sun kammala
komai ba kuwa sai wajajen k arfe biyu, duk saurin sa bai samu damar k arasawa office d in Najeeb ba sai pass 3.

A parking lot suka had u da Najeeb d in yana shirin fita shi kuma ya shigo.
Tunda ya hango Yashjub d in ya taho ya tsaya daga k okarin bud e k ofar motar tasa da yake yi ya zuba masa ido yana murmushi yana girgiza kai a ransa ya ce   Allah mai halittar kowa da yanayin nasa halin,
ya san zai zo kuma ya san ba lallai ya same shi ba amma ya d auki waya ya ce masa  ya jira sa kawai, shine yake ganin aiki, ya gwammaci ya zo Win in bai same shi ba ya juya  .

  Kai lafiyar ka kuwa! 
Yashjub wanda ya k araso kusa da shi yayi masa tambayar cikin tsare gida.

Y ar guntuwar dariya Najeeb ya saki kafin ya ce
  Mamakin ka nake yi, ka san wani abu ne ya d an rike ni, ba dan haka ba da na dad e da fita daga nan 

  Hmmm  Yash
ya ce
kafin ya d aura da cewa
  Ka kyauta kuwa, bani key d in in shiga idan ka gaji da tsayuwa ka same ni a office d in. 

Murmushi Kawai Najeeb yayi daganan ya mik a masa key d in ya wuce shi kuma ya bud e motarsa ya zuba kayayyakinsa a ciki ya rufe tukunna ya bi bayan Yashjub d in.


Kusan a tare suka shiga
Office Win wanda ya ke nan k all gwanin ban sha awa sai faman tashin ?amshi yake yi.

Fridge Yashjub ya nufa ya d auki ruwa da cup tukunna ya nemi guri ya zauna akan sofa kusa da Najeeb d in, yana zama ya b alle marfin ruwan ya zuba a cup ya kafa a Baki yayi bismillah ya shiga sha& ..

Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk e kafin ya ce
  Uncle ya ce in baka hak uri,
In sha Allah nan da sati biyu za a gama ginin estate Win..
k ofofin ne suka d an yi wahala
gashi ka ce dole sai irin na estate d in Abuja da Kano za a saka shiyasa abun ya d an yi musu tsauri amma yanzu haka an samu an yo order, ya ce kawai za a fara fenti da fixing electronics in ya so idan an kawo ?ofofin sai ya zamana shine last aikin da za a yi kawai. 

Kallon da ya ga Yashjub d in yana yi masa ne ya sanya ya ce   Menene kuma? Yash!..Uncle d ina ne dai, ido ya san na gida. 

Murmushi Yashjub yayi kafin ya ce
  Kallon da kaga Ina yi maka na mamakin yadda ka hau zuba ba tare da ka ji dalilin zuwana ne,ba.
Ko ce maka aka yi akan maganar estate na zo nan? 
Yayi masa tambayar yana me kafesa da ido.

Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk e kafin ya ce
  To naga ai shine priority d inka a yanzu mu kuma muna ta yi maka delay  .

  Yeah, days ago shine priority d ina amma yanzu kam ba shi bane ba, kawai dai tunda ka taso da maganar tou ka gayawa waenda ka ce sun ce suna son guda d aya rent su jira sai nan da one month idan za su iya. 
Yash ya fad a hakan yana sake zuba ruwan a cup sannan ya kai Baki.

  Ok 
Kawai Najeeb ya iya cewa
yana mai k ok arin fahimtar mood na Yashjub d in.

Wani d an guntun murmushi yaga Yash yayi, ba tare da ya kalle sa ba Ya ce
  Ina Manubiya? 

Da d an k arfi Najeeb ya ce   what!  Kafin ya d aura da cewa  wai dama da gaske kake kenan, kuma amma ka tsaya ka na ta yi mini kwana-kwana da fulatanci?
Ba fa a zurfin ciki a harkar nan dan in ka tsaya wasa tsaff sai dai ka ji sold out!wallahi.

Kaii amma na ji dad i, ni zan fara kaiwa Mommy good news Winnan.

Alhamdulillah  dutse is in love finally  .
Najeeb ya k arashe maganar yana mai fashewa da dariya.

Tsayawa kawai Yashjub ya yi yana Kallon sa bai ce masa uffan ba.

Haka nan Najeeb ya tisa shi a gaba yayi ta zolayar sa, sai da ya gaji dan kan sa yayi shiru tukunna Yashjub ya ce masa
  Ka gama?
Za ka iya saurarata yanzu mu yi abun da ya kawo ni, ko in tafi kawai? 

Cikin dariya k asa-k asa Najeeb ya ce
  Sorry, Ina jin ka Angon Manubiya  .

A hankali ya lumshe lumsassun dogayen idanuwansa ya bud e tukunna ya ce
  Najeeb ba wai son Yarinyar nake yi ba& .. 

Cikin tarar numfashinsa Najeeb ya ce
  Yet(tukunna..)
Amma ta burgeka ai ko?.
ai dama abunda za ka ji kenan yanzu tunda kwata-kwata sau d aya ka tab a ganin ta,haka abun yake ai. Ka yi ?o?ari ka santa ku sha?u!
InshaaAllah nan da ?an watanni za mu sha biki&  

  Ya Allah,
duk wani iri abun nan ya ke sa ni ina ji .
Yash ya fad a yana mai sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya.

Dariya Najeeb ya saka kafin ya ce
 Ai yanzu zan baza ka a groups, kaff friends d inmu sai sun san aljannar da ta aureka ta rabu da kai finally ko kuma ta mutu, wannan abun farin cikin har walima zamu had a. 

  Pls don t (dan Allah kar kayi hakan), haba Najeeb ya kake yi min haka?
Na zo maka da matsalata a matsayin ka na Abokina kai da ya kamata ace ka tsaya ka saurare ni amma sai faman shirme kake yi min,shikenan kawai bara in tafi&  
Yashjub ya fad a yana k ok arin mik ewa da alama ransa ya d an sosu.

Da sauri Najeeb
Ya ce
  Yi haku uri  yana mai rik o hannunsa sannan ya yi serious face ya ce   na daina,
Talk to me friend(mu yi magana Abokina).

Sai da Yashjub ya d an k ura masa ido tukunna ya koma ya zauna.
Ya dafe kansa da Hannu d aya ya d an sunkuyar da kan nasa ya lumshe ido a hankali ya ce
  Ba wai son Yarinyar nan nake yi ba Najeeb, saboda wallahi yanzu inda ace za a kawo mata guda goma a kulle musu Iyaka Idanunsu a bar ragowar fuskar a bud e to ba lalle in iya nuna ta a cikin su ba.
iyakar idanunta kawai na gani that very day(a wachchar ranar) amman tun daga lokacin na gaza sukuni&
Idan fa na lumshe idona har ganin idanunta nake yi,
sannan haka kurum sai in dinga ji kamar muryarta tana yi mini gizo a kunnuwana..
sannan in ba tunaninta nake yi ba ko maganarta as in(misali) idan na yi forcing kaina in cireta a raina to gaba d aya sai in ji Ina neman susucewa kaga alal misali yanzu haka maganar ta muke yi da kai ko?To ni kad ai na san irin peace of mind d in (kwanciyar hankalin) da nake samu, wani sanyi nake ji har k asan zuciyata da annashuwa sannan with each passing second na rayuwata
all i want to do (sannan duk wata da?i?ar da za ta zo ta shige a rayuwata iyakar abunda na ke ganin ya kamata in yi) shine
In san ta!!!.
Its like (ji nake) kamar akwai abun da yake pushing d ina (tura ni) akan in je in santa in yi bincike akan ta, in zama very close to her, like sooooo close..may be a friend
(In samu mu sha?u da ita, sha?uwa sosai, wata?ila kamar ko mu ?ulla Abota haka)
Ya k arashe maganar tasa a hankali yana mai d agowa ya kalli Najeeb wanda ya ga ya yi shiruu ya k ura masa ido kawai, sai da ya fesar da iska tukunna ya ci gaba da cewa
  Na san me kake tunani amma dan Allah karka fad a, I can t love her (ba zan iya in so ta ba) tunda ban riga na san ta kuma na ganta ganta sosai ba, shiyasa ma na riga na yi concluding abun as (na bar abunda na ke ji a kanta a matsayin) ba so bane ba!!!!.
it s definitely something else (dole wani abu ne chan na daban, amma ba so ba).
Dan haka
Ka bani shawara, mu tattauna a nemo mafita amma kar ka ce min son Yarinyar nan nake yi dan na san ba son ta nake yi ba. 

Da kyar Najeeb ya samu ya iya danne dariyar da take ta faman taso masa, duk da tausayin da Abokin nasa ya bashi amman kuma ya ba shi dariya duk a lokaci guda.
Gashi dai Yashjub is in love da ikon Allah saboda gaba d aya bayanan shi akan Manubiya
amsar d aya ce tak  KAUNA
although (dukda)bai ganta sosai ba
amma idanuwanta da muryarta da ruhinta sun riga sun hana shi sukuni tun yanzu
Ina kuma ga in sun kasance frnds d in (abokan)kamar yadda ya ke da buk ata a yanzun,
Lokacin da zai amayar da abun da yake ransa ma ba zai saniba!& .
Tabbas kuwa za a yi

17 / 51