Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   29 / 51

84K to 87K   out of 151.9K words

aurar da ita anytime..ya zama dole ya ajjiye komai a gefe dan Manubiya ce peace of mind d insa(kwanciyar hankalinsa)
Strength (kuzarinsa)
Happiness (farin cikinsa)
da komai na shi 

  Yash& . 
Muryar Najeeb ta katse masa tunani ta hanyar kiran sunansa da ya yi cikin k ura masa idanu.

A hankali Yash ya gyara zama yana kallon Najeeb d in tukunna ya ce   menene abun yi yanzu? 

D an fiki-fiki Najeeb ya yi da idanuwanshi tukunna ya ce   kana son nata kenan? 

Murmushi Yashjub ya yi tukunna ya d an d aga masa Kai alamun  yes kafin a hankali ya ce  a lot(irin sosai Winnan)
sai kuma da sauri ya nuna Najeeb d in da yatsa alamun warning sannan ya ce   don t laugh, kuma wallahi kar in ji maganar nan a Bakin kowa. 

Duk yadda Najeeb ya so hana kan sa yin dariya sai da ya yi, kafin daga baya ya yi shiru sannan ya ce   sorry Man, na ji dad in abun ne sosai shiyasa&
congratulations Allah ya baka Manubiya. 

A hankali Yash ya ce   Ameen  yana wani irin blushing.

Kafin Najeeb d in ya yi serious face sannan ya maida gaba d aya hankalinsa a kan Yashjub tukunna ya ce   yanzu abunda ya kamata ka yi shine& &  


BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*29*

A hankali Yash ya ce   Ameen  yana wani irin blushing.

Kafin Najeeb d in ya yi serious da fuska, sannan ya maida gaba d aya hankalinsa a kan Yashjub tukunna ya ce   yanzu abunda ya kamata ka yi shine, ka yi k ok ari sha?uwa ta shiga tsakaninku ta hanyar friendship&
In ya so idan Allah ya kaimu kamar nan da one week (sati Waya) to kana iya tunkarar ta da maganar, in ya so mu kuma sai mu je mu samu uncle, brother ko Mahaifinta a san da zaman ka 

Wani irin kallo Yash ya yi masa wanda ya sa Najeeb Win yin wata y ar siririyar dariya kafin ya ce   a tunanin ka yanzu idan ka ce mata kana son ta direct za ta amince ne?ai ya yi wuri sosai Yash..
Gara ka fara neman friendship d inta first.
kuma ba fa nan da wata d aya ko biyu na ce ba, iyaka sati d aya na ce maka, sarkin zalama.

Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya ce
  Najeeb, Manubiya fa ba zata saki jiki da ni har ta yarda mu zama friends ba, that too in one week time that s impossible(daWin daWawa a cikin iyaka sati Waya, gaskiya abu ne wanda ba zai yiu ba)

Saboda tanada kamun kai da nutsuwa sosai..she is not the type (ba irin ?an Matan nan bace) da zata zama friends da duk wani ba?on da ya shigo cikin rayuwarta bane tunda a yanzu dai hakan nake a wajenta(ba?o/stranger).
Amma tabbas maganarka ma gaskiya ce tunda ko da ace ban tab a soyayya ba na san kafin mutum ya samu guri a cikin zuciyar Mace ana buk atar shak uwa da kuma yarda da sauran su amma ni yanzu a hanlinda nake ciki yanzu haka Najeeb Ina so ka fahimceni ka fahimci yadda nake jin ta a cikin zuciyata..dan haka Ina ganin gara kawai in nemi su yardar tata daga baya amma for now abu na farko shine ta san Ina son ta&

kar fa ka manta bayan na gaya mata ta amince da ni
akwai fa su tambaya saka rana da buki a gaba kafin Waurin aure wnda na san Daddy da Mommy sai sun d an d auki lokaci dole su na shirye shirye kafin ayi auren,
Ni kuma gaskiya a matse nake ta zamto matata, ba wai lust(sha awa) ko wani abun ba a a abunda kawai na fi buk ata a yanzu shine ta yarda da ni ta aminta da ni in mallake ta ta zama tawa ni kad ai, ka fahimceni??  .

Numfashi Najeeb ya fesar kafin ya ce   Yash na fahimce ka amman kuma kaima ka fahimce ni,
gaggawa fa aikin shed an ne..
Gara mu bi komai a hankali. 
Najeeb d in ya fad i hakan saboda shi yana so su d an fara sha?uwa kafin komai dan ba zai yiu ace ya bata aiki Monday kuma Friday tashi d aya ya ce mata yana son ta ba, ba lalle ta fahimce sa ba zata ga kamar yaudarar ta ya zo yi&
&
A hankali, bayan zurfin tunani shima Yash d in sai ya ce   ok, bara in jira one week d in.
& & ..
Tunda Daddy ya koma d akinshi yake ta faman kai kawo, gaba d aya ranshi a dagule ya ke hankalinsa a tashe yake, sam ya rasa gane me yake damun sa ma!
dan shi kansa zuwa wannan lokacin ya fahimci a mugun birkice ya ke.
Tun kafin aje ko ina har ya fara tunanin bai kamata ya kori Ummi ba!
ta chanchanci hukunci tabbas dan bai kamata ta tab a masa y a ba amma kuma shima bai kamata ya ce ta bar gidan ba,
ko ba komai ya san tana son shi tun ba yau ba so na tsakani da Allah dan itama ba matsiyaciya bace balle ya ce kud i ta bi, tana business tana aiki kuma ya san mijinta ya bar musu mak udan kud ad e..

saboda shi (Daddyn) ta yi resigning aiki sam bata damu ba ta ce itama tafi so dama ta kula da shi da y ay an su&

A hankali ya dafe kansa yana jin yana wani irin sarawa & .


Da sallama Mommy ta turo k ofar d akin ta shigo a hankali ta k arasa kusa da shi tana d ar-d ar tace
  Daddy Yassir fa har yanzu bai farka ba, lafiya kuwa? 

Ba tare da ya cika kan nasa ko ya d ago ya kalle ta ba ya ce   lafiya,allurar tana da nauyi ne. 

Ahankali ta matso ta d an ri?e Hannun shi ta ce   am..i m sorry about umm.. 
Hannunsa rik e da Kai har yanzu ya d ago ya kalle ta tukunna ya ce   Get,out! 

Ta bud e Baki za ta yi magana ya yun?ura ya kamo kafad unta da Hannu biyu ya ce   in kin san kina da Hannu a koma meye ne to tun wuri tun kafin mu dena sheda juna ki janye ki fita a idanuwana Khadijah! 

Wasu hawaye ne suka zuba mata wanda hakan ya sa Daddy ya ji ina ma bai yi maganar ba.
A hankali ta ce   daddy i&  
Wuce ta kawai shi yayi ya fita da sauri yana da na sanin yi mata hakan dan bai kamata ya d aurawa kowa laifin abunda ya aikata ba.

Yana fita aka fara kirana sallar azahar dan haka ya wuce zuwa masallaci.


A masallacin suka had u da su Yashjub,
bayan an fito&
cikin girmamawa Najeeb ya gaida shi Daddyn kuma ya amsa da kulawa daganan Najeeb ya wuce side d in Yash ya barsu a wajen dan ya ga kamar suna buk atar space.

Najeeb na wucewa Yashjub ya bawa Daddy hak uri kafin ya fad a masa abunda ya yi wa su Ummi.

Bai yi murna ba kuma bai yi bak in ciki ba, makullin kawai ya karb a a hannun Yash ya wuce sama.


A zaune ya same su, su biyu, a kan gado. Kowacce ta yi tagumi amma fa sun had a kayayyakinsu tsaf gaba d aya sun juye a cikin akwatunan da jakankuna
sun jere su a gaban su.

Tun kafin ya ce wani abu suka mik e, ba tare da ta kalle sa ba ta ce   Yashjub ne ya kulle mu,
ka yi hak uri, yanzu za mu tafi 
Ta fad i hakan tana k ok arin jan akwatuna biyu waenda suke cikin jerin akwatunan gaban su.
A hankali Munirat itama ta mik e ta fara k ok arin jan wasu akwatunan&

cikin sanyin jiki Daddy ya matso kusa da ita(ummi) ya ce
  Ki tsaya mu fahimci juna & .. m

Munirat ji ta yi kamar ta kwala k ara dan takaici,
ya gama ci musu mutunci sannan yanzu ta ga da alama so yake ya hana su tafiya&

har ta bud e Baki za ta yi magana sai kuma ta ajjiye akwatin Hannunta ta fita dan already Daddy har ya kamo hannun Ummi ya hanata fara jan akwatin.


A parlourn ta nemi waje ta zauna tana addu ar  Allah kar ya sa Ummi ta yarda su ci gaba da zama a cikin gidan nan.

Shigowar Mommy ce ta katse mata tunani..
Ahankali Mommy ta sauk e nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce   Munirat na godewa Allah da baku tafi ba. na kira wayar mamanki bai shiga ba.
kar ku d au zafi kamar yadda shima ya d auka kin ji ko?
bara in shiga
In yi mata magana itama  .

Ahankali Munirat tace   ita da Daddy ne. 

Da sauri Mommy ta ce
  Yauwa perfect, bari in same su duk su biyun. 
Har ta nufi k ofar sai kuma tace
  Am..Munirat dan Allah, d an je ki kitchen akwai soup d in da na d aurawa Yassir, kar ya k one kafin mu gama.
ki juye a bowl ki kai masa d akinsa  .

Kamar Munirat za ta yi mata musu,
sai kuma kawai ta mik e ta wuce.  & ..Tun ranar da ta fara ganin Yassir ya d an burge ta!
Kyakkyawa ne ajin farko,
halayyarsa ce da ta fahimci ba ta da kyau da kuma yadda gwaggwo ta ja mata kunne kawai ya sanya ta cire rai da shi, dan a tashi d aya ma tun daga ranar ta ji ta tsane shi& .
amma duk kalar tsanar da ta yi masa ta kasa jin tausayinsa a yau Win, dan ta tabbatar inda ita aka yi wa wannan mahaukacin dukan to da tuni ta mutu& ..
Tana wannan tunanin ta ?arasa kitchen d in, ta juyo soup d in a bowl&

?akin da ta ga su Daddy sun shiga da shi Wazu ta nufa, tana zuwa ta d an yi knocking& .
jin shiru ya sanya ta tura k ofar ta shiga bakinta d auke da sallama.

Tana shiga ta ganshi a kwance a kan makeken gadon shi&
A hankali ta k arasa ta d an tsaya akan sa tana kallon yadda fuskarsa ta kumbura&
A take kuma sai ta fara da na sanin zuwa dan sai da ta ganshi ta ga yanayin jikin nasa tukunna ta fara jin haushin kanta na kasa hak ura da ta yi har sai da ta zo, dan haka ta ajjiye bowl d in da niyyar juyawa ta ji ya kira sunanta!.
Da sauri ta juya da niyyar fita amma sai ta kasa sakomakon magiya da hak urin da ya shiga bata yana cewa  sharrin shaid an ne! ta yi hak uri ba zai sake ba, kawai he got carried away by her beauty ne (tsananin kyawunta ne ya ruWe sa) ya biyewa feelings d insa towards her(shi kuma ya bari feelings Winsa gareta su ka yi galaba a kansa)..
Wallahi bai san me ya shiga kansa ya aikata mata hakan ba!
amma inshaaAllah ba zai sake ba. 

Yadda jikinta yayi sanyi shi kanshi Yassir d in ya lura da hakan, yana shirin ci gana da magana ta juya da sauri ta fita, dan tabbas in ta ci gaba da zama a d akin tou za a samu matsala& &

Munirat tana fita Yassir ya yi wani killer smile(shu umin murmushi)& .
 & ..Tun ranar farko da ya fara ganinta, dama ya fahimci Yarinyar za ta yi saurin shiga Hannu!!!!
Kum ya lura kamar tana d an son shi.
Dole ya san yadda zai yi ya samu abunda ya ke so daga gareta, ta ko wacce hanya!!!!
Sannan ya yi amfani da ita wajen hukunta Ummi! Dan ya lura lamarin Mommy da Daddy ya sake tab arb arewa kuma yana da tabbacin Ummi ce sila.

Sannan Yarinyar ta tafi da imaninsa, ya san baya sonta,
amma fa tabbas a cikin Mata idan za a tara a raba su kashi d ari tou kashi 1 zuwa biyu ne za a same su da irin zubin Jikin Munirat& .
Yana wannan lissafin yana murmushi, ya juya da niyyar d aukar bowl d in dan yunwa ya ke ji amma sai ya gagara sakamokon tsamin da Hannun sa yayi, dole haka nan ya hak ura..a hankali ya koma ya sake langab ewa saboda ko ina na jikinsa ciwo yake masa
 & & .ya kasa yarda! Har yanzu ya kasa yarda da cewar wai Yashjub ne ya yi masa haka da girman sa da kud in shi da class d in sa!!!! Abun kamar a mafarki.

Tabbas abunda Abokansa suke gaya masa na cewar
  In yayi wasa sai ya zama d an kallo a gidan  . Ya tabbata, kenan.

Shi fa daman tun farko kokawa kawai yake yi da zuciyarsa saboda ya san Yashjub d an uwansa ne kuma Mommy ba za ta so taga basa shiri ba
amma wallahi tun yarinta shi kam ya tsani Yashjub!
Duk wani abu da ya ke so ko yake son yi
to sai abun yayi ta zuwar ma Yashjub d in cikin sauk i.

Tun yana Yaro yake da burin zama business man babba sosai kamar Daddy&
Daddy ya ce sai sun yi phd tukunna zai basu jari
amma Yashjub ko da ya gama phd d inma already yanada estate all thanks to son kan da Daddy ya yi tun ranar da aka haifi Yashjub d in wanda hakan ya sanya da Daddy ya basa nasa jarin sai arzik insa ya sake nunkuwa, shi kuwa da aka
bashi nasa aka bud e masa company compared to na Yashjub(da na auna nashi da na Yashjub Win) duk sai ya rena nashin, dan a lokacin har ma a yanzu bai Isa ya tsaya ya ce zai goga da Yashjub a harkar business da kud i ba saboda ya fi shi ya tsere masa ta koina..
kuma har gobe Yashjub d in kamar wani aljani duk abunda ya saka a gaba tou sai ya cin masa kuma sai ya yi albarka, baya jin tun tasowar su ya tab a ganin abunda Yashjub ya nema bai samu ba.!

Shi yasa tun kafin a zo nan Abokanayensa suke ba sa shawarar ya tashi ya tsaya, dan it s clear (dan a baiyyane ne ga kowa) Daddy ya fi son Yashjub, ga shi ya fi shi kud i da fame, kuma shakka babu shekarun Mommy itama suna sake yin sama wanda ya fi arzik i a tsakanin su shi zata fi so&

Yana k ok ari, yana danne zuciyarsa ne dan baya so ya cutar da Yash amman gaskiya he can t take it anymore(ba zai iya ci gaba da dannewa ba!!) ya tsane shi tsana ba ta wasa ba! dariya kawai yake yi masa kasancewar shi d an uwanshi dolen shi sannan ya san ba shi da yadda zai yi da shi amma yanzu kam
lokaci ya yi da ya kamata ya tashi tsaye ya nemawa kanshi mafita kuma ya ga bayan Yash& &
ta hakan ne kawai k ima da martabar sa za su dauwwama a idanun y an gidan da ma duniya gaba d aya& .
& & &
Munirat tana fita Ummi ta ce
  Daddy kar ka ja in yi maka musu, ka yi hak uri komai ya wuce, amma dole in tafi.
Yaran ma ba sa k aunata, ba za mu zauna k ark ashin inuwa d aya da su lafiya ba 

Cikin katse ta ya ce
  Ummi I m not going to apologize (ba zan baki ha?uri ba) ke kin sani.

Kawai na ce ki zauna! kuma
i m expecting u to obey me
As my wife (kuma a matsayinki na Matata ina tsammanin ganin kin yi min biyayya, kin zauna Win.).

sannan su Yasmeen dolen ki ne
A cikin gidan nan, dan haka zai fiye miki idan kika nemawa kan ki mafita game da yadda za ki zauna ?alau da su&  

Ummi za ta yi magana kenan
Daddy ya toshe mata Baki da Hannunsa, yana kallon k ofa&
ba tare da b ata lokaci ba ya yi sauri ya yi wuff ya fice.

Da sauri Mommy ta shiga gyara d aurin zaninta wanda ta kamo bakin za ta kunto. a d an rikice ta ce   wajen ka na zo  bata jira jin mai zai ce ba!
sannan bata damu da kallon tuhumar da ya ke yi mata ba ta d aura da cewa  am..an bugi Yassir akan Munirat, but itama ya kamata a ja mata barrier (layi) akan zuwa d akin shi.
ita yarinya ce kar mu je Yashjub ya ce zai yi mata shegen dukan da ya yi wa Yassir dan kaga in hakan ta faru mamanta na san ba za ta daliliba ga kuma halin da ake ciki Daddy dan Allah ka d aga musu k afa mana& .

Cikin rashin fahimta Daddy ya ce  ban gane ba 
dan gaba d aya zancen nata a hargitse ya ke kamar yadda ita ma ta hargitse ganin an kusan kamata.

Dai-dai nan Ummi ta fito, da sauri Mommy ta matsa kusa da ita ta rungume ta ta ce
  Dan Allah ki yi hak uri akan abunda ya faru d azu, na yi masa magana hakan ba za ta sake faruwa ba,
ki zo mu je kuma ina son ganin ki, akwai maganar da za mu yi ni da ke in babu damuwa 
kafin ta kalli Daddy ta ce   za mu iya tafiya, dan Allah ?  .

A hankali ya d

29 / 51