Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   25 / 51

72K to 75K   out of 151.9K words


da kyar.

Lumshe idanunsa yayi ya bud e yana kallon yadda take kallon gefe kad an ita ala dole ba za ta had a ido da shi ba bayan kwanakin baya da kyar ta iya zare idanunta a nashi..bai san lokacin da wani murmushi ya kufce masa ba
wanda har sai da ta d an jiyo sautin kad an, kafin cikin kamala da dad in sauraro ta ji ya ce    Morning, you called me day before yesterday(kin kira ni shekaran jiya) 
ya fad i hakan har zuwa wannan lokacin idanuwansa na a kanta yana yi mata wani irin kallo kamar wanda yake so ya k irga duk wata b ular gashin da ke a fuskarta ne. Shi kan sa yana so ya d an d auke idanun nasa daga kanta amma sam ya gagara, babu abun da ya fi d aure masa kai kamar yadda tashi d aya ya shiga nutsuwa walwala da farin ciki da annashuwar da bai tab a shiga ba.

A hankali ya ji ta ce
 Sir Najeeb said you have a job for me, that s why I called.(sir Najeeb ne ya ce kana da aikin da za ka bani, shiyasa na kira).
Ta k arashe maganar a hankali
kamar tana jin tsoro.

Shiruu ya yi, yana kallon ta kafin chan yace  Yeah,i do,can i see your credentials.(eh, ina da aikin da zan baki, zan iya ganin takardunki?.)

A hankali ta lumshe idanuwanta dan sai a wannan lokacin ne ta tuna bata d auko na secondary school ba wanda ya ke shi a chan sama yake a cikin akwati, dama tana ta zuci zucin za ta d auko ta had a da ragowar sai dai kuma har ta fito Allah bai bata iko ba, haka nan ta mik a masa na primary da diplomar ta tukunna ta ce masa  ta manta na secondary school d in 
dan haka ya ce   ba damuwa, next zuwan da za ta yi, ta zo da shi  .

Ya d an jima yana nazari kafin
ya fara yi mata bayanin aikin
nata yadda zata fahimta& & .
  Akwai estate a Kano, Lagos da Abuja.
Bana so idan abu ya b aci a dinga kira na direct almost everyday (kusan kullum) sannan secretary d ina is very busy (aiyyuka sun yi
mata yawa) itama, dan haka zan tura musu number d inki ta yadda duk wani complain idan za su yi kawai za su gaya miki ki tara ki ajjiye, sai ki dinga reporting to me ranar Friday, duk Friday&
Kinga yau Monday to in four days time(to nan da kwanaki huWu) za ki zo nan kenan,
Amman idan akwai abu urgent(abunda ya ke bu?atar a duba cikin gaggawa), za ki iya kirana ko kuma ki gaya min ta online, ba sai kin jira friday ba&
k arshen wata zan dinga baki 30k.
Mun fahimci juna?  .

A hankali ta jinjina kai kafin ta ce   Yes,Sir
Thankyou so much. 

Jinjina kai kawai yayi yana mai sauk e wata b oyayyiyar ajiyar zuciya kafin ya mik a mata wata takarda mai d auke da wajen saka;
Full name
Address
Personal sickness
Email
Phone number,da sauran su& &
ya ce  ki yi filling wannan.(ki cike wannan).


Cikin nutsuwa ta zaro biro a jakarta, ta hau cikewa&
wajen phone number ne ta bari blank dan bata san ya za ta yi ba, da farko ta yi tunanin ta saka number Siyama tunda ita bata da waya sai kuma taga ai aiki ne bai kamata ta d aura mata komai a wayarta ta takura mata ba sannan anytime za  a iya kiran ta kar aji wata ta d auka ya zamana kamar bata d auki aikin ma da mahimman ci ba, shiyasa ta ga gara a yi
k ok ari a san yadda za ayi inshaaAllah ko mai torchlight ce su nemo sai ta taho da number tare da certificate d in nata, dan haka ta bar wajen blank
ta cike ragowar.
tana gamawa ta mik a masa, tana addu ar Allah ya sa daga wannan ya sallame ta.

D auka ya yi, ya kalla yaga ta bar wajen phone number blank
dan haka ya ce ta k arba ta k arasa cikewa.
Sai da ta d an yi shiruu tukunna tace masa   a yanzun ba ta da waya,amma inshaaAllah zata taho da phone number d in a next zuwanta tare da secondary school certificate d in nata. 

Shiruu yayi kawai ya zuba mata ido yana mamakin  ta ya kamar ta ace bata da waya
Wanda hakan ya sanya Manubiya ta ji kamar ta kurma ihu!..dan
gaba d aya ya d aure ta da idanuwansa, ta koina jin kwayar idanunsa take yi suna yi mata yawo a jiki.

Ya jima yana k are mata kallo kafin ya d an sunkuya ya janyo d aya a cikin drawer da ke jikin tebur d in ya zaro wata farar leda, jiya ya sayi A1 d in zai bawa mai wankin su da ya ce masa wayarsa ta fad a a ruwa&
A hankali ya mik a mata ya ce   ga shi,idan kin yi charji sai ki turomin messge da number ki meanwhile zan basu email d in ki idan number ya zama ready sai ki turomin in tura musu ta yadda za ki fara aikin asap. 
ya fad i hakan yana mai mik a mata wayar.

sai da ya sake cewa   ki karb a mana,consider it as an allowance 
tukunna a hankali kamar mara lakka a jiki ta sa hannu ta karb a ta ce   Nagode,sosai, 

dan dama har ga Allah bata san ta ina zata fara neman waya ba su da suke fama da abinci.

Ganin ya yi shiruu ya koma ya jingina kawai yana k are mata kallo ne ya sa ahankali ta sake cewa  na gode 
daga nan ta yi masa sallama ta mik e ta nufi k ofa tana adduar Allah ya sa kar ya sake tsayar da ita, a haka har ta fice daga office d in.
..
Tana fita ya lumshe kyawawan idanuwansa, ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake kai a zaune,
a hankali a fili ya ce
  It s official,I m in love
(Ta tabbata son Yarinyar nan na ke yi.)


Sai da ta fita daga office d in, ta tabbatar ta zugo k ofar tukunna ta bud e hancita ta sha?i iska sosai sannan ta sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya& .
Da kyar ta samu ta ja k afafuwanta ta nufi inda Ya Musbah ya ke wanda ya riga ya mik e tsaye tun lokacin da ya hango fitowar ta.
Kallon sa take yi tana jin k auna da tausayin d an uwan nata suna ratsa ta..
 dole haka nan za ta hak ura ta yi aiki da Yashjub ko dan y an uwanta& .domin ta samu ta bawa Ya Musbah jari sannan ta kula da ahalinta. dukda kuwa bata san ta yaya zata iya rayuwa da wannan mutumin wanda yake k ok arin tarwatsa mata zuciya ba amma dole ta dage ta taimaki ahalinta under any circumstances(duk rintsi), zata tsaya tsayin daka InshaaAllah ta ya?i tunaninta sannan ta taimaki kanta ta hanyar tirsasawa zuciyarta da tunaninta akan su daina yaba mata kyau,kwarjini,jarumta da nutsuwar Yashjub& .
inshaaAllah daga yau duk wani abu mai kyau nasa ita kuma zata yi k ok ari wajen ganin ta maidashi mara kyau a idanu da tunanin ta&
Opportunity comes at ones (Dama ta kan zuwarma wani lokaci
Waya kawai) hakan ya sanya ba za ta zubar da wannan damar ba, inshaaAllah za ta yi k ok ari ta daure ta dage ta yak i zuciyarta,ta samu ta taimaki ahalinta..
Da wannan tunanin ta k arasa inda ya Musbah yake tsaye.
Jarumta ta aro ta yafawa gangar jikinta ta k ak alo murmushi sannan tace  Na samu aikin, ya bani har da allowance na waya ma..
Aikin dole yawanci ta waya ne..
nan ta d an yi briefing masa (masa ta?aitaccen bayani) akan yadda suka yi da Yashjub. 

Cikin tsananin murna ya Musbah yace mata   congratulations Manu.
kin ga rabo ko? lecturer d in da kika tsana ga shi yau yayi miki gata.
na miki murna gaskiya&
gashi aikin ba wahala kwata-kwata, kuma na yarda da company d in a yadda yake d innan nasan an sanshi kuma ya na bin k a idoji, kinga kuwa ba za a cutar da ke anan ba..mu je 
Ya fad i hakan yana wucewa gaba,

a hankali Manubiya tace
  Tam  daga haka ta bi sa suka kama hanya suka fita& &
 Tana jin tsoron kasancewar ta tare da Yashjub amma ya zame mata dole ta taimaki ahalinta
Ta sake aiyyana hakan a ranta,
ahankali ta sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya..
 tabbas gaskiya Abbakar ya fad a ranar chan da ya ce mata Yashjub ne  crush d in ta,
Ta aiyyana hakan a ranta, da sauri kuma sai ta kawar da tunanin, a ranta ta ce
  Manubiya wake up(farka!!)&
mutumin nan ba sa an ki bane ba,
ki duba ki ga ko shekaru talatin ba lalle ya rufa ba amma ya mallaki estates nashi na kan sa&
matsalolin rayuwarki ma kad ai sun ishe ki, kar ki je ki jefa kanki ga halaka& 

BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*26*

Tun Shekaran jiya Munirat ba ta fito ba,
kasancewar ta gama exams Winta bata da abun yi da gurin zuwa ne ya sanya ko lek owa bata yi..
abinci ma bata sauk a ta ci kuma ko Ummi ta kai mata ba iya cin mai nauyin take yi ba, sai dai ta yi y ar kwalamar ta a fridge d in Ummi ko kuma idan dare yayi sosai ta sakk o ta dafa indomie ta ci ta koma.

Tun sassafe Yahanasu ta fita dan tana da client kasancewar ta independent lawyer,
ko da ta gama abun da zata yi bata komo gida ba direct sai ta wuce gidan k awarta.
Ya isha itama tana so ta d an yi wasu aiyyuka dan haka ta fita tare da Kausar domin ta rakata ta yi depending project d inta daga nan, yayinda
Yasmin take da surgery itakam tun 6 ma ta fita.
Yusra da Yadira suma duk suna da exams d in sassafe
Yadira ?ar level 1 ita kam biyu ne ma da ita safe da yamma& .
Yassira itama tun sassafe ta fita aiki !

Dan haka gidan ya rage daga
Mommy sai Ummi Baaba Larai Yassir da Munirat.

Sai wajajen 2 tukunna da kyar Munirat ta fito ta shiga taya Ummi aiki saboda yau Ummin za ta karb a girki kuma ta na so ta burge Daddy domin ta samu su sake shiryawa da shi sosai.

Sai kusa da k arfe 4 tukunna suka samu suka kammala,
kasancewar Munirat tana fashin Sallah ne ya sanya Ummi ta barta a kan ta jujjuye a flask ta kai side d in Daddy ita kuma Ummin ta tafi yin sallah da wanka.

Cikin nutsuwa take juye abincin a cooler suna hira da gwaggo mai aiki dan su Husaina da Asabe y an Matan (masu aikin) sun tafi shirin islamiyya& .
ji tayi kamar ana kallon ta dan haka ta d an juya a hankali..
da sauri ta d auke kanta ta juya ranta a d an Sace sai kuma ta ja kujera ta zauna
saboda riga da wando sai ?ar k aramar hula ne a jikinta, wandon pencil kuma ya kama ta sosai,
sam bata yi tunanin anan yake ba ta d auka a side d in Yashjub yake, ta san kuma Ummi ma ta manta ne da bazata bar ta ta zauna a hakan ba&
babu abunda ya fi bata haushi irin yadda ya kafe ta da dara-daran idanuwansa yana k are mata kallo..

  Ina wuni, d an albarka 
Muryar Gwaggo ta katsewa Yassir da Munirat tunani&
a hankali ya k araso cikin kitchen d in yana mai cewa   lafiya 
yayinda idanunsa su ke yawo a jikin Munirat wadda ko kallon inda yake bata yi ba..
ganin da yayi bata da niyyar gaida shi ne ya sanya shi ya gaida ita ta hanyar cewa  Anty Munirat,Ina wuni. 
Da mamaki ta d ago manyan idanuwanta ta d an kalle shi dan bata yi tunanin ya san sunanta ba,
sai kuma ta sunkuyar da kanta tace  ina wuni  a hankali.
Murmushi kawai yayi daga haka ya juya ya kalli gwaggwo ya ce   gyaran jiya bai fita ba fa, sannan kinsanni bana son white bedsheets, a cire a saka wani sannan a sake gyara d akin. 
Yana dire aya, da sauri gwaggo ta ce
  Yanzu kuwa d an albarka. 
Ta fad i hakan tana mai ficewa daga kitchen d in, daga nan ta nufi sama d akin nashi kusa da na Mommy, amma fa a ranta ta gama aiyyana yadda zata zaiyyanewa Munirat halayen Yasir, dan ba zata bari Yassir ya cuci y ar marainiyar Alllah ba, sarai ta lura da yanayin kallon da yake yi mata!!
bayaga tijarar da y an uwanshi suka yi mata shekaran jiya shine shima yake so zai d aura mata da nashi kalar cin zalin.

Gwaggo tana fita Munirat ma ta mik e zata fita, da sauri Yassir ya ce  We haven t met(ba mu samu
mun haWu sosai ba sai yanzu) sunana Yassir,3rd born (Wa na uku) na wannan family d in, I m an architect
C.E.O
Yassir Limited 
Ya fad i hakan yana mik o mata Hannunshi alamun su gaisa yana d an murmushi.

Ba tare da ta kalle sa ba ta ce   nice to meet you(madalla da haWuwarmu)
ta fad i hakan tana k ok arin wucewa

Da sauri ya sha gabanta yace
  Am..dama Ina so in baki hak uri a kan abunda su Ya isha suka yi miki the other day&  

Cikin katse sa tace
  Dan Allah ya Yassir ka bar maganar, za mu yi resolving (sasanta) a tsakanin mu, girls(Mata). 

Murmushi yayi yana yi mata wani irin kallo kafin kansa tsaye yace  you don t like me,Y?
(Kamar kin tsaneni! Amma Maiyasa?
kar ki damu ki fad a min ba zan ji haushi ba 

Cikin k aguwa tace  a gajiye nake, sannan Ina da damuwa, kai kuma ka zo kana ta magana, bana son yawan magana. 

A hankali yace
 Sorry dear!
Na fahimta, kuma ban ji haushi ba. 
ya fad a hakan yana mai matsawa sannan ya nuna mata hanya da hannunsa ya d an rissinar da kai yana wani kalar murmushi.

Da sauri ta wuce ta fita tana waiwayen sa kamar wanda akace zai biyo ta ya kama ta ne.


A Chan corridor ta lab e sai da taga hawan shi sama da juice da cake da alamun su ya zo d auka, tukunna ta fito ta koma
kitchen d in ta k arasa zuba abincin ta kai d akin Daddy,bragowar kuma ta jere musu a kan babban dining table d in tukunna ta zuba nata ta ci a kitchen d in dan sai yanzun ne yunwa ta fara kwak ular ta saboda rabon ta da abinci mai nauyi tun shekaran jiya& .

Gwaggo ta riga ta gama wanke wanke shiyasa itama tana gama ci ta shiga d auraye plate d in da ta b ata.
Tana cikin wankewa
Ya isha da Kausar suka shigo
suna hira&
ko kallon ta ba su yi ba haka suka ci gaba da hirar su kamar ba su ga mutum a kitchen d in ba, suna hira suna shewa Kausar ta d auko pizza a fridge ta sa a microwave ta d auko cake da drinks suka nufi d an mini dining d in da ke a cikin kitchen d in suka zauna.

Su ne ya kamata su kula Munirat duba da abunda ya faru a tsakanin su tunda itace bak uwa, sannan yanzu ma ita suka tarar a cikin kitchen d in& .Amma basu ko kalle ta ba..gudun magana ne ya sa har
Munirat ta juya za ta fita sai kuma ta koma inda su ke ta tsaya
tace
 Am..Ya isha sannun ku da zuwa, dama tun jiya ina so mu yi magana, amma sai ban samu ganin ku ba sai yanzu&
dama a kan abunda ya faru ne, ku yi hak uri mu fahimci juna, a samu komai ya wuce.

Dai-dai nan Kausar ta mik e ta nufi microwave d in da ta fara k ara Ya isha kuma ta d auko wayarta ta hau daddannawa.

  Ya isha 
Munirat ta sake kiran sunanta tana mai k ok arin danne zuciyarta.

Ba tare da Ya ishan t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a d ago ta kalle ta ba ta ce  Ni fa, waya zan yi da boyfriend d ina, so pls leave..dan na tabbata turare ko wankan da kika yi shekaran jiya bai gama barin jikinki ba!!
Najeeb is a very handsome and nice guy (Najeeb kyakkyawa ne kuma ya na da kirki) sannan ina son shi, dan haka ban shirya bar miki shi ba&  
Ya isha ta fad a mata hakan tana mai daddana wayarta
ba tare da ta kalli Munirat d in ba, kamar ma ba da ita take maganar ba.
Dai-dai nan Kausar ta dawo da pizza ta ajjiye musu suka shiga ci.

Har Munirat za ta ce wani abun
sai kuma ta juya kawai ta fita zuciyarta tana wani irin tafarfasa.


Tana fita Kausar ta kalli Ya isha ta ce  na san ni cousin d inku ce amman a yadda muka taso
Ni kamar sister nake a wajen su Yash da Yassir, sab anin Munirat dan haka ya kamata mu yi wa Ummi magana ta daina barin katuwar y arta tana yi mana yawo tib ir-tib ir a gida, dan naga kamar ma

25 / 51