Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   18 / 51

51K to 54K   out of 151.9K words

soyayyar da ba lalle an taSa yin kwatankwacin irin ta a tarihi ba dan ya lura da Manubiyan itama a ranar da suka fara had uwa da Yash d in.

  Najeeb 
Yashjub ya kira sunansa.

Kame-kame Najeeb ya fara yana tunanin mai zai ce masa, saboda shi dai ya riga ya gama fahimtar Yashjub d in tsaff to amma shi kuma gashi yace kar a ce masa yana son Yarinyar ne
Which is the absolute truth(wanda hakan ne ha?i?anin gaskiyar)&
Dan haka a hankali cikin son fahimtar da shi ta ruwan sanyi Najeeb yace
  Mai yasa kake tunanin ba son ta kake yi ba? soboda kai ba Mutum bane? 
Ganin ya ?i ma ya kula shi ne yasanya Najeeb cewa
  Shikenan bara zan san abun yi
amma gaskiya ni a yanzu ba zan iya nema maka mafita ba.
Frnds d in dai da ka ambata inshaaAllah zan had aku friendship (Abota) dukda ni ban ma san ta Ina zan fara ba tunda kaga ni Malaminta ne amma in sha Allah zuwa gobe za ka ji ni, zan nemo idea soon, bari zan jira dan kamar suna da exams d in Dr Auwal

Shiruu Najeeb d in yayi daga magana kafin ya sake cewa
 bari zan san yadda zan yi kar ka damu, na ma nemo idea  .

  Ok 
Kawai Yashjub ya ce
Kafin ya sake cewa
  Kuma wannan wanda na gan su tare kana tunanin akwai wani abun a tsakanin su  ?

Dariya najeeb yayi a ransa yace
  Ga wani sign din  kishi 
A fili kuma sai ya ce
  I don t think so, amma dai zan yi finding out 

Shiruu Yashjub yayi dan sai kuma ya d an fara jin haushin kansa na tambayar da ya yi wa Najeeb d in ta yanzu.
Ganin yayi shiru ne
Yasanya Najeeb kawo wata hirar daganan suka hau tattaunawa&
..
Kiran sallar laasar ne ya tashi zaman nasu
Yashjub ya wuce
Najeeb kuma ya nema wani ya aika shi inda su Manubiya suke exams yau yace masa ya kira mishi Abbbakar.
Daganan ya wuce masjid& ..
" " " "
Tun rabuwar Kausar da Yashjub da ta shige d akinta ta rufe bata bud e ba!
Mommy ta je har sau biyu&
Jin ta yi knocking ba a bud e ba
yasa ta yi tunanin ko ta fita ne maybe
dan haka ta hak ura ta
hau zaman jiran ta.

Ganin har yamma ta yi bata ganta ba yasa ta sake komawa domin ta sake dubawa dai-dai nan ita kuma Kausar d in tana shirin fitowa daga side d in nata.
Kana ganin fuskarta ka san ta ci kuka ba kad an ba.

A hankali cikin rashin jin dad i Mommy ta ce
  Haba Kausar, yanzu ashe tun Wazu kike ta faman kuka, mai ya faru haka, mai ya sameki? 
Ta yi mata tambayar tana mai tsare ta da idanuwa.

Fad awa ta yi jikin Mommy ta sake fashewa da wani irin kuka
cikin kukan ta ce
  Mommy ko kallo ban ishi Ya
Yash ba, ni gani nake ma kamar yq tsane ni,
tayaya kike tunanin zai kalle ni ma
Talkless of ya bani time da chance d in da zan kafa kaina a cikin Zuciyarsa?.
Ke da Baaba Larai kullum sai cewa kuke yi in jira in jira yau an fi wata d aya kuna cewa in jira, so kuke yi in yi ta jira har sai lokacin da ya had u da wata ya fara son ta tukunnna ni kuma in nuna mishi ra ayina?.
nikam a gaskiya Wallahi ba zan sake bin ta maganar ku ba ko zai
ko zai kasheni da duka zan gaya masa in yaso ke da Baaaba Larai ku san abun yi daganan. 

Da kyar Mommy ta samu ta zaro ta daga jikinta cikin son fahimtar da ita ta ce
  Kausar gaggawa aikin shed an ne, ki tsaya ki nutsu!!!
Na gaya miki na san abun yi kin ji ko? saurin me kike yi ?
Yash naki& . 

Cikin ture Hannun Mommyn daga jikinta tana kuka sosai ta ce
  Mommy dole in yi sauri, baki san ya nake ji game da shi a cikin zuciyata ba, ina tsoron kar ya sub uce min sannan ga fargabar kar Yasir ya sanya Daddy yayi min dole&
Ko da yaushe fa a cikin fargaba nake. Kar in rasa Ya Yash
In ya sub uce min mutuwa zan yi, wallahi mommy inban aure sa ba & & &

Tsit maganarta ta katse ganin Yash d in yana hawowa sama cikin main parlour d in saman

Cikin zuciyarta kuma sai ta ce
  Ai da ban yi shiru ba gara kawai in fad a ya ji ko zan huta, 
dan haka ta yi saurin kau da kai kamar ba ta gan shi ba, ta bud e baki za ta yi magana kenan shi kuma ya ce   Mommy  da d an k arfi.

Da sauri Mommy ta saka Hannu ta toshewa Kausar Baki dan har ta cigaba da cewa  wallahi&   .

Ba tare da ya kalli Kausar d in ba ya k araso wajen ya na kallon Mommy
Fuskarshi a murtuke kamar bai tab a dariya ba ya ce
  Barka da gida Mommy 
bai jira jin me zata ce ba ya d aura da cewa
  Mommy dan girman Allah kar ki sake aiko min Yarinyar nan side d inmu, tun da kin san bata da hankali kuma bata san ciwon kanta ba to
da baki turomin ita ba& .
ko mayafi fa babu a jikinta Wazun, a haka ta je min. 

Cikin rarrashi Mommy ta ce
  Yash wayoyinta fa da atms har ma da passport duk ka had a ka kwace yau kusan wata ko in ce fiye da wata d aya ma, kaga kuwa ai kai ka kira ta side d inka ba niba  .

Cikin fushi yace
  Au dama ba ke kika turo ta ba
zuwan kanta ta yi? 

Ya fad i hakan yana nufar Kausar d in a zuciye kamar zai make ta.

Da sauri Mommy ta sake shiga tsakanin su cikin rarrashi tace   A a ni na turota mana
Hausa ce nayi maka..
Anyways tunda baka gane ba shikenan
yanzu ka yi hak uri ka bata wayarta muna son ta kira Yasir dan ya kamata ace yayi hak uri haka ya dawo gida, naga alama Daddyn ku yana k ok arin mantawa dashi a cikin ya yan sa  .

Tunda Mommy ta fara magana idon Yashjub yana kan Kausar
wadda ta sunkuyar da kanta k asa,wata kalar hararar tsana yake jifan ta da shi.

Ahankali Mommy ta d an kamo hannunshi ta ce
  Ka ji Yash, d an uwanka ne kar
mahaifinku ya yi zuciya ta har abada da shi ata dalilin shirmen nan nasa, ka bata wayoyinta ita za ta san yadda za ta yi ta yi contacting Winsa,in ta yi masa magaa zai dawo. 

Sai yanzu ya d auke idonshi daga kan Kausar ya maida kan Mommy tukunna yace
  Na san inda yake,anjima zan je in taho dashi
Dan naga alama absence d insa yana k ok arin janyo min bala i  .

Shiruu duk su biyun sukayi
Mommy tana adduar Allah yasa ba maganar su ta yanzu itada Kausar ya ji ba,
Kausar kuma tana adduar Allah yasa ya ji d in.

Muryarshi ce ta katsewa duk su biyun tunani
Jin yana cewa
  Mommy dan Allah dan annabi kar ki sake turomin Yarinyar nan, zan kawo miki phones d in nata da komai anjima,
Ina shikenan? 
Yayi maganar yana mai d aga hannunshi duka biyu da gira d aya.

Murmushi Mommy ta yi
sannan ta sa hannu ta shafa kumatun shi a hankali tana murmushin ta ce
  Shikenan son,shikenan na gode  .
Kama Hannun Mommy wanda yake a fuskar tasa yayi kawai yana kallon ta,
Itanma shi take kallo tana nazartar shi
So take ta gano  ya ji zancen nasu ko a  a.

Bai bata dama ba kuwa dan k asa yayi da kansa ya furzar da iska ba tare da ya ce uffan ba ya cika Hannun nata ya juya ya fita ya nufi side d insu bayan ya tsaya ya d auki belongings d insa daga motarsa&

Ko shiga side d in nasu dama bai yi ba ya nufi wajen Mommyn dan ba kad an ba ya ji haushin zuwan da Kausar ta yi masa Wazu da safe bagatatan& ..


BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*19*

Kamar kullum yau ma tare Abbakar da Manubiya su ka fito
daga Wakin jarabawa.
Suna tafe yana bata labarin Baraka a jiya da ta je gidan su& .
Adashe ta ke yi ashe, ta kwashi nata har naira dubu d ari uku a jiyan!
Yana d akinsa na soro ya ji ita da maman shi da mamanta suna hirar  wai fili zata cika ta siya ta yi gini .

A hankali Manubiya ta sauk e wata nannauyar ajiyar Zuciya a fili ta ce   Allah ya sa ta fi haka!
Allah ya bata ikon siyan wasu filayen dayawa nan gaba.. 

  Abbakar! 
Suka ji an kira sunan shi.

Cikin yanayin maganarsa ta masu sanyin jiki ya juya ya kalli mai kiran nasa ya ce
  Na am  .

Dariya saurayin ya yi kafin ya ce   ka bi ka dagewa k awance da Mace dama kai ga ka ga yanayin ka yanzu kam ba marabar muryarka da ta Macen& .
ka je Sir Najeeb yana neman ka 
Ya k arashe maganar tasa yana me tapping shoulder d in Abbakar d in daga nan ya yi gaba ya wuce ya bar su nan tsaye.

Yana wucewa Manubiya ta ce
  Allah yasa lafiya 

Murmushi ya yi ya ce   InshaaAllah ma lafiya, mu je sai mu ji menene 

Dasauri ta ce
  Wa?Ni?tab!inaaaa..  .

wata kalar harara ya yi mata
kafin ya ce
  Ban gane ba, ba za ki raka ni ba?  .

Cikin nemo mafita da sauri ta ce
 Abbakar na fa gaya maka na bar aiki burjik a gidan Ammi, gashi yanzu 4har ya wuce, dan Allah ka yi hak uri kar mu je yau ma mu tarar yana da bak o mu yi ta zaman jiran sa in yi letti wajen Ammi, sannan kaga ga karatun exams d in jibi, ta yau ma ta bani wahala wallahi. 

Cikin sigar tsokana ya ce
  Ko dai ba kya so yau ma ki sake yin gamo da crush d in ki ba. 

Da sauri ta zaro ido sai kuma ta buga masa littafin Hannunta tana mai cewa
  To k arya dak ik in tunaninka ya baka, wallahi ba wani crush  .

Dariya ya yi yace
  Auch  .yana sosa inda ta buga masa littafin sannan still yana dariyar ya ce
  Shikenan, ki je sai mun had u gobe inshaaAllah. 

Hararar sa ta yi daga nan ta juya ta wuce.

A hankali ya sunkuyar da kansa yana murmushi kafin ya d aga kai ya bi bayanta da kallo& ..
sai da ta b acewa ganin sa tukunna ya sau?e ajiyar zuciya sannan ya juya ya nufi office d in Sir Najeeb&

Yana zuwa wajen ana shiga sallah, sanin halin Sir Najeeb d in ne ya sanya sai da ya je office d in nasa ya tabbatar da baya nan tukunna ya nufi masallacin shima.

Yana shiga ya tarar da shi a sahun gaban sa.
Cikin nutsuwa aka gabatar da sallar la asar ana idarwa shi da wasu a cikin masallacin da suka rasa raka a suka tashi domin ramawa masu addu a kuma suna yi.

Yana idarwa shima yayi addu a ya shafa daganan ya zauna zaman jiran Sir Najeeb
yana mai ha dawa da adduar  Allah dai yasa ba wani laifi ya kuma yi ba
dan bayan class rep in dai ka ganka a office d in Sir Najeeb to ba k aramin abu bane ba.
Ko wani abun ne ma kake da buk atar yi ko gaya masa to daman an san ka idarshi ka gayawa class rep shi kuma ya fad a masa & .

Ganin fitar sa ne ya sanya
Abbakar d in mi kewa da sauri ya bi bayan sa.

A bakin office d in nasa suka had u yana k ok arin bud ewa dan haka yana bud ewa suka shiga tare Abbakar ya shiga da sallama sannan ya shiga gaida shi da ladabi.

Cikin nutsuwa ya amsa masa
yana mai neman guri ya zauna akan d aya daga cikin
sofa d in dake a office d in kafin ya d ago ya kalle sa
ya ce   d an zauna. 

Cikin d an d ari-d ari Abbakar ya nemi waje ya d an d osana mazaunansa ya yi shiruu,
zuciyarsa tana masa sak e-sak e kala-kala.

Shiruu shima Najeeb ya yi yana tunanin ta ina ma zai fara ne,
Wallahi ba dan Yashjub bane Allah da babu abunda zai sa ya yi wannan abun
haba!student d insa fa abun ya yi wani iri da yawa, amma ya ya iya dole ya daure ko ba komai shima yana so ya ga Yashjub ya yi aure, kuma tunda har ya ga Yashjub ya zo ya same sa a kan maganarta tou kuwa ya san abun na gaske ne, wanda hakanne ya sa shima ba zai yarda ya Wauki batun da wasa ba.

Ahankali ya sauk e ajiyar zuciya ya d an yi gyaran murya
wanda hakan ya sanya Abbakar ya mik a masa
dukkannin hankalinsa.
Cikin nutsuwa Najeeb ya ce
  Akan wannan ?awar taka na kira ka, Manubiya

Shiruuu Abbakar d in ya yi da farko
kafin a hankali ya ce   Ok,Sir. 
Dan zuwa wannan lokacin
Kwakwalwarsa ta gama bashi
amsar dalilin kiran da aka yi masa.

  Tana da wata matsala ne?,as in family issue besides rashin lafiyar Mahaifiyarta? 
..
Manubiya ?awarsa ce da yake yi mata kallon kamar ma ta zama ?ar uwa, a ganin sa bai kamata ya kunce mata zani a kasuwa ba.
Dan haka ya ce
  A a rashin lafiyar Maman nata ne kawai issue d in ta  .

  Shiyasa take kuka kusan kullum a class? 
Sir Najeeb ya sake jeho masa wata tambayar cikin katse sa.

Shiruu ne ya d an biyo baya kafin Sir Najeeb d in ya ce
  Kamar yadda na fad a muku the other day
Malamai kamar iyaye su ke,
a yadda na ke ganin ta so disturbed (a dame) kullum na yi tunanin tana da financial issue ne.
Am na san ba hurumin mu bane
but Aboki na wanda ka ganmu tare ne yake da offer na aiki very simple wanda Mace ko tsoho za su iya yi& 
A Ta kaice Sir Najeeb ya yi wa Abbakar bayanin aikin da ya ga damar had awa a kansa a take a wannan lokacin kafin ya d aura da cewa
  Na yi tunanin tana da financial problem shiyasa na ce mishi akwai wadda zan nemo ta yi mishi aikin but tunda ka ce ba haka bane ba shikenan zan ce mishi ya nemi wata kawai  .

Shiruuu Abbakar ya yi, ya hau tunani& ...
 Tabbas ya san Manubiya za ta yi farin ciki da offer d in nan, to amma kuma& .

Cikin katse masa tunanin Sir Najeeb ya ce   Shikenan, u can leave, dama reason d in kiran naka kenan  .

Duk da b oye-b oye da kwana-kwanar da Sir Najeeb yayi tashi d aya Abbakar ya fahimci inda suka dosa daga shi har Abokin nasa, hakan ya sanya ya shiga tsaka mai wuya dan on the other hand, no matter how (a ta wani fannin, duk rintsi)& ko ma menene yake ji yake kuma tunani to fa bai kamata ya yi wa Manubiya bak in ciki ba!
Besides (baya ga haka ma) shi a rayuwa da ko da yaushe yana saka farin cikin ta ne a saman nashi..
Dan haka ya Wan gyara zama!
Da kyar ya iya danne zuciyarsa ya d ago manyan fararen idanuwansa waenda suka d an fara surkuwa da kalar ja ya ce   za ta yi, baku da matsala za ta yi cikin farin ciki ma, in sha Allah. 
Yana gama fad in haka ya maida kansa k asa.
Har cikin zuciyarsa ya yi wa Manubiya farin ciki da samun wannan aiki dan daga gani mai tsoka ne, ya san zata rage damuwa kwarai sannan za ta yi maganin matsalolinta, duk da kuwa ya riga ya san akwai wata Soyayyiyar manufa a bayan aikin da aka bata, amma dama tun ba yau ba ya dad e da yankewa  indai rana mai kama da ta yau ta zo, to ba zai bari zuciyarsa ta rinjayi tunanin sa ba .
Ya san ba wai Sir Najeeb d in ne yake son ta ba amma shakka babu kamar yadda ya lura da itama ta tab u da ganin wannan Abokin nasa haka zalika shima Abokin, tunda gashi ya fara fakewa da bata aiki& ..

A hankali ya fesar da iska a ransa yana sake jaddadawa kansa cewa   inshaaAllah, ba zai tab a bari shirme da mafarkinsa su shiga tsakanin Manubiya da auren wannan Mutumin ko aikin da ta samu ba.. 

A b angaren Najeeb shima shiruu kawai ya yi yana nazartar Abbakar d in kafin daga baya ya ce   ok,ga katin friend d in nawa, idan ta shirya sai ta kira shi ta ce masa itace Manubiya Musa wadda za ta yi masa aikin da Najeeb

18 / 51