Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   16 / 51

45K to 48K   out of 151.9K words

firgigit ta d ago tana kallon ta kafin ta samu da kyar ta had iye wani abu wanda ya tokare mata mak oshi tukunna a hankali tace  Ok  .
kafin ta kalli Muhsin wanda ya dawo daga mik a ruwan band akin ta ce
  Na gode auta,bari in yi in rage maka  .
Tana gama fad in haka ta mik e
ta d auki abubuwan da zata buk ata ta fad a band akin. &


BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*16*

Tana fitowa daga wanka,
aka aiko kiran su daga wajen Kaka Mallan.

Muhsin kawai suka bari a wajen Inna su duka suka d unguma.

Uncle,Ya Yusuf,Baba Habu Anty Umma sai Kaka Mallan suka tarar.
Ko gaisawa Uncle bai bari an yi ba dan yana lura babu Ya Musbah ya d au waya ya hau kiransa yana mitar  ya an ce za ayi meeting, amma an bar shi ya tafi,bai zo ba .

Sai da aka jira ya zo ya fara bud e taron da addu a tukunna Uncle ya bari ma aka gaggaisa.

Ba tare da b ata lokaci ba
Kaka Mallan wanda ya amsa gaisuwar su Baba da kyar ya kalli Baba ya ce
  Musa  !
Sai da Baba ya lumshe Idanunsa ya bud e tukunna ya ce   Na am,Kaka. 

Sai ya d an nisa tukunna ya ce
  Dazu d an uwanka ya zo ya same ni akan batun Matar senator da y ar wajen ka, an yi part 2 kenan? 

Shiruu Baba ya yo kafin chan ya ce
  InshaaAllah hakan ba zata sake faruwa ba, na tsawatar mata  .

Cikin d an daka tsawa Kaka Mallan Win ya ce
  Kai dallachan gafara, ka tsawatar kuma na yaushe, kwanakin baya ba an tsawatar matan ba amman ka ga alamun ta yi amfani da tsawatarwar?.
kuma tsabar cin fuska da rashin sanin ya kamata
MUSA, Yusuf fa da Mahaifinsa suna cikin gidan nan amman kuka barta take kula wani  Al ameen .

Dama na fahimce ka tun ba yau ba,komai naka daban yake& ..
Duk wata hanyar da zaka bi ka salwantar da had in kan zuri ar nan tou ka sani, kai kenan ace komai naka a botsare? kuma duk in ka je ka dawo baka ganin dai-dai sam amma taurin kai ya ?i bari ka saduda?
Ka duba kaga yadda ka kafe akan kasuwanci kana ganin babu riba amma dukda haka sai da ka d aura Musbahu akan kasuwancin shima, kana gani y an uwanka suna karatu amma kai ka nacewa abu d aya gashi yanzu a ta dalilin botsarancin ka kai da iyalin naka gaba d aya kun zama abun tausayi.

Da sauri Manubiya ta mik e ta juya za ta fita.

Cikin karsashi Kaka Mallan ya ce  Wallahi zan ci ubanki, ni zaki mik e ki fitarwa ina tsaka da magana, saboda na fad i gaskiya?dawo ki zauna tun kafin in saka Yusuf ya ladaftarmin da ke  .

Ko gezau Manubiya bata yi ba,
bata fitan ba kuma bata koma ta zauna d in ba, har sai da Ya Musbah ya daka mata tsawa ya ce   Wai ba da ke ake magana ba?  Tukunna ta koma ta zauna tana ji kamar ta fashe tsabar takaici.

Baba,
Kaka Mallan ya kalla kafin ya ce
  Ka gani ko?
kalli ka ga!!
Wannan ?ar sai ta gagare ka wallahi 
ya fad i hakan yana nuna Manubiyan kafin ya d aura da cewa
  Babu yadda ba a yi da kai akan ka aurar da ita ba amma ka nace akan karatun da aka kwad aita maka tun farko ka k i yi,shi za tayi.
Ita da take y a mace wadda ya ci ace yanzu ta yi Yara biyu ko uku ma, amma ka ja mata har ta yi kwantai&
tunda ni dai rabon da in ji sallamar zance da sunan ta har na manta,
ta d auki shegen girman kai ta azawa kanta bata kula waenda suke zuwa mata ai gashi duk sun gudu, ba fata nake miki ba Amman da wuya ki auru sai ki je ki rungumi littafi. 
Shiruu kowa ya yi baka jin maganar kowa sai ta Kaka Mallan ta inda ya d aura da cewa
  Duk da ka nuna ban Isa da kai ba dole zan saka baki a maganar Jidda wanda dalilina na biyu kuma shine
ba zai yiu ka tara Yara da kai kanka ku na ta kurmutsa a d aki a takure kuma kak i d aukar shawara sannan ka yi tunanin za mu yi shiru ba.

Ba zan zuba ido Yaranka mata har biyu su tagaiyyara ba.!
Ita Manu yanzu ta riga ta zama sai an had a da addu a, shiyasa tun kafin Jidda itama ta yi kwantai na riga na gama yanke shawara kowa ya saurara ya ji..
Nan da sati biyu dama za a kawo kayan sa ranar Siyama dan haka a tare a kuma rana d aya Yusuf shima zai bada na Jidda, in Allah ya kaimu nan da wata uku za  a had a a d aura auren tare da nasu Siyama a mik a ta d akinta, in kuma anan cikin gidan ma zai zauna shima sai a ware ma sa nashi fannin.

Sai maganar kud in Matar senator, Ummaa da Uncle sun bada dubu bibbiyu Habu ya bada uku nima zan bada uku a had a a bata kai kuma sai ka nemi cikon ka cikata mata, Allah ya rufa asiri.

Akwai mai magana?  .

Ahankali Anty Umma ta ce
  A a Kaka  .
Tana mai jin takaici a ranta, ita da take Mace kuma za ayi auren y arta, babu wanda a cikin su ya bata ko sisin kwabo, Yayar Siyaman sai ita ne kawai suketa fafutukar komai, hatta lemukan da za a tarbi bak i ita ce zata siya, an sakar mata komai an zuba mata ido kuma ta sab ba bayarwar za su yi ba daga nan har akai siyama d akinta,amma yanzu ita an hura mata wuta sai da ta bada dubu biyu&

A hankali Baba ya ce
  Kaka Mallan,Ina da magana 

Sai da Kaka Mallan ya d an k ura masa ido tukunna ya ce   Muna jin ka  .
Sai da ya fara yin godiyar karo karon kud ad en da suka yi masa tukunnna.
Cikin rashin jin dad in maganar da zai fad a ya ce
  Ka yi hak uri Kaka, ba wai jayayya zan yi da kai ba amma Ina ganin maganar auren Jidda da Yusuf
gara kawai a barta 

Ba tare da Baba Habu ya ce komai ba kawai ya mik e ya fice daga parlourn gaba d aya.

Cikin fushi Uncle ya kalli Baba ya ce
  To ai shikenan, gata nan sai ka kwad ata ka cinye, amma wallahi idan ta sake janyo magana kar a kuskura a sake involving d ina a ciki  .
Daga haka ya juya ga Ya Yusuf wanda ya sunkuyar da kansa yayi shiruuu
ya ce
 Yusuf dan Allah dan Annabi ka hak ura da Yarinyar nan, kana da degree d inka da sana arka babu gurin Yarinyar da zaka je ta k i ka  .

Anty Umma dai bata tanka musu ba hakanan ta jaa Bakinta kawai ta yi gum, tana kallon kowa.

Da dakakkiyar murya Kaka Mallan ya ce
  Musa, inaso ka gaya min laifin Yusuf kwara d aya tak  .
Ba tare da shakkah ba Baba ya ce
  Yusuf bashi da laifi Kaka kawai dai na ga a halin da Jidda take ciki na damuwa da rashin lafiyar Mahaifiyarta bai kamata a yi mata auren dole ba, kuma ni ban shirya aurar da Jidda ba har sai mahaifiyar su ta samu lafiya, InshaaAllah. 


Sai yanzu Anty Umma ta ce
  Ita Jiddan ta ce maka bata son Yusuf d in? 

Tun kafin Baba yayi magana Jidda ta yi k arfin hali da sauri ta ce   Eh,Umma  a hankali.

  Uhm, to ai shikenan 
Anty Umma ta ce, daganan ta ja bakinta ta sake yin shiru.

Tabbas ran Kaka Mallan ya b aci dan haka kawai ya ce  kowa ya tashi ya tafi 
Yanayinsa kad ai ya sanya kowa ya fahimci tabbas in ba da kyar ba to kuwa sun d aura gaba kenan da shi da Baba har abada..

Hakanan taro ya watse zuciyar kowa da k unci, dan shi kansa Baba saboda yaga ba yadda zai yi ne shiyasa yayi magana bayaso ya sako karatu su yi masa chaa amma yanaso Jidda ta fara ko da level one ne ta d an saka k afarta a jami ar tukunna a yi auren, ga kuma damuwar da suke ciki ga rashin lafiyar Inna, abubuwan da yawa!! Ya san dama ba lalle su fahimce sa ba.
Shiyasa washegari ya bi Kaka Mallan anty Umma Baba Habu da Uncle,
dan yana so su sasanta a tsakaninsu su manyan sannan ya fahimtar da su.
Amman sai abun bai yi masa dad i ba sam dan Anty Umma ce kawai ya samu ta d an saurare sa ya gama bayanin sa, ta ce
 Ba komai kawai.
Dama ita ?ar i don t care ce.
Uncle kuwa tun a masallaci ya ce masa yana son ganin su shi da Baba Habu in an fito amma suna fitowa ya shiga gidan da yake parking motarsa ya zari mota yayi gaba gashi ranar lahadi ne bare ace aiki ya je.
Baba Habu kuma ya ce masa bacci zai yi, lokacin siesta d insa yayi.
Kaka kuwa tun kafin ya k arasa shiga wajen nashi ma ya kore sa.
Tun daga ranar kuwa kan y an gidan ya sake tarwatsewa, da farko lamarin nasu rashin had in kai ne kawai yanzun kuwa abun ya had a har da jin haushin juna da fushi.
& .
Satin Manubiya d aya da fara zuwa aiki gidan Ammi.
most atimes (mafi yawanci) exams Win nata da safe suke yi shiyasa take zuwa gidan tun kafin gari ya fara haske saboda ta samu ta yi ta gama ta tafi on time,ranar na Sir Najeeb ne kawai ta rok i Ammi,
tun ana i washegari exams Win ta ce mata  Dan Allah ta yi mata hak uri
10 za ta taso InshaaAllah zuwa 11 za ta iso gidan ta yi aikin nata.
Allah ya taimake ta a lokacin da ta je ta na neman alfarmar
Mama tana d akin Ammin
tana shirya mata wardrobe d inta,ai kuwa tashi d aya Maman ta saka Baki&
Dan haka ba dan Ammin ta so ba sai dan girman Maman a idanunta ya sanya ta hak ura ta yardar ta amince& ..
Itafa so take ta maidawa su Manubiya rayuwar su living hell (mafi ?ololuwar azaba) amma ta lura Yarinyar ita da k aninta (Muhsin) kamar waenda ake jona musu charji, duk kalar uban aikin da ta tula musu kafin ace kwabo sun kammala shi tsaf.

A b angaren Manubiya kuwa sam aiyyukan da Ammi take tula mata basa damun ta, ita babban tashin hankalin ta a gidan ita ce Mama , kamanninta da wannan Mutumin sun yi yawa sannan in dai ta kalli fuskar Mama tou sai ta tuno shi kuma indai ta koma gida ta kwanta barci tabbas sai ta yi mafarkin shi maimakon ta yi mafarkin Mama tunda ita ta ke gani,
A a
Mafarkin Mutumin take yi
kuma kullum kamar sake ingiza mata tunanin sa ake yi.
Hakan ya sanya a ko da yaushe take k ok arin ganin ta yi nesa da Mama. Wanda zuwa wannan lokacin Hatta ita kanta Maman ta fahimci Manubiya wasan y ar b uya take yi da ita, bata san dalilin Yarinyar na guje mata ba gashi ita kuma har ga Allah Yarinyar ta shiga ranta, sosai& & &
" " " " "
Amaryar Daddy tana cika sati biyu da tarewa rana tsaka ya ce  ta had a kayanta za su koma main house d insa, .
*Ummi*
Mace ce mai sauk in Kai da fahimta ga hak uri, shiyasa tun kafin auren ma da ya ce mata ta ajjiye aikinta tashi d aya ta ajj??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????iye, sam bata yarda ta yi jayayya da shi ba shiyasa yanzun ma da ya ce su koma main house Win nasa tashi d aya ta ce   to  ,
Kuma ita har ga Allah bata ji komai ba dan by then (zuwa wannan lokacin) sun saba da Mommy da ?a?anta saboda bata yi k asa a guiwa ba sai da ta amshi numbers d in su kaf su ke gaisawa,
sam
bata damu da yadda a ko da yaushe ita take kiran su ba.

Basu samu dawowa ba sai
washegari, dama gado da set d in kujeru kawai ta yi amma hatta kayan kitchen a gidan ta je ta tarar dan haka aka kunto mata iya gadonta da kujerun
aka zo nan mansion d in aka kafa mata a side d in da Daddy ya nuna mai d auke da parlour mini kitchen dining area da two bedrooms, k ofar side d in nata yana kusa da na Kausar na Yasira kuma kusa da na Mommy.

Tare ta zo da ?arta Munirat, mai kirki sosai da hankali ga nutsuwa
Ga ta kyakkyawa sosai
doguwa dirarriya black beauty, ga gashi tubarkallah.
Ummi ta so Munirat ta zauna
a d ayan d akin gefenta(na cikin fanninta)
amma sai Mommy ta yi insisting
akan itama a ware mata nata d akin a gefen na su Yasmeen, hakan kuwa aka yi,
aka ware mata d aki anan side d in nasu su uku
Ita, Yasmeen sai Yadira
kowa da d akinta amman suna sharing parlour& .

Lamarin Yasir ya ishi Mommy
gashi gidan an dawo kamar komai bai faru ba dan hatta Kausar ta ware sosai ta ci gaba da shiga mutane&
Daddy shima ya d an sak k o yana d an wasa da yaran
Shi da Mommyn ne dai har yanzu daga gaisuwa shikenan
shima sai in a gaban yaran ne ya ke amsawa amma
Idan iyaka su biyu ne ko kallonta baya yi.

Amman shi Yasir har yanzu shiru Allah kad ai ya san inda ya je ya zauna.
Dan haka ta yanke shawarar tunkarar Daddy da maganar yau duk da bata san ya za su kaya ba amma ta saka a ranta zata yi koma menene muddin za a nemo mata Yasir d inta.

Dama yau Win ita ce da girki dan haka ana gama dinner bayan an d an tab a hira kowa ya watse itama ta je ta d an kimtsa ta nufi chan sama hawa na biyu inda side d in shi yake.


A parlournsa ta same shi yana waya dan haka ta koma gefe ta samu guri ta zauna.


BULAMA
'?
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*17*

Ya fi 1 hour yana wayar kafin finally ya katse kiran ya ci gaba da danna computer dake a gaban sa.

Ta ji zafin yadda ya yi mata, dama a wuya take dashi yau ko kunya babu haka ya dinga zolayar Ummi Wazu a wajen dinner a gaban kowa ita kuwa ko kallo ba ta ishe sa ba.

Da kyar ta samu ta danne abunda takeji yana taso mata, ahankali ta ce  barka da dare,Daddy  .

Ba tare da ya kalle ta ba
Ya ce   za ki iya tafiya, na gode. 
Yana gama fad in haka ya mik e ya tartare kayayyakinsa waenda ke zube a gabansa kan centre table Win, daga nan ya nufi hanyar d akinsa.

Da sauri itama ta mik e ta ce   a kan Yasir na zo mu yi magana  .

Kamar ba zai kula ta ba sai kuma ya ce   what about him?( me ya faru akanshi?).
Ba tare da ya kalle ta ba.

Sai da ta sauk e ajiyar zuciya tukunna ta ce
  Ba ka lura baya gidan nan ba?
Ya fi 4 weeks fa ba ya nan  .

Sun fi 2 minutes a tsaye dan sam Daddy bai so ya kula ta. Ya so ya danne fushin sa ya manna mata kawai ya yi wucewar sa amma sai hakan ya gagara..
A hankali ya juyo ya ajjiye computersa da wayoyin
a kan kujerar dake kusa da shi
sannan ya taka ya k arasa inda take ya ce
  Khadijah, kar ki yarda ki kai ni bango a cikin gidan nan, ba ki san ya nake ji ba idan na kalli fuskarki, ina zaune da ke ne kawai saboda ?a?an da ke a tsakaninmu da kuma alk awarin da na yiwa su Abba kafin su rasu sannan na dawo gidan nan ne domin na lura in dai na zauna a daban daban ni da ?a?ana tou tabbas za ki iya raba ni da su.

Banason yawan magana ta da ke! saboda na lura ba?in ciki, da tashin hankalina kike son gani, a ko da yaushe kin fi so ki ganni cikin tashin hankali& .
Dan haka na zab a yin nesa da ke!.

Ina samu lumana da kwanciyar hankali daga wajen Saddik a, abun da kika gagara ki bani. 

Bakin Mommy har rawa ya ke yi, ganin tana shirin fara magana ya sanya yayi saurin d aga mata Hannu alamun  wait(jira)
ya ce
  Ba na buk atar komai daga gareki, kin yi kuma kin ce me isarki& ..
Kin san bani da lafiya amma a wannan shekarun ki ka zab i ki tuna mini da case d in  Khadijah .
Ban san mai zan ce miki ba.
Amma kamar yadda na yi miki sutura na bar ki a cikin ?a?anki sannan bayan na zab i raba gida da ke na hak ura na dawo

16 / 51