Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   38 / 51

111K to 114K   out of 151.9K words


ya kira AIG yace   a dakatar da duk wani abu da ake gudanarwa a police station d in da Najeeb ya gaya masa su Manubiyan su ke
sannan yace  kar a bar kowa ya fita,dss suna hanya za su kama black snake  .

Tafiyar mintuna goma ce ta kai shi police station d in dan bashi da nisa da su, sannan bai bi k a idodin hanya da titi ko guda d aya ba sakamokon uban gudun da ya tsula kamar ba gobe.

Motarsa tana yin parking ta wani dss shi d aya ko uniform babu a jikinsa ta yi parking, da sauri ya k araso ya nunawa Yashjub id card d in sa kafin yace   kai ne ka yi waya ko? ina kusa sosai na ga assignment d in shine na k araso da wuri but mota biyar tana hanya, yanzunnan zaka gansu inshaaAllah. 

Sam Yashjub bai ji dad i ba, dan so yayi ace tawagar su ce tazo da wuri haka saboda ya san black snake baya yawo shi kad ai,
dan ga police station d in ma yanzu haka ya cika tapp da motocin da ya tabbatar nasa ne da shi da Jama ar sa.

Kamar yadda jami in dss d in ya nunawa Yashjub Id card haka ya k arasa ya nunawa ragowar y an sandan dake harabar wajen id card d insa dan haka a take suka sara masa suka bi bayan sa su ka yi ciki gaba d ayan su& &

& ..4 minutes before now.
(Mintuna huWu da suka shuWe)&

Ana shirin fara d aura aure
Dpo ya fita domin amsa waya,
kafin minti d aya sai gashi ya dawo& jikinsa har yana d an karkarwa.

Da mamaki black snake ya ke kallon sa yana shirin yin magana Dpo d in ya k arasa inda yake ya ce
  Muna da problem fa! an san kana nan 

Dariya black snake yayi kafin yace
  Relax(kwantar da hankalinka), babu wanda ya Isa ya yi arresting ko ya iya dakatar da ni 


Cikin yin k asa da murya dpo ya ce
  Ban san ya akayi ba, amman Dss ne a hanyar zuwa nan fa black snake, sun san kana nan gurin
Sun kusan ?arasowa ma yanzu haka, sannan oga kwata kwata ya kirani ya ce
In tsayar da koma me ake yi anan Win sannan in kama ka!!

da farko ma da suspending d ina ya yi, sai da na rantse masa akan ban san da case d in  ana neman ka ba tukunna ya bar ni yace in tabbata na kama ka! 

Take a alokaci d aya fuskar black snake ta chanza daga jin batun dpo, cikin fushi ya d ago yana kallon kowa& .sai kuma yayi lissafin ai mutanen nan basu da ?arfi da hanyar da za su kira someone influential (babban mutum) haka.
Wata?ilan dai wani Abokin hamaiyyarshi ne ya ji labarin zuwan sa shine akayi masa chune!.
Bayaga hakan ma ai tun d azu yana tare dasu Manubiyan kuma babu wanda ya ga yayi waya a cikin su.

Yana wannan tunanin ya ji dpo yace
  Sir,wannan ba lokacin tunani baneba,u need to leave, now!(ya kamata ka tafi, yanzu yanzu).
ka san su kamar aljanu, yanzun nan za ka ga sun k araso. 

Cikin fushi black snake d in ya juya buguzun-buguzun
Ya je shi ya damk i hannun Manu ya fara janta sannan ya cewa yaran nasa su kamo
Jidda
duk wanda kuma yayi yunk urin hanasu to su kaishi lahira.

Ya Nafi u ne ya danne zuciyarsa da kyar ya iya rik e Ya Musbah dan ya san muddin suka shiga to kashe su mutanen nan za su yi kuma in sun mutu ba za su samu su kwato su Jiddan daga hannunsu ba.


Da kyar Baba ya iya had a gaba d aya k arfinsa da ragowar kuzarin da ya rage masa ya samu ya mik e tsaye,jikinsa
yana karkarwa ya tsaya a inda black snake yake k ok arin bi ya wuce,yace  ka kashe ni kawai!
A kan dai in bari ka tafi da y ay ana har biyu a gaban idona, gara kawai ka kashe ni!  .

Wani wurgi black snake ya yi dashi wanda ya sanya shi ya tafi ya je ya daki gini& .
Cikin fushi black snake ya cd
  Ban tab a had uwa da tsoho mai audacity (tsaurin ido) irin ka ba!
kar ka damu ba zan kashe ka ba amma tunda na lura kamar ka fi son wanchan Yaron naka mai kama da kai a cikin y ayan naka maza to shi zan kashe  .
Ya yi maganar yana nufin
Ya Musbah.

& Now(yanzu)&

  Ba za ka kashe kowa ba black snake 
Muryar jami in dss d in da suka shigo taree shi da Yash ta
katsesu, sannan ta maida hankalin kowa gare su.


A take Yashjub ya ji ransa yayi wani irin b aci na ban mamaki, zuciyarsa ta cunkushe tana tafarfasa sakamokon yadda ya ga black snake ya k ank ame Hannun Manu,
gashi sai k ok arin kwacewa takeyi tana wani irin kuka, kuma ko damuwa ma bai yi ba.
Sannan daga ita sai doguwar riga da hula, wuyanta duk a waje!.
Bai san lokacin da ya k arasa ya fincike hannunta daga cikin na black snake d in ba sannan ya hankad asa gefe.

Wani irin murmushin takaici black snake yayi kafin ya ce
  Yashjub!the hero..we meet again!
(Jarumi Yashjub, mun ?ara haWuwa kenan& )

Banza Yashjub ya yi dashi, kawai ya juya inda ya hango hijabin da ya gani a yashe wanda yake da tabbacin na Manu ne, ya k arasa ya je ya d auko ya mik a mata yana mai k ok arin danne fushin sa.

Dai dai nan jami in dss tare da dandazon y an sandan da suka biyo bayan su da shi da Yashjub suka yi kan black snake

Ba tare da tantama ba
Black snake ya harbi ss d in a ciki
wanda hakan ya sanya gaba d aya y an sandan suka rufar masa, dama rabi a cikinsu duk bakinsu d aya da dpo ba wai son kama black snake d in sukeyi da gasken gaske ba.

Ai kuwa hakan ya bashi dama da shi da tawagar sa suka fice da gudu
Bayan ya kalli Baba ya ce masa  zan dawo d aukar matata, nan ba da jimawa ba 

Da sauri Yashjub yayi kan jami in da aka harba, ganin
yana motsi yasa yace gara a yi sauri danne gurin su kai sa mota a wuce dashi asibiti.
Shi kuma ya bi bayan su black snake da gudu
amman ya na zuwa
sai k urar motocin su kawai ya tarar.
  Damn it!! 
Ya furta da k arfi, yana jin
takaici kamar ya kurma uban ihu.
Dai-dai nan motar Najeeb ta k araso cikin harabar gurin tare da dandazon motocin jami an dss.


Najeeb yana k arasowa yace
  Kar ka damu,rabin motocin sun bi su,za a kama shi in sha Allah,bai dai tab a kowa ba ko? 

Cikin b acin rai Yashjub ya ce
  Ya harbi mutane uku 

A rikice Najeeb yace  subahanaallah,da wa da wa?? ina Manubiyan take? 

  Tana ciki! 
kawai Yash ya iya cewa,
daga haka ya juya ya nufi ciki
bayan ya kira ambulance,
dan wani irin takaici yake ji,ya riga ya san dole ba za a iya kama black snake ba.


Suna shiga polisawan da wasu a cikin ss d in suna fitowa d auke da jami in da aka harba.
Statement ya tarar ragowar ss d in suna karb a a wajen ya Musbah da ya Nafi u yayin da Jidda da Manubiya suke kuka suna dudduba Baba.


Dukda abunda black snake ya aikata sai da Yashjub ya karb i acc number d insa a wajen dpo ya tura masa 1 million d insa da yake bin Baba, bayan ya ji bayanin komai da ga Bakin dpo.

Zuwa wannan lokacin gaba d aya ran Yashjub ya kammala b aci daga jin bayanin, tabbas in da ace zai ga black snake yanzu to kuwa in bai kashe sa ba sai ya sumar da shi, musamman ma da ya ji cikakken labarin maganar auren da ya so a d aura masa shi da Manubiya!&
 wato da niyyar auren Manubiya ma yake yi!
Idan ya yi tunani akan
 Black snake d in fa yayi tunanin auren Manubiya, kenan
ta kwanta masa shima son ta
yake yi ,
sai ya ji kamar ya bazama ya nemo shi ya chaka masa wuk a.
Dan mai yasa zai yi wannan tunanin a kanta!.

how dare he!.
*MANNUBIYA*
*38*


Shiyasa har aka gama case Win& .aka gama karb ar statements d in su,
suka nufi asibiti sam fuskarsa babu walwala!
Ya had e girar sama da ta k asa, ko magana ma ya daina yi.

Private hospital aka nufa da Baba da Abbakar, suna zuwa aka karb esu emergency.
& &
Wayar da Yashjub ya yi aka tabbatar masa da  black snake ya gudu, ba a samu damar kamasa ba
ne ya sake harzuk a shi.


Dukda halin da take a ciki sai da ta lura da shi dama tun Wazu..
yanzun kuma ta tabbatar wayar da aka yi masa ce ta sake b ata masa rai&
So take yi atleast (ko ma ?a-?a dai)
ta je ta ce musu sun gode, dukda ta ga su Ya Musbah sun yi musu godiya sosai har karSar nambobin juna ma taga sun yiyyi, amma dai dukda haka ya kamata su je su yi musu godiya suma ita da Jidda, sai dai kuma tana shakkar kar ta je ya maketa!
Dan in ba lokacin da su ke exchanging numbers shi da su Ya Musbah ba to bataga ya saki fuska dede da na second d aya ba!& Sannan kuma
tana jin kunyar sa dan in ta tuna abunda ta yi masa jiya da safe gaba d aya sai ta ji wani iri babu dad i! duba da yadda yanzu yake tsaye tsayin daka akan al amarin da ya kusan tarwatsa rayuwarta da ahalinta.

Gashi yanzun kwata-kwata bata hango walwala a tare da shi ba,
masifa ya ke yi wa kowa hatta sir Najeeb yanayin yadda ta ga yana masa magana kamar zai rufe sa da duka take gani& .
waennan dalilan ya sanya ta d an dakata tana mai tunanin ta yadda za ta yi masa godiyar.


Sallar la asar aka kira, dan haka gaba d aya Mazan suka fita masallaci, su kuma suka nufi band akin da suka tambaya aka nuna musu&
Sallah kuma suka nemi waje inda babu mutane sosai, suka gabatar da ita cikin nutsuwa.
Bayan sun idar sukayi addu oin samun lafiya wa Baba da Abbakar, har ma da Inna.

Basu dad e da dawowa wajen ba su Yashjub ma suka shigo, shi da
sir Najeeb su Ya musbah a bayansu.

Ba k aramin dad i Manubiya ta ji ba, dan bata yi tunanin za su dawo su jira har sai an gama treatment d in su Baban ba,
hakan ya sanya har bata san lokacin da murmushi ya sub uce mata ba, tana murmushin tana kallon Yash d in& .
dai-dai shi kuma ya d ago kansa shima da niyyar ya d an saci kallon ta ai kuwa karaff suka had a ido da ita tana kallon sa tana murmushi.

Da mugun sauri ta sunkuyar da kanta k asa, ta fara wasa da y an yatsun hannun ta&
murmushi sosai ne ya kufcewa Yash wanda har sai da sautin murmushin ya fito fili!
Dasauri sir Najeeb ya d ago yana kallon sa&
ganin inda yake kalla yana murmushin ne yasanya Najeeb d in yin wata y ar guntuwar dariya kafin ya ce   Romeo, a asibitin ma ba za a d aga k afa ba? 

  Hmm 
Kawai Yashjub ya iya ce wa Najeeb, dan gaba d aya Manubiya ta sanya shi a wani yanayi, shiyasa ko iya juyawa ya kalli Najeeb d in ma bai yi ba, saboda gaba d aya idanuwansa da hankalinsa kacokam suna akan ta ne!
So yake ta sake d agowa ya kalleta amman sam tak i, ta ma yi k asa da kanta sosai.

Ganin ta ?i d agowa shi kuma zullumi yana shirin susuta shi ne ya sanya kawai ya nufi inda take.
Dama kuma yanata so ya d an yi mata maganar  ko akwai wani abun bayan wanda dpo ya gaya mishi amma ya lura tanata kuka, shiyasa ya d aga mata k afa saboda jin kukan nata yake yi har cikin ransa a lokacin da take yi& .dan har ga Allah ya san in ya je kusa da ita tana wannan kukan to tsaf za a iya samun matsala, kukanta yana cikin abubuwa mafi munin da baya buk atar gani a duniyar nan& & .

A take Manubiya ta fahimci inda take yake nufowa, dan haka tashi d aya fargabarta ta k aru, dama ga fargabar jikinsu Baba dan ma an tabbatar musu da jikin na Baba
Ba wani abu me muni bane
Abbakar kuma yanada rai.

Tana wannan tunanin ta ji shi a tsaye a kanta, ji ta yi kamar ta mik e tsaye ta ruga a guje.
Ba ta ida jan numfashin da ya mak ale take kokawar janyoshi da kyar ba ta ji yace  in zauna?? 

Dakyar da mugun kyar dan sai da ya sake maimaitawa tukunna ya ga tad an matsa kusa da Jidda sosai sannan ta ce masa  eh  a hankali.

Murmushi yayi kafin a hankali ya nemi gefenta da d an tazara kad an ya zauna cikin nutsuwar sa bayan yayi bismillah.

Yanayin zaman da ta yi sai da ta bashi dariya,
ya lura da yadda ta wani zabura lokacin da ya zauna d in ma sannan ta kuma matsawa jikin Jidda sosai.
Murmushi kawai yayi, ya amsa gaisuwar Jidda yana mai kallon ta
a hankali ya ji tace  Mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi 
Murmushi ya yi kafin ya ce   ba komai, Allah ya kare gaba ya ba su lafiya 

  Ameen  ta ce,daganan ta yunk ura zata tashi dan ta lura kamar yana d an bukatar space da Manubiyan amma sai ta ji Manubiyan ta yi saurin damk ar Hannunta ta rik eta gam.
A hankali Jiddan ta gyara ta zauna a wajen ba dan ta so ba,
itama ta sunkuyar da kanta ta shiga wasa da bakin hijab d in jikinta&
Har ga Allah ta jinjinawa Yashjub da abunda ya yi musu,
dan tun d azu da Manubiya ta ce mata  ai shine wanda take yi wa aiki
Jiddan take ta mamaki, dan a ganinta a zamanin nan na yanzu wanne employer (Oga) ne yake damuwa da matsalar employee d insa (ma aikatansa) har haka, a take wata zuciyar kuma sai ta ce mata   kodai!kodai!!  dan haka ta d an yi murmushi ita kad ai, ta ci gaba da lissafe lissafen ta.


Ba k aramin burge Yash su Manubiya sukayi ba& yadda suke da kunya da kamun kai
tabbas ya san iyayen su sun yi k ok ari wajen tarbiyyar su,
dan ko ba a fad a mishi ba
ya fahimci jiddda k anwar Manubiya ce sakamokon tsananin kamanni da ya ga suna yi..
Banbancin Jidda da Manubiya
yanayin girman jiki, kalar fata da ido ne kawai..Manubiya ta fi Jidda tsayi da jiki kad an, kalar
fatar Jidda fara ce ita tass sosai Manubiya kuma ba b aka bace ba kuma ba fara bace sosai,
Idanuwan Jidda sun fi na Manubiya girma sosai amma na Manu sun fi na Jidda kyau da d aukar hankali..a ransa ya ce   idanuwan da suka kusan haukatani
sai kuma ya d an yi murmushi kad an.

Shiruu duk suka yi kafin Yash ya katse shirun ta hanyar cewa Manubiya
  Sister d inki ce ko? 

A hankali ta d an jinjina kanta sai kuma tace   eh  daganan shiru ya sake biyo baya.

Still shi ne ya sake kawo k arshen shirun ta hanyar cewa   Baba zai samu sauk i, inshaaAllah.
kar ki damu komai zai daidaita. inshaaAllah 

A hankali ta ce
  InshaaAllah,  itama Jidda tace  inshaaAllah  a cikin ranta.

A hankali Manubiya ta lumshe idanuwanta, tana mamakin yadda k iri-k iri ta gagara yi masa godiyar da take ta zumud in son yi&
gaba d aya duk sai ta ji ba dad i ta inda ko ishashshiyar gaisuwa ta gagagara shiga tsakanin su..
Yo ta inama zata iya? itafa tunda ya zo ya zauna a kusa da ita shikenan ya sakawa tunani, kuzari da duk wasu lissafe-lissafenta full stop.
Ganin rashin kyautuwar abunda ta yi ne yasanya ta yi da gaske da kyar ta samu ta d an d ago kanta da niyyar ta kalle shi ta yi mishi godiya, suna had a ido ta yi sauri ta fara kallon gefen kunnensa sakamokon wani irin kallo da ta ga yana yi mata gashi sai wani tsadadden murmushi yake zuba mata.
Babu yadda ba ta yi ba amma da ikon Allah sai ta gagara cewa komai, ga wani mahaukacin bugu da zuciyarta ta shiga yi&
ganin da ta yi ba zata iya bane ya sanya ta yi sauri ta sunkuyar da kanta tana tunanin ta yadda zata aro jarumta ta yi masa magana ko da ace bata kalleshin ba dan zuwa yanzu ta fahimci abun kamar da wuya,a ranta ta ce   wannan wanne irin abu ne haka, wanne irin feelings ne wannan? 
ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsar ba.

A b angaren Yashjub kuwa kad an ne ya rage bai fashe da dariya ba a ransa ya ce 

38 / 51