Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   41 / 51

120K to 123K   out of 151.9K words

tambayar cikin rashin jin dad i.

Cikin fushi ta ce   ai dama na san ba za ku ga laifinta ba, to wallahi ku jirani a kotu dan ba zan yarda ba sai mun yi shari a da ku.
Amman kafin nan inaso in ja miki kunne!& .
Manubiya in dai har kin haifu cikin Musa da Amina tou kar in sake ganin ki a kusa da d a na.

Kalli cikin azabar da kika jefa sa da ke da y an uwanki da iyayenki& masifa ce ku wallahi!!!
shiyasa duk wanda ya rab e ku sai ya shafa, na yi k ok arin nunawa Abbakar ba so d aya ba ba sau biyu ba amman dayake kin riga kin shanyemin Yaro kalli sai da kika kusan kai shi lahira&  
Kukan da ya kufce mata ne ya sanya ta d an dakata, kafin ta sake d agowa a zuciye ta ce   na gaya miki yanzu zan sake maimaitawa  in dai kin haifu cikin tsinannun iyayen k&  

Nufar matar Ya Musbah yayi da niyyar kai mata duka amman sai maman Baraka ta shiga tsakiya ta rik e sa, zafin zuciyar da ta ciwo sa ne ya sanya cikin rashin sani ya yi cilli da ita, ya sake yin kan maman Abbakar Win&

Ganin yana shirin yin b arna ne yasa ya Nafi u ya taresa ya ce
  Musbahu ka yi ha?uri ka kyaleta ba dan itaba, ka duba fa Abbakar shi ne ya kira su Yashjub, ka rabu da ita, ta ci albarcin d anta. 
Daga haka ya juya ya ce mata
  mu za mu wuce yanzu.
Ga Abbakar nan, zan dawo in duba shi inshaaAllah zuwa anjima& muna buk atar mu yi mishi godiya.
An biya duk wasu charges,
abinci kawai zaki dinga basa,
Allah ya basa lafiya. 
Daga haka ya cewa su Manubiya  su wuce su tafi  .
Sai da kuwa yayi da gske tukunna shi da Jidda suka samu suka janye Manu dan ta tsaya kawai tana kallon maman Abbakar ne, so take yi ta maida mata da martani amman kuma darajar d anta ya sanya ta kasa yin magana.

Aikuwa har suka fice maman Abbakar ba ta yi shiru ba& babu kalar zagin da batayi musu ba&
Maman Baraka itama tana tsomo Baki
A cewarta   sirikinta ya hankad eta, ta fad i kuma ko
kallon inda take bai yi ba
kamar ba y a ta d auka ta basa ba!!!!
 Saboda shi Win d an marasa tarbiyya ne& shiyasa bai san darajar ta ba .

Hakanan Baba ya tsawatar musu yace   kar wanda yace uffan, su rabu dasu 
dan haka suka tartara yanasu yanasu suka fice bayan ya Musbah ya je ya karb i magungunan Baba.
K arfe shida dai-dai suka bar harabar asibitin suka nufi gida.

A gida suka fara tsayawa
suka ajjiye Baba, tukunna Baban ya ce musu  su duka su je su d auko inna, kar su damu ba komai zai iya zama shi kad ai  .

Da   to  suka amsa shi, daga haka suka nufi gidan Ya Musbah gaba d ayansu domin su je su d auko Innar. ce   dalla ni cikan& . 
*MANNUBIYA*
*41*

Suna fita Baba ya saki hawayen da yake ta k ok arin dannewa&
Dama baya so ya yi kuka a gaban su gudun kar ya karya musu guiwa ya d aga musu hankali..shiyasa yace su tafi gaba d ayansu.
Da ace yana da yadda zai yi to da ba zai tab a aurar da su Jidda yanzu ba,
ya so ?a?ansa su yi karatu, yaso ace Jidda ta gama ko da level one ne tukunna, amma yanzu kam sai dai ya bita da addu a da fatan alkhairi tare da rok on Allah ubangiji  ya had a Manubiya har ma da Jiddan da surukai na gari, ya sa su so
su
Dan kasancewar ya san mahaifin Yusuf ba shi zai sa ya k i yiwa y ar sa wannan addu ar ba!
yana rok on Allah ya sa su jata a jiki bayan auren, Manubiya kuma Allah ya bata na gari, a samu kowacce ta zauna lafiya a gidan ta, dan tabbas abunda su maman Baraka sukayi musu yau a asibiti ya tab a shi sosai, ya ji zafin abun.



A k ofar gidajen nasu biyu motar Ya Nafi u ta yi parking, dan haka suka fara firfitowa& ..
Ya Musbah ne ya fara shiga cikin gidan nasa, su kuma suna biye da shi a baya.
A k arshen soro kafin ya k arasa shigewa cikin gidan sukaga ya ja ya tsaya chak! Ya ?i yayi gaba sannan yak i yayi baya.

K arasawa kusa da shi ya Nafi u yayi yana mai cewa
  Ya dai? kar ka&  
A take maganarsa ta tsaya chak sakamakon hango Inna da shima yayi a yashe a tsakar gidan.

Da farko tunanin su basu ya yi
 watak ila ko ta yi k ok arin tashi ne sai Allah ya bata iko,
shine da ta fito kuma sai ta fad i a wajen &
amman kuma yadda suka ga an shimfid a mata zani sannan aka d aura kanta akan pillow ne ya basu tabbacin wannan aikin Baraka ne.

Cikin d aga muryar Ya Nafi u ya hau kwala kiran   Aisha! Aisha!! 
Sai kuma ya juya zai fita dai-dai suka yi kicib is da Aishar
dan tana jin tsayuwar motar tasa a k ofar gidan ta d auko kular da ta gama juye abinci a ciki ta janyo hannun y arta suka yo gidan.
Cikin fushi ya ce   ya akayi kika barta kika fita? ina Muhsin?? 

Inda-inda ta fara yi, tana shirin yin magana ta ga su Manubiya sun yi cikin gidan da gudu, wanda yadda ya Nafi u ya d an gota suka wuce ne ya bata damar hango Innar itama dan haka ta yi ciki da sauri tana salati.

A take
Jidda da Manubiya suka fashe da kuka saboda yadda suka ji jikin Innar ya d au zafi sosai! hatta kayan jikinta ya d au zafi! ga ranar la asar da ta kusan fad uwa ta haske mata fuska sosai gashi babu damar motsawa& & .


Dishi-dishi ya Musbah ya fara gani tsabar tsananin b acin rai da tashin hankali& da kyar ya samu ya iya cewa
  Baraka!! 
Da d an k arfi, dan jikinsa wani irin karkarwa yake yi, hatta muryar tasa rawa takeyi.


Tun lokacin da suka shigo ta jiyo su& ..dan ta gama watsa ruwa a jikinta kenan sakamokon zafin da akeyi
ta ji tsayuwar motar ya Nafi u.

Dan haka ta d auro zaninta, ta yafo mayafinta ta rik o kayanta a Hannu ta fito fuskarta a had e tamau!.
&
Tana fitowa Ya Musbah ya k arasa inda take ya tsaya..so
ya ke yayi magana amman sam sai ya gagara, in banda karkarwa babu abunda jikinsa yake yi, dan haka kawai sai ya kafeta da idanu, ya shiga karanto addu o i a chan k asan ransa yana mai neman tsari daga shaid an saboda a yadda yake jin zuciyarsa a halin da ake ciki ya san muddin ya ce zai Wauki mataki ko ya yi wani abun to ya san wallahi kashe Baraka zai yi!
sai ya kaita har lahira.

Tunda Baraka take a rayuwarta bata tab a ganin Ya Musbah a irin wannan yanayin ba, babu abunda ya fi tsoratata irin yadda taga idanuwansa sun yi jajawur hatta farar fuskarsa ta yi jaa!
gashi jikinsa sai wani irin karkarwa yake yi&
Shiyasa gaba d aya duk sai ta ji tsoro ya lullub eta, abunda bata tab a tunanin za ta ji ba kenan dan ko a mafarki bata tab a kawowa akwai ranar da zata zo ace wai ta ji tsoro ko shakkar Ya Musbah a rayuwar ta ba .
A lokacin da suke soyayya
soyayyarshi kawai ta sani, da suka yi aure kuma..hak uri juriya da lallashin sa kawai ta sani. Shiyasa a yanzu da ta ga asalin fushinsa abun sai ya bata tsoro matuk a.


Sai da ta d an yi k asa da kanta tukunna ta ce
  feshi na yi a d akin, shine na fito da ita waje& .. 

Basu ga k arasowar Ya Nafi u ba, sai sauk ar gigitaccen marin da ya d auke Baraka da shi kawai suga gani.

Da sauri ta d ago ta kallesa sai kuma ta kasa cewa komai kafin hawaye sharr ya wanke mata fuska, tama kasa maganar.

Dakyar da mugun kyar Ya Nafi u ya yi k ok ari ya danne zuciyar da take tunzura sa akan ya rufe Baraka da duka, yana wani irin huci ya
juya ya kalli Ya Musbah
Ya ce
  Yi hak uri Musbahu 
Daga haka ya wuce ya fice daga cikin gidan da sauri, dan ya san in ya cigaba da tsayuwa to tabbas sai an samu matsala.

Yana fita Baraka ta juya tana kallon Ya Musbah wanda yake nan tsaye ya kafeta da idanuwa&
A ranta tana mamakin yadda yana gani Nafi u ya d aga hannu ya zabga mata mari amman bai tab uka uwar komai ba, sannan ba shi da alamar yin komai a kan hakan har yanzun, dan haka ta bud e Baki zatayi magana kenan shi kuma ya riga ta ta hanyar cewa  ki tafi na sake ki! saki biyu 

Dede nan Manubiya wadda suka gama kai inna cikin d aki ta fito ta yo kan Barakar da niyyar ko dai ta illatata ko kuma su illata juna.

Da sauri Aisha wadda dama ta lura da abunda Manubiyan take shirin yi ta taho da gudu ta rik e ta.

Sai yanzu Baraka ta samu ta goge hawayen da suke zubo mata babu k ak k autawa tukunna da kyar ta ce
  Cika ta, cikata ta dakeni tunda ita mahaukaciya ce, nace muku
Feshi na yi amman hakan bai ishe ku ba, uwar taku gwal ce? 

Cikin fushi Aisha ta ce
  Mahaukaciya! Jahila! Dak ik iya!
Idan baki saniba to yau ki sani Baraka
 uwa ta fi gwal .
Da bata haife shi ba to da baki same shi ba, dak ik iya kawai.

Ya Musbah ya ce ya sakeki, dan haka za ki iya tafiya.
ki tartara kayanki ki koma gida a sake yi miki tarbiyya wata?il in kin gyaru ya dawo dake, dan tabbas ko ni ba zan bada goyon bayan
aci gaba da zama da ke da wannan halin da wannan zuciyar taki ba. 
Tana gama fad in haka ta juya ita da Jidda suka ja Manubiya da kyar suka shige d aki dukkan su Manubiya tana kuka sosai kamar ranta zai fita! dan ji takeyi idan bata daki Baraka ba yau tou sai ta mutu!.

Ita kanta Aisha ta san
tabbas in ta tsaya tsaf za su kwashi y an kallo ita da Baraka kuma a ganinta in bata kwantar da husuma ba to bai kamata ta iza wutar ba, dan haka ta zaSi su zauna a Waki sannan ta duk ufa tausar Manubiya.

Duk bakin Baraka yau kasa cewa ko yin komai ta yi
daga k arshe kawai sai ta juya
Fuuuuuu ta wuce d akinta& .

Ya Musbah ma bai ci gaba da zama a gidan ba!
Baraka
tana wucewa d aki ya lek a ya cewa su Manu  kar wanda ya kulata a cikin su,su barta da duniya 
daga haka ya juya ya fita.


Baraka tana shiga d aki ta fashe da kuka marar sauti mai
tsananin cin rai!
Bata tab a
tunani ba bata tab a kawowa a ranta Ya Musbah zai iya sakinta ba!!
 to me ya faru, ya akayi har ya iya sakinta! Yanzu ya za ta yi kenan???
Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsar ba.
Ta jima tana kuka tana tunani kafin ta share hawayenta a ranta ta shiga aiyyana
 Tabbas sai ta nunawa Musbahu kuskurensa wallahi!
sai ta jaa shi a k asa.Kallifa kalar cin mutuncin da suka taru sukayi mata,inaa!bazaiyiu ba wallahi da sake dole ta sake shiri zai ga ikon Allah, bama shi kaWai ba gaba d ayan su sai ta nuna musu wacece Baraka  .

Da farko da ta yanke ne akan babu inda zataje, sai kuma ta bawa kanta shawarar ta je ta samu su mamanta itama, a yadda su Ya Musbah suka hayayyak o sukayi mata wannan aika aikar
tabbas bai kamata ta yanke shawara ita kad ai ba& .

Tana wannan tunanin ta had a kayanta kaf, ko d an kunne bata bari ba a ganinta in tayi haka Ya Musbah zai ji tsoro ya zo biko da wuri.


Su Manubiya suna d aki sun zagaye inna suna yi mata fiffita sukaji fitowarta tana ta jidar kaya.
Babu wanda ya ce mata ci kanki a cikinsu,haka suna
jinta ta dinga kwasar kayanta
tana fitarwa one by one
har ta gama& &


Ya Musbah yana fita direct wajen Baba ya nufa, dan ya gama rayawa a ransa
 Idan ma za su maida Inna gida tou sai dare, dan so yake yi ya nunawa Baraka iyakar ta! Ta yadda tana ji tana gani sai dai ita ta fita ta barwa Inna gidan Wallahi .


A hanya ya had u da Muhsin da mai sunan baba sun dawo daga siyo madara, dan haka suka wuce wajen Baban da su&
Dama bayaso Baraka ta tafi akan idon me sunan Baba gudun kar yayi ta kuka ya ce sai ya bita.


Sun d an jima a wajen Baba bayan ya ce mishi
  Sunje sun tarar Aisha tana bawa innar abinci ne shine aka tsaya ta gama tukunna a kawo ta 

Sai da suka kuma d aukar lokaci tukunna ya bar Muhsin anan, shi kuma ya kama Hannun me sunan Baba suka nufi gidan nasa&
bai yi tunanin tarar da Baraka har zuwa wannan lokacin a gidan ba amma yana karya kwana ya tarar da ita da adaidaita sahun ta har uku tanata loda kayayyakinta ita da masu napep d in a ciki.

Ko iskar da ta d ebo ta bai yarda ya kalla ba, ya sake rik e hannun Yaron ya zo zai shige cikin gidan& suna zuwa da
Yaron ya gane ashe uwarsa ce tare da masu adaidaita sahun ai kuwa nan ya hau ihun sai ya bi ta.

Tana gani ya fara tsalle ana jan shi yana tirjewa ta dawo ta kama kunnesa ta ja tukunna tace
 in na sake jin sunana a bakinka sai na ci uban ubanka! shegen Yaro kawai sai kace dashi na zo 
daga haka ta juya zata wuce
ta ji Ya Musbah ya ce   Babana yi
hak uri, mu wuce mu shiga gida,
yawo a titi bai kamace ka ba 

Ai kuwa cikin fushi Baraka ta juyo
  Ai sai ka bari in gidan naka ne sai ka yi tink aho da shi, talaka mara matsugunni kawai,
gara ni idan na tafi yawo a titin ba a gidan haya zan k are ba!
kai kuwa nan da y an kwanaki za a zo ayi waje da kai dama darajata yasa mai gidan yake d aga maka k afa yanzu kuwa na san ba zai barka ka cigaba da zama daga kai sai uwarka b& & 

Da sauri ya d auke me sunan baba, ya wuce ciki ya banko k ofar dan bai shirya biyewa Baraka a k ofar gida ba&
Ta jima kuwa tana ta tijara ita kad ai sai da masu mashin d in suka ce mata  in bata shirya tafiya ba, zasu sauk e mata kayanta su yi gaba 
tukunna ta shiga ta zauna a take kuma sai ta fashe da kuka.

To dai Baraka tun kan aje koina sai da ta ji dama bata fito daga gidan mijin nata ba saboda d ayan mai mashin d in bai rik e mata amana ba& dukda kuwa tafiyar da sukayi bata wuce ta mintuna biyar a tsakani ba
amma
da yayi wura wura ya ga babu ido a kansa
chan ya chanza hanya.

Sai da ta Isa k ofar gidansu tukunna ta lura babu napep d aya.
" " " " " " " "
Tun lokacin da Yashjub ya bar office Daddy ya k ule, ganin la asar har ta gota bai kira kuma bai zo ba ne ya sanya shi ya kira Najeeb a fusace ya bashi sa ko amman gashi har bayan Magrib Yashjub d in bai iso ba.

Yassira ce ta guntsawa su Mommy abunda Yashjub d in yayi yau a office, gashi kuma har yanzu bai dawo ba..hakan kuwa ba k aramin sake d aga musu hankali yayi ba dan tashi
d aya suka yanke cewa
  wannan yarinyar da suke zargi ce ta kirasa 
Saboda Yasirar ta ce musu ko bayan da aka tashi daga office sai da suka biya d ayan company d in Yash d in ita da Daddy amma akace musu yau throughout bai je chan ba.
Ta tambayi Racheal kuma, ta ce mata   batun estates d insa komai stable(dai-dai) 
dan haka matslar ba anan take ba kenan.
Shiyasa suke da tabbacin wannan yarinyar ce kenan& tabbas kuwa zama bai kamasuba dan Indai har matsalarta zata sanya ya mik e tsulum ya fice ana tsakiyar meeting sannan ya ?i d aga wayar kowa har yanzu saboda tsabar yadda ya bata mahimmanci, to hakan ya nuna da akwai babban bound (abu) a tsakanin sa da ita wanda ya zame musu dole su tarwatsa shi tun wuri su yakiceta daga cikin rayuwarsa, tun kafin ya k ak abo musu k adangaren bakin tulu!.

Hakanan gidan ya kasance shiruu kowa da abunda yake tunani har aka yi dinner aka watse babu Yashjub babu alamar sa.


Zuwa wannan lokacin Daddy ya sauk o daga duk wani fushin da yayi da Yashjub!
dan duk hankalinsa ya tashi,
shiyasa ya yanke shawarar idan k arfe goma ta yi Yash bai dawoba tou zai kira y an sa????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? nda da

41 / 51