Mannubiya Book Compelet By Humaira Bulama

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   48 / 51

141K to 144K   out of 151.9K words

dai ta hak ura da shi ko kuma ta bi ta ko wacce hanya ta rabasu, dan ita kanta tunda ta ganta tashi d aya sai da ta raina kanta ga wani irin kishi da ta ji ya taso mata a take duk ya bi ya lulluSeta lokaci guda!!
To Ina kuma ga Kausar Win?!
Allah kad ai ya san me take ji!
Bata riga ta samu hankalin Yashjub d in bama, gashi har wata ta yi wuff da shi, dan a iyakar abunda ta gani a yau kawai tabbas ta san sunada aiki jaaa! A gaban su.

  Yassira har mu je gida kar ki sake cewa komai
Dan Allah 
Muryar Kausar ta katsewa Yasirar tunanin.
Tana gama fad in hakan ta ja motar da gudu suka wuce.


Suna zuwa gida ba ta ko kalli Yasira ba, ta bud e motar ta fice ta wuce sama.
Kai tsaye fanninta ta nufa, tana tafe Zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Tana shiga parlournta ta yi cilli da wayarta da d an ficicin mayafinta sai kuma ta fara kai kawo& .tana safa da marwa a cikin Wakin, kafin kuma
ta fara d aukar abubuwa tana farfasawa!!!
Wanda hakan ya janyo hankalin Mommy, dan
haka ta nufo side d in nata.

Tana shiga ta zaro idanu waje, sai
kuma ta k arasa inda Kausar d in take ta rik eta cikin tashin hankali ta ce
  Lafiyar ki kuwa? 
ta yi mata tambayar tana mai shafa fuskarta wadda ta yi jajawur idanunta suka sake k ank ancewa.
Tsabar tashin hankali kasa ma magana ta yi, kuma so take ta yi kuka sosai amma ta kasa dan shima hawayen ya k afe&

Suna tsaye a haka Yasira ta iso, tun daga bakin k ofar ta fara cewa  Kausar bani takardun nan akwai wanda ya ke jirana a office kins&  
Maganartace ta mak ale sakamokon kutso
kai da ta yi cikin parlourn.
Da sauri ta ce  Ya subahanallah! 
sai
kuma ta k arasa inda suke tsaye su duka biyun.
Tana zuwa ta rungume Kausar d in, sannan a hankali
cikin son kwantar mata da hankali ta ce   kar ki damu, za mu nemo mafita 

Da sauri Mommy ma ta shiga rarrashin Kausar d in dukda kuwa bata san dalilin fashe fashen da ta tarar ta na yi ba da Sacin ran nata amma dama tunda Yassira Wazu ta ce mata   za su je office d in Yash itada Kausar ta san za a rina& .


Suna nan tsaye wayar Kausar ta d au k ara& .

Dan haka ta janye Jikinta daga na Yassira a hankalia ta koma gefe ta durk usa ta d auki wayar tata
wadda ta duk farfashe dan tana shigowa dama da ita ta fara yin cilli.

Ganin mai kiran nata ne yasa ta d auka a take, sannan a hankali
ta ce   ina jin ka 

Daga chan d ayan b angaren ya ce mata  gani nan yanzunnan aka ajjiyeta a k ofar gidan nasu ta shiga 
daganan ya fad i mata adress da number gidan tukunna ya ce   ban samu
sunan yarinyar ba dai amman
Ina kan bincike. 



  Tam 
kawai Kausar ta iya cewa daga haka ta zare wayar daga kunnenta ta kashe sannan ta shiga cikin contact d inta& .


Zuwa wannan lokacin Yassira ta fahimci da wa ta gama yin waya dan haka ta matsa kusa da ita ta ce mata  Kausar me za ki yi ne?? 

Dai-dai nan ta kara wayarta a kunne ta ce   Hello!na am& zan turo maka adress d in wani gida yanzu!Inaso ku je duk wata budurwar da bata kai 25 ba a gidan ku yi resetting d inta& . 

A zabure Yassira ta wafce wayar ta yi jifa da ita
cikin fushi ta ce   Eh!lalle kam zuciyarki ta kama da wuta!!
kuma ba ki da hankali!

Cikin rashin fahimta sannan a d an tsorace Mommy ma ta
matso ta d an rik e Hannun Kausar d in sannan ta ce
  Kausar! Su wa kika bada order a kashe?? Yaushe kika fara harka da y an daba ba mu sani ba???? 


Ba tare da Yassira ta kalli Mommy ba ta ce   Matar da Yash yake so zai aura take so a kashe saboda mahaukaciya ce ita  ta fad i hakan still idanunta na akan Kausar d in.

Sai a sannan Kausar ta d ago ta kalleta itama tukunna ta ce   kina da wata idear(shawarar) ne bayaga  ku bani hak uri ku ce za a san abun yi
Bayan wannan Win??
Ki fad a min idam akwai wata mafitar da ta fi wannan
yanzu, ina so in ji  .


Cikin takaici da tsananin b acin rai Yassira ta ce   ban tab a tunanin abun naki ya kai har haka ba!
Ban tab a tunanin za ki iya kai har izuwa wannan hatsabibin matakin ba!
Kausar kin san menene rai kuwa??..
A kan Yashjub wanda idan Ubangiji bai rubuta Mijinki bane shi Win ko sama da k asa za ta had e baki Isa ki auresa ba shine za ki d auki jinin bama mutum d aya ba?
A Wan tsorace sannan a rikice ta kalli Mommy ta ce
 Tunda bamu san y an mata nawa ne a cikin gidan ba. 
Sai kuma ta yi shiruuu kawaui ta runtse Idanunta ta tsaya da magana saboda tsabar yadda al amarin Kausar ya k ulle mata kai ya bata tsoro gaba d aya yasa kanta har wani jujjuyawa yakeyi.

Sai da ta d an dawo dai-dai tukunna ta bud e Idanunta ta kalli Kausar ido cikin ido ta ce
  ki saurara ki kasa kunne ki jini da kyau!
Ina mai shawartar ki!
had e da gargadi!
mai tafe da zazzafan warning(jan kunne)! Da kuma threat(barazana!)&
Na rantse da Allah idan wani abun ya sami Yarinyar nan to
da Bakina zan fad awa Yash komai sannan babu ni babu ke har abada!Dan ban shirya zama a k ark ashin inuwa d aya da murderer (mashe?iya) ba.

Idan ba ki nutsu kin dawo cikin hankalinki ba to za ki rasa komai kuma za ki rasa kowa& duk tak amar ki da kuma isar ki baki kai Yash ba dan haka inaso ki saka a ranki cewa  idan kika kashe ta da shi za ki yi shari ah! .

Kar ki lalata rayuwarki da Hannunki!
wannan zafin da kika d auka babu inda zai kai ki sai garin da na sani, mu d in da muke ce miki  ki yi ha?uri, ki bi komai a hankali za a nemo mafita mu ne
masoyanki, kuma mun fi ki gaskiya.

Ki nutsu ki yi lissafi ki ga yadda duk iyakar k ok ari muna yi
amma sai da yayi budurwa, gashi yanzu har ana maganar aure!
Ba ki san menene a k asa ba ba ki san me Ubangiji ya binne ba dan haka mu bi komai a hankali, a samu a nemo mafita
amman kashe ran d an Adam sam ba namu baneba Kausar!.

Tun Yarinta ina tsaya miki tsayin daka akan dukkan al amura amma wallahi Kausar idan kika zarce iyaka na fad a miki na sake maimaitawa
Ni da ke pam!pam!!pam!!!.
Ta fad i hakan tana mai karkad e tafukan hannayenta duk biyun.


Jinjina kai Kausar ta yi cikin b acin rai ta ce
  Tabbas a yau Yassira na san cewa blood is thick(Jini ba ya ruwa)

Cikin tarar numfashinta Yasira tace  this isn t about blood Kausar
(Wannan ba akan batun ?an uwantaka bane ba Kausar) 


Cikin fushi Kausar ta ce
  To dan mai yasa kike komawa Sangarensa?
Ba ma fa ki san wannan Yarinyar ba amman a yadda ki ke yi Winnan ya sa na ji kamar har kin so ta, kuma na tabbatar farin cikin da kika gani a fuskar d an uwanki ne ya sanya kika fara sonta da har kike tunanin kareta.
Na san banida kowa Yassira amman ban yi tunanin kaWaicin nawa ya kai har haka ba
sai yau 


Matsowa Yassira ta yi ta kama kafad unta tukunna ta ce
  Kausar, wallahi yadda kika tsani Yarinyar nan nima haka na tsaneta, abu d aya da nake so ki gane shine
Duk rintsi ba zan tab a goya miki baya ki yi abunda kike shirin yi ba, kuma idan har ma kika aikata hakan ke a karan kanki kin san me hakan ya ke nufi??? 
Bata jira jin amsar Kausar d in ba ta ce
  yana nufin kin tsorata,
kin ji tsoronta! Kin bada Kai
kin san ta fi ki da komai,
kin yarda babu ta yadda za a yi ki iya kwace shi daga hannunta
Shiyasa har ki ka yi mata mai kan-kat! 


A hankali Mommy wadda tun d azu ta yi shiruuu kawai tana kallonsu ta ce   bari in je kiran Daddyn ku, shi ne ya kira ni na
na fito. Ina zuwa yanzu zan dawo 

  Tam 
kawai Yasira ta ce mata daganan ta ci gaba da cewa Kausar
 ita Mace ce! Kema Mace ce dan haka ki ya?e ta! A yi duk kalar ya?i da kissa da faWan da za a yi har mu samu mu yi galaba a kanta..
Wannan na yi miki al?awarin zan tsaya miki akai duk rintsi Kausar amman batun kisan kai kam ya fita daga tsari da lissafi dan haka a barshi, dan gaba Waya tunanin naki Kausar ya fita a kan hanya
Ta k arashe maganar tata a hankali.


  Wanne tunanin nata ne ya fita akan hanya?
And what
exactly happen in here(sannan me ya faru a nan haka?)
Yassir wanda shigowar sa kenan ya fad i hakan yana bin parlourn da kallo.

A hankali Kausar ta ce
  ba komai 
Sai kuma ta juya da sauri ta wuce d akinta ta rufe k ofar.

Ya jima yana kallon k ofar d akin nata kafin ya furzar da iska ya k araso ciki inda Yassira take ya tsaya yana kallon ta.

Ajiyar zuciya ta sauk e kafin ta ce   na yi tunanin ka na office, na ji Daddy ya ce ka samu contract, me ka ke yi a gida?? 

  Yasira yau fa Sunday, tun jiya ma kuma na gama abubuwan da na san su ne masu mahimmancin, yau kuma
P.A d ina yana chan.
Inada bu?atar hutu kuma na san zai yi handling (yin ) komai 
Yassir ya faiyyace mata hakan kansa tsaye.

Cikin rashin jin dad i Yasira ta ce   Yassir wannan dalilin fa ya sanya Daddy ya fi bawa Yashjub jari, saboda ya san ko an baka asara ne. Saboda Allah kalli yadda ka tarwatsa company d inka in banda ci baya ba abunda yake yi kullum!!!
Sannan ka d an samu contract da kyar amma dubi yadda kake wasa da damarka?&
Ka yi ha?uri da abunda zan gaya maka kai tsaye kuma a gaban idonka
Amma Yassir kana da matu?ar son jiki da kasala&  

  Am, Yassira! Me ya faru da Kausar??
Me kuke tattaunawa kafin na shigo? 
Yayi mata tambayar yana mai gyara tsayuwar shi.


Fusata Yassira ta yi, ganin
yadda k iri-k iri ya gwale ta,
ya ma k i sauraron ta&
dama ga takaicin Manubiya da Kausar shiyasa cikin fushi
ta ce   in ka matsu ka shiga ciki ka je ka tambayeta da kanka.
Daga haka ta bangaje shi ta fice.
Ta nufi d akin Mommy da
niyyar jiranta ta dawo daga d akin Daddy su yi magana
amman sai ta ganta a d akin nata a zaune ta zabga uban tagumi.

Ta d an yi mamaki amma sai ta kawar kawai ta ce
  Mommy, sai kin bud ewa Kausar ido fa!
Ina tsoron kar ta je ta yi wani shirmen, ganin
wannan Yarinyar nan da ta yi ya haukatata!!&
Ni kaina na tsorata Mommy
dan in dai wannan ce Yarinyar da ya ke so zai aura to gaskiya ba na jin
za mu iya kai labari& ..
Sannan ga dukkan alamu yana tsananin santa! Dan na manta rabon da in ji Yash yana bada hak uri amma ita in kinga yadda yake rarrashinta wallahi
sai kin yi mamaki&
Dan haka in dai har muka bari ta
shigo gidan nan
To a idanunsa da mu da kashi duk d aya!
Dan na san ita kawai zai dinga gani& .
Shiyasa ya zame mana dole mu yi wani abun amma kafin nan ya kamata ki tsawatarwa Kausar, kwata kwata wannan
shirmen nata ba shine mafi dacewar mafita ba&  

*MANNUBIYA*
*47*

A hankali Mommy ta ce
  InshaaAllah zan yi mata magana,
amman Yassira ban ji dad in yadda kika yi mata magana ba yau sam, kalaman da ki ka yi mata amfani da su sun yi tsauri da yawa  .

Ajiyar zuciya Yassira ta sauk e kafin ta nemi guri ta zauna a gefen Mommyn, ta ce
  zan bata hak uri Mommy, amma
ya kamata mu fara nuna mata kuskurenta tukunna. I love her ne shiyasa kika ga na yi mata hakan.
Kinga na farko abunda take shirin yi bai kamata ba

Abu na biyu kuma Mommy ni kad ai na san abunda na gani a kwayar Idanun Yash game da Yarinyar nan, idan Kausar ta yi gigin raba ta da duniya
wallahi ba ita ba bincike in ya biyo har ta kanmu sai mun ga tashin hankali dan kashinmu ya bushe har ke kanki kuma mu da shi har abada.

A ganina
gwara ya tsaneta da kansa cikin sauk i, tsana ta har abada. Akan ya tsanemu tsana ta har abada saboda ita. 

Dafe Kai Mommy ta yi tukunna ta ce   Kausar ba za ta yi komai ba inshaaAllah, Yash kuma na ce muku ku barni da shi,
da shi da yarinyar duk ku bar ni da su.
Yanzu ki je abunki, ina buk atar hutu sosai, ki koma office kin ce ana jiranki.

Shiruu Yasira ta yi tana jin wani kalar tausayin mahaifiyar tasu yana mamayeta!
Saboda Allah
ace wai d anka ba ya kulaka,
zai yi aure bama ka saniba sai y ar kishiyarka ya gayamawa.
Sannan yanzu ga Kausar ta sake d aga mata hankali& .shiyasa dole ta shiga damuwa& .

Har Yasirar ta mik e za ta fita sai
kuma ta koma ta rungume Mommyn, sun jima a haka tukunna ta cika ta ahankali ta ce   komai zai gyaru Mommy, inshaaAllah 
A hankali Mommyn ta ce
  Na gode Yassira, Allah ya miki albarka 

Murmushi
Yassirar ta yi
tukunna ta cikata ta ce   ameen,sai na dawo  daga haka ta fita
A ranta tana adduar  Allah ya kawo ranar da Mommy Yash Daddy za su had a Kai su so
juna su k aunaci juna komai ya dawo dai-dai Family ya gyaru ya yi dad i& & 


A b angaren Yassir kuwa,
Yassira tana fita ya k arasa k ofar d akin Kausar da niyyar shiga amman sai ya ji ta a rufe,
dan haka ya sake tabbatarwa
kansa
 Tabbas akwai abunda Kausar take b oyewa
Amma kuwa in ta yi masa haka to ta yi mugun janyowa kanta bala i da masifa& .
Bai bar bakin k ofar ba sai da
ya gama tsara abunda zai yi
 Zai jefi tsuntsu biyu da dutse d aya
Tsuntsun farko& zai kawo k arshen matsalarsa.
Tsuntsu na biyu kuma& zai fallasa masa Kausar& zai gano abunda take b oyewa, dan ya san in dai har da gaske Kausar son Yashjub take yi kamar yadda ya ke zargi
to
Idan ta ji labarin mutuwar Yashjub Win sai ta yi haukan da zai fallasa ta b aro-b aro.

Ta hakan ne zai gane gaskiya,
a daina wasa da hankalinsa kamar wani wawa!
Daga nan?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 kuma ya ci ubanta na wasa da hankalinsa Win da ta yi
sannan ya aureta
ba yadda ta iya& &



Ko gida Manubiya ba ta kai ga k arasawa ba Yahanasu ta kira ta& Tashi d aya kuwa ta ji Yahanasun ta kwanta mata a rai, itama Yahanasu nutsuwa da hankalin Manubiya yasa ta ji ta k ara sonta&
sun d an tab a hira daganan ta taya d an uwanta campaign kafin suka yi wa juna sallama.

A k ofar gidan nasu aka ajjiye ta, kamar had in Baki! Mai adaidaita sahun yana wucewa tana shirin shiga gida ta ji an kira sunanta dan haka ta juya.
Murmushi ne ya wanzu akan kyakkyawar fuskarta sakamokon had a idanu da suka yi da Mama.
Sai da ta gaida ita ta amsa tukunna Maman ta ce   ki yi hak uri nima kwana biyun nan ban ji dad i ba shiyasa ban samu na shigo na duba innar taku ba.

Murmushi Manubiya ta yi, tana mai jin k aunar Matar tana ratsata a lokaci guda kuma tana mamakin tsananin kamanninta da Yashjub kafin cikin kwantar da murya ta ce
  Allah sarki! Allah ya baku lafiya gaba d aya&
Innar ma na san bata nan, dan ba lalle sun dawo ba amman mu shiga dai mu duba 
Daga haka suka wuce tare bayan Mama ta ce   ameen 

Sai da ta yi sallama ta shiga tukunna Maama ta bi bayanta itama ta shiga Bakinta d auke da sallama.

Da ikon Allah kuwa har sun dawo dan  a cikin wata na ura
kawai aka saka Innar aka fitar
amman Dr Sofia ta ce   ta mayar da pt d in sau biyu a rana sannan su kwantar da hankalinsu dan babu wata matsala saboda abun nata ma ashe minor ne dan haka su tsammaci warkewarta a ko wanne lokaci muddin aka bata kulawar da ta kamata. 

Manubiya ta yi mamakin yadda ta gansu a zaune gaba d ayan su sun yi jugum har Ya Nafi u, bata gama nazartar su ba aka fara

48 / 51