Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
komai na bikin Naima zan saka ta dawo"
"Wannan kuma ai ba wata damuwa, kawai dai gara a tura ta ɗin, dan yadda kike ta maganar ta fetsare yanzu tom tsaf ta rusa wannan auren, tunda har naji kince ta iya kallon tsabar idonki ta ce muddun tana nan baza'ai auren nan ba, kinga kuwa ai gara ta tafin, bayan bata nan ɗin ayisa hankali kwance, ta dawo ta iske ƴar uwar tata a gidan mijinta. Nasan dai bazata so ƴar uwarta ta zama bazawara ba, dole ta haƙora idan taga an riga an ɗaura ai"
Jinjina kai kawai Iya take tana tunanin ta yadda zata ɓillo ma abun, da ita kanta uwar tasu.......
PAGE 16
*Ƙofar Marusa, Katsina state Nigeria*
"Wai saurin mi kike ne haka?"
Aunty Haja ta faɗa tana kallon Aunty Maryam dake saurin shafa lipstick a bakinta. Sanye take da abaya irin ƴar dubai ɗin nan tasha gayu na kece raini tana gyara zaman mayafinta ta ce.
"Wallahi sauri nake zan fita"
"Muje nima daga nan zaki sauke ni unguwar nan da kika taɓa sauke ni rannan"
Ɗan tsayawa Maryam tayi tana duban Haja kamin ta ce.
"Wai Aunty Haja da gaske dai Koton zaku shiga?"
"No ba zama zamuyi a Koto ba, kawai wajan Alƙali ne zai bani takardar saki, kuma shima Umar ɗin yau zamuje tare dashi, domin an kai masa sammaci shima"
Sauke lumfashi kaɗan kawai tayi tana faɗin.
"Shikenan tom, muje"
Tare suka fito daga ɗakinsu, su Aunty Sa'a na tsakar gidan suna ta aiki.
"Lahh Aunty Aysha dama kin iya ƙitso ne?"
"A'a banfa iya ba, nima yanzu ne Hannah tazo nake lallaɓe mata kan nata, kin sanshi da shegen yawa, ita kuma bata son zuwa gidan ƙitso"
Ta faɗa tana kallon Maryam datai maganar.
"A'a wai ina zuwa ne wannan wanka haka da kuka ɗauka?"
Cewar Aunty Sa'a tana binsu da kallo.
"Wallahi zanje wani biki ne ni, ita kuma zan rage mata hanya na sauke ta"
"Okey tom sai kun dawo, amma please Maryam banda gudu da Mota"
Murmurshi kawai Aunty Maryam ta saki tana duban Aunty Sa'a. Shi yasa take bala'in son ƴan uwanta, tunda take fita da Motar nan bata taɓa nuna cewar wai tata bace ita ta samo ta, ko tayi ma wani gori a cikinsu.
"Ke ni nama so tafiya da Hannah, amma next time zaki raka ni unguwa"
Ai Hannah da sauri take magana a cikin ranta tana cewa.
(Tabɗi jam ai wallahi ba inda zan ƙara binki Aunty Maryam, sai nasan yadda zanyi na zille tafiyar nan duk sadda kika tashin)
"Magana kike ne naga bakin ki na motsi?"
Girgiza kai tayi da sauri, Aunty Aysha dake mata ƙitso ta ɗan ɗuƙo tana kallonta ta ce.
"Mifa zata ce?"
"Ohh nasan ko magana zatai ne?, kin san Hannah ba'a taɓa cewa za'aje waje da ita bata ɓata ma mutum rai ba"
"To wai dole ne ma sai anje da ita?, koma miye a haɗasa dani man"
Cewar Fannah tana taɓe baki, dan ita haushin abun take ji ma, danmi za'a rinƙa wani cewa sai Hannah ita fa?.
"Sha kuruminki Fannah, ina yin aure zan ɗaukeku gaba ɗaya ku koma gida na, ni zan zaɓa maku mazajen aure"
"Ahhh, Aunty Haja aure fa kike magana?, keda har yanzu aurenki da Umar bai kai ga mutuwa ba, kike maganar wani kuma"
Murmurshi kawai Aunty Haja tayi tana duban Aysha datai maganar kamin ta ce.
"Hmmm, Aysha kenan, akwai wani shiri da nake yi, nan kusa zaku ji shi, ai wadda nake so na aura ne babban mutum ne, kuma ɗan siyasa ne sananne ne. Shi kuma wannan auren Umar da kike cewa yau insha Allah fitar nan da zanyi bazan dawo dashi a kaina ba"
"Kai wallahi harna ji daɗi Aunty Haja, wallahi gara ki auri mai naira wadda aka sani, ko muma mun huta"
"Ke yanzu gidan kishiya zaki faɗa Haja?"
Ammi ta faɗa kanta tsaye tana duban Aunty Haja, dan ita tuni tasan wadda take so ɗin.
"Ammi ai ba kishiya ba, ko mata nawa ne dashi zuciyata a yanzu tana garesa, kuma Ammi komi zai faru dole ne sai na shiga gidan Alhaji Ma'aruf Kangiwa"
Ido waje su Aunty Sa'a ke bin Aunty Haja da kallo dake tsaye ita da Maryam.
"Kai wai Alhaji Ma'aruf Kangiwa dai Mataimakin Gwammanan jahar nan Aunty Haja"
Aysha ta faɗa kusan ita da Fannah sukai maganar a tare dan mamaki ya kusa kashesu suma.
"Tabɗi jam, ke Haja yanzu duk mutumcin da naga kuna yi da matarshi ta biyun nan, kune fa kuke mata hidima, da zuwa ko wanne irin taro kuna fa bayanta. Kuma ai naga kamar matanshi biyu ne ko?, ke yanzu kece kike so kije ta uku kenan?"
"Kware da gaske Aunty Sa'a, kuma komi zai faru sai na shiga gidan nan"
Hannah dai sakin baki kawai tayi tana kallon Aunty Haja dake wannan furucin, daga gani tayi nisa bata jin kira.
"To amma dama kuna tare dashi?"
"Uhmm muna tare man, kin san ƴan siyasa, daga baya ne naga yana so ya fara ja baya dani, kuma can yayi min alƙawarin aure, amma yanzu wai yake shirin zille min, tom zai san ba'a taɓa irinmu a zauna lafiya wallahi"
"Yanzu Aunty Haja da auren naki kike kula wani kuma daban?"
"Ke naci ub*anki Hannah, akwai sa'anki a nan ciki iye?"
Ammi ta faɗa kamar zata kai mata duka.
Turo baki tayi tana faman ɓata fuska.
"Rabu da ita, mu dai sai mun dawo"
Aunty Haja ta faɗa tana juyawa ita da Maryam suka fice daga gidan.
"Tsakani da Allah ina jima Aunty Haja tsoron shiga wannan gidan, dan duk matan nan nashi ƴan asiri ne, ke bama matan nashi ba, ko matan da suke bi a waje nasan ƴan siyasa da bin matan banza, tom suma bafa haka suke barinsu ba, su matan wajen da suke bi ɗin"
Aysha ta faɗa tana ci gaba da yima Hannah kitso bayan fitar su Aunty Haja ɗin.
"Ahh, to wai miye a ciki?, kaima saika zauna sakaka haka kawai ne?, ai yadda suke a tsayen itama haka zata tashi tsayen, bari ma ta dawo zan raka ta wajan wata ƙawata tasan wajan Malamai wallahi da suke aiki kamar yankan wuƙa, kuma ba shirka suke yi ba, da ayar Allah suke aiki"
"Haba Aunty Sa'a harda ke kema?, wallahi wannan koda mi zasuyi aiki dashi indai wadda zai gusarma da wani hankali ne tofa sunansa asiri"
Tsura mata ido kawai Aunty Sa'a tayi kamin ta ce.
"Ke Hannah ki fita daga ido na rufe wallahi, kai daga yanzu ma idan muna magana karna ƙara ganin wani shege daga ke har Fannah a zaune a nan wajan a cikinmu, tunda dai mu ba sa'anninku bane. Sai ana magana kuna katse mutane sai ka ce kune manya a cikinmu?. Ke gaki wacce kika san dai-dai ko?, mu ai da yake bamuyi Islamiyar ba sai ke hamshaƙiya?"
"Nifa Aunty Sa'a ba haka nake nufi ba, kawai fa na ƙara tunatar daku ne ba wani abu ba"
"To ki riƙe tunatarwar taki, wallahi Hannah kina shiga hanci na, so kike saina fyato ki tukunna ko?"
Ammi ta faɗa tana nunata da yatsa.
Zata sake magana Aunty Aysha ta ce.
"Kinga, kifa tsaya na idasa miki kitson nan, ko wallahi na sakar miki kai. Ke ace tun ɗazu bakin ki kawai ake ji?, ita baga Fannah nan ba a zaune a wajan kinji tana magana ne?, sai ke kina ƙarama ma a cikinmu amma kina sako ma mutane baki?, kina ƴar haka dake, mima kika sani game da duniyar ne iye?"
"Hmmm, rabu da ita da'allah, bata san miye ake ciki bane shi yasa, dan ub*anki idan ba'a neman taimakon Malaman mu zaki ganmu mun zama haka ne shashasha"
Ammi ta faɗa tana mata wani kallo.
Hannah dai shiru tayi tana haɗiyar zuciya kawai, tana kuma takaicin wannan hali na ƴan gidansu. Wata rana sai suyi kamar sun gyara wani lokacin kuma sai kiga sun ƙara komawa gidan jiya, ta rasa wane irin bahagon tunani ne dasu?, amma ita dai kullum addu'arta Allah yasa su gane gaskiyar cewar duniyar ma duka nawa take, da zaka je kaita ɗora burin duniya a cikinta?. Kuɗi ne dai yanzu zata iya cewa babu wacce bata kama kuɗaɗe a cikinsu, saboda kowacce Allah yasa mata albarka a cikin sana'ar da take yi, yanzu kam zata iya cewa basu rasa ci ba bare sha, sai ma sune suke taimakama wasu a yanzu, amma duk da hakan taga su ba nan suke su, su tsaya ba, su suke suga sun wuce kowa ana damawa dasu a ƙasar, ta lura fa yadda suka ɗauki duniyar da zafi suka ɗauke ta........
PAGE 17
*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*
A hankali ta aje abunda ke hannunta tana duban Naima dake ƙoƙarin saka Hijab ta ce mata.
"Na'ima dan Allah kiyi ƙoƙari ya faɗa miki inda za'a iya samun nata, sana kiyi hakuri kuyi magana mai daɗi dashi, tunda naga shi yana son haɗin auren naki"
Ƙasa da kanta kawai Na'ima tayi tana amsawa da to.
Zata fice daga ɗakin kenan Mubeena ta faɗo ɗakin tana faman kallon Na'ima haɗe da riƙe ƙugunta tana cewa.
"Wai ina zaki je naga kinsa Hijab?"
"A'a ina ruwanki da inda zata je?, ai kinfi kowa sanin inda zata ɗin, baki ji an aiko cewar taje Musa na waje ba yana son ganinta ba?"
Taɓe baki Mubeena tayi tana zama akan katifar dake zube a ɗakin tana cewa.
"Naji Inna, dan harma naje wajan na ce mas..."
"Kika ce masa mine Mubeena?. Kar dai ace zuwa kikai kika koresa?"
Cewar Inna tana fiddo ido waje.
Mubeena na turo baki ta ce.
"Ni kawai zuwa nayi na ce masa daga yau karna sake ganin ƙafarsa a ƙofar gidan nan. Haba Inna kin gansa kuwa?, kamar baki san ya Musa yake ba?, yanzu haka wallahi idonsa jawur yazo nan, na fita na iskesa sai zuƙar taba fa yake a wajan"
Inna kamar zata kai mata duka ta ce.
"Wallahi ke bazaki ɗora min hawan jini ba Mubeena. Ina ruwanki dashi ma?, bance ki daina shiga abunda bai shafe ki bane wai?"
Zatai magana suka fara juyo kwakwazon Iya a waje sai cewa take.
"Kuna ina ne?. Ina ita marar kunyar da har zata je ta kori musa, tunda naga ƙofar gidan ita ce ta ginasa da kanta, kaga ƴar banzar yarinya kawai"
Iya sai faɗa take ta inda take shiga bata nan take fita ba. Inna ta dube Mubeena tana nuna mata ƙofar waje tana cewa.
"Kin gani ko Mubeena?. Ke kenan ace kullum kece mai jawo min magana da zagi a cikin gidan nan?"
"To wai ma ina ruwanki ne Mubeena?, ba dai ni ce za'a aura ma shi ɗin ba?, to daga yau karki sake ɗaukar wani mataki indai akan auren da za'a min ne, naji na yarda zan aure san, koba shikenan ba?"
Ya Naima ta faɗa tana kallon Mubeena dake cike da mamakin lafazin data faɗa.
Miƙewa tsaye Mubeena tayi da wani kalar mamaki tana cewa.
"Yanzu Ya Naima keda kanki kike cewa kin yarda zaki auri Musa?"
"Kware kuwa sai kuma mi?"
Girgiza kanta Mubeena take tana faɗin.
"Haba Ya Naima karki yi haka dan Allah, mi kike so ki maida rayuwarki ne?, idan fa kika sake kika amince da auren mutum irin Musa to wallahi kashe rayuwarki kawai zakiyi. Mutanen da baida sana'aryi"
"Babu dai ruwanki daga yau na dai gaya miki"
Inna ta ƙare maganar suna iya juyo Iya dake ƙara banbamin faɗa a tsakar gidan.
"Wai bazaku fito bane kuna jina kuma?, ko tsabar rainin hankali ne yau naku ya motsa gidan nan?, to wallahi dai-dai nake daku ai"
Kusan gaba ɗaya suka fito, har Mubeena dake kan gaba, dan ita kwata-kawata bata wani shakkar Iya da duk abunda zata ce.
"Sannu marar kunya dangin marassa kunya. Ke har kin isa kin kai Musa yazo gidan nan, har ki wani ce masa karya sake zuwansa?, gidan naki ne?"
Tana turo baki ta ce.
"Yo dama Iya ni na ce gidan nan nawa ne dama?"
"Kince mana marar kunya"
"Ni wallahi bance ba"
Ta faɗa tana turo baki.
"Ai kin gama nunawa marar kunyar banza, kuma wallahi nasan maganinki, kuma kusa-kusa zanyi maganin naki"
"Yanzu dai Iya kiyi hakuri dan Allah"
Inna ta faɗa tana kallon Iya data jefa mata wani irin kallo.
"Sai anyi magana ki rinƙa bawa mutane haƙuri. Kenan kullum baki isa yima yaranki faɗa ba, sai dai kawai ki barsu suna abunda suke so?"
"To wai Iya ina ruwan Inna a nan ciki?, Inna ma fa bata san ya akai ba, bare tasan miye na aikata"
"Zakiyi ma mutane shiru ne ko sai na gwafje miki baki?"
Inna ta faɗa kamar zata kai ma Mubeena duka a bakin nata.
Shiru tayi ta ɗan matsawa gefe tana turo baki haɗe da hararar Iya ƙasa-ƙasa.
"Ke kuma Na'ima maza kije yana waje yana jiranki, ni na hanasa tafiya, sana daga yau ma ki ce masa ya rinƙa shigowa gida, ai gidan dama ba baƙonsa bane, tunda ai da shigowarsa yake ciki kawai, ni banga ma dalilin tsayawar ba waje"
Ɗaga kanta kawai Na'ima tayi tana yin hanyar ƙofar gidan, Mubeena ta bita da kallon mamaki haɗe da yin kwafa kawai.
"Mtsww na kusa yin maganin marar kunya ai"
Iya ta faɗa tana yin cikin ɗakinta.
Sosai furucin da Iya keyi kesa Inna cikin fargaba, idan tana irin wannan zantukan to wani abu ne take gaf shiryasa ga Mubeena ɗin, tafi kowa sanin wacece Iya.
"Kinga abunda kike shirin jawowa kanki ko?, kinfi kowa sanin Iya da abunda zata aikata ai, koma miye kika ja tayi miki kece kika sayesa da kuɗinki wallah. Ki kiyaye Mubeena, bana son maganar da kike yawan sani a gidan nan wallahi, ba yadda zanyi da kene, Allah dai ya shirya min ke"
Inna ta faɗa tana yin gaba itama ta bar Mubeena a tsaye tana faman ɓata fuska.
Ƙofar ɗakin Iya tabi da wata hararar tana cewa a fili.
"Wallahi ba abunda zaki iya min Iya, ai kan mage ya waye, suma su Ya Na'imar su suka so, ni dai kam wallahi da ni ce aka ce za'a ma irin wannan abun, ai da yanzu wata maganar ake ma ba wannan ba wallahi tabɗi jam lallai ma"
Mubeena ta ƙare maganar haɗe da riƙe bakinta, tana ayyana inama ita ce aka ce za'ai ma hakan.
A waje koda Na'ima ta fita, yana daga zaune har lokacin yana zuƙar taba yana wani fesar da ita.
Jin fitowarta da sallamar data masa yasa shi sakin tabar da yake sha ɗin ya yarda ita ƙasa ya take ta.
Murmurshi ya saki, haƙoransa suka bayyana, duk da tabar da yake sha, da kuma zuƙe-zuƙen kayan maye da yake yawan amfani dasu, amma haƙoran nasa fess suke.
Musa baƙi ne amma ba irin can ba, danma shaye-shayen da yake yi ne yasa baƙin nasa ƙara linkuwa, dan lips ɗinsa yanzu yayi baƙi sosai, idonsa ma kullum a jawur suke.
Yana da hanci shima kamar dai irin nasu Na'ima ɗin, danma har suna ɗan yanayi dasu, saboda jini ɗaya ne dai yayo su, tunda Mahaifinsu Na'ima ɗin Yaya ne ga Mahaifin shi Musa uwa ɗaya uba ɗaya suke.
Su duka kuma kyakykyawa ne, asalin Kanuri ne su, gara ma su Mahaifiyarsu Na'ima data kasance Bafullatana ce, shi yasa suka fi su Musa ɗin kyau har a cikin dangin.
Shima Musan ba laifi da nasa kyan, dan yana da wani irin ido mai girma sosai, ga girarsa mai yawa ce, bakinsa ɗan dai-dai, yanayin jikinsa ya dace dashi, kawai abunda ya ɓatasa wannan shaye-shaye da yake yi shine kawai, amma da ace Musan nutsatstse ne babu wata macen da zata ce bata ƙaunar haɗa aure dashi, saboda babu wata makusa a tare dashi.
"Masoyiyi har kin fito?"
Ya faɗa yana kallon Na'ima data ɗaga kanta kawai tana binsa da kallo, yadda yake magana muryar nan tasa ta fashe sosai, gashi daga kallesa ka saurari yanayin muryasa nan take zaka shaida shaye-shayen ma ya matuƙar kama jinin jikinsa.
"Ɗazu ne kawai wannan ƙanwar taki Mubeena ta wani zo zata ɓata min rai, Allah wallahi saura kaɗan na ɓarar da ita a wajan nan, Allah kawai ya taimaketa wallahi saiga Iya ta fito, ita ta cece ta"
"Yanzu dai to kayi hakuri bazata sake ba ai"
"Allah ko masoyiya?, ai taci arziƙinki ne wallahi, da tuni fuskar nan tata ta kunbura da mari, dan banda haƙuri kin ganni nan"
"Yanzu dai abar maganar Mubeena, dama wani abu ne nake so na tabbayeka dan Allah, dan da hali kayi min"
"Miye kike so Masoyiya?, kawai ki faɗesa kanki tsaye, koma miye zanyi miki shi"
Murmurshi kaɗan Na'ima ta saki tana jin kwanciyar hankalin sanar dashi ɗin, tana kuma jin da sauƙi tunda har yana sonta ma, bazata sha wahala gare sa ba sosai, sai dai ita sam bata son ko ganinsa dauriya kawai take, amma tayi ma kanta alƙawarin cewar zata koyama kanta zama dashi da kuma son nasa, kuma zatayi iya bakin ƙoƙarinta wajan gyara halayensa marassa kyau......
PAGE 18
*HANNAH POV*
"Eh insha Allahu yau zaku samu Cake ɗin, wajan ƙarfe biyu haka mai delivery zai kawo"
Hannah ta faɗa tana sauke wayar dake manne a kunnenta bayan ta gama wayar.
"Wallahi naga kina samu da yin Cake ɗin nan fa"
"Sosaima Aunty Sa'a, ƴan gayu ne dai kusan kullum nake ganin suna saka Order na Cake ɗin"
Zatai magana Aunty Haja ta shigo fuskarta ɗauke da ɗan murmushi kaɗan.
"A'a har kin dawo?. Yaya dai anyi sakin ne?"
Cewar Aunty Aysha dake zaune itama a tsakar gidan.
Zama tayi tana aje jakarta, ta shiga cire gyalenta tana murmushi haɗe da sauke wata ajiyar zuciya ta ce.
"Wallahi fa anyi. Amma da kyar ya iya sakin nawa, kuma saki duka biyu yayi min, naso ace ukun ya cikashe min, amma yaƙi"
Ta ƙare maganar tana fiddo da wata farar takarda tana nuna masu, alamar takardar sakin ce.
Taɓe baki Aunty Sa'a tayi tana faɗin.
"Yo ai a banza, koda baiyi