Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ta ce.
"Insha Allahu Mlm za'ayi kamar yadda kace ba wani kuskure. Sana yanzu mi za'a bada Mlm kafin alƙalami?"
"Aikina ai ba'a biyana sai aiki yayi, kuje kawai kuɗin sadaka kawai zaku bayar yanzu sai aiki yayi sai a dawo a bani kuɗin aikin"
Amsawa sukai kusan a tare Sa'ade na ƙara masa godiya.
Yana tashi ya fita yana ɗan jima saboda rubutun da yayi ya kawo masu ɗaure a leda da duk abubuwan da zatai aikin dasu.
A tsaye ya basu saboda jama'ar dake danƙare a waje suna zaman jiransa.
"Toni zan koma ciki saboda akwai jama'ar dake jira na suna da yawa, fatan dai ta gane duk abubuwan dana ce, kuma kin riƙesu dai ko, kar a samu kuskure"
Murmushi Aunty Haja tayi tana cewa.
"Mlm na riƙe gaskiya, kuma yauma inaga zan fara aiwatar da aikin, idan na gama zan amshi numberka wajan Aunty Sa'ade, sai na kira ka na shaida maka. Sana ga wannan kuɗin sadakar"
Ta miƙe masa wasu kuɗi a dunƙule masu yawan gaske da ita kanta bata ma san nawa bane kawai ta ɗakko su ne a jaka ta miƙa masa, dan ita kam daɗin da take ji yanzu Allah ne kawai ya sani, sai ma yanzu ne take jin son mallakar Alhaji Ma'aruf ɗin sosai ashe haka take sonshi bata sani ba?, dan yadda take jin wani irin zumuɗin fara aikin ke bata mamaki ma.
"To ba komai saina jikin. To ke Sa'ade ba dai wata matsala a wajanki ko?"
"Babu Mlm, ai da akwai tun lokacin dana kiraka a waya zan faɗa maka, komai na tafiyar min dai-dai yanzu"
"Tom masha Allahu haka ake so ai. Saina jikun"
Ya faɗa suna ƙara sallama dashi suka fito.
"Wai Allah gaskiya daga jin wannan aikin ko wadda baya fashin sallah akaima shi saiya kamasa, bare irinsu Alhaji Ma'aruf dake harkar siyasa ai dole aiki ya cisu tunda suma dai suna bin wa'innan irin Malaman"
"Hmm ai wallahi bamai sallah ba koma mi yake yi wuyarta ta fara aikin nan ta gama kawai Sa'a nake gaya miki, aiki ne kamar yankan wuƙa nan take ranar data gama saiya neme ta wallahi kinji na gaya maku, ai shi ɗan adam akwai shagala da addu'a da wasa da ibada shi yasa idan akayo mana asiri kobai kamamu gaba ɗaya ba sai ya cimu koda kaɗan ne"
"Hakane kam, ai dole a fara aikin nan yau, dan kin san da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, so nake komai nayi sa da gaggawa ayi komai a wuce wajan, dankarma wata matsala ta kunno kai"
Aunty Haja ta faɗa dai-dai lokacin da suka ƙarasa inda suka aje Mota. Shiga sukai Aunty Sa'a ta tayar da Motar suka bar wajan, suna tafe kan hanya suna labarin Malamin da yadda mutane ke rubibin zuwa wajansa ai daga gani ya iya aiki, da bai iya aiki ba da bazasu ga wa'innan jama'ar dake tururuwar zuwa inda yake ba.........
PAGE 22
*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*
"Ina jinki Masoyiya, kinyi shiru kuma lafiya dai?"
Sauke ajiyar zuciya Na'ima tayi tana gyara zamanta sosai ta kallesa kamin ta ce.
"Dama.dam..dama abunda nake so na tabbayeka shine, dan Allah ina zamu samu number Aunty Zubaida please"
Wani kallo ya jefa mata na wasu mintina. Ganin hakan yasa Na'ima saurin ƙara cewa.
"Kaga fa ba wani abu bane, kawai Inna ce ke son number nata. Kasan kuma tsawon shekaru nawa bamu ji labarinta ba, tun fa lokacin da kake zuwa lagos rabon da muji wata ɗuriyarta"
Wani shegen murmushi ya saki yana karkace baki irin na ƴan shaye-shayen nan yana cewa.
"Zubaida yanzu samunta gaskiya sai an kai ruwa rana ko a can Lagos ɗin, dan gaskiya yanzu labarinta da nake ji a wajan abokaina dake can har yanzu, dan gaskiya Zubaida ta kai matakin da ku kanku idan kuka ganta zaku rantse cewar ba Zubaidar da kuka sani bace"
Jinjina kanta kawai Na'ima takeyi kamin ta ce.
"Yanzu dai duk ba wannan ba Musa please dan Allah number ɗin da kasan za'a kira a sameta kawai muke so wallahi"
"Eh to za'a iya samun numberta a waje na, a wayar nan, amma gaskiya wannan number ɗin tsohuwar number ɗinta ce, ba lallai a sameta da ita ɗin ba, amma dai ku gwada ko Allah zaisa ayi sa'ar tana aiki da layin har zuwa yanzu"
Da sauri Na'ima ta amshi wayar daya fiddo daga aljihunsa tana duban number daya kamo a cikin wayar yayi seving da Zubaida Lagos kawai a jikin number.
Kai tsaye saita fara kiran number, sai dai kiran farko aka fara ce mata a kashe number ɗin take, ta sake kiran sai kuma taga ansa layin busy yake.
"Amma number nan kamar zata shiga, zan ɗauki number ɗin zuwa anjima sai mu sake gwadawa, na gode"
"To yayi ai ki ɗauka ɗin kawai. Sana wane shirye-shirye kika fara na bikinmu?"
Bayan ta ɗauki number ta miƙa masa tasa wayar tana sauke lumfashi kaɗan ta ce.
"Ban fara komai ba gaskiya"
"Amma kin san saura baifi sati biyu ba auren namu ko?"
"Hakane na sani"
"To ya kamata fa ki fara shirye-shirye, amma mi kake ganin zaki shirya"
"Ni ai ba wani shiri da zanyi gaskiya bana buƙatar yin komai ne"
"Haba dai masoyiya kin san bikinmu bazai yiwu ace anyisa salaf haka ba gaskiya, dole ne ma bikinmu a girgije asha shagali Allah wallahi"
Miƙewa Na'ima tayi tsaye saɓanin da, da suke zaune akan wani dakali na ƙofar gidan nasu tana kallonsa shima ya miƙe yana dubanta ta ce.
"Ni dai gaskiya ban shirya wani abu ba, kuma bana jin zan shirya a yanzu, sai dai kai ko idan zaka shirya ɗin saika sanar dani saimu je tare, amma gaskiya bana so a shirya abu ko wani party cikin dare, a shiryasa ko da yamma haka please"
"To ai shikenan tunda ma kin amince ai hakan ma normal ne Masoyiya"
Ya faɗa yana sake kallonta sosai.
"To ni zan shige ciki sai munyi waya"
Shima murmushi ya saki yana kallonta harta shige ciki sai shima ya juya ya yabar ƙofar gidan. Yana jin daɗi dan har wani canza tafiya yake yana wani rangaji na jin daɗin yau ta sauraresa har sunyi magana mai tsayi haka.
Wani kallo Mubeena ke bin Na'ima dashi harta shigo ɗakin nasu ta zauna ta sauke ajiyar zuciya ta cire Hijab ɗin dake jikinta.
"Miye haka Mubeena wannan kallon fa?"
Taɓe baki ta sake yi tana sake duban Na'ima datai mata maganar ta ce.
"Kawai mamaki nake ai, ke yanzu dai kin yarda kin amince zaki auri wancan giɗi-giɗin ɗan shaye-shaye?"
"Da alama kin fara raina ni Mubeena ko?"
Girgiza kai kawai Mubeena tayi tana ɗan murmushi kaɗan sai kuma ta tamke fuska tana turo baki. Har cikin ranta bata son wannan haɗin kwata-kwata dasu Iya suke son ƙullawa dan cutar da ƴar uwarta kawai.
"Kin san Allah Ya Na'ima kawai ki bani dama Allah kuwan saina rusa wannan auren, kawai goyan bayanki nake so, ina da shirin da zanyi da za'a fasa auren nan"
"To bazata goyi bayan naki ba kinji ko?"
Cewar Inna dake shigowa cikin ɗakin yanzu ta tsinci maganar da Mubeena ke faɗa.
Shigowa sukai ita da Khadija dake bayanta.
Khadija ta zauna tana kallon Mubeena dake ɓata fuska yanzu.
"Wai ke Mubeena ina ruwanki a ciki iye?, ke ce zaki zauna dashi ne ko ita?, nima na bata shawara karta yarda amma taƙi, sai kawai na koma gefe na barta ita da Inna"
Inna ta watsa masu wani kallo tana nunasu da yatsa ta ce.
"Ku dai ɗi nan baku jin magana wallahi, duk cikinku ba wacce ta biyo hali na irin Na'imar ai shi yasa duk abunda na ce mata yi kawai yi take amma banda ku"
Ta ƙare maganar tana nunasu gaba ɗaya.
Khadija ce ta sake cewa.
"To amma Inna tsakani da Allah ai Ya Na'ima tafi ƙarfin Musa, bama sa'an yinta bane, kawai su Iya tsabar mugunta ce tasa sukai wannan haɗin gambizar"
Mubeena ta amshe da cewa.
"Shine ai Ya Khadija abunda nake so ta gane kenan ita da Inna amma idonsu ya rufe gaba ɗaya, ai hanyar jirgi daban ta mota ma daban, ina wani dacewa a tsakanin Ya Na'ima da wancan shashashan?"
"Kunga ku tashi ku bani waje karna ɓata maku rai gaba ɗaya yanzun nan"
Murmurshi mai ciwo suka saki suna sake zama sosai dan sun san ta faɗa ne kawai.
"Bazaku tashin ba?"
"Kinga Inna kyale su kawai. Ni maganar ma Aunty Zubaida zan miki"
Sosai Inna ta juya tana fuskantar Na'ima ɗin ta ce.
"Yawwa fatan an dace, nima maganar tata ce ke cin raina na wallahi, amma wa'innan yaran sunzo sun fara saka min ciwon kai"
"Ki rabu dasu Inna, ai duk yara ne"
Dariya kawai Khadija ta saki tana cewa.
"Wai naji ana maganar Aunty Zubaida mi za'ai da maganarta kuma?"
"Ina ruwanki"
Cewar Inna.
"Ba ruwana Inna, amma ai gani nayi itama ta yada mu, kusan shekara nawa bata neme ki ba"
A yadda Khadija ke maganar zaka san tana jin haushin Aunty Zubaidar.
Mubeena kam taɓe baki tayi tana juya masu ƙeya.
"To ina ruwanki a ciki?, ba yar uwarta bace ne?, kin taɓa ganin inda aka raba hanta da jini?"
Girgiza kai kawai Khadija tayi tana kallon Na'ima datai zancan.
"To dan haka dan Allah ku daina irin haka"
"Ni banga dalilin da zaku riƙe Zubaida a ranku ba, bance kuma ku sawa zuciyarku tsanar Zubaida ba, dan Zubaida dai jinina ce, kuma ƴar uwata ce ɗaya tilo a duniya data rage min. Bari kuji Zubaida ni ce nayi mata laifi bawai ita ce tayi min laifi ba, saboda ita tana gudar min irin wannan rayuwar ne da muke ciki yanzu, gashi kuma abunda take gudar min ɗin gashi yanzu muna cikinsa. Kuma ke Mubeena shirin da muke ma wajanta zan turaki, dan Iya ban san wane mataki zata ɗauka akanki ba kema"
A mugun zabure Mubeena ta juyo tana kallon Inna ido waje ta shiga cewa.
"Inna ina zanje wajan Aunty Zubaidar zaki kai ni?"
"Kware kuwa"
"Haba dai Inna waye ma yasan inda take yanzu fisbilillahi?, kina fa ji yadda Musa ke kawo labarin yadda Aunty Zubaida ta zama fa a can Lagos ɗin"
Cewar Khadija.
"Ke nan har kin yarda kin amince cewar Zubaida zata iya zama yadda shi Musa ke zuwa yana faɗar ta zama ɗin?. Ni nasan ƴar uwata bazata taɓa zama mutuniyar banza ba, na dai san tabbas tana da zafin neman na kanta, duk inda sana'a take to zatayi ta domin rufa ma kai asiri, amma na tabbatar Zubaida bazata zama Karuwa ba kamar yadda ake faɗa ina da yaƙinin hakan"
Su duka shiru sukai suna kallon Inna dake maganar da yaƙini sosai a cikin ranta, domin tafi kowa sanin wacece Zubaida ɗin.
"Ni dai gaskiya Inna ba inda zani, yanzu kawai sai a ɗauke ni a wani kaini Lagos nima na zama irin...
"Ai ko wallahi gaba ɗaya daga ke har Khadija muddun na sake jin maganar banza ta biyo bakinku akan Zubaida saina saɓama mutum, saina ɓata masa rai wallahi, zakuga kuma fushi na ne wadda baku taɓa tunani ba. Kuma dan Allah ranar da aka tashi kaiki Lagos ɗin ki gudu ƙarewa ki tafi wani wajan ko ki shiga duniya sai insan ke ce kika isa da kanki ai ko?"
Sosa kanta Mubeena ta farayi tana kunbure fuska kamar zata saki kuka.
"Wato ma bazaki bata hakuri ba ko?"
Tana turo baki ta kalli Na'ima datai maganar.
"To ni...
"Kinga riƙe haƙurin naki bana so, amma tafiya Lagos dan ub*an mutum dole ne yayi ta ko yaƙi ko ya so, wannan umarni ne ma, bawai shawararki ko yardarki ake nema ba, ai ba ke ce kikai kanki ba, haihuwarki akai"
Sosai suke kallon Inna dan bata taɓa zaginsu kamar haka ba, da alamar yau kam an kaita ƙarshe ne kuma da alama ranta ya kai ƙololuwar ɓaci ne shi yasa har take irin wannan furucin.......
PAGE 23
*MIMI POV*
Haka rayuwa ta rinƙa tafiya yau daɗi gobe akasin hakan. Har gashi su Mimi suna cikin wata na biyar da aure. Wajan Jafar shi mai yawan tafiye-tafiye ne, idan ya dawo baya wuce wata ɗaya ko ƴan kwanaki ya sake komawa wajan aikinsa, zuwa yanzu dama Mimi ta saba zama ita ɗaya kwana ita kaɗai idan yayi tafiyar.
Kamar yau ma zaune take tana cin abinci tana kuma kallon cikin wayarta.
Kaɗan-kaɗan take murmushi da alamar wani abu take karantawa daya ɗauke mata hankali haka nan.
Sallama ta fara ji sama-sama. A hankali ta ɗago daga kallon wayarta da take yi, tana ɗan mamakin jin muryar kamar ta Shamsiyya.
A hankali take bin ƙofar shigowa parlon nata da kallo bakinta yayi nauyi tama kasa amsa sallamar da ake yi, saboda ita dai iya saninta tun biki bata sake ganin Shamsiyya ba, haka kawai sai taji gabanta ya yanke ya faɗi.
Ita ɗin ce kuwa ta shigo parlon tana wani yatsine baki haɗe da kallon Mimin sosai tana buɗe baki ta ce.
"Anata sallama mutanen gidan basa amsawa mutane sallama ne dama?"
Mimi kamar wacce ta dawo duniyar tunani ta miƙe da sauri tana ɗan ƙaƙaro murmushin dole ta ce.
"Sorry wallahi banji bane, hankali ne ya tafi wani wajan"
"Hmm mamakin dai ganina ake da alama"
Shiru kawai Mimi tayi idonta ya faɗa akan akwatin dake janye a hannun Shamsiyyar wadda ya ƙara sakama Mimi wani shakku a cikin ranta.
Samun waje Shamsiyya tayi ta zauna, harda su ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya, tana wani bin parlon da kallo.
Kasa zama kawai Mimi tayi domin mamaki so yake ya karta tana tsayen.
"Kinyi tsaye lafiya dai?. Au na manta fa dole ne zakiyi mamakin zuwa na, harda su akwati ko?"
Girgiza kai kawai Mimi tayi tana aro wata jarumta ta yafa ma kanta zama kawai tayi kamar mai tsoron wani abu tana sake kallon Shamsiyya ta ce.
"Kawai nayi mamakin zuwan naki ne, tunda naga ba zuwa kake yi gidan nawa ba tunda dai akai bikina ban sake ganin ko giccin irinku ba"
Wani murmushi Mimi taga Shamsiyyar ta saki harda su girgiza ƙafa, zuwa can ta buɗe baki tana cewa.
"Ah yo muda gidan ɗan uwanmu kema ai kin san koba daɗe koba jima dole ne mu dawo garesa ai ko?. Yanzu ma zuwa nayi nan ɗin naɗanyi wata uku haka, ina so na ɗan huta ne, a can gida hayaniya tayi min yawa ne"
Ido Mimi ta zaro waje da wani irin maɗaukakin mamakin daya kashe mata gaba ɗaya ihahirin jiki da ruhi da kyar bakinta na rawa ta iya fisgo magana a bakinta tana faɗin.
"A wane gidan zakiyi wata ukun?"
Wani shegen duba Shamsiyya tayi ma Mimi tana taɓe baki ta ce.
"Nan gidan mana, ko akwai wani gida bawan wannan ne?"
Da wani irin sauri Mimi ta miƙe tsaye bata san lokacin data ce.
"Wallahi abunda bazai taɓa yiwuwa ba kenan ma"
Itama sai Shamsiyyar ta miƙe tana riƙe ƙugunta ta ce.
"Tunda gidan naki ne ai dole ki ce bazai yiwun ba. Kuma wallahi baki isa ba. Gida ne na ɗan uwana ne dole na zauna nayi abunda raina ke so yake kuma muradi, ko anƙi ko an so ma kuwa"
Ta ƙare maganar tana wata irin jijjiga ta tsananin rashin kunya da rashin tarbiyya.
Hankali a tashe Mimi ta rarumo wayarta data aje akan kujera ta nufi bedroom nata jiki na rawa, dan ita wallahi bata jin zata iya zama da Shamsiyya yarinyar dake son mijinta, kawai saita bari tazo mata gida tayi har wata huɗu, ga mijinta da kusa dawowa bai wuce sati mai zuwa ma zai dawo ba, kuma tabbas tasan da biyu aka bir Shamsiyyar tazo mata gida, to bazai yiwu ba wallahi, tafi kowa sanin ƙudurin Shamsiyya, gata bata da kunya ko misƙala zarratin, ƙaramin aikinta ne ta hanata zaman lafiya a cikin gidanta.
Number ɗinsa ta shiga kira ta kasa zama bare tsayawa waje ɗaya sai zarya take a bedroom ɗin.
Yana ɗaukar wayar kawai Mimi ta sakar masa kuka mai ciwo.
Bawan Allah duk sai ya ruɗe ya shiga tabbayarta mike faruwa ne?, lafiya kuwa mike damunta?.
Saida tayi mai isarta yana jinta kamin yaji ta sauke ajiyar zuciya tunda ta fara kukan zuciyarsa ke masa zafi, yayi tabbayar yayi-yayi amma taƙi shirun, sai kawai yayi shiru yana sauraron sautin kukan nata dake sa masa zafi a zuciya.
"Love mike faruwa ne?, mike damunki please?, kin san yadda kukan nan naki ya tayarmun da hankali kuwa?"
Turo baki tayi kamar tana gabansa ta ce.
"Ba dole nayi kuka ba My D, kawai fa ina zaman zama na sai ga Shamsiyya a gidana"
"Shamsiyya kuma, miye ya faru to?"
"Wai zuwa tayi da wani ub*an akwati wai sai cewa tayi ta dawo gidan nan da zama harna tsawon watanni uku"
"Whatttt wata uku?"
"Yeah mana D ya za'ai kawai yarinyar da nasan tana bala'in sonka kawai sai a bari tazo min gida?, kuma kasan fa ba wani shiri muke da Shamsiyya ba"
"To ai ni ban san ma da wannan zuwan nata ba, ni ba wadda ya kira ni ya sanar dani, da waye suka yanke wannan abun?"
Mimi na sauke ajiyar zuciya zatai magana ya rigata ƙara cewa.
"Bari ina zuwa"
Taji ya yanke kiran, saita bi wayar da kallo kawai.
Acan kuwa Jafar na yanke wayar zaune yake a Office nashi na Doctors da yake aikin Likitanci yake, a Jigawa, idan yayi tafiya wajan aikin nasa dama yana sati biyu ko uku bai waiwayi gida ba. Ya so ma tafiya da matarshi amma Hajjarsu ta hanashi, amma da wannan dawowar da zaiyi yana son tahowa da matarshi kawai, saiga wannan matsalar na son kunno kai kuma.
Bayan Hajjar tasu ta ɗauki waya ya shiga gaida ita. Da ɗan mamaki ya sake duban cikin wayar ganin ita dai ya kira ba wata bace, saboda mamakinsa yadda Hajja ke amsa masa sallamar ciki-ciki sai kace an mata dole.
"Hajja waye yaba yarinyar can damar zuwa gidana?, tsakani da Allah Hajja kin san kuma basa shiri da Mimi, kuma