Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   37 / 47

108K to 111K   out of 140.3K words

da take ciki da fargaba ta ci gaba da masa uzuri kawai.

Gaba ɗaya dangi da ƴan uwa sun samu labarin auren da Jafar ɗin zai ƙara, an fara surutun cewa duka yaushe yayi auren da har zai sake wani?, cikin ƴan uwan Mimi harda su Hajiya ake maida mata magana a status sai saka abubuwan biki suke, tana mamakin su Hajiya ace ƴan uwanta ne ke murna wai za'ai mata kishiya?.

Ana saura kwana biyar ɗaurin aure ta ce masa zata je gidansu please yabarta taje ta gana da Mama kota samu sauƙin abunda take ji tasan Mahaifiyarta zata bata shawara ta kuma kwantar mata hankali.

Da kansa ya ɗauketa ya kaita bayan sunje sunyo shopping ya aje ta ƙofar gida ya shigo har ciki suka gaisa da Abba da Mama a nan ya barta sai zuwa anjima sai dawo ɗaukarta.

Koda ya tafi Mama na lura da Mimi kuma dama tana son taga ƴarta tayi kewarta tunda ta samu labarin ƙarin auren da zaiyi tasan ƴarta na can cikin damuwa sosai, saida ta ganta kuma taga ma da sauƙi ba kamar yadda take tunani Mimin zata ɗaga hankalinta ba.

Mimi saita rungume Mama kawai ganin yadda Mamar ke kallonta cike da tausayi irin na uwa da ƴarta, saita saki kuka mai sanyi tana jin natsuwa kasancewarta a jikin Mahaifiyarta.

Sosai Mama ke bubbuga bayanta tana rarrashinta a aikace, saida ta gama kukan Mama ta natsu ta shiga bata shawarwari wadda zasu taimaketa sosai zamanta da abokiyar zamanta da za'a kawo mata, sosai kuma Mimi taji daɗin shawarar da Mama ta bata sai taji hankalinta ya kwanta sosai ba kamar da take cikin damuwa da nauyin zuciya ba.

(Sai nan gaba zaku ga aiki da irin shawarwarin da Mama bata). Sosai taji hankalinta ya kwanta da irin yadda Mama ke kwantar mata da hankali, harda wasu sirika Mama ta sake bata da dabarun zama da kishiya, duk dai Mama bata taɓa zama da kishiya ba amma ta zauna da facaloli wadda har yanzu suna kishin sauri da ita. Koda Jafar yazo ɗaukarta sosai yaga ta sake ba kamar lokacin daya kawota ba, sai yaji farin ciki da yaga ta fara dawowa dai-dai........

PAGE 68

*Logas Nigeria*

Zaune take bakin gado kanta a ƙasa tana share hawaye harda jan majina.

A hankali ta ɗago kanta jin an buɗe ƙofar ɗakin an shigo.

"Dan Allah Aunty Badi'a miye nayi ma Aunty Zubaida ne da bata amsa gaisuwa ta?"

Badi'a dake mata kallon tsaf ta sauke lumfashi mai nauyi ta ƙaraso ta zauna a kusa da ita tana dafa kafaɗarta ta ce.

"Ai kinfi kowa sanin abunda take so kiyi, amma kike ƙoƙarin watsa mata ƙasa a ido"

Ɗagowa Mubeena tayi da sauri tana kallon Badi'a hawaye na zubar mata ta ce.

"Wani fa take so na aura, mai mata har biyu fa"

Badi'a ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai ta ce.

"Kin kuwa san waye Doctor Nura Mubeena?, miye idan yana da mata har biyu, dan kinzo ta uku miye a ciki?, gobe dai zaizo ki gansa karki sake kiyi masa wulaƙanci ko ki nuna cewar bai miki ba, dan zaku ƙara samun matsala ne da Haj"

"Amma....

"Kinga shawara ɗaya zan baki karki sake wannan damar ta wuce ki, dan koni da ace ni ce Doctor Nura ya nuna yana so ba ƙaramin daɗi zanji ba, amma sai ya nuna ke yake so daga ganin photonki Haj ta ɗora ki a status nata yayi mata maganar shifa yaga mata, ai wallahi kinyi sa'a, bafa ƙasar nan yake aiki ba a can ƙasar India yake aikinsa, amma matansa duk suna nan Lagos kowacce yana tafiya da ita ne idan lokaci yayi, bare ke da wahala yabarki a nan"

Ita dai Mubeena kanta a ƙasa tana jin yadda jikinta ke daɗa yin sanyi, yaya zatai dole ne ta amince ko bata so.

"Ni dai na baki shawara a kyauta, ya rage naki kuma amfani da ita ko kuma ki watsar"

Badi'a ta faɗa tana miƙewa ta fice mata daga ɗakin.

To idan ma bata amince ba ai tayi butulci ga Aunty Zubaida, babu fa abunda zata ce tana so Aunty Zubaidar batai mata shi ba, wani abun ma tun kamin ta ce tana so zata ga anyi mata shi, dan wannan buƙatar tazo mata sai ita kuma ta kasa mata ita?, ai bata kyauta bama kwata-kwata, gashi yanzu hatta su Inna hutawa suke ta dalilin Aunty Zubaida ɗin.

Tunaninta ne ya katse jin ƙarar shigowar kira a wayarta dake kusa da ita. Sauke lumfashi kaɗan tayi tana kallon cikin wayar ganin number Inna ce yasa kawai taji gabanta ya faɗi.

Kar dai ta samu labarin bijirema Aunty Zubaida da take so tayi?.

Bamai bata amsa dan haka ta ɗauki wayar kawai jiki a sanyaye.

Ai ko tana ɗaukar wayar taji Inna ta fara rufe ta da faɗan da tunda take bata taɓa mata shi ba.

"To bari kiji Mubeena idan har ni ce na zuƙunna na haifeki wallahi idan har baki amince da abunda Zubaida take so ba to duniya ban yafe miki ba"

A zabure Mubeena ta miƙe bata sani ba ido waje ta dafe ƙirjinta baki buɗe tsabar mamakin furucin Inna a kanta.

Baki na rawa Mubeena ta ce.

"Inn....Inna....Inna miya kawo wannan maganar dan Allah kayi hakuri?"

"Ni dai na faɗa miki. Ashe baki da hankali ban sani ba Mubeena?, baiwar Allahn nan kullum ƙoƙari take taga ta ingata rayuwarku tayi kyau shine ke tana ƙoƙarin miki gata amma kina son nuna mata ita bata isa dake ba kenan?, kin gama nuna mata cewar ba ita ce ta haife ki ba, to bari kiji idan kika saɓama Zubaida tamkar ni ce kika saɓamawa. Ke ko ma wani abu baki ji ba dan Allah?, har zaki buɗe baki ki ce ma Zubaida wai baki son wadda ta zaɓa miki dan ubanki dan kawai yana da mata biyu ki wani ce ke baki sonshi?, idan ba'a auren ke za'a aure ki ne?. Yanzu baga ƴar uwarki Na'ima ba, ita tana son Musa ne lokacin da aka aura mata shine?, amma yanzu ba sai tashin zance ba, komai ya wuce tana son mijinta, tayi hakuri ta rungumi ƙaddara gashi komai yazo ya wuce a ɗan ƙanƙanin lokaci, hatta Musan yanzu sai abunda Na'ima ta ce yake yinsa, ya shiryu ya zama nitsatstse son kowa, kuma arziƙinsa sai ƙara haɓɓaka yake, har gida ya sake masu mai kyau, ke bana ma Zubaida ke ce min zata biya mana Saudia nida su gaba ɗaya muje, ke hatta Iya wacce a da take jin haushinmu yanzu dole ta sakko take binmu sauda ƙafa, duk da ba haka taso ganinmu ba, wani lokacin idan abun ya dame ta zauna tayi ta mita kenan wai an mallake mata jika sai abunda muke so shine yake yi, kuma duk ba albarkacin Zubaidar muke ci ba?, shine ke kike ƙoƙarin mana baƙin ciki wato?"

"Dan Allah kiyi hakuri Inna insha Allah na amince da zaɓin nata"

Tana jin lokacin da Inna ta sauke wata ajiyar zuciya tana sake ce mata.

"Yawwa ƴar albarka, kuma kije ki bata hakuri yanzun nan, saboda nima Badi'a ce ta kira ni take gaya min, domin ita bata ma nuna min wani abu na faruwa ba, kije ki bata hakuri ki kuma gaya mata kin amince kinji ko?"

"Insha Allah Inna yanzu zanje"

"Yawwa to Allah yayi maku albarka. Kuma zamuyi magana ma da ita domin dama ta ce min idan kuka zo bikin naki zata tafi da Khadija itama kinga lokacin an kauda ki kema, sai Khadijar kaɗai ce a gabanmu itama, duk dai Iya sai masifar kinƙi dawowa take yi, tayi-tayi Musa wai yaje ya dawo dake amma ko sauraranta ma bayayi yanzu daga shi har Mahaifin nasa yanzu sun daina jin maganarta, kin san idan akaga kana dashi yanzu sai kikaga anayi da kai, to kusan hakan ke faruwa yanzu, karki so ganin dangin Mahaifinku yadda suke mana yanzu, amma ina kallon kowa ne dan nasan badan Allah suke yi ba"

Cikin jin haushinsu Mubeena ta ce.

"Wallahi Inna badan Allah suke yi ba, dan kawai yanzu sunga Allah ya buɗa mana ne. Kuma Inna dan Allah ki yarda mana ki koma gidan da Aunty Zubaida ta saya miki mana, ga gida an sai miki mai kyau amma kince wai ba yanzu ba kinƙi ki koma"

Daga can Inna ta saki ƴar dariya ta ce.

"Bawai naƙi na koma bane Mubeena, ina ɗan jiran wani abu ne, amma dole na tashi mana, dama ai zamanku ne nake yi a gidan nan, da badan babu ku ba ai da yanzu bana cikin gidan nan, duk lokacin dana ga aurenki naga an ɗauke Khadija to nima ranar zamana a gidan ya ƙare insha Allah"

Mubeena ta sauke ajiyar zuciya tana sakin murmurshi kaɗan itama ta ce.

"Na gane Inna"

Inna na saka mata albarka sukai sallama tana sake jaddada mata ta je tabawa Aunty Zubaida hakuri kuma karta sake wani abu irin wannan ya sake faruwa.

Bayan sun gama wayar ta sakko ƙasa jikinta a sanyaye saima taji kunyar zuwa inda Aunty Zubaidar take, domin wancan lokacin data kirata tana mata bayanin wadda zaizo ganinta shine kuma ta zaɓa mata a matsayin miji bata ɓoye mata komai ba hatta aikinsa da kuma matansa, a lokacin kwata-kwata Mubeena batai shawara ba ta yanke hukunci nan take wai ita fa wallahi bazata je ta auri mai mata har biyu ba, ita taji ma koma waye tun kamin ta gansa bai mata ba ta tsane shi, ta rinƙa kuka tana faɗama Aunty Zubaida hakan. Lokacin kyaleta kawai Aunty Zubaidar tayi, ta ɗauka ko zata sakko ne, sai taga da an mata maganar zuwansa sai yarinya ta botsare, ganin fa kamar da gaske take zai iya zuwa ta soke abun yasa Aunty Zubaida fara nuna mata fushinta akan abun, ta daina amsa gaisuwarta idan ta fito waje sai Aunty Zubaida ta tashi tabar mata wajan, ganin fa abunda ke faruwa yasa Mubeena cikin tashin hankali sai ta rinƙa kuka idan ta gaida ta bata amsa ba kota zo kusa da ita ta tashi.

Yanzu ma a parlo ta isketa ita da Badi'a suna ƙirga wasu kuɗaɗe.

Ganinta yasa Aunty Zubaida ci gaba da abunda take yi bata ma nuna ta ga fitowar tata.

Mubeena jiki a sanyaye ta zauna a ƙasa kusa da ita sosai ta kira sunanta a hankali, ai ko ɗagowa batai ba bare ma tasan da wata halitta a zaune kusa da ita. Sai Mubeena ta haɗe wani miyau bushashshe a maƙoshinta, to dama haka Aunty Zubaida take idan tayi fushi?, lallai kam bata da daɗin sha'ani idan har ka bari ta ɗauki zafi dakai, yo ita duk sai taji duniyar ma ta mata zafi, gaba ḍaya garin Lagos sai taji ta gaji dashi sai ta fara jin gida kawai take son komawa kusa da Innarta.

"Aunty dan Allah kayi hakuri"

Again bata tanka mata ba, ganin hakan yasa Mubeena fashewa da kuka, sai Badi'a taji tausayinta ta dubi Aunty Zubaida zatai magana ta ɗaga mata hannu tana cewa.

"Badi'a zakiyi abunda ke gabanki ne ko kuwa zaki tsaya wata maganar da bata da amfani?"

Shiru tayi kawai tana sadda kanta ƙasa.

Kamo ƙafar Aunty Zubaida Mubeena tayi tana kuka ta ce.

"Dan Allah kiyi hakuri ki daina fushin nan dani, wallahi na yarda na amince da auren nasa"

Nanma bata ɗagowa ta kalleta ba danta ɗauka ko wasa ne take mata dan ta dawo ta sakko kawai ta faɗa ne ba har cikin zuciyarta ba.

"Allah da gaske nake Aunty na amince ko yanzu a ɗaura auren idan har haka kike so na yarda na amince"

Sai lokacin Mubeena taga ta tsaya da abunda take yi tana juyowa ta fuskanceta ta ce.

"Mubeena bana son wasa a cikin al'amarina, wanene yaje ya tilastaki amincewa ko kuwa radin kanki ne kika ga dacewar hakan?"

Girgiza kai tayi da sauri ta ce.

"A'a Aunty dacewar hakan na gani, kuma naga ai bazaki taɓa zaɓar min abunda zai cutar dani ba, naje nayi tunani ne abunda nayi miki ban kyauta ba, kiyi hakuri bazan sake ba wallahi"

Saita shiga sauke ajiyar zuciya tana ɗan sakin fuskarta da murmurshi kaɗan ta jawo hannun Mubeena ta zaunar da ita kusa da ita ta ce.

"Tom shikenan Allah yayi miki albarka, kuma gobe Doctor Nura zai shigo ƙasar, ina saka ran goben zaizo ganinki, idan kika gansa ma na tabbatar zai miki, Doctor Nura ba irin mutane normal da kika sani bane, ke bari na gaya miki Doctor Nura babu wata ƴa macen da zatayi tozali dashi ta ce bai mata ba, sai dai idan bata samu ba"

Murmurshi Mubeena ta saki tana jin kwanciyar hankali a yanzu da aminta da abun har cikin zuciyarta, sakkowar Aunty Zubaida daga fushin da take da ita sai yasa ta jin daɗi da sakewa sosai, da duk a takure take a gidan sai kace wata marainiya.

"Wallahi Aunty da kika daina fushi dani har naji gidan ya fara min daɗi, duk ba daɗi da gaba ɗaya"

Aunty Zubaida na murmurshi ta ce.

"Ai ko da bawai fushi nake dake ba, domin fushin nawa bai kai har zuciyata ba, kawai ina nuna miki hakan ne dan ki gane kuskuren da zakiyi ma kanki a nan gaba shine yasa kawai nake nuna miki kamar fushi nake dake, amma ni ban taɓa fushi dake ba"

Rungumeta Mubeena tayi tana jin wani sanyi har cikin ranta, tana jin ɗuminta kamar na Mahaifiyarta, dan jinta take kamar Inna ce ta rungume, domin Aunty Zubaida basu da banbane da Inna banbancin kaɗan ne kawai, amma kama ta jini har muryarsu kusan iri ɗaya ce, dan wani lokacin idan tayi wani abun Mubeena har mamaki take domin sak koma mata take kamar Inna ce ta gabanta.

Itama tana murmushi da jin farin ciki tayi mata sauki a jikinta, tana jin daɗin amincewar Mubeena ɗin, domin harga Allah tana so ne tayi masu gatan da har idan babu ita baza su sake tagairaya ba a rayuwarsu, tana su ta inganta rayuwarsu ne sosai ta gyara kuskurenta na barinsu da tayi a baya, duk da a bayan Mahaifiyarsu ce taja koma miye ya faru, ita ta guje ma auren Mahaifinsu domin guje mata wahala, amma taƙi, sai gashi wahalar dai da take guje mata da tozarci saida abun ya risketa, amma idan ta tuna rabon su Mubeena ne yakai Inna aurensa sai taji kwata-kwata batai dai-dai ba barinsu da tayi harta manta dasu, har sai lokacin da ita kanta Innar ta nemi inda take, duk da dai-dai lokacin itama take shirye-shiryen zuwa har garin domin neman ƴar uwarta sai gashi ita ta fara nemo ta, shi yasa ma lokacin bata wani ja ba suka yafe ma juna, cike da so da ƙaunar junansu da kuma kewar junansu da sukai, shi yasama data faɗa mata ƙudurinta na kawo mata Mubeenar cikin murna da farin ciki ta ce a kawo mata ita kawai..........

PAGE 69

*HAJA POV*

Cike da wani irin farin ciki yake dubanta ya rungumota a jikinsa yana shaƙar ƙamshin jikinta ya dafa cikinta yana cewa.

"Da gaske kike my dear?"

"Yeah haka Doctor ya tabbatar mana"

Wata irin ajiyar zuciya taji ya sauke yana sake rungumeta, sai kace wadda ba'a taɓa ma haihuwa ba, sosai taga farin ciki a cikin idonsa wadda ya bata mamaki.

"Amma please ranka ya daɗe bana so kowa yasan ina da cikin nan please"

Ɗan sakinta yayi yana ware idonsa akanta ya ce.

"To why?"

"Hmm haka kawai dai ina so sai idan ya fito mutune sun san dashi kawai please"

"Shikenan ban san mi kike nufi da hakan ba, amma shikenan ba wadda zai sani"

Jawota yayi suka zauna akan bed tare yana shinshinar wuyanta da alama yayi tsananin kewarta ne dama sai gashi dawowar tasa ta kasance ita ce keda miji.

Tana cikin jikinsa ta ce.

"Ni ko ranka ya daɗe ba Abeed ne ya dawo ƙasar nan ba, naga sai hidima ake a cikin gidan nan?"

"Yeah shine ya dawo, amma bai ƙaraso gidan nan ba, a gidan Hajiya ya fara sauka, ita ce ta fara tarbarsa, suma basu san zai fara sauka can ɗin ba ai da duk basuyi wannan haukan da suke yi ba, shi bai cika son abubuwa da suke masa bama na tarbar tasa"

Jinjina kai Aunty Haja tayi kamin ta ce.

"Amma ranka ya daɗe mi yasa ni ba'a sanar dani da wuri zai dawo ba?, banfa sani ba"

Sauke lumfashi kaɗan yayi yana sake matseta a jikinsa ya ce.

"Kinga dai bana gida nima, bansan ma da dawowar tasa ba, wani lokacin haka yake dawowa ba wadda ya sani, suma ina mamakin yadda akai suka san zai dawo ɗin, Abeed da kike ji da gani wani irin murɗanɗɗan mutum ne, tunda matarsa ta rasu ya ƙara zama wani iri, anyi-anyi ya fitar da mata ta sake wani auren amma yaƙi, duk dai Hajiya ta fara gajiya da zaman nashi a haka ta ce idan ta samu mata zata aura masa ita kawai koda baya so"

Farin ciki ne kaɗan ya samu Aunty Haja amma saita shanye tana addu'ar Allah yasa ƙanwarta ta ce Hannah zata zama matar tashi.

A nan saida Alhaji ya sauke mata duk gajiyar daya kwaso dama yayi kewarta, kuma da tafiyar tashi saida tasha gyara dama tasan ita ce zata amshi miji, shi yasa a sati biyun da yayi baya gidan ta dage da gyaran jikinta, ai ko taga yadda Alhaji ya sake ruɗewa yana mata sanbatu dasa mata albarka.

Washe gari da dawowarsa ya kawo mata kyautar wata jifgegiyar Mota mai azabar kyau, ranar saida Aunty Haja tayi kuka tsabar daɗi saboda dama gaba ɗayansu suna da Mota ita ce kaɗai bata da Mota a cikin gidan. Abunda yasa Haj Saratu ta kusan tayar da fitina ai ko Alhaji yayi mata mugun gargaɗin idan ta ce zata tayar masa da hankali to zai mata abunda bata tunani, danya lura wani lokacin tana abu kamar marar lissafi, Mota ce ya sai mata ai ita matarsa ce kuma duk matsayinsu ɗaya a

37 / 47