Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   47 / 47

138K to 140.3K   out of 140.3K words

yayi kwari, dan gida har Abeed ya kira ya sanar da halin da ake ciki.

Murna dai wajan dangi da abokan arziƙi sai kiran waya suke suna ma Hannah barka.

Surayya kam ranar da suka samu labari ita da Haj Saratu kwana sukai cikin baƙin ciki, dan yanzu ko magana basa yi da Aunty Haja kowanne harkar gabansa yake.

Dole ƙanwar naƙi Surayya ta fitar da wani saurayinta dake mugun sonta, dama sai lallaɓata yake taƙi amincewa dashi. Haj Saratu ba haka taso ba amma Surayya ta riga da fitar dashi dan idan ta ce zata tsaya jiran Abeed tofa zata mutu ne babu aure.

Gaga-gaga rayuwa ta ci gaba da gudu dan yanzu har cikin Hannah ya kai wata biyar sai lokacin suka fara shirin dawowa gida.

Lokacin har anyi bikin Surayya sai dai suka ji labari, Hannah sosai tayi murna tana kuma taya ta murna data ƙale mata mijinta.

Lokacin da zasu dira Nigeria a filin jirgin dake Katsina dan kai tsaye Katsina suka sauka.

Kusan gaba ɗayansu ne suka zo tarbarsu, harda Maryam ai ko Hannah harda kukan murnar ganin yadda ƴan uwanta kusan gaba ɗaya suka zo tarbarta, cikinsu Aunty Sa'a ce babu da Fannah dan suma sunyi nisa ne shine yasa.

Cike da murna da farin ciki suka nufi gida kai tsaye gidan Hajiya suka sauka dan Hajiya ta ce wajanta Hannah zata zauna.

A part ɗin Abeed dake gidan suka sauka.

Kwanansu biyu Hannah ta fara ziyarar ƴan uwa babu gidan da bata je ba tare da Abeed suke zuwa kullum yana tare da matarsa.

Satinsu biyu ta shirya taje gida wajan Ammi ta kwana biyu ta dawo Ammi sai murna take ganin Hannah cikin kwanciyar hankali harda rabo a jikinta.

Abeed da kansa ya ce zata je har Abuja gidan Fannah harda shi akai tafiyar, tare da Motoci na jami'an tsaro, kwana ɗaya sukai a Abuja suka dawo, sosai Fannah tayi murna da zuwansu, Hannah taga yadda Annur ke nuna kulawa da so wajan Fannah ɗin, ita kanta yanzu Fannah tana son mijinta, sosai Hannah tayi farin ciki ganinsu a hakan, cike da kewar juna suka baro Abuja, daga Abuja suka tsaya Kano gidan Aunty Sa'a, suka yini suka dawo ita tayi murna da ganin Hannah a haka da kewarsu itama suka baro gidan suka dawo Katsina.

Kwana biyu suna hutawa ko nan da waje baya bari ta fita saboda kwana biyu suna tafiye-tafiye.

Ya so su koma wajan aikinsa amma Hajiya taƙi dan ta ce har sai Hannah ta haihu tayi arba'in sana zasu koma, badan ya so ba ya aje tafiyar har sai lokacin da matarsa ta sauka, dan yanzu cikin nata ya shiga wata na takwas sosai yayi wani irin girma dan yanzu da kyar take tashi, ba inda take zuwa daga wajan Hajiya sai part ɗinsu nan ne kaɗai take zuwa ko awon ciki sai dai azo gida ayi mata shi, tashi da kyar zama da kyar, sosai Abeed ke tausaya mata dan ji yake kamar ya ɗauke mata cikin saboda duk ta zama wani iri fuskarta ita kanta ta kunbura duk kammaninta sun sauya, mutane har sun fara zargin ko dai ba ɗa ɗaya bane a cikin Hannah ɗin saboda girman da yayi, Likitoci dai basu ce masu komai ba kuma Abeed ɗinne ya nuna basai an faɗi ga abunda zata haifa ba kawai a bari aga Ikon Allah, danshi bai cika yarda irin wa'innan abubuwan ba.........

PAGE 79

*MUBEENA POV*

Zaune take a jikinsa tana murmushi a hankali ya ɗan ɗago yana kallonta.

"Yaya dai Ginbiya?"

Ɗan taɓe baki tayi tana gyara zamanta akan cinyarsa ta ce.

"Wai yaushe zamu koma Nigeria ne?"

Ta ƙare maganar tana kwaɓe baki.

Dan kusan watansu shidda da tahowa ƙasar India, abubuwa da yawa sun faru a wata shiddan nan, ciki harda ɓari da Mubeena tayi na cikin data fara samu bai zauna ba, tasha wahala danma a nan India abun ya sameta, kuma sosai doctors wadda suka san aikinsu suka bata kulawa dan har wankin ciki akai mata, tun lokacin dai bata ƙara ɗaukar wani cikinta ba.

Sai ta ɓangaren Inna tuni Inna ta koma nata gidan wadda Aunty Zubaida ta saya mata, Iya ranar harda kukanta wai karda Inna ta tafi ta barta, ita idan ta tafi ta barta ina zata saka kanta?, tausayin Iya ya kama Inna yasa ta cewa Iya idan har taga zata iya zama da ita to zasu iya tafiya tare.

Ai ko ranar harda rawa Iya tayi, a tare suka tare a sabon gidan Inna mai girman gaske, kuma sosai suke rayuwarsu cike da girmama juna.

Aunty Zubaida arziƙi nata cin uwar nada, dan wannan shekarar ta biya ma Inna harma Iya aikin Hajji zasu je tare, harda Musa da kuma Na'ima Khadija dama tare zasu tafi da Badi'a.

Ita dama Mubeena sunje Umara ita da Doctor Nura saida suka fara zuwa Umara sana suka dawo India.

"Zamu koma mana, amma sai kin haifa min yara"

Kukan shagwaɓa ta saki tana bubbuga ƙirjinsa ta ce.

"To bakaƙi kamin cikin ba"

Dariya ya saki yana kamo fuskarta ya ce.

"Ohh ni ne ma naƙi nayi maki cikin ko?"

"Uhm yo eh man, kayi min mana ka dage"

"Hhhh to shikenan my Ginbiya zan dage da haƙar rijiyata har sai nayi miki cikin"

Murmurshi ta saki tana ɓoye fuskarta a ƙirjinsa dan sai yanzu taji kunya ta rufeta ma da maganar datai na yaƙi mata ciki.

Murmushi ya sake saki yana ƙara mata masauƙi a ƙirjin nasa.......

**************** Ta ɓangaren Shamsiyya dole ta daina yada maganganu marassa daɗi saboda Hajja yanzu bata ji bata gani akan yaran Mimi da ita kanta Mimin.

Itama watan haihuwar na tsayawa ta koma gida kusa da Mami.

Ranar wata asabar ta tashi da naƙuda koda aka je asibiti cewa sukai bazata iya haihuwa da kanta ba dole sai anyi mata aiki.

Hankali a tashe Mami tana gani aka shige da Shamsiyya ɗakin tiyata.

An shafe kusan awa nawa ba'a fito da ita.

Koda aka fito da ita tana ɗakin hutu akai masu jagora Office ɗin Doctor dake son ganinsu.

A nan ne yayi masu bayanin cewa ɗan data haifa baizo da rai ba.

Kuka ranar Mami tasha shi ita da Shamsiyya dan sun kwallafa rai da cikin nan, dansu a nasu tunanin da buri ma so sukai Shamsiyya itama ta samu ƴan biyu koma fiye da Mimi, sai gashi ƴa mace ce ta samu itama kuma bata zo da rai ba.

Shamsiyya kuka dai kam da kyar aka samu tayi shiru, duk sai jikinta ya sake yin sanyi dan susuku ta koma kamar ba Shamsiyya mai tsiwa da rashin kunya ba.

Gaga-gaga rayuwa na gudu Mimi da Shamsiyya sun dawo gida bayan komai ya wuce. Mimi ganin Shamsiyya ta sauya suna zaune ƙlau ne yasa ta ɗaukar ƴarta mace wacce taci sunan Hajja ta bata ita kyauta.

Ranar dai kuka Shamsiyya ta rinƙa yi tana ma Mimi kallon mamaki, dama akwai kishiyar da zata iya bawa kishiyarya kyautar yaro ba tare da jin komai ba?. Ta rinƙa roƙon ta yafe mata dan Allah. Inda Mimi ta ce mata ita dama bata taɓa riƙeta a rai ba, dan haka komai ya wuce karta damu.

Kowa yaji abunda Mimi tayi sai ya yaba mata, wasu surutu da zuga suka rinƙa kawowa wajan Mimi amma ta toshe kunnanta, hatta Mama bata ce mata komai ba sai fatan zaman lafiya data ƙara masu, Hajja ma taji daɗin abun, amma kai tsaye Hajja tayi ma Shamsiyya gargaɗi saura taci amanar da aka danƙa mata.

Sai kuma wani ikon Allah yasa ma Shamsiyya son yarinyar kamar ranta, hatta Mami ma son yarinyar taji kamar mi, su duka sai Ubangiji yasa masu ƙaunar yarinyar da tsananin sonta suke har cikin ransu.

Sai hakan ya ƙara haifar da zaman lafiya a tsakaninsu.

Sai dai yaran nayin shekara ɗaya da haihuwa aka fahimci macen na ɗauke da cutar Sikila, ranar da aka gane hakan Shamsiyya tafi kowa shiga tashin hankali kowa saida ya tausaya mata.

Danma Jafar Doctor ne kuɗin da aka fara kashewa wajan magunguna da allurar da ake mata duk asibitin da yake aiki ne suka ɗauki nauyinsa, dan haka komai sai ya rinƙa zuwar masu da sauƙi, amma duk lokacin da ciwon ya tashi kwana suke ba bacci gidan gaba ɗaya.

A haka suka ci gaba da yaruwa dai yarinyar sai ta kasance ita kaɗai ce bata saurin girma dan ƴan uwanta da aka haifesu tare su tuni harsun fara rarrafe ita ko bata fara ba sai dai jan gindi shima da kyar take yinsa, duk ta zama ƴar ƙarama da ita su ko sai girma suke idan ka gansu ma zaka iya rantsewa ba tare aka haifesu ba.

Sosai suke tausayama yarinyar bare ma Mimi wani lokacin idan ciwon nata ya tashi kwana take kuka a ɓoye itama.

Danma ana iya bakin ƙoƙari wajan kulawa da lafiyarta.

Yanzu tsakaninsu da Shamsiyya sai zaman lafiya ko baƙar magana basa ma junansu, yawanci ma kulawar da suka taru gaba ɗaya suna nunama yarinyar ne ya ƙara haifar masu da zaman lafiya a tsakaninsu.

Maryam ƙawarta sosai tayi murna da zaman lafiyar da yanzu suke a tsakaninsu, su Hajiya kam tunda hakan ta faru sai suka tattara suka dawo wajan Mimi, Shamsiyya taga abu, dole tasa ta ƙara hankali da mutane.

*****************Kusan gaba ɗaya ahalinsu Hannah ne dana su Abeed zaune a babban asibiti, wasu suna daga tsaye kowa ka kalla farin ciki ne kwance akan fuskarsa.

Domin Hannah aka kawo tun cikin dare tana naƙuda ita ce bata haihu ba sai gabanin asubahi tasha wahala sosai dan har ana shirin mata tiyata ma dan Abeed hankalinsa a tashe yake ganin wahalar da take sha yasa ya ce kawai ayi mata tiyatar, sai kuma Ubangiji yayi ikonsa ta sauka da kanta lafiya, ta samu yara biyu duk maza, manyan gaske yadda kasan ba haihuwar ranar ba, dan kowa ya gansu sai yayi magana kamar ba ranar suka fito duniya ba.

Gaba ɗaya ƴan uwa da abokan arziƙi sai zuwa ake asibitin.

Ganin yadda asibitin jama'a tayi yawa yasa Doctors sallamarsu kawai saboda dama ba wani abu dake damun Hannah daga ita har yaran suna cikin ƙoshin lafiya.

Dan haka kai tsaye gidan Hajja a ɓangarenta aka sauke Hannah.

Ranar suna yara suka ci sunan Mahaifinsu Hannah ɗayan kuma yaci sunan Mahaifinsu Abeed amma za'a rinƙa kiransu da sunayensu na Hassan da Husaini.

Sosai taron sunan ya tara jama'a da yawa su Fannah tun ana saura kwanaki biyu suna suka iso, itama da cikinta da baifi wata shidda ba, Maryam kam tayi nauyi itama dan harta shiga watan haihuwarta, dan kyar ma Fu'at ya barta tazo sunan nan danma Hannah ce, dan ko bikin Nihal da akai sati biyu da suka wuce bai barta taje kowanne irin party da aka shirya ba, gata babbar ƙawa, bikin ne kawai ya bari taje shima sai ranar da za'a ɗaura aure taje, Nihal nata masa tsiya.

Anyi suna an gama lafiya kowa ya watse ya koma nasa gidan.

Tana gama arba'in ta koma gidan Aunty Haja tayi mata gyaran jiki na sati ɗaya. Duk dama can Hajiya a nan ta fara gyarata itama da nasu dabarun.

Ana gama gyaran jiki ta fara yawan arba'in har Kano taje gidan Aunty Sa'a ta kwana ɗaya ta dawo, taje gidan Maryam dake jan ciki haihuwa yau ko gobe taje gidan Aysha ma dake ɗauke da ƙaramin ciki itama.

Dama tuni taje gidan Ammi dan a can ma tayi sati ɗaya, data je Kano kuma taje har wajansu Aunty Bintu.

Har gidajan su Hadiza saida taje da babban gidan.

Abeed ba yadda ya iya ne ya barta tana wannan yawon dan saida Hajiyarsu ta tsawatar masa dan da murje ido yayi ya ce ba inda zata je.

Bayan ta gama yawon arba'in suka fara shirin komawa ƙasar Malesia, dan anata nemansa wajan aikinsa, danma babba ne a wajan aikin shi yasa aka ɗaga masa ƙafa har tsawon wannan lokacin.

***************Tsaye take tana kallon yaran bayan sunyi bacci sun kwantar dasu akan gadonsu na yara.

Ji tayi an rungumota ta baya, a hankali Hannah ta sauke ajiyar zuciya tana juyowa gaba ɗaya tana fuskantarsa.

Ƙara jawota yayi jikinsa sosai har suna shaƙar lumfashin juna.

Ɗage mata gira ɗaya yayi hakan yasa Hannah sakin dariya kaɗan dan tasan yayi ƙoƙari ma yaushe rabonsa da ita tunda ta shiga wata na takwas da cikinta har zuwa yau da suka dawo wajan aikinsa. Tasan dama daren yau ai ba ɗaga ƙafa dan haka itama a shirye take ta shayar dashi zumar dayayi kewa a tare da ita.

A hankali Hannah ta jawo fuskarsa da hannunta tana lumshe ido ta haɗe bakinsu waje ɗaya, kusan a tare suka saki ajiyar zuciya.

Wani irin shan bakin juna suke daka kallesu kasan ba ƙaramar kewar junansu sukai ba.

Tsayuwar ma gagararsu tayi dan haka suna tsotsar bakin juna ya ɗauketa kamar baby sai akan bed.

Da wata irin soyayya mai tsafta mai tsayawa a zuciya da ruhi suka raya wannan dare cike da shauƙin juna tare da mararin junansu da tsantsar ƙaunar juna.

*END*

*Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Duka duka a nan na kawo ƙarshen wannan book ɗin nawa TAURIN KAI Darasin dake cikinsa Ubangiji ya bada ikon amfani dashi, akasin hakan kuma Allah ya bada ikon watsi dashi. Abunda na mance ban saka ba dan Allah amin uzuri mantuwa ce wata ƙila, dan adam azizi ne, sana iyaka abunda Ubangiji ya hore min na rubutu kenan*

*Ban yarda a sauya min labari ta kowacce siga ba saida izinina a kiyaye*

Ka biya ko ki biya ki karanta cikin salama ƴar uwa ko ɗan uwa naira dubu ne kacal 1k.

Account number 8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank.

Shaidar biya 08130479973.

*SADAUKAR*

*NA SADAUKAR DA WANNAN BOOK ƊIN GA MAHAIFIYATA ABAR SONA A KULLUM, INA SONKI MY MAMA UBANGIJI YA ƘARAMA KOWACCE UWA LAFIYA TARE DA FARIN CIKI MARAR YANKEWA I LOVE YOU KOWACCE MAHAIFIYA*

47 / 47