Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
dafawa da kwai data soya taji kamar motsin shigowar Shamsiyya Kitchen ɗin.
Dan haka juyawa tayi tana kallonta da mamaki, dan ko cire kayan bacci batai ba, sanye take da wasu kayan bacci riga da wando kai ka ce gidan mijinta ne nan ɗin ba zuwa kawai tayi ba.
Sosai Mimi ke kallonta sama da ƙasa tana jin wannan yarinyar dama da abunda ya kawota gidanta, da manufar data zo da ita, bawai haka nan kawai tazo mata gida ba.
Ganin zata ɗauki filet tana niyar itama zuwa a zuba mata indomi take nufi yasa Mimi sake kallonta a shaƙe ta ce.
"Kinga Malam wannan ɗin da kikaga na dafa nawa ne ni ɗaya iya cikina, dan haka bazai yiwu kizo gidana ba sana ace wai ni zan girka miki kina ci, hakan bazai yiwu ba, idan kinga dama ki tashi ki dafa da kanki amma wallahi ub*an kuturu yayi kaɗan na dafa dai kina zaune sai dai kici kawai, sana gyaran gidan nan shima daga yau zai dawo kanki ne, dan bazai yiwu kina cikin gidan nan ba bazaki rinƙa min komai ba"
Jinjina kai kawai Shamsiyya keyi tana ƙarema Mimi kallo sama da ƙasa ta wani taɓe baki ta aje filet ɗin data ɗauka ta juya kamar zata bar kitchen ɗin sai kuma ta dawo baya kaɗan tana nuna kanta ta ce.
"Ke nayi miki kama da wacce tazo miki aiki a gida?. To bari kiji ko tsinke baki isa na kauda miki ba, ai gidanki ne, ya zama bola mana ko a kwalar rigata, idan kin gyara ma kanki kikai mawa bawai ni ba, sana abinci da kike cewa san kira shi mijin naki kina ji kina gani zai turo min kuɗin da zan rinƙa sayen abinci har nabar gidan nan, idan naga dama kuma na tashi na shigo kitchen ɗin na dafa da kaina, daɗin abunma ai abincin Yayana ne ke kawosa ba daga gidan wani aka taho dashi ba mtswww"
Ta ƙare maganar tana sakin tsaki tabarta baki buɗe da mamakin daya kusa kasheta.
"Kai ni Shamsiyya na tsaya tana gaggaya min magana har haka?. Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"
Mimi ta faɗa tana jin wani irin tashin hankali akan zuwan Shamsiyya tun yanzu sun fara kenan?.
Abincinta ta dauƙa tana fitowa parlon babu kowa da alama tana ciki.
Zama tayi tana chakular abincin kwata-kwata ma sai taji ta kasa cin abincin damuwa ce sosai danƙare a cikin ranta.
Wayarta dake cikin bedroom taji kamar ƙarar shigowar kira.
Dan haka ta miƙe tsaye tana nufar bedroom ɗin jikinta a mugun sanyaye da lamar Shamsiyya dan taga abun nata azimun ne.
Mijinta ke kira dan haka ta samu waje ta zauna a bakin gado tana ɗaukar kiran bayan ta gaida shi muryarsa taji kamar da ɓacin rai a cikinta.
"Love miya faru tsakaninki da Shamsiyya kuma?, yanzu fa Hajja ta kira ni wai tunda kince bazaki dafa mata abinci taji ba ni na tura mata kuɗin masu damar da zasu isheta hidimar yau da kullum"
Wata ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara sadda kanta ƙasa zuwa yanzu kam tasan Hajja an shiga tsakaninsu ne, da wuya idan haka su Shamsiyya suka bar Hajja.
"Ina magana kinyi shiru Love?"
"Mi zance D?, kawai ina so ka sani cewar bata isa na dafa tazo ta zuba taci ba wallahi bazai yiwu ba, daga taci kenan saita kwanta shine ya kawo ta?, kaima kanka kasan bazan yi ba wallahi yarinya tun yanzu ta gama rainani ina faɗa tana faɗa"
Daga cikin wayar taji ya saki hucin lumfashi mai zafi wadda har tana iya jiyo sautinsa.
Muryarsa da wani irin ɓacin rai sosai ya ce.
"Kiyi hakuri Love, zan tura mata kuɗin domin koni kaina bazan goyi bayan hakan ba, amma dole ne na dawo zuwa jibi garin"
"Kaga D ka bari please ka gama iya kwanakin daka riga ka ɗaukarma kanka zakayi, kar wannan abun yasa ka katse aikin dake gabanka ka taho, kuma koda ka taho ɗin ba abunda zai sauya fa"
Ta faɗa dan tasan bazai sauya ɗin ba, tunda har abun sun haɗasa da Mahaifiyarsa ne, wadda sun san bazai taɓa mata gaddama ba.
Sallama sukai kawai Mimi na sauke wayar ta shiga kallon wani waje daban tana zurfafa cikin tunani sosai.
Sauke ajiyar zuciya tayi tunowa da Maryam, ita ce kaɗai zata kira ta faɗama damuwar ta tasan zata iya bata shawara kota kwantar mata da hankali.........
PAGE 26
*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*
"Ina jinki ya kuka yi dashi?"
Na'ima ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Inna da kyau ta ce.
"Inna dana gaya masa mamaki ma yayi, kamar yana zargin ko wani abu ne yasa muke neman number Aunty Zubaida ɗin, sai na ɗan gaya masa bafa komai kawai dai kece ke son sanin halin da Aunty Zubaidar ke ciki shi yasa ma ake neman number nata"
"To Allah yasa dai an dace samo number ɗin?"
"Eh Inna an dace ya ce wai amma number ɗin da kyar idan za'a iya samunta da ita, saboda wai yadda muke tunanin Aunty Zubaida fa ta wuce nan, dan yanzu ta zama mai kuɗi ganinta wahala yake ko a Lagos ɗin, duk dai ya ce yanzu gidan abincinta sai masu kuɗi ne kawai ke iya zuwa, amma dai mu gwada mu gani, ko Allah zaisa a dace, amma ɗazu dai na gwada kiran nata a layin Musan amma dai bata shiga ba gaskiya"
Na'ima ta faɗa tana ɗakko wayarta ta shiga number Aunty Zubaida ɗin tana miƙama Inna wayar gaba ɗaya.
"To ki gwada kiran nata mana yanzu ko Allah zaisa ta shiga ɗin"
(Hmm Ubangiji yasa ma karta shigan)
Mubeena ta faɗa a zuci tana kallonsu gaba ɗaya dan ita kwata-kwata ma an gama da ita wallahi, wai Lagos za'a kaita?, sai kace wacce ta zama annoba a cikin dangi?.
Tunaninta ne ya katse jin kamar number da Na'ima ta latsa kiran nata kamar fa tana shiga.
"Lahhh Inna kamar fa tana shiga naji?"
"Nima haka nake ji Allah yasa dai ta ɗauka"
Da amin Na'ima ta amsa tana jin daɗi har cikin ranta.
Mubeena taɓe baki tayi haka kawai taji gabanta na faɗuwa da shigar kiran.
Khadija ma tashi tayi tabar ɗakin dan ita ma ba wani murna take da tafiyar da Mubeena zatai ba.
Sai dai harta katse ba'a ɗauka.
Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya daga Mubeena ɗin harsu Innar.
"Bata ɗauka ba ko?"
"Eh Inna gashi nan ma ta yanke ba'a kai ga ɗauka ba, dama shigar kiran kamar network ɗin sai a hankali da kyar take shiga"
"Sake kiran nata muga"
Sake danna kiran Na'ima tayi, wannan lokacin kuma kwata-kwata ma ba alamar number ɗin na shiga, dan shiru ma kake ji, daga ƙarshe kiran ya tsinke.
"Ba'a ɗauka ba Inna"
Inna ta sauke lumfashi mai zafi tana jinjina kai kamin ta ce.
"Za'a ɗauka insha Allah, a bari zuwa anjima sai a sake gwadawa"
"To wai Inna mi yasa zakuyi ta kiran ta?, ai kamata yayi ace ita ta neme ku tunda nasan tabbas tunda har number ta shiga zata ga kiran naku ai, ba sai ta biyo kiran ba?, sai kuma ace kune zaku sake wani kiranta?"
"Mubeena bana ce karna sake jin bakinki a nan ba?"
Turo bakin tayi tana tashi tsaye tayi hanyar waje tana ƙunƙunin faɗin.
"Nifa naga Inna kamar ma kin fara tsana ta a gidan nan, daga ina neman mana ƴancinmu sai kuma ya zama laifi?"
"Mi kike cewa?"
Saita tsaya tana girgiza kai da sauri tana cewa.
"Ni Ya Na'ima mi kika ji na ce dan Allah?"
"Ai ji nayi kina magana ƙasa-ƙasa"
"Toni ba abunda na ce, bada ma ku nake ba"
Ta faɗa tana neman ficewa daga ɗakin kawai Iya ta sawo kai ciki, saura kaɗan suyi karo da juna.
Da sauri Mubeena ta tsaya tana kallon Iya.
"Ke marar kunya da'allah matsa ki bani guri"
Tsayen Mubeena take bata matsa ba, ba kuma alamar zata matsa ɗin, sai kallon Iya take da wani kalar taƙaicinta, dan ji take ai duk ita ce silar da za'a kaita Lagos duk ita taja mata.
"Baki ji ne ina magana marar kunyar banza?"
"Nifa Iya gaskiya abunda kike min yafa fara kaini bango"
"Tooo, ko zaki dake ni ne fitsararra marar kunya?, tunda har na kaiki bango ai duka ya kamace ni ko?"
Bakinta baya shiru har zata buɗe baki tayi magana dan ko kaɗan yanzu bata tsoron Iya bare barazanarta. Inna ce ta kwatse ta da cewa.
"Zaki matsa ne ko sai nazu wajan na kikkifa miki mari?"
Da sauri ta waigo tana duban Inna datai maganar da mamaki. Kai yaufa taga Innar zafi ta ɗauka da ita, dan taga da tayi magana kaɗan sai Inna ta taso mata da wata magana marar daɗi, kuma ita dai iya saninta basa haka da Innar, dan faɗa tana mata amma ba irin wannan ba.
"Kika tsaya kina tsare ni da ido"
Inna ta sake faɗa tana miƙewa gaba ɗaya kamar a zafafe, Na'ima ma miƙewar tayi da sauri tana kamo hannun Inna dan tsaf zata iya ɗauke Mubeena ɗin da mari yadda take cike da ita yau ɗin.
Matsawa kawai Mubeena tayi mamaki kam ya gama kashe ta.
Iya ta wani taɓe baki tana kallon Inna ta nunata da yatsa tana faɗin.
"To nan har wani abun arziƙi kikai ne?, ace ƴarki kina ki kina gani ta tsaya tana min rashin kunya tun farko baki tsawatar mata ba saida ta fetsare ta gagari ub*an kowa?"
"Haba Iya kinga fa faɗan datai mata yanzu"
"Keee kema za'a fara koya miki rashin ta idon?"
Iya ta faɗa tana nuna Na'ima da hannu.
"Na'ima karna sake jin bakinki kinji na gaya miki?"
Ɗaga kanta kawai Na'ima tayi tana haɗe wani miyau a maƙoshinta tana jin wani irin malolan baƙin ciki daya tokare maƙoshinta, dan itama fa tana jin zafi da kishin abunda ake ma Innar tasu, kawai suna kauda kaine Mubeena ta fisu rashin haƙuri dama, ita bata iya jure wulaƙanci shi yasa ma Iya ke ganin ta fetsare yanzu, amma ko ada can Mubeena ɗin a haka take tana maida ma Iyar magana kawai na yanzu ne yafi tsamari.
"Iya yanzu dai kiyi hakuri. Ke kuma Mubeena ki bata hakuri yanzu na ce"
Mubeena ta sauke ajiyar zuciya zatai magana Ya Na'ima ta ce.
"Kinga ki bada hakurin da akace kawai ki wuce inda zaki"
"To ni Ya Na'ima miye ma nayi da har zan bata hakuri?"
"Kinji ko?, na ce kin dai ji ko?, ai wannan yarinyar mai ido a tsakar ka saita gagare ki wata ranar, wannan kinga wannan da kike ganinta Allah dai ya kyauta, amma ke Allah dai ya wadaran....
"Haba Iya karki yi mata baki mana, kalmar Allah ya shirya kawai ta wadatar Iya bawai a zagi mutum ba ko a aibata shi ba"
Inna ta faɗa tana kallon Iya data saki baki tana riƙe bakin da hannunta.
"Ah ba shakka, ni zaki gaya ma haka?, to bazance hakan ba, asa kaina gabas a yanka mtswww"
"To kiyi hakuri. Ke kuma fice a nan wajan kibawa mutane waje"
Fita Mubeena tayi tana ɗage kafaɗarta alamar ko a jikinta ma.
"Ohh ni ƴaso jikar mutum huɗu, ke yanzu a haka kike bawa ƴaƴan nan tarbiyya dama, suyi abu ko dukansu ban taɓa ganin kin kawo hannu kinyi ba, sai faɗa a baki, ai dole su raina mutane"
Shiru su duka sukai mata dan abun Iya ya fara wuce na hankali sai dai ayi mata uzuri kawai rikicin tsufa ke damunta.
"Ke ni bama wannan ba, kunyi magana da Musa kuwa?"
Cewar Iya tana maida dubanta ga Na'ima.
Na'ima da mamaki ta dubi Iya ta ce.
"Iya magana kuma ta miye?"
"Au na manta, ban gaya miki ba shi yasa. Idan ya sake zuwa ki ce masa ya shigo gida ina son ganinsa zamuyi wata magana dashi ne, idan munyi ɗin sai kuji tukunna"
Ta idasa maganar tana wucewa daga ɗakin suka bita da kallo kawai.
"Tofa mi zata ce ma Musa kuma?"
Na'ima ta faɗa tana dawo da dubanta inda Inna take tsaye. Inna ta sauke ajiyar zuciya mai zurfi tana cewa.
"Waya ma sani Na'ima?, Allah dai yasa lafiya kawai ba wani abun take shirin kuma ƙullawa ba, dan nasan Iya bata abu haka kawai, yanzu haka da wata manufar neman nasa da take yi"
Inna ta ƙare maganar tana kaiwa ƙasa ta zauna tana sake sauke wata ajiyar zuciyar.
Zama Na'ima itama tayi tana dafa Inna ta ce.
"Inna ba wani abu insha Allah ki kwantar da hankalinki dan Allah"
Na'ima ta ƙare maganar tana bin fuskar Inna da kallo sosai, dan ta yanayinta ta gano harta shiga fargaba da maganar Iya data zo tayi yanzu taga tashin hankali akan fuskarta Inna data shiga yanzu.........
PAGE 27
"Yawwa yaran nan sunyi bacci Ammi ko?"
Cewar Aunty Sa'a suna fitowa tsakar gidan gaba ɗaya jin shirun yayi yawa.
Ganin Ammi ce kaɗai a tsakar gidan da alamar sun shige ɗakinsu sun kwanta yasa su Aunty Haja samun waje suka zauna, Aysha ce kawai babu dan itama bacci ne ya sake ɗauketa saboda ciwon kan da take fama dashi.
Ammi ma na zaunen gyangyaɗi kawai take jin maganarsu yasa Ammi wastsakewa tana sauke lumfashi kamin ta ce.
"Nima fa na fara baccin ne a zaunen nan da kuke gani, bacci nake ji sosai a ido na"
"To Ammi kodai zamu bari sai da safe ne?"
"Haba dai da safe Aunty Haja?, ashe kuwa kamar wa'incan yaran sun gama ji ne"
"To ai Maryam bacci take ji ne sosai kinga fa idonta cike yake da baccin da gaske"
Ta ƙare maganar tana nuna Ammi dake murje idon nata tana cewa.
"A'a kawai ku gaya min yadda kukai da kuka je wajan Malamin sai na tafi na kwanta nima, kuma ko kun samu ku huta haka nan"
"Yawwa Ammi munje, kuma tsakani da Allah kamar za'a samu nasara dai indai anyi yadda ya dace aikin daya banin, kuma yau harna ma fara ɗaya, dama aikin na tsawon kwanaki uku ne kawai"
"To masha Allah, ai indai kin gane yadda ake yi to ya wadatar niba sai an sake gaya min ba"
"A'a Ammi garafa ki sani, dan karma kiga ana abu ki tabbaya cewar miye wannan?, ko mi za'ai da wannan ɗin?"
"Shine ai Maryam gara kawai a sanar dake Ammi komai dan ki sani gaskiya shine dai-dai ma"
"To ina jinki Haja"
Ammi ta faɗa tana maida hankalinta sosai gareta.
Nan ta zayyane mata duk abubuwan da Mlm ya ce tayi da sauran abubuwan.
Ammi taja ajiyar zuciya tana jinjina kai ta ce.
"To saifa kunyi takatsantsan, dan wallahi kunga Hannah kawai ko zata iya ɓata maku aiki, tsaf ma kuga taje zata tone murhun idan har aka kuskure taji wannan shirin, sai ku kiyaye, ko ranar da za'a binne abun a aike su kawai subar gidan kamin su dawo kin gama binnewar"
"Kuma fa hakane Ammi"
"Ai hakama za'ai kawai Sa'a dan ni nafi ku sanin wacece Hannah ne shi yasa ma na faɗi hakan kawai"
Jinjina kai sukai a tare kamin Ammi ta miƙe jiki a sanyaye saboda baccin da take ji sosai ta ce.
"Ni zan wuce ɗaki sai da safe, ki tado Aysha ta dawo ta kwanta a ɗaki"
"Ammi ai Aysha tayi bacci a ɗakinmu sai dai ko yau Maryam ta kwana dake"
Aunty Sa'a ta faɗa.
"To yayi ai duk ɗaya"
Ammin ta faɗa tana shigewa ɗakinta.
Maryam ta juya zuwa ɗakinsu tana cewa.
"Bari na ɗakko wayana da sauran ƴan tarkace dan nima bacci ne a idon nawa wallahi"
Bin bayanta sukai suna magana ƙasa-ƙasa saboda dare ne sosai magana ta fiye tashi cikin dare.
"To sai da safenmu"
Maryam ta faɗa tana ficewa daga ɗakin ta barsu suna shirin baccin suma.
Washe gari da safe su Fannah ne suka fara tashi a gidan.
Dan Hannah tunda ta tashi da Asuba bata koma ba, dama haka take yi a kullum, idan ta tashi Asuba inda tayi sallah bata sake miƙewa sai haske ya fara, saboda tana karatun al'qurni har hasken rana ya fara fitowa kaɗan.
Kwanciya take so tayi saboda zuwa ƙarfe takwas tana da aikin yin Cake kusan na mutum uku kuma biyu kusan masu girman gaske ne, da alamar kamar na biki ne kamar a wajan dinner ake son amfani dashi.
"Na ɗauka bazaki koma baccin ba ai?"
"A'a zan ɗan kwanta zuwa ƙarfe takwas haka ko bakwai da rabi"
"To amma ba takwas naji sun ce zasu zo a amshi cake ɗin ba?"
"A'a Fannah na ce masu sai wajan goma za'a iya samunsa gaskiya. Yo yaushe na tashi ma nayi aikin gidan nan nayi masu cake ɗin duk a ƙarfe takwas kuma?"
Sauke lumfashi kaɗan Fannah tayi tana daga kwance suke maganar ta ce.
"Nima yau ina da masu ƙunshi nasan tun safe zasu zo, dan yau asabar akwai ɗaurin aure da yawa, kema nasan Cake ɗin nan kamar na biki ne zakiyi masu da alamar hakan"
Hannah zatai magana wayarta dake jikin chaji ta fara ringing.
"Waye kuma tunda safen nan?"
Hannah ta faɗa tana tasowa daga inda take kwance ta zaro wayar dake jikin chajin ta duba ganin number ce yasa ta ɗauka kawai da sallama.
"Eh to za'a iya samu, amma gaskiya sai zuwa da yamma haka wajan ƙarfe uku"
Hannah ta faɗa bayan ta gama jin abunda aka ce daga cikin wayar.
Daga cikin wayar aka ce.
"A taimaka dai kar ya akai uku sister, wallahi a wajan dinner za'ai amfani dashi, kuma dinner ɗin kusan ta ƙarfe huɗu ce bata dare ba, to so muke a gama shirya komai kamin ma ƙarfe biyun, shi kansa cake ɗin anfi so ya iso da wuri shi yasa"
"To abunda yasa gaskiya baiwar Allah ina da aikin yin Cake ne da yawa a yau ɗin, shi yasa ma na ce miki zaku samu ƙarfe ukun, shima kawai dan naji kuna sone sosai, dan gaskiya ma yau wa'inda na amshi Order nasu na ce nasu kaɗai zanyi a yau, koda wani ya sake kawowa bazan amsa ba, saboda aikin Cake yana