Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   38 / 47

111K to 114K   out of 140.3K words

wajansa, dan haka ta kama kanta, ranar harda sakar masa kuka tana faɗar ai dama Aunty Haja da asiri ta shigo masu gida ta gama da Alhaji, idan ba gamawa tayi dashi ba tunda ya dawo yake rawar ƙafa dan yasan dama ita ce da miji, taitai faɗar maganganu son ranta, yo a banza dan Aunty Haja tashi tayi tabar mata parlon abunda ya sake saka Haj Saratu jin baƙin ciki kenan.

Ga baƙin cikin Abeed ya sauka ƙasar amma ko saka shi a ido basuyi ba, duk irin abubuwan da suka shirya masa sun tashi a banza kenan.

Sai masifa take wai tsohuwa ta zame masu ƙarfen ƙafa.

Maryam data tsinci maganganun da take saki sai abun yaso bata dariya.

Ta shigo tana girgiza kai tana ɗan sakin murmurshi ta zauna kusa da Aunty Haja dake zaune a ƙasan kafet tana shan kankana, sai Fannah dake ɗan zaune kusa da ita tana shan kankanar itama.

"Mi ya faru naga kin shigo kina murmurshi haka?, sai ka ce wacce akai ma albishir"

"Hmm bafa wani albishir Aunty Haja, kawai mutuniyar taki ce keta sakin maganganun da bata gajiya ma dasu, ita ko bakinta baya ciwo ne?"

Taɓe baki Aunty Haja tayi tana gyara zamanta a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana cewa.

"Ina zata gaji kuwa ai tayi sabo ne"

"Hmm waifa ji nayi tana faɗan wai Hajiyarsu Alhaji taje ta riƙe Abeed miye da miye tsohuwa ta hanasu rawar gaban hantsi"

"Ahhh kaji wani iskanci irin na Haj Saratu, yo shida uwarsa sai yaƙi zuwa inda take?"

Aunty Haja ta faɗa tana riƙe baki.

"Shin kema kin faɗa dai nima haka na gani shine yasa ma nake dariyar nan haka, saboda maganganun nata ma dariya suke bani ni"

"Kanta ya fara kwance ne wata ƙila tana mancewa da Mahaifiyarsa na raye, amma ni ina mamakin ma yadda yake zaune a gidan nan"

Fannah ta faɗa tana mamaki.

"Ba abun mamaki bane ai, ita Hajiyar ce ta bada umarnin zamansu a waje ɗaya, ita dai Alhaji ya gaya min tun farkon tarewata a gidan nan cewa yaso itama ta dawo nan gidan saboda akwai shashinta a nan gidan babu abunda ba'a saka ba amma taƙi, ita bata son zama cikin matansa suga kamar ta takura masu ne, amma dai su shida Abeed zasu iya zama waje ɗaya, to shi yasa fa aka ware ma Abeed nasa ɓangaren a gidan nan, canma gidan Hajiya ɓangaren nasa yaso ma yafi a nan gidan da muka je gidan, shima gidan Hajiyar tasu ai ba ƙarami bane babban gaske ne dan inaga da kaɗan yafi wannan ma, gashi an zuba mata ma'aikata masu mata hidima"

"Ai Aunty Haja haka ake so wallahi sunyi dai-dai sun gama da duniya lafiya ai"

Jinjina kai Aunty tayi tana kallon Maryam datai maganar zatai magana Maryam ɗin ta sake cewa.

"Ni wai ina Hannah ne?"

Taɓe baki Fannah tayi tana cewa.

"Tana can ɗaki mana tana waya, wallahi ni sai nake ganin kamar alamar ta fara soyayya ne da wani fa"

Ido waje Maryam da Aunty Haja ke kallon Fannah.

"Ke Fannah bana son shirri fa?"

"Na rantse miki, wai bada ita nake kwana a ɗaki ɗaya ba?, kullum zanga tana chat tana murmushi wani lokacin harda su dariya take yi, idan ko aka kirata waya a toilet take shigewa ta daɗe tana wayar"

"Kan uba to ma yaushe hakan ta fara faruwa ni ban lura ba?"

Cewar Maryam da mamaki.

Aunty Haja dai tayi shiru dan ita abun mamaki yake bata sosai.

"Tashi ki kira min ita"

Cewar Aunty Haja.

Miƙewa tsaye Fannah tayi tana yin hanyar bedroom nasu.

Jim kaɗan sai gasu sun fito a tare Hannah na hararar Fannah ƙasa-ƙasa.

Zama sukai a ƙasa a tare, Aunty Haja ta shiga ƙarema Hannah kallo kamin ta ce.

"Abunda naji Fannah ta faɗa haka ne?"

Turo baki Hannah tayi kanta a ƙasa ta ce.

"Wane abu kuma Aunty Haja ni ban san mi nayi ba?"

"Ke buɗe baki zakiyi kiyi magana munafuka"

Da sauri Hannah ta ɗago da kanta tana duban Aunty Maryam datai maganar.

"Amma yanzu Aunty Maryam miye nayi da har za'a kira ni da munafuka?"

"To na kira ko zaki dake ni ne?, idan ba munafurci ba miye kikai iyee?"

"Yanzu dai Maryam ya isa haka nan. Ke Hannah faɗa min gaskiya kin fara soyayya da wani haka ne?"

Kanta ta ƙara saddawa ƙasa ta ce.

"Eh hakane Aunty"

"Lahh Ilah yanzu ke......

Ɗaga mata hannu Aunty Haja tayi, hakan yasa Maryam rufe bakinta kawai tayi shiru tana bin Hannah da kallon mamaki.

"Amma ya akai hakan kika bari ya faru?, bayan kin san ƙudurinmu akanki Hannah?"

"Ni wallahi Aunty Haja ina son Annur a yanzu bazan iya auren wani idan ba shi ba, bana jin zan iya auren Abeed ɗin nan ni tsoronsa ma nake ji tun kamin na gansa ido da ido, ko a photo fa kwarjini yake ma mutane inaga kuma ka saka shi a ido, ni bana so gaskiya na auri wadda bazan iya kallon tsabar idonsa na gaya masa ga abunda nake so ba, ko wadda bazamu yi wasa da dariya a tare ba kullum ace fuska a murtuƙe ni gaskiya bazan iya ba"

"Tabɗi jam sannu Hannah"

Cewar Maryam tana jinjina kai haɗe da riƙe baki.

"Hmmm naji duk abunda kike ce, yanzu shi Annur ɗin waye shi?, kuma ɗan gidan waye? a ina ma kuka fara haɗuwa ne?"

Kanta ta ƙara saddawa ƙasa ta ce.

"A Instagram muka haɗu dashi, kuma shima iyayensa ƴan asalin Katsina ne amma suna zaune a Kano yanzu"

"Innalillahi a social media kuka haɗu?, wacce irin haɗuwa ce wannan haka?"

"Kinga Maryam barta kawai, badai shi kike so ba?, to ke ce masa ya turo iyayensa idan har da gaske yake"

Da kyar ta iya ɗaga kanta tana amsawa ta miƙe simi-simi tabar wajan suka bita da ido da mamakin furucin Aunty Haja ɗin.

"Amma Aunty Haja"

Sai kuma tayi shiru. Aunty Haja na murmurshi kaɗan ta dubi Maryam ta ce.

"Idan yaro ya fara soyayya to kawai abu mafi kyau a kyalesa da wadda yake so ɗin, saboda nima ai nayi nasan kuma yadda ake ji, shi yasa ma kawai na yanke a kyale tan, ai ba ita kaɗai bace, baga Fannah ba idan ta kama sai mu saka Fannah a abun, idan har abun zai yiwu saboda yadda Alhaji yake faɗa min Abeed nima jikina ya fara sanyi dashi wallahi"

"Ni kuma Aunty Haja, ni ina zan kai Abeed, tabɗi jam, ai inaga garama Hannah ko, ni ko haɗa hanya mukai dashi inaga kwana zanyi ina rawar sanyi"

Filo Maryam ta ɗauka tana jifar Fannah dashi sai Fannah ta miƙe da sauri tana dakin dariya ta wuce bedroom nasu da gudu.

Murmurshi kawai Maryam ta saki ta dawo da dubanta wajan Aunty Haja dake girgiza kai.

"Wallahi so duka sun cika tsoro da yawa"

"Ba tsoro bane ai Allah ne ya zubama Abeed ɗin kwarjini ko a fili ko a photon da suke ta faɗa ai gaskiya suke faɗa kowa ma ya sani, ni shi yasa su Surayya ke bani mamaki ma da ƙarfin halin saƙewa a al'amarinsa"

Maryam na taɓe baki ta ce.

"Ko ub*an mi zaiyi dasu ma, yara sai rawar kan tsiya?"

"Hmm Allah dai ya kyauta kawai"

Cewar Aunty Haja tana miƙewa tsaye sai kuma ta dakata tana duban Maryam ta ce.

"Jibi zaku wuce gida ko?"

"Eh wallahi Ammi ma so tayi mu dawo yau gaba ɗaya, saboda su Aunty Bintu gobe zasu iso, kin san ɗaurin auren na juma'a ne"

"Hakane waje ya ƙure wallahi, amma dai goben kuma saiku tafi, saboda ma ƙunshin da zakije, yau na idasa miki gyaran jikin daya rage insha Allah"

"To Aunty ke yaushe zaki taho gidan?"

"Saina tabbaye shi naji, ni zai barni ma da tare mukai tafiyarmu wallahi, tunda gobe ne nake fita aiki, amma zan gwada tabbayar tasa naji abunda zai ce"

"To Allah yasa ya barkin nasan halin maza da iko"

"Haka suke ai"

Aunty Haja ta faɗa tana barin wajan..........

PAGE 70

Ranar dasu Maryam suka shirya zasu koma gida gaba ɗayansu suna zaune parlon Aunty Haja suna sallama da ita.

"Yanzu Aunty Haja sai yaushe kenan zaki taho?"

Cewar Fannah dake gyara gyalen jikinta.

"Inaga sai ana gobe, ɗaurin aure, danna tabbaye shi wallahi bai barni na tafi daku ba"

"Ai ni dama na sani da wahala ya barki kam, a hakan ma ai yayi ƙoƙari, saboda yanzu bake kaɗai bace kuma bare ya sani gani zaiyi za'a wahalar masa da baby ne"

Murmushi kawai Aunty Haja ta saki tana miƙewa ta ce.

"Wannan saƙon kibawa su Aunty Bintu dan Allah sai nazo ɗin, ai naga zaku yi party ma gobe ko?"

"Eh gobe da jibi duk zamuyi, gobe Kamu za'ai jibi kuma sai an ɗaura aure ne a can ɓangaren angon suka shirya dinner"

"Okey ƙila naje dinner ɗin amma itama ƙila ne"

"Hmm aure maisa mace natsuwa waje ɗaya"

Cewar Maryam tana dariya.

Sallama sukai suke da kewar juna da yake akwai Motar da Maryam ta taho da ita ta Aunty Sa'a. Suna fitowa suka loda kayan a ciki suka shiga suka bar gidan.

Dan har lokacin Abeed bai zo gidan ba yana can gidan Hajiyarsu da alama wannan zuwan zaiyi wahala ya zauna gidan.

Sai dai da tafiyarsu Maryam ba daɗewa wasu Motoci suka fara shigowa cikin gidan kusan su biyar a jere.

Aunty Haja ta koma parlonta ta zauna kenan tana kallon TV taji wayarta kira ya shigo.

Tana duban cikin wayar ganin Alhaji ne yasa ta saki murmurshi kaɗan tana ɗaukar wayar.

"Hello ranka ya daɗe"

Can ta jinjina kai jin abunda ya ce yasa miƙewa da sauri tana cewa.

"Okey yau Abeed ne yazo gidan kenan?, kace muna da babban baƙo, to sai kun shigo ɗin"

Ta sauke wayar tana nufar kitchen da sauri. Tsaye take a kitchen ɗin tama rasa miye zata haɗa masa mai sauƙi wadda zaiji daɗin sha ko ci.

Wani Cake ta gani a cikin firiza wadda Hannah ta haɗa mai Chocolate yayi kyau sosai an yayyakasa ƴan ƙananu dai-dai sawa a baki, da sauri ta ɗakko faranti ta jerasa a ciki, saita fara haɗa masa wani lemo mai ƙaurin gaske fari tas sai tashin ƙamshi yake, dandanan ta gama ta jerasa a kyakykyawan faranti ta fito dashi parlon ta ajesa akan table dake tsakiyar parlon.

Ta shige bedroom wanka tayi ta sauya kaya na mutumci tana yafo gyale ta fito sai tashin ƙamshi take parlon ma saida ta ɗan gyarasa tasa masa turaren wuta ko ina na part ɗin nata ƙamshin turaren wuta kawai ke tashi, dan har fita yake babban parlon daya raba nata dana Haj Saratu, zaka iya jiyo ƙamshin har nan yana fitowa.

Ta zauna da ƴan mintoci taji shigowarsu haɗe da sallamarsu.

Ɗagowa tayi da sauri tana sauke idonta akansu.

Kodai bata ji da kyau bane, ai sai take jin kamar muryar su ɗaya yadda kasan Alhaji ne ke magana shi ɗaya, bata ƙara mamaki ba saida idon nata ya sauka akansu kusan ruɗewa tayi tsabar kamar da suke da Alhaji, ai kamar ma ta ɓaci sai dai shi Abeed yafi Alhaji yarinta ya kuma ya fishi kyau da kaɗan amma kamarsu tayi yawa, sai kuma kwarjini da kamewa daya fi Alhaji, dan baiwar kwarjinin a jikinsa take shi kam.

Dan hatta tafiyarsa cike take da kamewa da tsantsar kwarjini idonsa a nan kwarjinin yake a cikinsu.

Da murmurshi ta tarbesu ya shiga gaida ita a mutumce wadda bata taɓa tsammanin zaiyi hakan ba.

Shima Alhajin sosai farin ciki dan sai yaga yama fi sakewa da Aunty Haja akan sauran matan, kodansu rawar ƙafarsu tayi yawa sunfi ma saka ƙannansu a gaba idan yazo gidan shi kuma abunda baya so kenan, dan yanzu ma suna can sai iyaye suke kowacce na ɗaukar wanka a nan ya fara shigowa wajan Aunty Haja su kam dama sauran ba shiga ɓangaren kowacce yake ba sai idan an haɗu a babban darning cin abinci, sai idan dama ya dawo ƙasar ake zama cin abinci a kusan a tare, kuma wannan tsarin Alhaji ne yasa shi, shi kam Abeed kwata-kwata baya son wannan tsarin dandai baya da gaddama shi kuma yana tsananin biyayya ga Yayan nashi.

Cike da ƴar sakewa Aunty Haja ta gabatar masa da abun motsa baki tana nazarinsa a tsanake, tsakani da Allah itama kwarjini yake mata, baccin tana auren Yayansa ai da tuni da suka gaisa tabar parlon, dan yanzu ɗin ma ji take duk a takure take.

Shi kam gogan naku ko a jikinsa bayan ma sun gaisa sai fito da wayarsa ya shiga latsawa hankalinsa na ga wayar tasa sai Aunty Haja ke mamakin hali irin nasa ita bata taɓa ganin mai hali irin na wannan da take gani ba, tunda suka gaisa bai sake buɗe baki yayi magana ba, koda ta gabatar masa da abunda ta haɗa masan ɗaga kai kawai yayi yana murmurshi kaɗan, murmurshin shine maganar tasa kenan fahimtar da tayi.

Alhaji shima dake zaune kusa da ita yana ɗan jansa da fira jefi-jefi sai dai ya ɗaga masa kai ko ya girgiza masa kai.

A hankali yasa hannunsa kamar baya so ya ɗauki Cake ɗin, shima dan yaga yayi masa kyau a ido sai kuma baya son Aunty Haja taga kamar ko bai kyauta ba idan baici abincinta ba, tunda yau suka fara haɗuwa, bai kyautu yayi mata wani abu da zata fahimci wani abun can daban ba.

Kamar zaisa kashi a bakin nasa a yamutse ya saka yana taunawa kamar baya so, sai dai yana sakashi a bakin nasa ɗanɗanon abun ya gama gauraye masa baki, bai san lokacin daya haɗe na bakin nasa ba, yana lumshe ido dan ba ƙaramin daɗi Cake yaji yayi masa ba, a hankali ya sake kaiwa bakinsa wadda ya rage a hannunsa nan ba ɓata lokaci ya haɗesa.

Lemon ma ya ɗauka yasha sai yaji ya rasa ma wanne yafi wani daɗi tsakanin Cake ɗin da kuma lemon.

Sai dai sukaga yana ta cin kayansa ba magana dai abincin ma a yangance yake cinsa, a yanayinsa saika ɗauka ko bai masa daɗi bane dole tasa yake ci, sai dai wadda yayi mugun fahimtarsa ne zai gani ba ƙaramin daɗi ya masa ba, ita kanta Aunty Haja lokaci ɗaya ta gama fahimtar waye Abeed ɗin, murmurshi dai ta saki tana jin daɗin yadda ya ɗan sake da ita harya ke cin abunda ta haɗa masa.

Fahimtarsa da tayi kuwa kai tsaye shine shi ɗin kai tsaye yake abu, idan zaiyi idan ko baiyi niyyar abuba bazai yi ba, abun nan kuma idan bai masa ba to har abada bai masan ba, saboda yadda suke fira da Alhaji ta gama fahimtar hakan, wani abun idan ya ce masa kai tsaye zai girgiza kai amsar da zai bada ɗaya ce kuma bazai sake magana akan abun ba, koda Alhajin ya sake masa ita bazai tanka akanta ba.

"Ni wai naga sai cin abun nan kake, bari na ɗanɗana tunda ba'a mana tayi, kin gwangwanje Ƙanin naki da kayan daɗi ni ko Oho ko"

Alhaji ya ƙare maganar cike da raha, Aunty Haja ta saki murmurshi kawai bata ce komai ba dai shi kam mutunan naku abunda yake yi kawai yasa a gaba wato latsa wayarsa da kuma ɗan shan lemon da Aunty Haja ta haɗa yana kurɓa kaɗan-kaɗan.

"Uhmm gaskiya Cake ɗin nan yayi daɗi, hala Hannah ce tayi sa kamin su tafi ko?"

"Eh ranka ya daɗe ita ce tayi sa ai basu daɗe da tafiya bama"

(Hannah) Abeed ya mai-maita sunan a zuci, yana tabbayar kansa wace haka?, ashe ma da Aunty Hajar ce tayi Cake ɗin ba, sai kawai ya samu kansa da ƙurama sauran Cake ɗin kallo, da Alhaji ke ci yana santi.

Basarwa yayi kawai yana kauda tunanin wata Hannah a ransa, yana mamakin ma yadda ya wani riƙe sunan nata.

A hankali ya miƙe yana gyara zaman rigarsa ya ce.

"Big bro ni zan wuce part nawa, and zan ɗan huta zuwa anjima na koma gidan Hajiya"

Ya idasa maganar kamar yayi wani aiki mai yawa, dan da kyar yake maganar kamar baya so, dan sai Aunty Haja tayi mamakin dogowar maganar ma da yayi ɗin.

"Okey, amma na ɗauka ka dawo nan ɗin harka koma, naga duka wata huɗu zaka yi a ƙasar?"

"No wannan zuwan na Hajiya ne kawai big bro"

Jinjina kai yayi yana masa amsa shi kuma ya fice yana tafiyar nan tasa mai cike da jan aji da izza haɗe da kwarjini.

A hankali yake takawa saiya maida wayar tasa a haljihun wandonsa ya maido da hannuwansa baya yana takawa a hankali ya fito babban parlon part ɗin nasu.

Yana gaf ficewa yaji wata murya cike da iyaye da zallar yanga tana cewa.

"Ya Abeed sannu da zuwa ina wuni anzo lafiya?"

A jere tayo masa tabbayar tana jifansa da wani irin murmurshi na zallar ƙaunarsa dake nuƙurƙusar zuciyarta.

Bai tsaya ba domin yasan muryar wace, yasan Surayya ce marar hankalin nan, daya raɗa ma suna marar kan gado.

"Ya Abeedddd"

Ta faɗa a shagwaɓe ganin ya fita ko tanka mata baiyi ba.

Wani irin abu taji ya daki ranta jiki a sanyaye ta shiga kallon jikinta, yadda taci uban wankan nan ace koma juyowa baiyi ba ya kalle ta?, wai wane irin mutum ne Abeed?.

Ta shiga tabbayar kanta jikinta a sanyaye.

"Ke lafiya kika tsaya a nan, ba wajan Abeed ɗin zaki je ba?, nasan ai yana shashinsa a yanzu, ko so kike waccar uwar feleƙen Ihsan ta rigaki zuwa inda yake ne?"

Sai taga Surayya ta samu waje ta zauna tana tagumi hannu biyu-biyu ta shiga cewa.

"Aunty nifa na fara sarewa da lamarin bawan Allahn nan wallahi, yanzu fa na gansa ya fito daga part ɗin waccan matar yana murmurshi amma daga jin muryata ya ɗaure fuska, ina gaida shi amma wallahi ko juyowa baiyi ba bare ya amsa min"

"Kuturun uba, kika ce wai ya fito daga part ɗin Haja?"

"Wallahi daga can ya fito, kin san dai ba abunda ke

38 / 47