Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   42 / 47

123K to 126K   out of 140.3K words

ta shiga gyara mata jiki gyara ɗaya da akai saida Aunty Sa'a taga canzawar fatar jikinta, ai ko taita jinjina ma Aunty Haja ɗin, dan yanzu sosai ta kware wajan gyaran jiki duk yankin yanzu ba kamar ta.

Aunty Haja ta shiga tabbayar wai ina Fannah ne bata biyo ta bane?.

Aunty Sa'a na dariya ta ce.

"Wallahi nayi-nayi tazo mu tafi amma taƙi, saima taga Aysha zata fita shopping ita da Naseer daya zo ta ce zata bisu ai ko suka tafi da ita tun kamin ma na fito sun riga da sun wuce"

"Hmm rabu da ita ai zata zo ta iske ni ne, waifa soyayya ta fara itama, bata so Hannah najin tana soyayyar shi yasa taƙi dawowa saboda ɗaki ɗaya ai suke kwana, gara kinga ai can ɗakin ita ɗaya ce yanzu tayi yadda take so"

Dariya kawai Aunty Sa'a ta saki suka ci gaba da gyaran jikin, sai wajan yamma lis tayi mata sallama ta tafi, duk sai Hannah taji kamar ta bita itama, dan tayi kewar Fannah ɗin, har kiranta tayi tana cewa mi yasa wai bata dawo ba?.

Sai ce mata tayi tana ɗan hutawa ne a gida sai anyi bikin tarewar Aunty Sa'a zata dawo, ƙarshen wayar da faɗa aka gamata dan Hannah ce mata tayi kar Allah yasa ta dawo ma gaba ɗaya, ita kuma ta ce mata ohho dai can ita ta sani, kuma gasu nan ita da Aunty Aysha zasu je gidan Aunty Maryam bayan sun gama shopping, ta faɗa tana mata gwalo kamar tana gabanta tana mata dariya ta kashe wayar.

Cikin jin haushi itama Hannah ta sauke wayar taje wajan Aunty Haja tana mata shagwaɓar itama tana son zuwa gidan Aunty Maryam, ga Fannah can sun tafi ita da Aysha.

Aunty Haja na murmushi ta ce mata karta damu zata saka driver gobe ya kaita saita yinar mata, dan tasan dama Fannah jan faɗa kawai yasa ta faɗa mata, Allah dai ya shirya ku.

Aunty Haja ta faɗa a ranta tana murmushi haɗe da girgiza kai ganin yadda Hannah ɗin ta saki ranta harda sakin murmurshi itama........

PAGE 74

*MUBEENA POV*

Zaune take kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

Shi kuma yana daga gefenta yana jifanta da murmushinsa mai zautarda ita.

Ai ita bata taɓa tunanin cewa Doctor Nuran ya kai haka nasaba da kwawun fuska ba ga kyan hali, a ɗan zaman da sukai dashi yau ta shaida Aunty Zubaida ba zaɓen tumun dare tayi mata ba.

Gata ne tayi mata, da ace ta bijire ai da tayi ma kanta.

"Uhmm my dear ina magana kinyi shiru, Allah dai yasa na miki karki ce nayi miki tsufa?"

Ya ƙare maganar cike da raha, dan ta gane ɗabi'arsa ce raha murmushi kam baya barin kyakykyawar fuskarsa.

Kanta a ƙasa sosai ta kasa ɗagowa ta sake kallonsa, dan tunda tayi masa ganin farko bata sake ɗagowa ba, ya haɗu kyawunsa yayi mata ita kam, ba yaro bane tabbas dan zai iya kaiwa shekaru arba'in da wani abu, amma shekarun nasa sun ɓoye saboda kuɗi da huta, dan gemunsa har ƴar furfura ta fara fitowa amma ƴar kaɗan ita sai taga ma kamar kyau ne ta ƙara masa, fari ne amma ba can ba sosai farin nasa tsaka tsakiya ne, sana dirarran mutum ne tsayayye ne ingirma ga ƙirar mazantaka, cikin idonsa take hango kwarjini sosai a cikinsu shi yasa ta kasa ɗagowa ta sake kallonsa.

Murmushi kaɗan ya saki yana sake matsowa kusa da ita kaɗan ya ɗan leƙa fuskarta, Mubeena na sakin murmurshi kaɗan ta sake sunne kanta ƙasa.

"Please ginbiyata kiyi magana mana, kina sawa hankalina na tashi fa, karki sa na fara zargin ko banyi miki bane?"

Ai Mubeena bata san lokacin data girgiza kanta da sauri ba, sai kuma kunya ta kamata kusan gaba ɗaya suka saki dariya daga ita har shi, ai ko da sauri ta miƙe tabar parlon da gudu, ya bita da murmushi yana lumshe idonsa dan ya gama gane itama dai ta faɗa tarkon ƙaunarsa daga ganin farko, hamdala yayi yana ciro wayarsa ya kira Aunty Zubaida ta fito.

"A'a wai har kun gama ne?, ina ita Mubeenar?"

"Kunya ta hanata tsayawa muyi sallama mana"

Murmushi Aunty Zubaida ta saki tana cewa.

"Fatan dai ta amince da kai Doctor?"

"Komai yayi babbar yaya"

"Ohhh harna koma babbar yaya ma?"

Dariya ya saki yana shafa gemunsa kaɗan da alamar hakan ɗabi'arsa ce idan abu yayi masa daɗi.

"Yeah babbar yaya ai dole kin koma haka, nida zaki bawa mata sukutum da guda ai kin koma uwa ma"

Itama tana murmushi ta ce.

"Hakane kam, amma yaushe zaka koma ne?"

"Wai India?, ai idan kinga na koma can to tare da amarya ta zan koma insha Allah, yanzu abunda yasa na tsaya so nake mu gama maganar auren nan dake, nifa a shirye nake babbar yaya, idan har zaku bani dama ma bana so ya wuce nan da sati ɗaya ko biyu ayi bikin nan"

Ido waje Aunty Zubaida ta fito tana riƙe baki ta ce.

"Kai Doctor Nura baiyi wuri ba?"

"Ko kaɗan baiyi wani wuri ba, ni dai a haka nake son ayi bikin da sauri gaskiya, amma zan barku kuyi shawara duk abunda kuka yanke sai a kira ni, kince ai ba'a nan za'ai bikin ba ko?"

"Eh ba'a nan ba a can garinmu ne Ƙanƙara, sana hatta neman auren a can za'aje ayi, amma suma dai sun san da neman auren nata da za'a zo, dan haka zuwa gobe zan kira ka insha Allah idan masu neman auren suka je sai muma daga baya mu tafi domin shirye-shiryen bikin muyi a can"

"Yayi hakan insha Allah ba abunda zai gagara yanzu sai na jiku kawai, sana akwai kaya a Motar dana zo dashi please ki aika yara su ɗakko ni zan wuce amma ace ma Ginbiyar tawa ina son sake ganinta"

Murmushi Aunty Zubaida ta saki tana girgiza kanta tana ce masa bashi da dama dai, ta lura son da yake ma Mubeena mai yawa ne.

Shima tana fita ya miƙe ya fita zuwa waje.

Ta aika Ɗan Lami suka je suka ɗakko kaya masu yawan gaske da kayan ciye-ciye sai wani akwati guda dake cike da kaya na ƴan mata irinsu kayan kwalliya ne da Abaya irin ƴar ƙasar Dubai ɗin nan ta kusa guda goma kaya ne sosai na ƴan gayu harda sarƙar gwal aka sako a ciki har guda biyu sai kwalin waya a ciki IPhone 17.

Ai Aunty Zubaida ruɗewa tayi ganin uban kayan da tulo, koda ta ɗauki waya ta kirasa lokacin ta tura Mubeena wajansa da kyar ya ɗauki wayar yana murmurshi yana kallon Mubeena da kanta ke ƙasa tana murmushin itama.

Koda yaji abunda Aunty Zubaida ke faɗa wai kayan sunyi yawa.

Kai tsaye ya ce mata ai kaya na Ginbiyarsa ne tsarabarta ce ta India dan haka baiga kayan da zai sayo mata ba ace sunyi yawa, ai shi wannan a wajansa kaɗan ne ma.

Tama rasa godiyar ta zata fara masa tana farawa ko ya yanke wayar danshi kam bai cika san godiya ba yafi so kayi masa addu'a.

Sun daɗe da Mubeena a cikin Motarsa yawanci shike janta da fira ganin kunyarta yayi yawa yasa shi murmushi yana jin farin ciki sosai dan dama yana son mace mai tsananin kunya, haka kawai yaji ta ƙara shiga ransa ta samu waje ta zauna tayi kane-kane.

Da kyar ya barta sukai sallama ta fita tana masa bye-bye shima yana ɗaga mata hannu suna jifan juna da murmushi mai narkar da zuciya.

Koda ta koma ciki itama kayan sun ruɗata ganin wayar daya saya mata wacce bata daɗe da fitowa ba a duniya, wacce take ganinta wajan manyan masu kuɗi da ƴan films dake gasar sayenta, wai yau ita ce riƙe a hannunta a matsayin tata.

Ai bata san lokacin data buga tsallan murna ba tana rungume Aunty Zubaida harda sakin ihun murna ta rasa inda zata saka kanta dan daɗi. Aunty Zubaida na murmushi take cewa ita fa karta karyata ta faɗa tana mata hararar wasa.

Sauran kayan ta ci gaba da nuna mata tana ce mata ta kirasa tayi masa godiya gaskiya.

"Ai dole Aunty na kirasa godiya ma wacce zaiyi farin ciki da ita"

"Yawwa ƴar gari kiyi masa abunda zaiyi farin ciki shima kinji"

Amsata ta hanyar jinjina kai tana kallon sarƙar da Aunty Zubaida ke nunata tana mata bayanin irin tsadarsu.

"Ni Aunty ai kawai ki ɗauki ɗaya, ɗayar kuma na tafi da ita nabawa Inna ita"

"A'a baza'ai haka ba Mubeena, ni ina da sarƙoƙi irin wa'innan da yawa ki ɗauki ɗaya dai ki saka kiyi masa kwalliya da ita ya gani, ai zaiji daɗi ɗayar kuma saiki kaima Innar taki"

"To amma Aunty kefa"

"A'a karki damu ina dasu ai kin sani"

"Amma gaskiya ki ɗau wani abu ciki to kema please kinji Aunty?"

Murmushi ta saki tana saka hannunta taja kumatun Mubeena tana cewa.

"Allah yayi miki albarka, ai ni kin gama biya na da har kika amshi Doctor Nura hannu biyu-biyu baki watsa min ƙasa a ido ba. Sana kaya kuma bazan ɗauki ko ɗaya ba saboda kaya danke aka kawo su, nima ai ga kayan ciye-ciye nan a tare zamu ci ai ko?"

Da amin Mubeena ta amsa tana sakin murmurshi itama kanta a ƙasa ta ce.

"Aunty ni ce zanyi miki godiya ai, kin gama min gata na gidan duniya, da ace nayi butulci ga zaɓinki da ace Aunty Badi'a bata zo ta nuna min kuskure na ba, da ace bata je ta gaya ma Inna abunda nayi miki ba har Inna ta kira ni tayi min faɗa ta sake nuna min cewar kema uwa ce bazaki taɓa zaɓa min abunda zai cutar dani ba, da yanzu ƙila wata maganar ake ba wannan ba"

Jinjina kai Aunty Zubaida tayi tana ɗago kanta sai suka haɗa ido da Badi'a dake tsaye yanzu ta shigo parlon murmushi suka sakar ma juna.

Ganinta yasa Mubeena miƙewa da sauri taje inda take ta rungumeta tana jin ƙaunarta har cikin ranta, itama Badi'ar rungumeta tayi tana sakin murmurshi.

Ai ko saida Mubeena ta ɗibarwa Badi'a dogayan Abayoyi kusan guda uku ta bata, ta kuma ji daɗi sai murna take tana mata godiya, da kyar Mubeena ta lallaɓata ta daina mata godiyar dan ita kunyar gode matan da take yi ma taji tana yi.

Abu kamar wasa Aunty Zubaida ta ɗauki waya bayan kwana biyu ta kira Inna ta gaya mata duk abunda ake ciki.

Ita kuma Inna tana murna ta shiga sanarma su Kawu Isa da Musa, ai ko suna murna suka gaya ma sauran dangi aka fara shirye-shiryen tabar baƙi wa'inda zasu zo neman auren Mubeena, koda aka gaya ma Iya bata ce komai ba sai Allah yasa alkhairi dan yanzu tayi laushi saboda yanzu duk wani daɗi da take ci a gidan ta dalilin Innar ne da kuma Musa, dan yanzu shima ya zama mai kuɗin kansa sosai suke jin daɗi shida matarsa Na'ima dan har gata da ciki na kusan wata biyar hankalinta sosai ya kwanta sai ƙiba take abunta, abunda Iya bata taɓa tunani bane sai gashi rayuwar yaran nata sauyawa, komai da tayi dan ya zame masu matsala sai gashi ya zame masu shine alkhairinsu.

Aunty Zubaida Inna ta kira ta, ta shaida mata komai kuma zasu iya zuwa ta sanar dasu Kawu Isa, kuma sun shirya zuwan nasu.

Cike da farin ciki ta kira Doctor Nura ta shiga masa albishir, wannan magana mai daɗi data gaya masa yana murna tana sauke waya saida taga alert ɗin kuɗi har naira million biyu, koda ta kirasa a ruɗe tana tabbayar na miye kuma?, ai sai ya ce mata tukwaicin albishir ɗin data masa ne.

Kai tafa rasa ina ma zata fara masa godiya ta ƙara jaddada yadda yake son Mubeena so ne bana wasa ba. A ranar yazo ya ɗauki Mubeena suka zo akai mash awon jini kuma ba'a samu matsala ba dansu duka A'A ne.

Washe garin data gaya masa dama manyansa na can sun san da maganar neman auren da yake yi hatta matansa sun san da wannan aure dan yadda yake nunawa dole tasa su sakkowa suma suna tayasa farin ciki duk dai ta ciki na ciki.

Washe gari suka hau jirgi sai Kano daga Kano da jirgi ya sauke su sai Ƙanƙara zasu nufa a Mota.

Zaune Mubeena take a tsakiyar gado suna waya da Doctor Nuran sai zuba masa taɓara take wani abun ba bata san ta iya shagwaɓa da iya salon magana ba saida ta haɗu da Doctor Nura dan ita kanta mamakin kanta take yadda lokaci ɗaya ta sake dashi soyayyarsa kuma tayi mata mugun kamu itama.

Tana cikin wayar dashi Aunty Zubaida ta shigo ɗakin da sauri ta miƙe ganinta tana waya tana murmushi kamar bakinta zai tsage sai kuma taji ta saki buɗa mai ƙara tana ƙara sakin wata buɗar da alama da Inna take waya.

Itama sai tayi sallama dashi tana miƙewa tsaye da sauri sai taji duk jikinta yayi sanyi ƙlau ta dubi Aunty Zubaida dake waya da Inna har lokacin, da ido take mata maganar mike faruwa?. Sai taga kawai Aunty Zubaida ta jawota tana rungumeta a jikinta ta shiga shafa kanta tana ci gaba da wayar da take yi.

Zuciyarta na bugawa da ƙarfi dan a maganar da suke saita fahimci kamar mafa auren aka ɗaura daga zuwa neman aure?.

Bakinta taji ya bushe da kyar ta iya ɗaurewa Aunty Zubaida ta gama wayar ta shiga tabbayarta mike faruwa jikinta har rawa yake.

Sake rungumeta Aunty Zubaida tayi tana raɗa mata a kunne cewa ta zama matar Doctor Nura an dai ɗaura aure, dama da shirinsu suka je garin kuma Kawu Isa baija da maganar ba ya ɗaura auren nan take yanzu haka ƴan uwa na can suna can ana shagalin auren da aka ɗaura.

Ai Mubeena bata san lokacin data saki wani irin kuka ba, ta rasa ma kukan miye take yi ne na farin ciki ne ko kuma akasin hakan.

Sake rungumeta Aunty Zubaida tayi tana bubbuga bayanta.

A hankali ta zame daga rungumar da tayi mata sai Aunty Zubaida taga ta duƙa ƙasa tana yin Sujjdar godiya ga Allah ta daɗe a Sujjdar kamin ta ɗago saita ƙara tashi ta rungume Aunty Zubaida dake mata murmushi itama idonta duk ya fara cika da ruwan hawaye.

Bayan Aunty Zubaida ta fita bayan tayi shiru kiran Doctor Nura ya sake shigowa, saida ta kusa tsinkewa kamin ta ɗauki wayar ai ko tana jin yana ce mata amaryata sai ta sakar masa kuka dama jira take.

Ya ci gaba da aikin rarrashinta ita kuma ta sake masa taɓara son ranta bawan Allah duk yabi ya ruɗe, harda cewa kodai yazo ya rarrashi kayansa, ta noke kafaɗa kamar yana ganinta tana taɓe baki, kamar yasan abunda take yi ya shiga ƙara rarrashinta yana ce mata to tayi hakuri yasan yayi laifi amma zai goge laifin nasa.

Gaga-gaga aka fara yima Mubeena gyaran jiki a nan Logas na kusan sati guda ta canza tayi kyau abunta har wata ƙiba ta ƙara, a satin da aka fara mata gyaran jikin nata Aunty Zubaida bata sake bari sun haɗu da Doctor Nura ba ta ce har sai an kai masa matarsa zai ganta amma banda yanzu, ba yadda baiyi ba amma fufur Aunty Zubaida ta hana haɗuwar sai dai a waya kwana suke suna waya ana zuba soyayya kamar ba za'a daina ba, wani lokacin ma har sai Mubeena tayi bacci da waya manne a kunneta kamin ya kashe wayar tasa gaba ɗaya yarinya ta sauya masa tunani, dan ma iya bakin ƙoƙari baya bari matansa na fahimtar irin ɗubin son da yake mata, baya taɓa waya da ita a gabansu kowacce yana ƙoƙarin kare mata haƙƙinta, ita kam wajan Mubeena mancewa take dama yana da mata har biyu, dan ita kaɗai take hango kanta a matsayin matarshi.

A sati na biyun da zasu shiga suka shirya suka nufi Ƙanƙara a jirgi suka tafi suka sauka Kano dan Doctor Nura ne ya biya kuɗin komai na tafiyar da zasuyi, ciki harda Badi'a a tafiyar.

Ranar da zuka sauka a Ƙanƙara kwanan murna sukai tsakanin Inna da kuma su Na'ima dan Na'ima a gidan ta kwana aka kwana ana firar yaushe gamo, bar ma tsakanin Inna da kuma Aunty Zubaida su kam harda kukan ganin juna sukai.

Iya dai ta zama ƴar kallo, ganin yadda suka zo da abun duniya gashi Mubeena ta sauya mata sai ma take ganin kamar ba Mubeenar data bada aka kai Logas ba, kamar wacce aka sauyata dan ta ƙara zama ƴar gayu tayi kyau abunta ga ƙiba tayi, kasa ma magana Iya tayi saida Mubeena ta fara janta da faɗan data saba kamin Iyar ta saki jikinta dasu suka fara firar da ita, sosai Mubeena ke mamakin yadda Iya ta zama mai sanyi kamar ba itama ba, lallai rayuwa, duk wadda ya ɗauketa da zafi ma ya sauke.

Kwanaki uku da zuwansu aka fara shirye-shiryen biki kota ina jama'a ke tururuwar zuwa wannan biki, gida ya cika maƙil da jama'a.

A ranar ne Doctor Nura ya kira Aunty Zubaida cewar yau ƴan Kawo lefe zasu zo dan yanzu hakama sun taho, mata ne dai guda biyu da wata yayarsa sai kuma wata cikin ƴan uwansa zasu kawo lefen, a jirgi suma zasu taho daga Kano zasu ɗakko hanya da lefen, zasuyi tashar Mota su kaɗai ta kawo su.

Dandanan aka fara shirin tabarsu, kamin isowarsu har an gama shirya komai na tarbar tasu.

Sosai sukaga karamci da dattaku a wajansu sosai suma suka saki jikinsu dasu suna jin daɗin inda ɗan uwansu ya ɗakko mata, ita kanta Mubeena ɗin sunga yadda ta tarbesu cike da girmamawa sun ƙara gasgata lallai ɗan uwansu baiyi zaɓen tumun dare ba, dan yadda sukaga Mubeena tama fi sauran matansa iya ma'ala da mutane da sakin fuska.

Kota ina zuwa ake ganin lefe dan kusan akwati takwas ne amma kayan ciki fa nan ne kallon yake, kaya ne masu tsadar gaske danma wasu ba sanin yawan kuɗinsu sukai ba,

42 / 47