Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ke Fannah ke kike cewa wai kinfi ƙarfin yin ƙunshi?, wacece ke?, ai kin bari ki zama wani abu tukunna zaki fara tanƙahon kin wuce yin sana'ar ƙunshi"
Bubbuga ƙafa Fannah ta fara yi cike da shagwaɓa tana jin zafin abunda Aunty Maryam ke faɗa ta ce.
"Ni dai gaskiya Aunty Maryam bana son yin ƙunshi mutum duk ya koma kamar wani mahaukaci, duk ka wani ɓata jikinka, gaskiya da ne nayi ƙunshi kam amma yanzu kam ya fita a kaina. Kuma Ammi ai zamu zama kamar yadda kike so ɗin"
Ammi zatai magana akai sallama aka shigo gidan. Masu ƙunshin ne harda babbar Auntyn tasu kuwa biye dasu, dan ba ƙaramin iya ƙunshi Fannah ɗin tayi ba, ta iyasa sosai kamar ba ita ke yinsa ba, idan har ta zana maka lallai sai ka rantse cewar ba ita ce tayi sa ba...........
*TAURIN KAI*
*Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.......*
PAGE 5
*MIMI POV*
Hawaye ne masu zafi ke mata zuba a gefen fuskarta. A hankali take sauke lumfashi kamar bata so, motsi kaɗan take yi, saboda ƙarin ruwan dake aka saka mata.
Kwata-kwata jikinta bata jin daɗinsa, ga rayuwar ma gaba ɗaya jinta take kamar ta mutu ma kota huta da yanyin da take ciki.
Shigowar Mama ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Mama harta zauna kusa da ita.
"Kukan dai Mimi?"
"Mama dan Allah ki taimaka kiyi ma Abba magana mana wallahi Allah ni bazan iya auren Mubarak ba"
Sosai Mama ta zuba ma Mimi ido kawai tana karantar yanayinta sosai kamin ta ce.
"Kiyi hakuri fa Mimi, suman nan da kikai hakan bai hana Abbanki janye ƙudurinsa ba, dan yanzu haka kamin ki farka sai da Mubarak ya zo duba ki, kuma da alamar yasan da maganar auren da aka maida naki akansa"
Girgiza kai Mimi ta fara yi hawaye na sake wanke mata fuska, cikin muryar kuka muryarta na kyarma take cewa.
"Mimi mutuwa zanyi wallahi zuciyata zafi tak....
Tashi tsaye Mama tayi tana duban Mimi da kyau, danta fara kaita bango kuma ta nunata da yatsa tana cewa.
"Bari na fito miki a mutum Mimi, banga wadda zaka ce wai dan babu shi bazaka iya rayuwa ba, idan kinga ana hakan sai dai idan abun bai zo kanka bane. Ke yanzu akan wani kike son kassara rayuwarki?, wadda duka-duka ma yaushe kuka huɗun?, baki ce zaki mutu danmu ba sai dan wani?, to ai bismillah Mimi kinga idan kika kashe kan naki ai bashi keda asara ba, koda baki duniyar zaije ya auri wata ne nama gaya miki"
Mama na faɗar haka ta juya ta barta tana hawaye, tun tana hawaye har kukan nata ya fara fitowa fili. Su Mama basu san yadda take jin Jafar a ranta bane, ta tabbatar shima bazai iya rayuwa ba ita ba, bazai taɓ barin ta ba.
Ƙarar kiran wayarta ne ya katse mata tunanin data faɗa.
Saida ta kusa tsinkewa kamin tasa ɗayan hannunta wadda ba'asa ƙarin ruwan ba ta ɗakko, dama tana kusa da ita.
Ganin mai kiran yasa ta saki murmurshin daya taho da wasu guntun hawayen da suka bi mata ta gefen fuskarta.
Tana ɗaukar wayar ko gaisa basu yi ba Jafar ya fara jefo mata tabbayar ya jikinta, duk hankalinsa a tashe.
"Love, Abba na zo amma ya hanani shigowa inda kike, wai zan ƙara tayar miki da hankali ne. Haba Mimi mi yasa Abba zaiyi saurin yanke hukunci?. Nima yanzu haka gani nan kwance bana jin daɗin komai nawa. Yanzu shikenan ina gani za'a rabamu?"
Kuka mai ƙarfi ne ya ci ƙarfin Mimi ta kuwa sakar masa shi. Bawan Allah duk sai ya ruɗe ya shiga rarrashinta.
Mimi bata san Mama ta shigo ɗakin ba sai dai kawai taji tasa hannunta ta amshe wayar dake kange a kunnanta.
Sai lokacin Mimi ta ɗan zubara kaɗan har tana shirin guje ƙarin ruwan da aka sa mata wadda ya kusa ƙarewa saura kaɗan.
"Wato Abbanki daya hanaki waya da Jafar shine kike yi ko?, ance kiyi nesa dashi hakan zaisa ki samu ƙarfin zuciyar da zaki iya rabuwa dashi cikin sauƙi, amma da yake ko duka shaiɗan na maku kuwwa a kunne kuna zama kuna sake zuge junan baza ku iya rayuwa babu ɗaya ba ko?. Ya za'ai ku iya rabuwa kuwa kuna haka?. Wallahi Mimi kifa fita daga ido na rufe. Tunda har yau an maida ma Jafar kayan aurensa an amshi na Mubarak ya kamata ki tsaida hankalinki ga Mubarak kawai, ki manta da Jafar"
Kuka sosai Mimi ta saki tana sake girgiza kai ta ce.
"Mama bazan iya auren wani idan ba Jafar ba, dan Allah ku gane mana"
"Mtsww, gobe ki shirya zaku je awon jini dashi Mubarak ɗin"
Ai sai Mimi ta fara addu'ar Ubangiji yasa shima jinin nasu yazo ɗaya taga yadda za'ai ayi auren, ita da auren wani ba Jafar ba gara ta mutu ba aure haka take ji.
Zuwa can kamar a maganar ta zo mata a cikin kanta taji Mama na faɗin.
"Duk da dama ya ce shi yasan nau'in jininsa A'A ne, amma zuwa a ƙara tabbatarwa yafi"
Wani tashin hankali ne ya rufe Mimi tana haɗe wani abu a maƙoshinta, tana sake jin fargaba da tashin hankalin rasa Jafar. Wata zufa ce ke yanko mata sai zare ido take tana jin yadda ƙirjinta ke daka, addu'a take Ubangiji yasa nau'in jinin nasa ya sauya zuwa A'S.........
*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*
A hankali ta sauke botikin tallar tana sauke lumfashi ta dube Iya dake ƙirga kuɗin data miƙa mata na cikin tallar.
"Ya naga babu naira ɗari biyar kuma, ina ta shige?"
Na'ima ta yi ƙasa da kanta tana cewa.
"Iya yinwa naji shi yasa na ci"
Baki buɗe Iya ke duban Naima tana nunata da yatsa ta ce.
"Ban gane kinci abinci ba?, yanzu ke Naima har abincin ɗari biyar ɗin kika cinye?"
"Iya yinwa fa naji shi yasa, kuma ai banci komai ba shi yasa na ci ɗin"
"Ai kuwa yau zaki gane kin ci abincin ɗari biyar yarinya"
Inna na daga zaune ƙofar ɗakinta tana girgiza kai, tausayin yaran na kamata.
Ɗaukar waya Iya tayi tana danna ma Kawu Isa ya zo dole ne a matso da aurenki da Musa nan kusa-kusa tunda kin fara nuna kin gagari mutane"
Fashewa da kuka Naima tayi tana nufar inda Inna take tana cewa.
"Wallahi bana son Musa"
"Marar kunyar banza, ɗan uwan naki kike ikirarin baki so?, to idan anyi auren naku kisa kansa gabas ki yanka dan tsohuwarki"
Mita kawai Iya keyi har Khadija ta shigo gidan itama ɗauke da kayan talla.
Bata tsaya wani abu ta miƙa ma Iya kuɗin tallar itama tana nufar inda Naima take zaune sai kuka take.
"Ke ina kuma zaki je?, ai kin tsaya dai na ƙirga kuɗin ko?"
Shiru Khadija tayi tana yin gaba ta rabu da Iya, danta lura yau dama Iya da rigima ta tashi.
"Ya Naima miya faru kike kuka?"
Naima na hawaye ta ɗago zatai magana Mubeena ta shigo gidan.
Bata idasa saida abun tallar nata ba ta shigo gidan, tana dungurar ma da Iya kayanta ta wani damƙa mata kuɗin tana yin gaba wajan ƴan uwanta tun daga can take cewa.
"Miya faru kuma?"
"Ke wai Mubeena mi yasa baki da kunya data ido ne?, ni zaki dungure ma abinci?, tsabar rainin wayo ma ko baki saido min abincin ba"
"Iya bana da lokacin ki a yanzu"
"Lahhh haula walaƙuwata. Mubeena rainin naki har ya kai haka?"
"Mi ya faru ne Ya Khadija?"
"Ba komai"
Cewar Naima.
"Ya Khadija miya faru ki gaya min?"
"Nima wallahi Mubeena ban sani ba, tabbayar da nake mata kenan nima, sai gaki kuma"
"Dan Allah ki gaya min Ya Naima"
Tashi Naima tayi tana nufar ɗakinsu tana cewa.
"Ba komai"
"Wai mi yasa zurfin cikin Ya Naima yayi yawa ne?, ita da Inna halinsu ɗaya, yaushe zaku zauna ana danne maku haƙƙi amma kuyi shiru?, idan bazaku iya ba ku gaya min mana ni na ɗauki mataki"
"Ki ɗauki mataki ke a su wa iyee, ƴar nema?"
Juyawa tayi tana duban Iya kanta tsaye ba shakka ko tsoro ta ce.
"Ni a ƴar uwarsu kuma jininsu man. Duk da nasan abunda ke faruwa bai wuce kece musababinsa"
"Mubeena karna sake jin bakin ki a nan wajan, wuce kiyi abunda ke gabanki"
"Amma Inna dan Allah mu shikenan bamu da ƴancin yin komai sai Iya?, ita zata rinƙa yankewa duk wani abu na rayuwarmu ne? dan kawai....
"Bakin ki bazai iya shiru ba kenan?. To kiyi yadda kikaga dama Mubeena"
Inna ta faɗa tana tashi ta shige ɗaki.
"Eh da anyi magana ƴarki tana yi ma mutane rashin kunya iyaka abunda zaki ce mata kenan ai, tsabar dama kece ki zuge ta tana min rashin kunyar, wallahi duk na kusa maganinku daga ke har ƴaƴan naki"
Wani tsaki Mubeena ta saki tana kallon Iya da wani bala'in haushi, danji take kamar taje ta make Iya, dan tasan ba mai hassasa duk wannan abun sai ita.........
*TAURIN KAI*
*Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO...*
PAGE 6
*Ƙofar Marusa, Katsina state Nigeria*
*HANNAH POV*
"Babu fa duk inda naje"
Cewar Hannah tana miƙa mata kuɗin dake hannunta.
"To wai ke dole sai kinci indomin da kwai?, kawai kisa a sayo miki awara man, yanzu rana ta take dama ya za'ai a samu masu shaguna?, ai sun tafi gona tunda yanzu dama Kaka ce aikin gonaki yayi yawa"
Taɓe baki tayi tana duban Maryam datai maganar ta ce.
"Nifa nama gaji da fita tun ɗazu nake fita fa, ga yinwa na fara ji"
Ammi dake fitowa daga ɗaki ta ce.
"Yo yinwa ko ai dole kiji ta. Amshi nan kije ki sayo awara ta ɗari biyu"
"To Ammi ni fa?"
Cewar Fannah tana turo baki.
Wata hararara Ammi tayi ma Fannah tana cewa.
"Ai ko ina bawa kowa ke kam bazan iya baki ba. Ba jiya kinyi ƙunshi nan-nan masu ƙunshin nan suka zo kika yi masu suka baki kusan dubu biyar amma ko naira biyar baki bawa kowa ba, saima ɓoye kuɗin naki da kikai kika fice kikayo sayayyarki, dan haka kina da kuɗi bada a sayo miki, dan itama nasan babu su ne shi yasa zan bata wallahi"
Turo baki tayi tana shigewa ɗaki ta ɗakko naira ɗari biyar ta fito.
Aunty Haja dake zaune gefe tana danna ƙatuwar wayarta ta dube Hannah ta ce.
"Kije cikin ɗaki ki ɗakko min jakata ta nan kizo"
Murmurshi ta saki tana wucewa ɗakin nasu ta ɗakko ta dawo.
Amsa tayi tana kallon Aunty Sa'a ta ce.
"Ke ba abunda za'a sayo miki ne?"
"No banda ko sisi ni wallahi. Amma bari Aysha ta zo ina binta dubu ɗaya ko za'a samu wajanta"
Jim kaɗan Aysha ta fito tana cewa.
"Yawwa kinga ga ma kuɗin nan naki amma fa a account suke. Muje ke Fannah na fitar dasu saina baki"
"Yanzu dai yadda za'ai a haɗa kuɗin nan ga dubu biyu nan a hannu sai a sayo abinci a dafa ina ganin shi yafi, saiya fima isarmu akan a rinƙa sayo na waje"
"Hakane kam sai yafi. Ke Hannah ki sayo taliyar turawa da wake kwata, taliyar guda biyu ta isa, sai manja da yaji nan makwaftanmu ana sayar da dakakke, sai aci taliyar da wake da manja da yaji"
Kowa yayi na'am da abunda Maryam ta ce suka fita ita da Aysha.
Suna zaune iskar tsakar gidan na kaɗasu suna ɗan labarai kaɗan ijunansu, har su Hannah suka dawo da sayayyar a hannunsu.
Dandanan Hannah ta fara kiciniyar ɗorawa.
"Ke Fannah ki tashi mana ki kama mata, ance komai sai dai ita tayi"
Turo baki Fannah tayi tana miƙewa tana cewa.
"To ba ita ce ƙarama ba?"
"Ahh, to dan ita ce ƙarama sai aka ce kullum ita ce mai aikin gidan nan?, duka ma wai shekaru nawa ne kika bata ba biyu bane wai?"
"Yo amma Aunty Haja ai na dai batan kuma na girmeta ko?"
"To yanzu dai ki gyara mata wake ita kuma tayi sauran, dama ai ta saba"
Cewar Ammi.
Aysha ta dubi Fannah ta ce.
"Kawai ki raba masu aiki, uwar mi take a gidan"
Sake turo baki tayi tana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa, dan tasan Aysha dama da iya zuga mutum, dan sunga sune manya sai abunda sugaka dama suke yi.
Ammi na shirin magana akayo sallama cikin gidan daga zaure.
"Ah ah wa nake jin muryarsa ne kamar fa Kawu Sama'ila?"
Faɗin Aunty Sa'a tana sake gyara zamanta da mamaki.
"Muryarsa ce mana, ko uba*nmi ya zo yi a gidan nan?. Yaushe rabon da muga irinsu a gidan nan?"
Kusan kowa daga cikinsu bai amsa sallamar da yake ta kwaɗawa ba, sai Hannah ce mai ƙarfin halin amsawa.
Ammi kam tashi tayi tana saka Hijab ɗinta dage akan igiya tana faɗin.
"Ai wa'innan ƙannan Uban naku basa da mutumci. Bari naji dame ya zo kuma, nasan dai ba haka nan ya zo ba, tashi ce zata kawo sa"
Kamin ta ƙarasa ya sanyo kai cikin gidan.
Yana wani basa ido yana zaro su waje.
"Wato ma ana jina shine ina ta kwaɗa sallama ko a samu wadda zai amsa min, kuma gaku nan zube a tsakar gidan?"
Ammi bata damu ba ta ce masa.
"Yanzu nake shirin maka iso ai. Ina dai fatan lafiya ko?"
Wani kallo ya jefa mata yana cewa.
"Kamar ya lafiya?, nida gidan Yayana na zo kike kiran lafiya dai?, ga ƴaƴansa nan a zube dan nazo sai ki wani ce lafiya?, ko ana canzawa tuwo suna ne?"
Wani murmurshin taƙaici Ammi ta saki ta ce.
"Ohh Allahu sarki, ai na ɗauka ko hannun naku ya raɓe ne ku yanke kun yar ai?, saboda ni banga alamar cewar ƴaƴana naku bane. Kawai ka faɗi miya kawo ka dan nasan ba haka nan zaka zo nan ba"
Cike da ɓorin kunya ya fara nuna Aunty Haja dake banka masa hararara su Maryam na taya ta wajan aika masa wani kallo.
"Wato ita wannan tsabar bata da hankali da aure a saman kanta take zuwa tana tsayawa da wasu mutanen banza ko?. To shi mijin nata ya zo ya same ni, dan haka dole zata zo ta koma ɗakin mijinta tunda dai ba sakinta yayi ba"
Ai Aunty Haja bata san lokacin data miƙe tsaye ba tana cewa.
"Wallahi ba inda zan koma. Wato shine ma yaje ya kai ƙarata wajanka ko?, to yayi a banza, dan babu inda zani, aure ne na gamasa da shi wallahi"
"Keee Hajara ina magana kina magana dan ƙaniyarki?"
Turo baki tayi tana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.
"Ke yanzu Salame kina ji tana gayan magana amma kikai shiru?"
"Ahhh, to miye kika so na ce mata?, haka kawai ku baku san cinsu ba, ku baku san shansu ba, baku san ya muke rayuwa ba, kun watsar damu, sai kawai abu ya zo ku rinƙa nuna isa da gadarar wai ƴaƴanku ne, to wallahi bazai yiwu ba, ƴata dai ta ce bazata koma ba, dan haka bamai mata dole wallahi"
"Haka kika ce Salame?"
"Haka na faɗa ko da magana ne?"
Ta faɗa kanta tsaye tana jefa masa wani irin kallo.
Girgiza kansa yayi yana yin wata kwafa ya juya kamar zai tafi sai kuma ya dakata tana cewa.
"To bari kuji, koma miye yaje ya dawo a cikin rayuwarku babu saka hannu na a ciki, tunda ke Salame baki da tunani da hankalin da zaki saka ƴaƴan nan sunyi abunda shine dai-dai, kin fara ɗorasu akan hanyar da bamai ɓillewa ba ce"
"Ahayee ashe har kasan dai-dai kai?, ai idan kunsan dai-dai gaba ɗayanku bai kamata ku bar ƴaƴan Yayanku wadda duniya ya gama maku gata ba, lokacin da yana raye miye baiyi maku ba da ƙarfinsa da guminsa ba?, amma sai bayan ransa kun kasa tsayawa tsayin daga ku riƙe masa ƴaƴansa, kun watsar dasu, sai kuma ace abu ya taso sai ku rinƙa nuna isar cewar ƴaƴanku ne?, ai bazai yiwu ba wallahi. Kuma cire hannu ka daɗe baka cire ba wallahi, yo fita daga rayuwarsu na nawa ne bakuyi ba?, ko yanzu miye kuke masu?, ai babu shi, dan haka na faɗa na sake faɗa ƴata bazata koma ba, sai naga yadda za'ai kuma"
Ganin yadda Ammi ke faɗa har muryarta na rawa zata saki kuka, dan sosai abun ke taɓa ta, tunowa da Mahaifinsu Hannah ɗin lokacin da yake da rai, yadda ya rinƙa bauta ma ƴan uwansa baya son laifinsu ko kaɗan, amma su sai gashi bayan ransa sun watsar da nashi.
Ficewa yayi gidan yana wani banbamin faɗa da borin kunyar Ammi na masa rashin kunya taje kuma zata gani.
"Taga alheri wallahi ta Allah bata mutum ba"
Cewar Fannah tana tashi itama ta kamo Ammi ita da Haja suka zaunar da ita akan tabarmar da suke zaune Aunty Haja ta ce.
"Haba Ammi ki daina kukan nan mana. Yanzu akan Kawu Sama'ila ne zaki zauna kina ɓata ranki a banza?, kamar baki san halinsu ba?"
Goge hawayen Ammi tayi tana duban Haja ta ce.
"Kin san abunda ya ɓata min rai ɗaya ne, yadda na tuno da Mahaifinku lokacin da yake dashi yana raye, yadda suke masa kamar su kwanta masa, idan sukaga kuma sun gama cin moriyarsa dama haka suke masa su watsar dashi, sai wata hidimar ta tashi suke sake nemansa, sai gashi yanzu baya da rai sun manta da bayansa daya bari, sai yanzu wai zasu fara nuna isar tasu, to wallahi bazan taɓa yarda ba"
"Ai muma nan Ammi bafa yarda zamuyi ba yawwa, sunma gama abunsu, nuna isa kuma ta banza, tunda bamai baka ci ko sha a cikinsu, bare wai har kaji tsoron ya daina baka"
Cewar Aunty Sa'a cike da jin haushin dangin Mahaifin nasu.
Kowa daga cikinsu sai tofa albarkacin bakinsa yake akan dangin uban nasu, da dama cike suke da bala'in haushinsu.
Hannah ce kaɗai baka jin muryarta a tsakar gidan tana ta aikin abincin da take dafa masu, duk da itama sosai take jin haushin dangin Baban nasu.
To amma ya zasuyi