Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
Isa nan ba, sai abunda suka ce shine kike yi, yanzu ba gashi ba yadda ya ce jikinki na rawa kike ƙoƙarin kare kanki ba, sai mu dan..
Tassssss
Inna ta ɗauke Khadija da wani kyakykyawan marin da yasa ta gigicewa tana dawowa cikin hayyacinta, dan ita kanta bata san lokacin da ɓacin rai ya ɗebe ta ba harta furta maganar.
"Innahhhhhh"
Khadija ta faɗa a zabure da mamaki.
"Na mare ki, ita ɗin sa'arki ce ko kuwa shi Yaya Isan sa'anki ne da zaki tsaya kina faɗar magana kanki tsaye kamar haka?. Rakiya dai kuka fito dama kuyi ma Mubeena ko?, to ta isa haka nan, ku wuce ku bar wajan nan tun kamin na ɓata ranku ku duka"
Inna ta faɗa tana nuna masu hanyar komawa ɗaki.
"Yo na banza wallahi tunda dai yaran nan ba ganin kowa suke da gashi ba, kuma Khadija ni dai kike gaya ma haka ko?, zan ɗauki mataki ne akanki kema dan ubanki"
Iya ta faɗa tana nuna Khadija da yatsa haɗe da yin kwafa tana cije baki.
Kalmar ɗaukar matakin da Iyar ta faɗa ce tasa ma Inna jin gabanta ya yanke ya faɗi, daurewa tayi tana duban Musa ta ce.
"Ya kamata zuwa yanzu kunzo ku tafi ko?, waje nata ƙurewa"
"Eh Inna Binta ya kamata muzo mu wuce kawai, ke ɗakko taho mu wuce"
Ya ƙare maganar yana kallon Mubeena dake binsa da wani mugun kallo.
Iya ta taɓe baki tana cewa.
"To Allah ya tsare Musa sai munyi waya ko?"
Da kyar ya iya amsa mata dan haushinta yake ji, yayi gaba abunsa.
Mubeena ta take masa baya Kawu Isa ma yayi ma Iya sallama yabi bayansu dan dashi za'a tafi har zuwa wajan Motar da zasu bi zuwa Lagos ɗin.
Inna ce ta kamo hannun Mubeena suka nufi wajen tana sake mata nasiha sosai haɗe da damƙa mata wata waya tana ce mata gata nan ta neme su ata wayar nan sun rinƙa jin yaya take, dan jiya tasa Na'ima Musa ya sayo wayar sai yau dama idan zasu tafi ta ce zata bata wayar, saura kaɗan ma hayaniyar da taso ta zama faɗa yau ɗin ta mantar da ita ta bawa Mubeena ɗin.
Har ƙofar gidan Inna ta rako ta tana kallonta harta ɓacema ganinta.
Inna saida ta goge hawaye kamin ta koma cikin gidan tana jin kewar ƴarta sosai, hankalinta ya ɗan kwanta ne kawai dan sunyi magana da Zubaida, har Zubaidar ke faɗin insha Allah zata rinƙa masu aike akai-akai, tunda har ita Innar ta sake nemanta ta kuma yafe mata, shine kawai jin daɗinta.
Mubeena kam taka ƙafarta kawai take tana bin bayansu Kawu Isa da Musa dake tafiya, tana yi tana kallon garin nasu wata kewar garin na saukar mata.
A haka har suka ƙaraso bakin wata babbar Mota irin wacce masu tafiya Lagos cirani ke hawa.
Kawu Isa ne yayi magana aka ce ita ta hau gaban Motar kusa da driver ita da wani karan Mota suka shige gaban Motar, da kyar Mubeena ta hau Motar saboda uban bisan Motar wajan hawa, shi kuma Musa bayan Motar ya hau inda samari suke cike da bayan Motar. Matasa ne da yawa wa'inda suka saba tafiya cirani Lagos kowanne ka gani da kullin kayansa wani ma ko kayan babu riƙe a wajansa, kowa ya samu waje ya zauna, ga bayan Mota a buɗe Allah yaso su lokacin zafi ne ba'a fara ruwa ba, amma wasu harda barguna suka taho saboda cikin dare.
Shima dai Musan ya taho da nasa dan cikin jakarsa harda bargon yayo guzurinsa, haka kuma dama ya faɗama Na'ima a haɗuma Mubeena komai da suka sani na amfani, dan a aƙalla sun iya kwanaki biyu ko uku kamin su isa Lagos............
PAGE 47
*HAJA POV*
Wayar dake hannunta ce kira ya shigo tana cikin amfani da ita tana kallon wani films tana daga zaune a tsakar gidan.
A zabure take kallon cikin wayar tata da wani irin maɗaukakin mamakin wadda ke kiran nata a yau, ai da wani irin sauri ta miƙe mamaki kwance akan fuskarta sosai.
"Aunty Haja lafiya dai?"
Aysha ta faɗa tana binta da kallo ganin yadda duk ta ruɗe lokaci ɗaya.
Saida ta ƙara mai-maita mata maganar danta faɗa cikin tunani sosai.
"Aunty Haja ki ɗauka mana lafiya har kiran ya tsinke wani ya sake shigowa, waye haka mai kiran naki da har kika kasa ɗauka?"
Wani irin lumfashi ta sauke tana jin wani iri a jikinta mamaki na daɗa kashe mata ilaihirin jiki.
"Kin san waye yau ke kira na kuwa Aysha?"
"Ya zan in sani ya kamata ki ɗauki kiran ai ko?"
Jiki na rawa haka ma hannunta ta latsa wayar ta ɗauki kiran shiru tayi kawai tana jin sautin muryarsa da duk duniya ke sata cikin wata irin faɗuwar gaba, muryar bawan Allahn na sakata cikin wani irin hali wadda ita kanta bata ce gashi ba.
Abunda ya faɗa mata ne ya sake bata mamaki, jiki na ɗan rawa hakama muryarta ta amsa masa da insha Allah zai iya zuwa tana nan gida yau
A ƙarshe taji an yanke wayar.
Wata irin harbawa zuciyarta keyi da kyar ta iya saita kanta ta dawo da dubanta inda Aysha take zaune tana mata kallon mamaki.
Zama kawai tayi inda ta tashi tana kallon Aysha.
"Mike faruwa ne wai?, waye ma ya kira kin?"
"Hmm bari Aysha wai yau ni ce Alhaji Ma'aruf ke kira da kansa, anya-anya kuwa ba ɓatan number yayi ba?"
Da wani irin sauri Aysha ta zaro ido tana rufe bakinta da hannu cike da murna ta ce.
"Wallahi da gaske shine ɗin?"
"Shine wallahi Aysha"
"To ba wani ɓatan number da yayi, wallahi addu'ar da kika dage da ita ce Ubangiji ya fara amsa miki, na yarda da maganar Hannah da take cewa sallar dare nada mugun amfani ga bawa, ai ko koni zan dage da yinta. Ke kinga ikon Allah?"
Aysha ta ƙare maganar tana riƙe baki.
"Ai shi dama Ubangiji buyi ne gagara mitsali, babu abunda yafi ƙarfin Allah, bare dama sallar daren nan da nake gaya maku, wallahi komai wahalar abu idan har kina yinta kika dage wallahi komai wahalarsa sai kin cimmasa a rayuwa"
Jawota Aunty Haja tayi tana kallon Hannah ta ce.
"Ni banma san wace irin godiya ce zanyi miki ba ƴar ƙanwata, da har kika iya tunasar damu wannan abu, da muna can muna wahalar banza a wajan Malamai maƙaryatan banza, sai cinye mana kuɗi suke, ga Ubangijin da basai ka basa ko sisi ba jira yake kawai ka roƙesa shi yayi maka"
Jinjina kai Hannah tayi tana murmushi ta ce.
"Ai Aunty Haja dama su wa'innan Boka ko Malaman duk yawancinsu wallahi maƙaryata ne, saboda ƙarya suke su san abunda zai iya faruwa gobe ko anjima, wannan ai sai Ubangijin da yayo mu kawai shine masanin abunda ke fili dana ɓoye. Shi Ubangiji idan har zaka roƙesa da zuciya ɗaya sana ka koma gefe kayi hakuri to tabbas zaka ga biyan buƙata a lokacin ma da baka taɓa tsammani ba, sana shi Ubangiji idan yayi abu yayi kenan fa. Da ace aikin Malaman nan ne ya ci Alhaji Ma'aruf harya zo inda kike to da zance miki wallahi kinyi a banza, saboda kowanne lokaci abun nan fa na iya sakinsa ya ƙarye shikenan kuma zaiji kamar ma bai taɓa saninki bane, yaya akai harya aure ki, idan ma har anyi auren kenan, shi ko Ubangiji idan har yasa masa sonki da son kasancewa tare dake yafa saka masa ne na har abada"
"Allahu Akubar Hannah, mu kam ai sai mu gode ma Ubangiji daya sakaki a cikinmu, ai duk wadda zaiyi abu ya rasa mai faɗa masa gaskiya, to tsakani da Allah yayi babbar asara babba kuwa"
Cewar Aunty Maryam dake fitowa daga ɗaki itama tun cikin ɗaki take juyo maganar Hannah ɗin na masu wa'azi.
Ammi ma fitowa tayi daga toilet tana kallon Hannah cike da alfahiri tazo ta zauna akan kujera tana dubanta ta ce.
"Sai yau ne naji ina alfahiri dake ƴar nan Allah dai yayi maku albarka"
Da amin suka amsa Hannah na murmushi zatai magana Fannah ta ce.
"Gwanar iya magana ce ke Hannah, amma wai ma duk ina kika san wa'innan fatawowin ne?"
"A Islamiyarmu mana, kuma Ya Ustaz ke yawan koya mana duk abunda kika ji na faɗa, shi yasa lokaci ɗaya ya shiga raina, amma gashi duk ke ce silar na daina zuwa makarantar ma"
Hararara ta zafga mata tana taɓe baki.
Ammi tayi murmushi kaɗan ta ce.
"Hannah nifa bazan bari kije ki auri wani Ya Ustaz ba yawwa, garama kawai ki ciresa a ranki, dan bama sa'anki bane, kinfi ƙarfinsa yawwa kiji da kyau"
Girgiza kai Hannah tayi da sauri tana duban Ammi da mamakin furucin wai tafi ƙarfinsa, har yanzu dai bazasu daina wani halin nasu ba kenan?.
"Ammi kifa sani babu wadda yafi ƙarfin wani, haka kuma babu wadda yafi wani a wajan Ubangiji sai wadda kawai yafi tsoronsa yafi bauta masa haka kum.....
"Ke kinga ya isa haka nan Hannah, a aje wata maganar Ustaz, dan ko ni nan ba bari zanyi ki auri wani Ya Ustaz ba, na riga da nayi miki miji ma tuni danma ki sani"
Cewar Aunty Haja tana kallon Hannah ba wasa akan fuskarta ko cikin maganarta.
Da mamaki Hannah ke duban Aunty Haja da kyar ta iya fisgo magana a bakinta ta ce.
"Miji kuma Aunty Haja?, to ni kenan baza'a bari na zaɓi wadda yayi min ba?"
Wani kallo ta watsa mata na baki da hankali kamin ta ce.
"Ke har kinyi girman da za'a barki ki wani zaɓo miji da kanki?, to bazai yiwu ba, garama ki buɗe kunnan ki da kyau kiji miji ne anyi miki shi yawwa, gara ma idan kin aje wani a cikin ranki to kiyi gaggawar fitar dashi"
"Amma...
"Ke bama son rashin kunya da'allah, ana ƙoƙarin miki gata a inganta rayuwarki amma kina ƙoƙarin botsarewa?"
Aysha ta faɗa tana watsa mata wani mugun kallo itama.
Hannah ta haɗiye wani abu daya tokare mata wuya. Wai shikenan su ƴan gidansu ba'a taɓa zama dasu a tashi haka nan sai sun ɓata ma mutum rai?, bare ma ita dan gani take sunfi ma tsanarta akan kowa.
"To idan bata so sai a kyale ta, ai ba dole a ciki, ai ita ce zatai ma kanta asara, ub*an waye zaiƙi wadda kike so ta aura ɗin?, itama tana duk wannan abun dan bata san waye wadda kuke nufin an mata mijin dashi ba"
Juyawa sukai suna kallon Aunty Sa'a dake fitowa daga ɗaki. A shirya take dan kamar fita ma zatai ta fito tana faɗar haka.
"Ina zuwa haka kuma Aunty Sa'a?"
"Wallahi Maryam zanje wani taro ne da aka gayyace ni jiya, kin san mu mukai abincin taron to yau da suka zo da safe amsar abincin suke ce min dan Allah na ɗaure naje, shine fa na amsa masu da insha Allah zanje"
"Ahhh ai ko ki tsaya ni bari na shirya nazo mu wuce tare, ai ni ina son harkar girma, naga suna da capacity ai, daga gani ba ƙananun kwari bane"
Maryam ta faɗa tana miƙewa da sauri ta nufi ɗaki domin ta shirya, dan ita kam duk inda za'ai harkar manyan masu hannu da shuni to tana nan, bata harkar ƙaranta a rayuwarta.
Murmushi kawai Aunty Sa'a tayi tana girgiza kai tana mamakin Maryam.
"Ohhh ni Aunty Maryam sai ka ce wacce aka haifa a cikin masu kuɗi, ita dai tana son harkar masu kuɗi a rayuwarta"
"To idan banda abunki Aysha ai harkar girma tayi a rayuwa, ina harkar ƙaranta tayi?"
Jinjina kai kawai Aysha tayi tana kallon Aunty Haja datai maganar.
"Na dawo kanki Hannah, mi kike cewa ne ma kamin na fito?"
Ɗagowa tayi tana kallon Aunty Sa'a data jefo mata tabbayar.
"Nifa ba abunda na ce, kawai dai na ce ni mi yasa baza'a barni da zaɓi na bane?"
"Hmm lallai ke nan har wani zaɓi gare ki?, kin taɓa saurayi ne dama bamu da labari?"
"Kuma kika buɗe baki kika faɗi sunan Ustaz ɗin nan saina bige miki shi wallahi, domin kwata-kwata ma baya ɗaya daga cikin wa'inda suka cancanci zama a jerin samarin da kika taɓayi a rayuwarki"
Cewar Aunty Aysha dake mata kallo na gargaɗi.
Turo baki tayi tana yin ƙasa da kanta zatai magana Ammi ta katse ta da cewa.
"Kinga Sa'a ya isa haka nan, ku rabu da ita, aure ne idan Allah yasa yazo hannu dan ub*anta sai anyisa idan yaso idan akayi ta datsesa da hannunta mu gani"
Da wani irin mamaki ta ɗago tana kallon Ammi daga maganar.
To waye ma wannan da suke ta magana akansa ne?, waye shi haka?, wane irin yazo hannu kuma?, mi suke nufi ne da ita wai?, ta shiga tabbayar kanta tana nazarinsu gaba ɗaya ta shiga binsu da kallon mamaki ganin yadda suke magana akansa, wadda bata san dashi ba ita kwata-kawata......
PAGE 48
*HAJA POV*
Miƙewa tayi tana buga tsallan murna harda duƙawa tayi sujjada ga Ubangiji. Su Aysha sakin baki kawai sukai suna dubanta.
Maryam ta ce.
"Aunty Haja yaya dai?"
Tana ɗagowa ta shiga sauke lumfashi ta ce.
"Messages ne naga Alhaji Ma'aruf ya turo min, ya ce zai zo gida muyi magana idan har na shirya aure shima a yanzu ya shirya bada wasa zai zo ba, ɗaurawa kawai za'ai, yanzu zasuyi wata tafiya zuwa Abuja suna dawowa zai zo da manya ayi maganar auren kawai"
Wata irin buɗa Aysha ta saki mai ƙarar gaske tana sakin wata shewa haɗe tashi tsaye tana tiƙa rawa.
"Wani abunma sai an ɗaura ahayeeee nanayeee"
Su duka dariya suka saki harda Hannah dake zaune, duk da tana cikin tunanin abunda yasa suke ce mata wai sun mata miji, toma waye wai?, abunda take jefama kanta tabbaya kenan tun ɗazu.
Zama Aunty Haja tayi tana murmushi zuciyarta fall murna mai tsananin gaske, ta ce.
"To amma ni gaskiya bazan so su Alhaji Ma'aruf su zo su ga gidan nan a haka ba gaskiya, ya kamata ace mun haɗa kuɗi anzo an rushe gidan nan an sake yin na zamani ko yaya yake ya ɗanyi dai kyau haka"
"Yawwa Aunty Haja wallahi nima abunda ke raina kenan kin riga ni faɗa ne, yaushe zaka bari maneman aurenka manyan mutane su zo suga gidanku a haka"
Fannah ta faɗa tana nuna gidan, dan Allah ya sani kullum so take dama a gyara gidan nasu.
"Ni kam so nayi kawai mu tashi daga unguwar nan ne gaba ɗaya aje can a sayi wani gidan, dan ni gida nake so mai bala'in kyau"
"Idan banda abunki Maryam yanzu ɗin ma karo-karo zamuyi gyara za'ai masa bana wasa ba, zaki ga yadda zai koma irin na ƴan gayu, ni bana so mu tashi daga gidan nan, saboda kinga dai gidan yana da faɗi da manyan ɗakuna, idan aka rushesu zasu isa ayi kowanne irin gini da muke so"
"Hakane kuma Aunty Sa'a gaskiya ba ƙaramin gida za'ai ba a nan wajan"
Ammi dake jinsu ta ce.
"Ni ai nafi so mu zauna a nan ɗin, ta yadda wa'incan dangin uban naku zasu rinƙa ci garo da ci gaban da kuke samu idan yaso baƙin cikin hakan ya kashe su, ai idan muka tashi anyi ba'ai bama kenan"
"To gaskiya kowannen ku ya kawo abunda ke hannunsa ta yadda zamu samu gini wa'inda bazai wuce a cikin sati ɗaya su haɗa gida mai kyau"
"Taya za'ai a sati a iya haɗa gini?"
"Mtsww kefa wani lokacin ƴar ƙauye ce Hannah, kuɗi ne fa ke aiki, wallahi ko a kwana ɗaya kake so sai an gama maka gini, ai kawai wuyarta ka saki kuɗin Mlm"
Fannah ta faɗa.
"Kware kuwa a kwana ɗaya ma za'a iya. Amma fa ni ason samu na ne ina so harda bene wallahi, tunda naga gidan zai iya yin gini harda bene, tunda unguwar nan gashi harda gidaje masu bene"
"Ke kuma Maryam abunki ai yayi yawa, wane irin bene kuma?"
"Wallahi Aunty Haja ko nawa ne ni naji zan bayar ina so kawai a ɗora mana harda benen komai hawa biyu ne haka"
"Kai Aunty Maryam ko dai mai hawa ɗaya ai ya isa aiko?"
"Ko dai ku rabu da ita, ba ita zatai kashin kuɗin ɗora gini ba?"
Ammi ta faɗa tana binsu da ido.
"To yanzu waye kuke ganin zamu kira a sama mana masu gini wa'inda suka iya sosai kuma cikin sauri"
"Eh ina cin garo da masu gini a Instagram kuma a nan Kt suke, zan ɗauki number su kawai sai a kira"
"Ai kawai Maryam yanzu zaki ɗauki number taso a kira su aji idan har suna da lokaci azo daga yau a fara, saboda nafi so kamin isowarsu Alhaji Ma'aruf an gama"
"Karki damu bari a ɗakko min wayarta tawa"
Ta ƙare maganar tana duban Hannah ta ce.
"Tashi ki ɗakko min wayata tana nan akan katifarmu"
Miƙewa Hannah tayi bayan ta wuce Maryam ta sake cewa.
"Sana na ɗauki nauyin kayan ɗaki insha Allah kowanne ɗakinmu zai an zuba kaya masu azabar kyau, parlo kam na saukar baƙi ba'a magana, muda muke sana'ar su ai dole gidanmu ya kasance babu ƙarya, dan idan aka gama gyaran nan lokacin ne zan fara kawo ƙawayena na amana wallahi"
"Ke ni ba wannan bama, kayan da zan tafi dasu gidan Alhaji Ma'aruf nake so kiyi min Order nasu, zan zaɓa saina turo miki, dan so nake gaba ɗaya shashina sai yafi nasu haɗuwa, ta yadda tsakanina dasu ba raini"
"Ai hakanma shine dai-dai dama, karki wani ji kin damu kawai ki turo min duk kalar da kike so za'a nemo su duk faɗin duniyar nan ne"
Dai-dai Hannah ta ƙaraso da wayar ta amsa tana shiga Instagram ta duba number ɗin tayi copy nata tana nuna masu irin gina-ginan da suke yi.
"Kam gaskiya sun iya gini sosai ma, dubi wani nan da suka gama yayi kyau wallahi"
Cewar Fannah tana leƙa cikin wayar da murna.
"To zan kira so amma fa sai mun zaɓi irin ginin da muke so mun