Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
yanzu kana nufin ka amince da aurenta da Jafar?"
Murmurshi mai ciwo ya saki irin nasu na manya kamin ya sake gyara zamansa ya ce.
"Abarta tayi abunda take so, wata rana da kanta zata zo ta ce a raba auren, bawai fata nake mata ba, amma idan yaro ya dage sai kawai ka barshi da zaɓin nasa, wata rana zai gane ashe gaskiya fa iyayen nan nasa ke faɗa masa, kuma abunda babba ya hango yaro ko ya hau tsauni bazai iya hangosa ba. Yanzu idan muka dage zata rinƙa ganin kamar ma mun danne mata haƙƙinta ne, muna son rabata da wadda take so ne. Kuma kinga shima kansa Jafar ɗin har yanzu basu zo suka ɗauki kayansu ba, duk da maganar da nayi masa, har yanzu banji daga garesu ba"
"Hmm hakane Mlm, shi yasa fa na ɗauke duk wani abu nashi na ɓoye, na gaya mata cewar sun aiko an masa dan kawai ta fitar dashi daga ranta, amma dai kagani kamar ma sake tusa mata son nashi ake. Ni na rasa gane wannan soyayyar zamani da yaran yanzu suke yi. Mu a lokacinmu ai sai dai kawai kaji ance anma wance miji, kuma baka isa ka ce a'a ba, amma banda yaran zamanin nan"
"Idan banda abunki Zainab ai mutanen da a tsaye suke akan ƴaƴansu, kuma yaran da na yanzu ai ba biyayyarsu ɗaya ba, yaran yanzu a haka ake haifosu da shegen wayonsu suke faɗuwa duniyar, baka isa ka ce ga abunda yaro zaiyi ba, sai yazo maka da wata maganar, Allah dai ya ƙara shiryar mana dasu kawai, amma yaran yanzu ba kunya ko kaɗan a tattare dasu"
"Ni Mlm abu ɗaya fa nake gudar masu daga Jafar ɗin har ita Mimin wallahi. Gashi dama ƴan uwa kamar jira ake har an fara yayato wai an fasa bikin har sun fara shirin ƙaƙuba masa wai Shamsiyya"
"Uhmm nima naji, dama ai can ita Shamsiyyar tana nuna tana son nashi, ƙananun maganganu ne daga cikin family nashi da namu mu kanmu duk ina jinsu suna dawowa ƙunne na, Allah dai ya tabbatar da alkhairi idan kuma babu Allah ya kauda abun shine kawai"
Sun daɗe suna tattaunawa akan al'amarin bikin Jafar dana Mimi daya zo masu da tangarɗa..
*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*
Zama tayi tana yin shiru sosai, tun bayan abunda ya faru da Iya ta sanar dasu ta kasa gane kan Ya Naima.
Yanzu ma zaune take tayi shiru tayi tagumi. Daga Inna har Ya Naimar sun zama sai a hankali.
"Wai Inna bazaku iya sanar dani miye yake damunku ba?, nida Ya Khadija, nake ganin ai damuwarku damuwarmu ce ai ko?"
Inna dage shirin magana suka jiyo maganar Kawu Isa.
Kusan lokaci ɗaya da Inna da Naima suka ji wata irin harbawar zuciya, bare ma Naima data ji kamar an aiko mata da mutuwa.
Tashi Mubeena tayi tana yin waje tana iya juyo firarsu Iya da Kawu Isan.
Riƙe baki tayi tana jin abunda suke son ƙullawa.
"Ohhh wato abunda yasa su Inna cikin damuwa kenan ba?"
Can ta sake jinjina kai ta ce.
"Ai ko bazai yiwu ba, muddun dai ina raye"
Har Kawu Isa ya fito bata sani ba sai ji tayi Iya na faɗin.
"Ya rasulu Manzon Allah, ke yanzu dama laɓe kike mana Mubeena?, abun naki har ya akai kina min laɓe?"
Turo baki tayi tana ƙunƙuni.
"Ke dama abunda kike yi kenan a gidan nan?, to zaki ci ub*anki ne wallahi marar kunyar banza"
Kawu Isa ya faɗa yana nunata da yatsa.
Hararara ta zafga masa a fakaice tana turo baki.
"Ina ita uwar taki take ne"
Ya ƙara faɗa tana kallon ƙofar ɗakinsu.
Fitowa Inna tayi tana ɗan sakin murmurshi kaɗan ta shiga gaidasa, sai cewa yayi.
"Ohh ashe ana ciki?, to dama saƙo zan isar miki, sai ku fara Shirye-shiryen bikin Musa da kuma Naima, nanda sati biyu masu zuwa"
"Sati biyu kuma Yaya Isa?"
"Eh Sati biyu ku da akwai wani abu ne?"
"Ai nake ganin kamar yayi wuri da yaw.....
"Ke kinga Binta bana son rashin ta ido, wane irin yayi wuri kuma?, muna son kauda ƴaƴan nan dake gabanmu gasu nan sun kawo girma, kina neman kawo mana wata maganar banza"
Cewar Iya tana faɗa tana ma Inna wani irin kallo.
Lumfashi kawai Inna ta sauke tana girgiza kai bata ƙara magana ba ta juya ta koma ɗaki, tana iya juyo kukan Naima, da alama duk taji abunda su Iyar ke cewa.
Ita kam ya zatayi da rayuwarta, ita ba wasu ƴan uwa ba, sai ƴar uwarta ɗaya kuma tayi nesa da ita dan yanzu haka tana Logas tana sana'ar abinci, dan yanzu haka bata san inda zata same ta ba, da number tana shiga amma ta zo bama ta shiga kwata-kawata, damuwar tayi mata yawa gaskiya, ta rasa waye zata kira su raba damuwar nan a tare.
"Makira"
Iya ta faɗa tana bin Inna da kallo.
Ta juya wajan Kawu Isa suka ci gaba da magana akan bikin.
Ita kam Mubeena ta tsaye kamar ma sun manta tana tsaye a wajan, sai zagar mata uwa suke.
Kawu Isa na tafiya Mubeena tayi gyaran murya tana gyara tsayuwarta ta kalli tsabar idon Iya ta ce.
"Iya wai ko kunya ma baki ji ina tsaye wajan nan kuke zagar min uwa?. To indai ina nan wannan auren da kuke son haɗawa wallahi saina rusa shi"
Tana faɗar haka ta wuce tabar Iya sake da baki.
Riƙe baki Iya tayi a fili ta furta.
Wannan ƴar fa shaiɗaniya ce tsaf zata iya rusa abun nan fa. Anya bazanyi wani abu akanta ba itama?, bari dai Saude ta zo ita ce zan tunkara da yadda za'ai da Mubeena ta tabbatar bazata rasa shawara a wajanta ba.
Iya ke maganar a cikin ranta.
Ta sake yin kwafa kawai Iya tayi tana ƙara faɗa a zuci cewar zaki ci uwarki ne daga ke har munafukar uwar taki dake ɗaure miki gindi, duk sai nayi maganinku wallahi.......
*TAURIN KAI*
*Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.....*
PAGE 9
Zaune take akan kujera tana wanke-wanke a hankali kuma ta ƴan waƙoƙinta.
Aunty Haja ce ta fito daga ɗaki tana duban tsakar gidan tana sake dawo da dubanta inda Hannah take tana wanke-wanke ta ce.
"Gidan nan har yanzu ba'a shire shi ba?"
"Eh Aunty Haja so nake na gama na shire, yau bacci ne ya kwashe ni shi yasa ban gama aikin da wuri ba"
"Ina ita Fannah take ne wai?, ace sai ke kaɗai kullum zatai ta fama da aikin gida?, bata yiwuwa wallahi"
Shiru kawai Hannah tayi tana jin Aunty Haja ta kwala kiran Fannah ɗin dake linke a ɗaki tana shaƙar baccinta hankali kwance.
"Wai zaki fito ne ko sai nazo miki ɗakin?"
Fitowa tayi tana turo baki kamar zata saki kuka ta shiga murja idonta dake cike da bacci tana cewa.
"Gani nan fa Aunty Haja, miye nayi kuma?"
"Maza-maza ki ɗauki tsintsiya shara zaki yi, kuma daga yau kece zaki rinƙa shara a gidan nan, itaa barta girki da wanke-wanke"
Sake turo baki tayi gaba tana kwaɓe fuska ta shiga cewa.
"Yo Aunty Haja baccin ma girkin ba kullum ake samu ana yinsa ba, wani lokacin ma ai wanke-wanke ba tarasa muke bafa"
"Zaki fara sharar ne ko kuwa?"
Ta faɗa kawai tana sake zuba mata ido.
Ɗaukar tsintsiyar tayi tana jin kamar ta ɗauke Aunty Haja da mari, sai dai tasan kar tasan kar, domin duk abunsu a gidan baka isa kaga babba ya bada umarni ƙarami yaƙi yi ba, wannan tarbiyyar tun Mahaifinsu na raye shine ya tsaya tsayin daka wajan basu ita, shi yasa ma suka tashi da hakan.
Tana sharar tana mita a ranta sai sakin tsaki take yafi a ƙirga.
Tana gamawa zata koma ɗaki Aunty Haja tabi tsakar gidan da kallo, bawai dan ya sharu ba, domin sharar badan ana so aka yi ta ba.
"Dawo ki shinfiɗa min tabarma"
Wayyo Allah na, wai tabarmar ma sai an shinfiɗa ma mutum?.
Fannah ta faɗa cikin ranta tana sake ɓata fuska.
Tabarma ta ɗakko ta shinfiɗa tana yin gaba abunta dan bata ma so Aunty Haja ɗin ta sake sata wani aikin daban kuma.
Zama tayi tana latsa wayarta, bata daɗe da zama ba Maryam ta fito itama tana ɗaukar bota zata shiga bayi.
Jin babu ruwa yasa ta nufi inda ake saka masu ruwa, sai dai nan ɗin ma ba ruwan.
"Ah ah ke Hannah dama babu ruwa a gidan kuma kike wanke-wanke tsakani da Allah?"
"Wallahi Aunty Maryam babu nima haka na tashi naga gidan yau ko ruwa babu, nima nan naje kusa damu na samo shi nazo ina wanke-wanken, saboda duk babu ko kwano ɗaya na amfani duk an ɓata su"
Wani tsaki Aunty Maryam taja tana tsayawa kawai zuwa can ta ɗakko kujera kusa da Aunty Haja ta zauna tana ƙara cewa.
"Kai jama'a mu gidan nan daga yau a tashi babu kaza babu kaza, haba wallahi na gaji da rayuwa local gida irin wannan haba"
Da kallo kawai Aunty Haja tabi Maryam dashi wata dariya na ciyo ta, dan tasan Maryam dama duk ta fisu son rayuwar jin daɗi.
"Tom ki kira Fannah mana ta nemo mai ruwan sai a saya ai ko?"
"Kuma fa dan ub*anta dama ba abunda ta iya sai kwantawa tayi baccin asara"
"Fannah zo nan"
Ta kwala mata kira.
Ai Fannah dake ɗaki ji tayi kamar ta ɗora hannu sama ta kurma ub*an ihu kota huta da taso ta gaba da sukai yau, tafa gane dama gidan nan bamai sonta.
Fitowa tayi ko amsa kiran batai ba tana ɓata fuska kamar kunun kanwa tana duban Aunty Maryam.
"Au dama kina jina koma ki amsa?, kin wani fito kina ɓata fuska, mi akai miki?"
"Mifa za'ai mata aiki ne bata so, da Hannah ce wallahi ko aike nawa zakai mata bata taɓa canza maka fuska, amma kinga wannan mai son jikin tsiyar ba abunda ta iya sai taci ta kwanta kawai, sai ka ce ɗiyar ɗan gwate"
Cewar Aunty Haja.
Ita dai Fannah ji take ai kawai yau sun tashi da jin haushinta ne shine suke hucewa, kowa gani take ya saka mata ido a gidan, dan ita kam bata ga wani son jiki da rashin son aiki da take yi ba.
"To ai ta bari ta aje, ta kuma je nata gidan sai ta rinƙa wannan mulkin ai ko?"
Ta dawo da dubanta inda Fannah take tsaye kamar ta haɗiyi zuciya tsabar jin haushinsu gaba ɗaya.
"Ruwa zaki samo mana, gidan babu ruwa ko ɗaya"
Wani iri taji tana bin Aunty Maryam da kallo da sauri ta shiga ƙara kwaɓe baki tana ƙunƙunin cewa.
"Nima zan samo ruwan tabɗi jam?"
"Mi kike cewa ne?"
Cewar Aunty Maryam na ƙare ma bakinta kallo dake motsi.
"Ni ba abunda na ce. Cewa nayi a samo almajiri mana ya samo mai ruwan, ni yanzu fisbilillahi Aunty Maryam ina nasan inda zan samo mai ruwa a unguwar nan"
Ƙanƙance ido Aunty Maryam tayi tana jefa mata wani kallo kamin ta ce.
"Ke yanzu a unguwar nan ina ne baki sani ba Fannah?, bafa nason iskanci kinji, zuwa zakiyi ki wuce wancan fanfon na ƙofar gidan Buda ki samo muna mai ruwan a can"
"To ni idan an samo ma fa nacan basa bada jarka biyu ko rabin baro, baro guda fa suke saida maka, kuma kusan naira dubu baro ɗaya fa"
"Munji jeki ki samo ruwan ga naira dubu nan a hannu na"
Cewar Aunty Haja.
Turo baki tayi ta juya cikin ɗakinsu tana jin wani bala'in haushin zuwa ta samo ruwan nan kamar ita zata je samo wani ruwa.
Tana fitowa ƙofar gidan bayan ta amso kuɗin ruwan ta samu waje ta zauna tana kwala kiran wani almajiri data ga hango nesa da ita kaɗan.
Yana zuwa ta ce masa.
"Kai yaron Mlm zaka iya samo min mai ruwa can fanfon gidan Buda?, ku taho dashi tare har nan idan kazo zan baka naira ɗari ladar samo mai ruwan"
Yaro ya washe baki yana amsawa ya ruga da gudu ya tafi samo mata mai ruwan ita kuma ta sake ɓararrajewa tana sakin tsaki a fili ta ce.
"Ni naje na samo maku mai ruwa?, ai wallahi bazai yiwu ba, yadda kowa take ji da kanta nima haka nake ji da nawa kan, yo haka kawai"
Tana rufe baki kamar ance ta ɗaga kanta ta hango kamar tahowar Ustaz ɗin Hannah. Ai wani murmushin mugunta ta saki dan dama yau har Hannah ɗin ta bata haushi.
Harya ƙaraso ƙofar gidan tana kallonsa.
Shi kam da sallama ya ƙaraso wajan yana dubanta a tsanake cikin muryar nan tashi irin ta Ustazai ya shiga tabbayar ta Hannah na cikin gidan kuwa?, fatan tana lafiya?. Yana sake tabbayarta yaga yau kusan kwana biyu kenan bata je Islamiya ba.
Tashi tsaye Fannah tayi tana sake kallonsa sama da ƙasa.
Shi kam Ustaz ganin kallon da take binsa dashi ne yasa shi fara bin jikin nasa da kallo shima, ko zaiga abunda Fannah kema wannan kallon wulaƙanci haka.
"Wai Mlm dan Allah kana haka da kai har kake ikirarin wai kana son mace kamar Hannah?, dan Allah kai kanka kaga dacewar ku ne?"
Gyaran murya yayi yana cewa.
"Ban fahimci inda maganar ki ta dosa Yahh ke Fannah?"
Taɓe baki tayi tana jin wani ƙarƙabu wajan Ustaz wai za'a ce Fannah sai an wani ce yahh ke Fannah.
"Au baka fahimta bane?. To bari nayi maka gwari-gwari, to Hannah dai Ammi ta soke soyayyar nan taku, sana daga rana irinta yau bakai ba ƙara zuwa ƙofar gidan nan da sunan neman Hannah, kai a ƙarshe ma Islamiyar bata sake zuwa"
"Subhallahi, Subhallahi Subhallahi, wa'iya zubillahi"
Wani ja da baya Fannah tayi tana kallonsa da wani maɗaukakin mamakin wannan a'uzubiyya daya ja sai kuma saki murmurshi ta ce.
"Shaiɗan ka gani ko baƙin aljani yahh Ustaz da kike tajan wannan salati?"
"Akan mi zaku hana Hannah zuwa neman ilimi?, idan dan ni ne na haƙura da son nata amma abarta dai ta rinƙa zuwa neman iliminta"
"Mtsww eh ba shakka saura daga can tana zuwan kuna haɗuwa ka rinƙa samun damar hure mata kunne ba?"
Ustaz zaiyi magana kawai suka ji kukan Hannah daga zaure ta fashe da kuka. Dan tsaf ta gama jin yadda Fannah ta gama zubar mata da mutumci a gaban Malaminta. Dama tazo fita ne Aunty Aysha ta aketa ta sayo masu fulawa da mai da kuma yis za'ai fanke a samu a karya da safen, kawai ta sayo kai taji tashin maganar Fannah shine ta tsaya tana jin yadda Fannah ke zubar masu da mutumcin gida a gaban wadda take tsananin kunya.
"ke kuma miye haka?, zaki wani zo kina sakar ma mutane kuka a nan?"
"Wallahi Allah Aunty Fannah kin gama dani, miye haka yanzu a gaban Malamina, kika tsaya kina zubar min da mutumci a gabansa?, ina ruwanki da alaƙalar dake tsakaninmu ne wai?"
Wani irin kallon mamaki Fannah ke bin Hannah dashi kamin ta ce.
"To naje na faɗa ɗin, kuma daga yau bake babu shi, ke wallahi ma saina zuga Ammi har Islamiyar baki sake zuwa, kina wasa dani kenan ko?"
Kuka kawai Hannah ta saki tana fitowa daga gidan ta wuce tabarsu tsaye Ustaz na son tsaida ita amma tayi nisa dan da sauri tabar ƙofar gidan.
Shi kam rasa mima zai ce yayi, sai kawai ya shiga girgiza kai yana barin ƙofar gidan shima jiki a sukwane.
"Ohhh abu kamar ba namiji ba, ji wata tafiya dan Allah, ita kanta tafiyar ma sai an mata iyayi"
Fannah ta ƙare maganar tana bin yadda yake tafiya da kallo.
Mai ruwan da almajiri ya samo ne suka ƙaraso da yaron, tana murmushi ta sallami yaron, tana ma mai ruwan magana ya shigo da ruwan ta fara basa kuɗin ruwan a hannu tayi gaba zuwa cikin gidan mai ruwan na bin bayanta da ruwan zuwa cikin gidan.......
*Idan kuna son ci gaba da karanta wannan book zaka biya naira dubu ɗaya ne 1k kacal ba yawa, kai tsaye za'a fara tafiyar da kai, karka bari karki bari a baka labari, domin salo da wata zazzafar soyayya na daban ne a cikin wannan littafi. Yanzu ne ma aka samo tafiyar, saboda wasu taurarinma basu gama bayyana ba tukunna, saboda yanzu muka fara kutsawa ainafin cikin labarin*
*Kaidai kawai ka saka kuɗinka ata asusun dake ƙasa👇*
Account number 8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank.
Shaidar biya 👇
08130479973.
*TAURIN KAI*
*Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO......*
PAGE 10
"Wai minene kin shigo kina ma mutane kuka?"
Ammi ta faɗa tana kallon Hannah dake zaune gefe tana kuka.
Fannah kam taɓe baki tayi tana ƴan waƙoƙinta ta wani juya ƙeya ko a kwalar rigarta.
"Ba magana ake miki ba wai?"
Cewar Aunty Aysha.
Cikin shashashakar kuka Hannah ta fara cewa.
"Ammi ba Fannah ba ce kawai daga fita ta na iske tana ƙorar Ya Sayyadi na Islamiyarmu ba, miye yayi mata dan Allah?, inama ruwanta dashi to?"
Riƙe baki kawai Ammi tayi tana kallon Hannah da mamaki. Aunty Aysha dake zaune da Aunty Haja suka saki wani ɗogon tsaki.
"Ke yanzu dama duk akan wannan Ya Ustaz ɗin kike kukan nan haka?"
Turo baki tayi tana ƙara ɓata fuska jin abunda Aunty Haja ta ce.
"Rabu da ita Haja wallahi ub*anki zanci, kuma ni Fannah kin min dai-dai ma, ai da ni ce ma abunda zan masa kin san sai yafi na wadda Fannah ɗin tayi masa, ai wata ƙala tayi masa da sauƙi ma, yo ina ruwan biri da gada ma?, ai hanyar jirgi daban ta mota ma daban, dan haka ki kiyaye ni fa Hannah tom"
Ammi ta ƙare maganar tana nuna Hannah da yatsa.
Wani kukan ne ya sake sarƙeta tana tashi tsaye cikin muryar kuka ta ce.
"Haba Ammi kin san miye ta ce masa ma?, cewa fa tayi wai ban sake zuwa ma har Islamiyar"
"To naje na faɗa, baki sake zuwan sai kisa kaina gabas ki yanka marar kunya kawai"
Fannah