Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 47

21K to 24K   out of 140.3K words

fara sana'arta itama, dan yanzu gidan ita kaɗai ce bata wani abu, dan yanzu Fannah ita kanta masu ƙunshi har layi ake yi, taji uwar bari ta koma ƙunshin gadan-gadan, dan ba ƙaramin samu take da ƙunshin ba yanzu, dan yanzu sai tai ƙunshi a bata har dubu hamsin kai wasu ma ƴan gayun idan suka zo har fin haka bata suke, har fasta aka maƙale mata a ƙofar gidan ta ƙunshin da take yi yanzu. Aunty Aysha ma kaya ne take saidawa a online itama irinsu atamfofi da shadda, suna kasuwancinne da wani ɗan Kwari a Kano, kana turo kuɗinka duk inda kake za'a kai maka. Maryam dama ita tuni tata sana'ar ta yo Order kayan ɗaki, kama dana kitchen duk tana yi yanzu, da yake tana tare da ƴan gayu da yawansu suke mata cinikin, kuma tana ɗora ribarta tana samu sosai.

"Eh Aunty Haja na iyasa"

"Wai ni kam a inama kika koya ne?"

Cewar Aunty Sa'a.

"Haba kin mance lokacin tun Baba na raye ne ya saka ta makarantar koyin Cake kowanne iri ne?. Ai lokacin komi take so shine yake mata, saboda ta zo a auta, kuma mai sunan Inna ce ai ko?"

Maryam ta faɗa tana duban Aunty Sa'a datai tabbayar.

"Haka akai sai yanzu ma na tuna wallahi"

"Tom shikenan yanzu tunda kin iya Cake ɗin sosai, kuma nan wajan Aunty Sa'a akwai kayan sarrafasa da yawa, zan baki wasu kuɗin gobe keda Fannah ta raka ki kuje kasuwa ku ƙaru abubuwan yinsa, da komai da komai, sana zan sai miki waya kema sai ki fara tallar kina yinsa, zaki ga an fara saka Order insha Allah kema ki fara sana'a, dan bana so ana tabbayata kuɗi ko wani abu. Kema Fannah zan baki dubu ɗari biyu ki ƙaro kayan Lallai dasu Mahallabiya da dai sauran kayan ƙunshin ki aje a gida"

Wani kalar daɗi ne ya rufe Hannah har ta kasa ɓoyewa tana miƙewa tsaye taje inda Aunty Haja take ta rungume ta tana godiya.

Fannah kam tsallan murna ta fara tana murmushi.

"Nima Aunty Haja zan sake wayar domin tarin kuɗi na nake dama zan sayi IPhone ne mai camera kin san mu masu yin lallai dole sai da waya mai camera yanzu"

"Itama ɗin IPhone zan saya mata ai, saboda idan tayi Cake ɗin ta rinƙa ɗaukarsa photo mai kyau ta yadda za'a gani ana sha'awar zuwa wajanta ayi Order"

"Kai ai ko nima gaba ɗayanmu zamu tafi ya kamata nima na mallaki IPhone ɗin nan"

Cewar Aunty Sa'a.

"Ko wai dama nasan duk zaman nan dole zaku dawo amfani da ita ai, shi yasa nida Aunty Haja dama can bama iya riƙe wata waya sai IPhone"

Maryam ta faɗa tana kallonsu gaba ɗaya. Dan dama ita tuni IPhone ɗince a hannunta, dan yadda take shiga wajan ƴaƴan manya dole tasa ta tara kuɗi ta saya, dan yanzu haka babbar ce a hannunta irin wa'inda manya da ƴan gayu ke riƙewa a hannunsu, ita kam Aunty Haja dama kyautarta aka basu can wajan siyasar da take yi, bata da matsalar riƙe waya kowacce iri ce.

Ammi na shirin magana akayo sallama cikin gidan.

Ɗagowa sukai suna bin Kawu Sani da kallo daya shigo gidan kansa tsaye.

Sannu kawai sukai masa ya amsa cikin wata irin sakin fuska kamar bashi ba, har abun yaso basu mamaki, amma sai kowannensu ya share.

"Wajanki na zo fa Hajara"

"Ni kuma Kawu Sani?"

Aunty Haja ta faɗa tana nuna kanta da hannu da mamaki.

"Eh fa dake. Sana akan yaron nan Mijinki Umar. Mi yasa bazaki haƙura ba ki koma ɗakin ki ba?"

Wani lumfashi ta sauke mai zafi, ganin yadda yau yake mata magana cikin rarrashi ba tare da faɗa ba, sai itama ta dubesa da Ammi zatai magana amma Haja ɗin tayi saurin cewa.

"Kawu Sani bazan iya komawa gidan Umar ba, dama abunda yasa muka rabu gaskiya bawai na gujesa haka nan kawai bane a'a, na fara harkokin siyasa ta tun a gida, tun kamin na auresa dama ina da wannan burin na shiga siyasa nima a dama dani, amma da yaga munyi aure sai ya fara murje idonsa cewar ban isa nayi wata siyasa ba, kai hatta sana'a wannan cewa yayi bazanyi ba, bazata yiwu na rinƙa tara masa mutane a cikin gida ba, shi yasa ni kuma duk yadda nake son zama dashi na kakkaɓe auren nasa na taho gida, shine kawai, kuma yanzu hakama idan bai bani takarda ta ba wallahi Koto zamu fara zama dashi"

"Kashhh kayya dai Hajara, da kin aje komai kin koma gidan mijinki wallahi, ai shi aure dama ɗan haka ne kuma ai ibada kika je. Yanzu kin gwammace zama a haka ba aure ga Yayarku nan Sa'adhatu itama ba auren?, ga sauran ƙannanku nan uku suma babu auren, ku shikenan gaba ma kuke da auren ko?, kun gwammace ku zauna ku jera da uwar taku gata nan ita hakan da bama damunta yayi ba?. Ni ban taɓa ganin uwa irinki ba Salame wallahi"

Kawu Sani ya ƙare maganar yana nuna Ammi dake jinsa tana kuma masa wani irin kallo.

(Daka ji yadda yake maganar tasa ai kasan da baƙin cikin ci gaban da muke samu ne, ɗan baƙin ciki kawai).

Fannah ta ƙare maganar zucin tana hararar Kawu Sani a fakaice.

"Yaya Sani abunda ya kawo ka kenan ko akwai saura?"

Ammi ta faɗa kanta tsaye tana kuma kallonsa.

"Bashi kenan ba ai tukunna"

"Tom saika ƙare abunda ya kawo kan ai ko?"

"Yanzu kuma ke Sa'a haka kika fara tara ƙattin maza a ƙofar gidan nan harma da ciki ance shigowa ake?, wai abunda kuke gaba ɗayanku ya dace kenan?"

Tashi tsaye kawai Ammi tayi tana ma Aunty Sa'a alamar tayi shiru kawai.

"Nifa na kasa gane inda kuka dosa Yaya Sani?. Ya za'ai ace ƴaƴan nan sun kama sana'a itama basu tsira daga zagi da zunɗansu da akeyi ba?, duk da yanzu a tsaye suke da ƙafafunsu ba wani abun ashsha suke ba, da basa yin komai kunce yawon iskanci suke, yanzu sun dawo suna sana'ar kansu shima kuna shirin fara masu wata shaida daban, gaskiya to bazan lamunci hakan ba wallahi"

"Ke ai dama bakya son gaskiya, kuma gidan nan ai baku kaɗai ne dashi ba da har wasu ƙattin banza zasu rinƙayo sallama cik...

Wani irin kallo Ammi ta watsa masa tana binsa da wani kallon mamakin, da yasa shi kasa ƙarasa maganar da yake yi, tana nunasa ta ce.

"Banji miye kace ba Yaya Sani?, ɗan ƙara mai-maitawa naji, ko dai kunne na ne banji da kyau ba?"

"Wallahi Ammi haka dai da kika ji shine yake son faɗar wai gidan nan ma ba namu bane duka"

Cewar Fannah ta faɗa tana murguɗa masa baki.

"Ke kinci gidanku dan ub*an..

"Kaga Yaya Sani, basai ka zagar min ƴa ba ai. Gida kuma wannan ne kunyi kaɗan kuci wai harda shi yanzu ma zaku ci gado. Wai ko kun mance yadda kuka bi kuka handame sauran Gonakin da Mahaifinsu ya bari ne?, yabar Gonaki har biyar amma yanzu suna ina?"

"Miya kawu wannan maganar Salame kuma?"

"Ahhhh, yo wai ai idan ka mance bari na sake tuna maka ne ai. Wannan gidan shine kaɗai kuka bar mana nida ƴaƴan nan gasu nan, sai kuma yanzu anga sun fara zama mutane shine shima ɗan gidan kuke shirin kwace mana shi kenan?"

"Bafa haka ni nake nufi ba, ki tsaya kiji sauran maganar da nake so na ce mana?"

"Ba wata maganar da zaga faɗa ni Yaya Sani, da dai ban san halinku bane. Sana dan Allah idan ka gama abunda ya kawo ka mun gode zaka iya tafiya"

Sake da baki yake kallon Ammi. Shifa dama ba wani abu ne ya kawosa ba sai dan yazo ya cika cikinsa, domin ƙamshin abincin da suke yi duk ya cike unguwar gaba ɗaya, sun fara samun labari ne, shine yake son lallaɓowa shima ya ɗanci rabonsa, amma yanzu ya ɓata abun, dama kuma Kawu Sama'ila ne ya faɗa masa yaje idan an samu dama shima ya ɗan shigo ya kwashi nasa rabon.

"Ke Sa'a ɗan zubo min abincin nan"

"Ahhh yo naga ikon Allah, koma kunya baka ji Yaya Sani?. Ohho dama abinci ne kawai ya kawo ka, shine ka tsaya kike ta cika baki haka?, ai da kawai ka ce a zubo maka ba sai ka tsaya kana wani isa kana gadara ba"

Shi dai bai ce komai ba sai borin kunya yake yana wani mazurai.

Yo a banza dan su Fannah kam dariya suka saka ciki-ciki.

Aunty Sa'a ta girgirza kai duk da tana jin haushinsu amma saita miƙe ta zubo masa abinci shinkafa da miya harda naman kaza, domin dai ta tura masa aniyarsa, kuma su san da ba kamar yanzu ba ce.

Koda aka kawo masa abincin cike da mamaki yake kallonsa, sai magana ake a zuci yana jinjina kai, yana ci yana ƙara jinjina kai, sai saƙa wani abu yake a cikin ransa.

Kuma yana gamawa ya miƙe bako kunya ya ƙara gaba ba gode bare na gode.

"Ohhh ni ƴasu, koma kunya baya ji?"

"Hmmm Ammi kenan, yo su ai indai kunya ce ai basa da ita, har kin mance lokacin da Babanmu na raye ne?, ai haka suke masa, sai sunyi kusan wata basu nemesa ba, amma da wata hidimar ta taso zaki gansu sun fara maƙale masa. Tofa da kinga hakan, wani abun ne suke so yayi masu"

"Tabbas kuwa hakane ai ya za'ai na mance da halayen wa'innan dangin uban naku Maryam?"

"Hmm Allah dai ya kyauta"

"To ke yanzu Haja da gasken Koto zaki kai Umar ɗin?"

"Wallahi Ammi can zan kaisa, dan na gaji da yawo nake da igiyar aurensa akaina, gara kawai Al'ƙali ya raba auren sai yafi"

"Tom hakan ma yafi ai"

Cewar Aunty Sa'a tana sake gyara zamanta sosai ta ce.

"Hakama zakiyi dan nima ai haka mukayi da Rabe, dole yasa na kaisa ga Al'ƙali. Yaushe za'a ce ka auri namiji amma yana maka baƙin cikin samunka?, ai ina bazan iya zama da irin mazajen da muka aura ba a da, ai kan mage ya waye yanzu kam"

Aysha dake gefe tana murmushi ta ce.

"Ai da, da nake faɗa maku ai gani kukai kamar wasa ne, wani lokacin da yin auren nan gara zama babu shi, domin ko a cikin musulinci ai ba'a ce dole ne yin auren ba"

Haka dai suka ci gaba da maganganunsu duk akan dangin Mahaifinsu da kuma abubuwan da suka rinƙa faruwa a baya, da abunda ya shafi tasu rayuwar a tsakaninsu......

PAGE 15

*MIMI POV*

Hidimar bikin kam ake gadan-gadan a cikin gidan su Mimi, dan da kawo lefen dama sati biyu aka yanke, dan haka kullum Amarya bata zama ita da ƙawarta Maryam kullum suna kan hanyar gyaran jiki. Kai da ka kalli Mimi kasan tana matuƙar ɗoƙin auren nan kamar mi.

Kamar yau ma bayan sun dawo gyaran jiki suna zaune dan yau ne za'ai Qur’ani Day, yau ta kama talata kenan.

Su Hajiya ma dai sai suka haɗe Qur’ani day ɗin dana Mimi duk dai ba haka taso ba.

Ba laifi Qur’ani day ɗin yayi kyau, amma da yake su Hajiyar na son ɓata abun dama basu wani fito da wuri akan lokaci ba, saida dare ya fara tukunna aka samu aka fara, shi yasa duk pictures ɗin da akai a Qur’ani day ɗin basu yi wani kyau ba saboda dare yayi sosai.

Washe gari Mimi taji daɗin da Ball za'aje kuma ango ne da abokansa suka shiryata, dan haka banda su Hajiya, dansu ma nata angon ya shirya tashi Ball ɗin shima.

Ƙawayensu Maryam sunzo na cikin unguwarsu da wa'inda sukai school tare, duk da dai wasu sai ƙananun maganganu ake da yanayin bikin nasu, dan gaba ɗaya an gama fyesawa mutane cewar haka nan dai za'ai bikin amma nau'in jininsu baizo ɗaya ba.

Kamar yauma bayan duk an gama shiryawa amarya tasa wata Abaya ƴar dubai mai azabar kyau, tasa baƙa tayi mata kyau sai walwali take tana ɗaukar ido, dan gyaran amare da akai mata yayi matuƙar taimakawa wajan ƙara haska farar fatarta, ga duk inda ta gifta saita bar maka ƙamshi, suma ƙawayen Amarya kowacce tasa tata kalar Abayar.

Wasu ƙawayensu ne zaune suna ɗan ƙus-ƙus wata daga ciki ta wani taɓe baki tana ce ma ta kusa da ita.

"Ni kam Mimi tana fa ban mamaki"

"Mamaki kuma na miye to?"

"Hmm ke dai bari Yasmeen, ace kuyi aure kuzo a haifi mai sikila, ai akwai damuwa kam sosai"

"Ke wai dama da gaske ne ita AS ce shima haka?"

"Eh man, ke da duk baku yarda ba Yasmeen?"

Girgiza kai wacce ake kira da Yasmeen tayi tana ƙara magana ƙasa-ƙasa ta ce.

"Ke wallahi ni Asma ban yarda bane kawai dai naji ne. Kuma ni duk ɗaukata ai ba'a taɓa aure sai an kawo takardar awon jini, kamin maɗaurin aure ya ɗaura aure, kenan to zasu je ne a sauya masu ita?"

"Haka zasuyi mana, saboda kin san ba'a taɓa ɗaura aure sai an kawo takardar awon jinin nan"

"Tabɗi jam tom Allah ya kyauta, soyayya ce ta rufe masu ido, kayi magana yanzu kuma ace ko kana baƙin ciki da auren da zata yi ne"

"A'a yo to kai dama Yasmeen ina ruwanka?, sun daɗe basuyi aurensu ba, ina ruwan wani, ai duk abunda ya faru da mutum ai shi ke janyoma kansa ko?"

Jinjina kai kawai Yasmeen tayi suna maida hankalinsu wajan miƙewa jin cewar abokan ango sun ƙaraso da motoci za'a ɗauki ƙawayen Amarya da ita kanta zuwa wajan da za'ai Ball ɗin.

Motoci ne kusan guda biyar aka kawo, dan haka dama ba wani gayyata tayi sosai ba, lafiya lau motocin suka ɗaukesu, Mota ɗaya kuma ita kaɗai ce aka ɗauka, dan daga nan za'a wuce da ita a ɗauki ango shima.

Kamar yadda zasu tsara haka ta kasance an ɗakko ango yasha wata farar shadda sai kyalli take, tunda suka ƙaraso inda za'ai Ball ɗin mai camera ya fara kashe masu picture masu azabar kyau tun a cikin Mota, masu IPhone cikin ƙawayen Amarya ma suka fara masu videos dan ba ƙaramin kyau sukai ba, tabbas dan dacewa kam sun dace da juna, kowannen su zaka kalla fuskarsa cike take da annurin zai mallaki muradin ransa.

Anyi Ball cikin tsari itama ansha pictures kamar baza'a daina ba, wajan ƙarfe sha ɗaya na dare aka tashi Ball aka maida kowacce ƙofar gidansu amarya kamar yadda aka ɗakkosu.

Da yake gidansu Maryam suke kwana duk unguwarsu ɗaya dama yasa gaba ɗaya ƙawayen nufar gidansu Maryam ɗin, da ita kanta Amarya, dan gidansu Amarya yayi cikar da baza'a iya sauka a can ba dama tunda bikin aka farasa Mimi ta dawo gidansu Maryam ɗin.

Su Hajiya ma nan kusa dasu gidan wata mata Mmn Baffah suka koma da yake suna yi da ita sosai.

****************

*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*

Zama Inna Saude tayi tana kallon Iya dake aje mata ruwan sha zata ƙara tashi Inna Saude ta jawo hannunta tana cewa.

"Ki zauna mana muyi magana, sai hidima kike dani, sai ka ce wata baƙuwar zuwa gidan nan?"

Zama kawai Iya tayi tana cewa.

"Ai dai kin san ba baƙuwar bace, kawai kyautatawa ce nayi miki ta yadda zaki iya ban shawara mai kyau akan abunda zan gaya miki"

"Tom kawai ina jinki tafi kanki tsaye"

"Yawwa akan auren nan da nake so na haɗa na Naima da Musa ne, wata ƴar matsala ke son ɓillo min Saude"

"Matsala kuma?, wacce iri ce?"

Inna Saude ta faɗa tana aje ƙofin ruwan dake hannunta tana kallon Iya.

Iya ta sauke lumfashi tana cewa.

"Bari wannan ƴar iskar yarinyar ce mana Mubeena ke son ɓillo min da matsala"

"Wannan ƴar tatsitsiyar yarinyar?"

"Itafa da kike ganinta nan, yanzu idonta a buɗe yake da rashin kunya, yarinyar duk ta fetsare"

"Hmm ke kika so ai ƙawata, ai ni da ni ce da tuni nayi maganinta wallahi"

"To ni Saude miye kike ganin zanyi mata, karfa tazo ta bani matsala?"

"Ba abunda zai faru, ai za'ayi bikin ne ma bata nan"

"To ke ina kike ganin zan kaita kona turata?"

"Kwantar da hankali ƙawata zaki ji yanzun nan"

Inna Saude ta ƙare maganar tana jinjina kai, zuwa can ta ƙara gyara zamanta tana kallon Iya sosai kamin ta ce.

"Ba kince da akwai wata ƙanwar mahaifiyarsu ba dake Logas tana sana'ar Karuwanci ba?"

"Eh tabbas ta can ma, koba Zubaida ba kike magana?"

"Yawwa ita fa Zubaida"

"To amma miya kawo maganar Zubaida a wannan maganar?"

"Kashhh kin tsaya dai ai ko kiji ƙarshen zan can"

"Tom ina jinki. Na matso naji mafita ne shine yasa"

"Yanzu ke ina kike ganin za'a iya samo number ɗin ita Zubaidar?"

"To wai Saude duk mi za'ai da number ɗin wannan marar kunyar itama?"

"Kin jiki ko?, kefa baki cin ribar canza wani lokacin fa"

"Shikenan kiyi hakuri, amma inaga za'a iya samo labarin inda take a bakin Musa, dan kin san dama shike zuwa Logas ɗin yana kuma kawo mana labarin ita Zubaida ɗin, duk dai yanzu kamin ya ɗan dakata da zuwa yazo mana da labarin wai ta shahara a can Logas ɗin harta buɗe gidan abinci na kanta, tsabar Karuwanci ya mata rana"

"Yawwa to abunda nake so dake shine, kawai kisan yadda za'ai ki tura ita Mubeena can wajan Zubaida ɗin"

Ido waje Iya ta zaro tana dafe ƙirjinta ta ce.

"Wajan Zubaida dai?, so kike na kaita itama a lalata mata rayuwa ko mi?"

"A'a ke kam Ƙawata, ba abunda zai faru da Mubeena, ai ita kanta Zubaida bazata taɓa bari tasa Mubeena a harkar da ita take yi ba, wai kin mance ita ɗin jininta ce?"

"To ke kin mance cewar Zubaida bata so auren Binta da ubansu Naima ba?"

"Na sani, amma duk wannan bashi bane, ai jinin ƴar uwarta dai ne sune su Mubeena ɗin, kuma bazata taɓa bari susha wahala ba, duk da tana fushi da ƴar uwarta"

"Hakane kuma maganarki, amma gaskiya zan yarda ne Mubeena taje na ƴan kwanaki, ana gama dai-daita

8 / 47