Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
shi kuma yana bayanta ya riƙe ƙugunta suna tsaye a bakin madubi suna kallon kansu ta ciki.
"Yinwa fa nake ji muje ki samamin abunda zan ɗanci kinji Love"
"Amma dai kasan ya kamata kaje gidan Hajja tasan da dawowarka ko?"
"Ina so naje zuwa anjima idan na gama abunda nake yi"
"No hakan fa bai kamata ba ka sani, bai kamata ta fara jin dawowarka daga wajan wani ba"
"Na sani Mimi zanje fa, ya za'ai na dawo dama banje inda take ba. Yanzu dai Oya muje ki samama mijinki abunda zai karya"
Tare suka fito parlon shi ya zauna akan kujera ita kuma ta wuce kitchen ɗin.
Dankali ta fere ta soya masa tayi masa wani haɗi da kwai da ƴar miya tasa masa a kyakykyawan filet ta haɗo masa da shayi wadda yaji na'a-na'a ta fito parlon. Dai-dai fitowar tata kawai ɗagowar da zatai taga Shamsiyya ma na fitowa daga nata ɗakin sanye take da wa'innan kaya ko ɗan gyale bata saka ba wadda zai rufe mata jiki, ta fito kamar gidan mijinta ne itama.
Ƙirjin Mimi ne yayi wata irin masifaffiyar bugawa da ƙarfi, saura kaɗan ta saki abunda ke hannunta tayi saurin riƙesa a ruɗe, wani irin bala'in kishi ne yazo mata wuya tana kallon Shamsiyya kawai kamar ta samu TV tsabar mamaki.
Shi kam ganin ta tsaya yasa shi juyawa inda ta ƙurama ido, shima da maɗaukakin mamaki yake duban Shamsiyya.
Ai ba shiri ya miƙe yana nuna Shamsiyya da yatsa ya ce.
"Keeee dama abunda kike yi a gidan nan kenan?"
"Ban gane ba Yaya Jafar?, miye nayi kuma?"
"Baki ga shigar da kikai bane kenan?, maza-maza kije ki cire ta, daga yau karna sake ganin gilmawarki da irin wannan ƙazamar shigar taki wallahi idan ba haka ba na lahira sai fiki jin daɗi"
"To ma miye shigar tawa tayi?, har idonka ya kai inda bai dace ba da har ka iya kallon shigar tawa"
Ai bai san lokacin daya zubara ba batai aune ba sai gashi a gabanta ya wanke fuskarta da wani kalar mari wadda yasa ma jinta da ganinta barazanar ɗaukewa na wucin gadi.
A mugun zabure take kallonsa da mamaki.
"Zaki bar wajan nan ne ko sai na sabautaki?"
Ya ƙara faɗa a mugun tsawa ce.
Bata daddara ba, hawayen takaici sun cika mata ido ta buɗe baki ta ce.
"Yanzu Yaya Jafar nika ɗaga hannu ka mara akan waccar matar taka ta gama da kai?, dan nayi wannan shigar dan kar taji haushi shine kake ta irin wannan hargagi?, dan kawai ta ce kayi abun arziƙi?"
Kai bai san lokacin daya ware idonsa sosai ba yana kallon Shamsiyya, zuciya ce ta zo masa wuya bai san lokacin daya kwanto bel ɗin dake ɗaure a ƙugun wandonsa ba, kawai sai dai Shamsiyya taji ya fara zafga mata shi a gadon bayanta.
Ihu ta saki iya ƙarfinta, shi kam ya zage sai jifga mata shi yake.
A zabure Mimi ta aje kayan dake hannunta ta matsa wajan da kyar da kyar ta amshe belt ɗin dake hannunsa tana nishi itama dan baƙaramar wahala tasha ba wajan amsar belt ɗin, dan itama harda rabon duka tasha.
Shamsiyya da kyar ta miƙe tsaye tana rusa kuka kamar ranta zai fita.
"Wallahi Allah Mimi ki rubuta ki aje wannan dukan da akai min saina tabbatar tozarcin da Yaya Jafar yayi min na lilka miki shi sau dubu, kuma zaki gani"
Ƙara yinƙurawa yayi zai kawo mata mari a fuska Mimi ta shige tsakiya, ita kuma Shamsiyya tayi saurin rugawa ɗaki.
"Haba dai bafa halinka bane bugun mace, kayi hakuri haka nan please?"
"Wannan ƴar iskar yarinyar dama haka take miki a gidan nan?"
Shiru kawai Mimi tayi, dan shiru sai yafi zama alkhairi gare ta dashi kansa, amma idan ta ce zata faɗa masa irin rashin kunyar da Shamsiyyar ke mata ai ransa ne zai ƙara dugunzuma wajan ɓaci azo ya sake mata wani dukan ta lalgwaɓe masu tazo taje ta haɗa wata masifar a wajan Hajja, ko yanzu ma tasan sai Allah kawai.
Shamsiyya kam na shiga ɗaki ta figo Hijab ɗinta tasa ta fito parlon tana wani irin kuka kamar wacce ake zare ma rai.
Ba wadda ta kalla su duka ta fice daga parlon.
Ai sai Mimi taji gabanta ya yanke ya faɗi, har wani jan ajiyar zuciya tayi dan tabbas fitar Shamsiyyar tasan bata alkhairi ba ce zuwa zatai gidansu ta haɗo wani bomb ɗin wadda zai kusa tashin zukatansu.
Shi kam gogan naku abincin sa kawai yake ci hankali kwance, sai ka ce bai san abunda ka iya zuwa ya dawo ba, Mimi saita zuba masa ido kawai tana sakin tagumi.
"Love mike damunki ne haka?, kin zuba min ido kamar yau kika fara gani na, ko na miki kyau ne ƴan mata na?"
Ya ƙare maganar cike da zolayar da yake so ta ɗan saki ranta.
Ta ɗan murmusa kaɗan ta ce.
"Ai kullum kai mai kyau ne a waje na, kawai abunda ya faru ne yanzu tsakaninka da Shamsiyya, kasan fa gida ta nufa kuma Allah kaɗai yasan mi zata je ta faɗa ka sani. Dan ni wallahi daka sani ma baka fara taɓa ta ba ka kyale ta kawai"
Aje cin abincin yayi yana matsowa inda take ya jawota jikinsa ya ce.
"Wai mi kike tsoro ne haka Love, ki kwantar da hankalinki zan fahimtar Hajja kinji?"
"Amma ai kasan....
Shiru tayi jin ƙarar wayar Jafar ɗin dake can ɗayar kujerar daya taso.
Shigowar kiran sai sakama Mimi bugawar zuciya mai tsananin gaske. Saita bisa da ido kawai lokacin daya miƙe yaje inda wayar take.
Ɗauka taga yayi cike da ladabi ya fara gasar da Hajja da taji ya kira sunanta, ai sai ta sake jin wata irin faɗuwar gaba.
Daga cikin wayar tana iya jiyo yadda Hajja ke faɗa a tsawa ce.
"Wato Jafar ka fara nuna ni ban isa da kai ba ko?"
"Hajja mi....
"Dakata na ce, ban baka damar ce min komai ba ai. Wato har ka iya dirowa cikin garin nan ace tun jiya amma bazaka iya zuwa inda nake ba?, sai wajan matarka data riga ta gama da kai ko?. Sana yanzu Shamsiyya ta shigo min nan tana kuka jikinta duk a fashe take gaya min kaine kayi mata wannan dukan akan matarka ƴarso ko?, harda cewa tabar maka gida. To bari kaji na gaya maka Shamsiyya nan bada daɗewa ba itama zata zamo matar taka, idan yaso idan matar taka naji na saita haɗiye zuciya ta mutu, amma ko bana raye wallahi Shamsiyya matarka ce kaji na gaya maka, sana kamar yadda ka ce yau Shamsiyya bazata kwanar maka a gida ba, kaima ina baka umarni daka kai har matar taka karku sake ku kwana a gidan nan, idan ba haka ba wallahi Jafar zanyi maka mugun baki...
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Hajja?"
Jafar ya faɗa a zubare yana dafe kansa da mugun mamakin furucin Hajja ɗin garesa.
Mimi yake kallo yadda itama ta miƙe saboda duk tana iya ji yadda Hajja ɗin tada murya kamar zata fasa cikin wayar.
A guje Mimi ta nufi bedroom ɗinta tana sakin wani irin kukan baƙin ciki dama tun ɗazu take so ta sake san, dan wani irin abu ne taji ya tsaya mata a wuya, tunda taji Hajja na cewa Shamsiyya matar Jafar ce koda bayan ranta.
"Kuma kazo gidan ina son ganinka"
Zaiyi magana kenan ta datse kiran.
Zubewa yayi a ƙasa yana dafe goshinsa. Ya ake so yayi ne?, anya ma Hajja tana cikin hankalinta kuwa?, ta sauya ba yadda yasanta ba.
A zabure ya miƙe yana duban Mimi data haɗo kayanta a ƙaramin akwati ta fito sanye da Hijab har ƙasa tana share hawaye.
Wani kalar tashin hankali ne ya rufe Jafar, bazai taɓa barinta taje gida a wannan yanayin ba, dama kuma ya aka samu akai auren, yanzu ta fara zuwa gidansu da wata matsalar ai sai ayi masu dariya ma............
PAGE 51
*MUBEENA POV*
Tafiya yankin azaba ce, tunda Mubeena take bata taɓa tafiyar mai nisan wannan ba da kuma haɗarin wannan ba.
Tafiya ce miƙaƙƙa suke yi ba tsayawa ga wani irin gudu da mai tukin Motar yake shararawa.
Sai kusan dare lokacin da suke gaf shiga Benin city (Edo), a hanya har ƴan fashi suka ci garo dasu Allah ya taimake su basu idasa tsakiyar daji ba suka samu waje nesa suka faka Motar. A cikin Motar ma sai da akai ta ƴan ƙananun rigingimu wajan bacci, dan wani ya make na kusa dashi wai yana kwanto masa jiki, aka kaure da rigima ana dambe da kyar aka rabasu, wani daren na ƙarayi da kyar ake ƙuƙutawa a bacci ido rabi da rabi, saboda yadda suke a mugun matse, gashi kowa gaji ta rufar masa abu kaɗan sai kaji ana danna ashar yadda kasan ana ganin hanjin juna a cikin Motar. Sai asubahi suka samu waje suka tsaya
Mubeena tsabar gajiya kasa fitowa tayi, saida Musa yazo ya kawo mata abinci ta ci, ya taimaka mata ta sakko tayo alwala, tayi sallah, kusan a zaune suka kwana, suna gama sallar asuba kowanne ya koma Mota suka kama hanya. Daga Benin suka shiga Ore (Ondo), tafiya ce mai nisa daga nan ta kawo su Ijebu-Ode (Ogun), daga nan akwai tazara mai yawa ta shigar dasu Lagos.
Tafiya ce mai nisa da ke ɗaukar fiye da kilomita 900, kuma za ta iya ɗaukar awa 15–18 idan ba a samu cunkoso ba.
*LOGAS*
Jahar Lagos tana cikin yankin kudu maso yammacin Najeriya. Tana daga cikin tsofaffin wurare da turawan mulkin mallaka suka fara zaune a ciki. A da, Lagos wani ƙaramin ƙauye ne da ake kira *Eko* wanda mutanen *Yoruba* suka fara zama a ciki. Daga baya ne Turawan Burtaniya suka karɓe ta suka mai da ita babban birni na Najeriya har zuwa shekarar 1991 da aka maida babban birnin ƙasar zuwa Abuja.
Lagos ce cibiyar kasuwanci ta Najeriya kuma wuri ne da ake samun dimbin mutane daga sassa daban-daban na ƙasa da ma wasu ƙasashen Afirka.
Lagos na da yawan jama’a mafi yawa a duk faɗin Najeriya. A halin yanzu ana kiyasta cewa *mutane sama da miliyan 20–25* ne ke zaune a Lagos. Akwai tarin mutane da ke kwarara Lagos kullum saboda neman aiki, kasuwanci ko karatu, da kuma masu Cirani neman kuɗi, mafi yawanci ƴan Arewa suna tururuwar zuwa Logas neman kuɗin da yawansu a nan ne suke rasa rayukansu.
Ko da yake asalin Lagos na ƙabilar Yoruba ne, yanzu haka akwai kowa a cikinta Yoruba (masu yawan gaske)
*Yaroba*
*Hausa*
*Igbo*
*Fulani*
da sauran ƙabilu kamar Kanuri, Tiv, Ijaw, Ibibio, Nupe da sauransu.
Lagos na da ƙananan hukumomi guda 20 (LGAs), kuma kowanne na da unguwanni da yawa. Wasu daga cikin manyan unguwannin sune:
Ikeja Babban birnin jahar Lagos
Lagos Island Tsohon birni
Victoria Island Yankin masu kudi da ofisoshi
Lekki Sabon yanki mai ci gaba
Ajah
Surulere
Mushin
Agege
Ikorodu
Badagry
Ojo
Yaba
Epe
da sauransu.
*wannan kenan*
Tunda Mubeena take bata taɓa ganin garin daya tara mutane ƙabila-ƙabila kamar jahar Lagos ba, gata da uban cinkosun daya gigita tunaninta. Gajiya dai kam ita ta hanata shan kallon wasu unguwannin da suke ta wucewa, dan hatta ƙafarta harta fara fushi saboda zama da tafiya.
A wata unguwa da ake kira da Agege taji mai Motar ya faka kowanne ya sauka duk wadda sukai tafiyar dasu, dan ya ce a nan zai takata wadda ke son ƙarasa inda zai je zai iya biyan abun hawa ya idasa shi.
Musa ne yazo ya kamo hannunta da kyar ta sakko daga Motar tana jan lumfashi dan ba ƙaramar gajiya tayi ba, sai taɓe baki take.
"Ke adireshin da aka bamu na Zubaida yana wajanki ko?"
Cikin jakarta ta fiddo wata farar takarda ta miƙa masa ta ce.
"Gata nan"
Amsa yayi yana yima wa'inda suka zo tare sallama yaja ta suka ƙara gaba, Mubeena tana kallon wa'inda sukai tafiya dasu a Mota ɗaya kowanne ya kama gabansa sai ɗai-ɗaiku ne a tsaye a wajan.
Wata Mota suka tsaida taji Musa na cewa Ojo, dai-dai gidan Karuwai.
Shiga sukai bayan ya gama masa jawabin inda zai kai su.
Mubeena dai tana biye dashi suka shiga, sai hamma take dan ba ƙaramar yinwa kuma take ji ba.
Saida suka tsaya a wani waje inda wata mata ke dafa abinci saboda cinkosan ababen yawan daya rutsa dasu sun daɗe akan titi kusan awa biyu basu isa ba, Mubeena sai ɓata fuska take, kai ita tunda take bata taɓa ganin garin dake da yawa irin Lagos ba, ace tafiya harta awa biyu ba'a isa unguwar da zasu isa ba?.
"Nifa yinwa nake ji"
Ta faɗa tana kallon Musa.
Wani murmushi ya saki yana ma mai Motar magana, sai ya dakata wajan wata mai sayar da abinci, shima mai Motar dama da tashi yinwar a tare suka sauka wajan Musa ya sayo ma Mubeena shinkafa da wake da miya da nama zubo-zubo, dama su Lagos akwai cin nama idan har zaka ci abinci to da nama, su can baya masu wahala.
Koda ya kawo mata tana ci yana daga gefenta shima yana cin nasa saida ya haɗe wata loma kamin ya ce.
"Wallahi yarinya darajar masoyiya kawai kike ce har muka iso Lagos lafiya, amma ba dan haka ba da horan da zan miki sai kin gwammace dama baki yarda kika biyo ni wannan tafiyar ba"
Ya ƙare maganar yana cije baki.
Hararara ta watsa masa bata ce dai komai ta ci gaba da cin abincinta, dan sosai take jin yinwa, ga jikinta da ya gaji ya mutu murus, idan ta ce zata biye masa to tasan shi tsaf yanzu yaga ba idon Inna ko Na'imar ya kamata ya bibbige, sai dai kawai ta rinƙa binsa da hararar da murguɗa baki.
Suna gama cin abincin Musa da kansa ya fita ya maida abunda suka ci abincin dashi wajan mai abincin, ya sayo masu ruwa harda lemo, ya kawo suka ci gaba da tafiya.
Kai ranar Mubeena tasha mamaki, tafiya suke yadda kasan zasu je wani gari, dan ita a kiyasinta tafiyar da sukai tayi daga Kano zuwa Kaduna, idan ma bata fi ba, tasha dai kalle-kalle, kai har saida bacci mai nauyi ya ɗauke ta.
Tana cikin bacci taji Musa na bubbuga kafaɗarta, a zabure ta farka tana kallonsa, tsaki yaja yana fita daga Motar yana cewa.
"Sai ki fito ai ko, yarinya sai bacci kamar kasa?"
Ya faɗa yana sallamar mai Motar.
Fitowa tayi tama kwaɓe fuska dan sosai gajiya ta rufar mata da kyar take iya taka ƙafarta tsabar yadda tayi sanyi.
Wani gida taga sun nufa a ƙofar gidan akwai yawan jama’ar dake zaune wasu nashan taba wasu na saida abinci wasu na caca wasu a tsai-tsaye samari maza da mata ana taɗi, wasu kuma suna shige da fice a cikin gidan.
Tabbaya ce Musa yayi ma wani dake zaune a ƙofar gidan kai tsaye ya ce masa tabbas yazo gidan Haj Zubaida.
Juyowa yayi yana duban Mubeena ya ce.
"Ina wayarki?"
"Ni waya gare ni dama?"
Ƙanƙance ido yayi yana cewa.
"Ke karki raina min wayo mana, jiya ina wayar da Na'ima ta bani na sayo miki?, ko ba'a baki ita bane?"
Sai lokacin ta tuna da wayar da Inna ta miƙa mata lokacin da zasu taho.
Fiddo tayi daga cikin jakar kayanta ta miƙa masa tana harararsa ta ce.
"To ni ba na manta da ita bama"
Amsa yayi yana jan dogon tsaki.
Number Zubaida ya shiga kira, kusan kira uku bata ɗauka, sai jan tsaki yake dan Allah ya sani ya tsani rainin hankali. Kira na biyar ne da yayi mata ta ɗauki wayar.
"Haba Inna Zubaida ace ayi ta kiran wayarki sai anga dama ake ɗauka"
"Kai Musa baka da dama wallahi, yi hakuri ina can wajan jama’a dan kasan zamu fita ne gidan abinci na yau munyi rana da yawa. Ya hanya ne? kun kusa ƙarasowa ai ko?"
"Ai gamu ma a ƙofar gidan naki"
"Kai masha Allah amma fa kunyi sauri, bari na turo Badi'a tazo ta shigo daku"
Katse wayar tayi jim kaɗan saiga ga wata mace tasha uban gayu kai ka ce gasar kyau ta duniya zata tafi, sai wani rangwaɗa take tana kallonsu tayi masu iso tayi gaba suna binta a baya.
Mubeena sai ta zama ƴar kallo, yadda suke ratsa mutane suna wucewa duk inda suka ratsa sai an kalleta, ita dai har wani tsoro ya shige dan gidan babu ƙabilar da babu da alamar gidan hayi ne ma, domin harda sama da ƙasa kusan hawa uku ne a gidan.
Mubeena sai taga sun shigo wani shashi na gidan wadda babu yawan jama’a babu yawan hayaniya sai masu aikin abinci a kawai a wani babban kitchen dake gidan suna ta aikin abinci wasu na toƙa tuwo wasu nayin sakwara da amala, wasu na yin miya kai kowanne da aikin da yake yi.
Wani babban parlo ne taga Badi'ar tayi masu jagora zuwa ciki.
Wani irin lumfashi Mubeena ta sauƙe jin wani sanyi daya ratsa mata jiki shigarsu parlon, ga wani ƙamshi dake busowa.
Shi kansa Musa bin parlon yake da kallo yana jinjina kai. Ahh lallai Zubaida ta samu duniya ta kama ƙasa.
Zama sukai akan kujerun dake parlon Badi'a ta ce bari ta kira masu Haj ɗin............
PAGE 52
*HANNAH POV*
A hankali ta miƙe tana miƙama Fannah kayanta da suke jerawa a wardrobe ɗinsu.
"Wallahi karki so jin yadda ake ta surutun kyan gidan nan, amma yawanci surutun rabi da rabi zaginmu ake yi wai muna neman maza"
Dariya Fannah ta saki tana sake kallon ɗakinsu wai yanzu duk wannan uban ɗakin nasu ne.
Ta wani ɗaga kanta tana shaƙar ƙamshin gini sabo tana sake bin ɗakin da wani irin kallo na zallar murna da alfahiri kamin ta ce.
"Wallahi Hannah ko a jikina sun daɗe basuyi maganar ba, ni dai tunda nasan ba haka muke ba ai shikenan haka kuma Allah ma ya sani, maganar mutane ni ai yanzu ta daina damuna wallahi"
Girgiza kai kawai Hannah tayi ita kam tana ɗan taɓa mata rai, kawai dai bata cika