Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
gidan nan, dan naji Aunty Salamatu ta ce mana wai ko zuwa basuyi ba, naji kuma jiya Hadiza tazo wajan Maryam nasan ita zata je ta faɗa masu gara suzo su kashe kwarkwatar idonsu"
"Ai ko wallahi hakane Aunty Bintu ita ce ma zata basu labari, shine zasu fake da wai aiki zasu zo taya wa"
Maryam ta faɗa tana taɓe baki.
Aunty Sa'a ce ta miƙe tana cewa.
"Ni bari naje na watsa ruwa. Ke Fannah ki kawo min nawa abincin dan ina ci zan kwanta, gobe akwai hidima da yawa, danma Kamun ƙarfe uku ne"
Da to ta amsa.
Ita kuma ta kalli Aunty Haja dake zaune tana cin abincin ta ce mata sai ta shigo ita tayi gaba, dan bazata iya zama a parlo yadda ta gaji haka ba taci abinci dole saita watsa ruwa gaskiya, ɗaga mata kai kawai Aunty Haja ɗin tayi ta ci gaba da cin abincinta tana sauraron firar su Aunty Bintu da Ammi duk akan Kamun da za'ai goben.
Washe tunda safe wajan ƙarfe tara su Aunty Haja suka fice daga gidan, Makeup suka tafi dan daga can sai wajan Kamu zasu wuce kai tsaye.
Maryam ma sunyi waya da Nihal akan su haɗu wajan mai masu Makeup daga can suma sai su wuce wajan Kamun kai tsaye, ita da Aysha suka tafi aka barsu Fannah dan itama akwai wata ƙawarta Salma dake kwalliya ita ce zata masu daga can zasu wuce suma dan harda Salma ɗin zasu tafi Kamun idan tayi masu.
Aka barsu Ammi a gida su Aunty Bintu ma wata mai kwalliya Aunty Sa'a kamin su wuce ta kira ta dake nan a cikin unguwarsu ta iya sosai zata zo tayi masu, dan har Ammi sai anma kwalliya, da dai taƙi amma su Maryam dasu Aunty Badiya suka dage, wai tana uwar amaya mai capacity ai dole su ƙanƙaro mata capacity a wajan Kamun nan.
Ai ko sosai mai Makeup ɗin nan ta zage ta tsantsara masu mai azabar kyau, tayi masu ɗaurin ɗankwali irin na zamani, suka fito kamar wasu taurari, kaya iri ɗaya suka saka Ammi dasu Aunty Bintu, sai suka fito kamar wasu ƴan uku, wani azababban boyal less ne mai kalar ja da ruwan ƙasa, ya haska farar fatarsu tayi azabar kyau, suka fito suna taku ɗai-ɗai.
Daga can kuma aka aiko Mota aka fara ɗaukarsu zuwa wajan Kamu, wajan ƙarfe uku. Dan sunyi waya dasu Aunty Haja suma suna hanya.
A ɓangaren su Fannah ai su tuni sun jima da isa inda za'ai Kamun dan su da wuri Salma ta gama masu kwalliyarsu suka suka saka wani kalar leshi suma nasu kalar daban mai azabar kyau nasu kalar pick ne, sai yayi masifar haska su kamar ka sace su ka gudu.
Wajan su Maryam ƙirjin biki kam itama itada Aysha kalar nasu daban su kuma leshi ne kalar ruwan ƙasa da yayi masifar amsarsu suma. Da suma Atamfar Kamu suka so sawa amma Maryam daga baya ta sauya tunani ai gara ace su fita daban asan dai dole sune da biki, suka barwa mutane ankon Atamfa su saka su kaɗai, sai daga baya ta zaɓar masu duk kayan daya kamata su saka, dan ita da kanta ta shiga kasuwa ta zaɓar masu ana saura kwanaki uku, kuma basu faɗa ma kowa ba, sai dai aga gansu da shigarsu ta ban girma daban sun fita daban.
Sosai mutane ke binsu da kallon mutuƙar sha'awa, bare da taro ya fara ɗaukar harami lokacin da aka jerosu suka taho cikin hall ɗin Kamu, amarya na zaune a inda ya kamata ta zauna, Aunty Sa'a na kusa da ita tana mata magana a tsaye, itama da kalar kayanta amma ita iri ɗaya tayi dasu Ammi da aka ware masu wajan zamansu daban.
Su Maryam ma bayan sun gama rawa sun jero sun shigo suka nemi waje suka zauna. Duk inda taje suna tare da Nihal sai raɗa take mata tana sanar da ita wani abu da alamar abun mai mahimmanci ne a wajanta. Mc sai koɗa su yake da uwar amarya anata sakin wakoki masu daɗi sai tsuma ƴan mata suke suna daga zaune suna kaɗa kai.
Su Hadiza dasu Inna Hindatu fa duk sai suka raina kansu, wallahi duk sai suke ganin kansu a wasu muggan ƴan ƙauye, amma ganin ba wulaƙanci yadda ake raba ma kowa abinci da abubuwan Kamu sai wadda ka zaɓa kawai sai suka saki jikinsu suka fara kwasar ganima suma, suna shan kallonsu Maryam da sukayi masifar kyau suka tafi da imaninsu, sai jinjina kai suke suna ƙara shan mamaki, wato dai arziƙi kashi, wai yau su Maryam ne da suka raina a baya sune yanzu suka zama wani abu har haka?, lallai duniya juyi-juyi ce.
Ana shan shagalin Kamu waje sai ƙara ɗaukar harami yake, dan hatta su Ihsan tazo ita da wani saurayin da Maryam ya ɗan bata mamaki, ai iya saninta dai Ihsan Abeed take mugun so, ko yanzu ta gaji ta aje makaman yaƙinta ne ta rungume wani?.
Bamai bata amsar hakan, dan haka kawai ta share zancan amma yadda ta gansu a tare daga gani kasan masoya ne, sai ta birge ta kuma, dan har zuwa tayi suka gaisa tasa aka cika table ɗin da suka zauna da kayan ciye-ciye na Kamu.......
PAGE 61
"Wai Maryam sai binki nake tun ɗazu ki tsaya ki saurare ni mana pleaseeee?"
Nihal ta faɗa kamar a ɗan shagwaɓe.
Tsayawa kawai Maryam tayi tana fuskantarta ta ce.
"Oya ina jinki"
"Amma ai kinfa ji abunda na ce"
"Ai sai nake jin abun kamar mafarki ne ko tatsuwaniya"
"Wallahi Allah da gaske nake ƙawata, da kansa Ya Fu'at ya ganki a wajan nan ya ce na miki magana shifa yana ciki"
"Ni da kaina Ya Fu'at ɗin?"
"Na rantse miki"
Nihal ta faɗa tana nuna da gaske fa take wallahi.
Wani lumfashi ta sauke tana gyara tsayuwarta kamin ta ce.
"Yama akai har Ya Fu'at yazo wajan nan, nidai a sanina ai maza basu cika zuwa Kamu ba?"
"To ai ki duba kiga wajan nan ga maza nan wasu sunzo da samarinsu, amma ai duk suna waje yawanci, shima yanzu haka yana cikin Mota ya ce na miki magana Allah, kuma ai shine ya kawo ni, kin san na ce miki idan yana gari baya bari muna yawon banza muje mu daɗe a waje, nan ma dansu Mome sun san ke ce fa"
"Okey okey shikenan bari idan na gama zanje wajan nasa, idanma ƙarya kike ai zanji ne"
Murmushi ta saki tana ɗan rungume ta tana raɗa mata a kunne cewar.
"Ai ko baki so sai kin shigo gidanmu a matsayin surukarmu"
Tana ƙare maganar ta matsa da sauri tana mata gwalo.
Murmushi Maryam ta saki tana girgiza kanta da sauri, dan ita abun ma mamaki yake bata, da ita har tana tunanin Fannah zata ma hanyar aurensa sai gashi Ubangiji na shirin sauya lamarin, (Allah kenan).
Ta faɗa a cikin ranta.
Haka Kamun ya cika gaba da gudana, komai a cikin tsari, hatta dangin Alhaji Ma'aruf sunzo wasu daga ciki mata, kuma anyi komai a cikin al'ada.
Mai camera sai kashe su da pictures da videos yake zafafa.
Maryam ta sha'afa da zuwa wajan Fu'at dan komai ita ke jagorantar shi, saida aka kusa tashi tayi wuf taje inda yake shingiɗe cikin Mota ya ɗan lumshe kyakykyawan idanuwansa, saida Maryam tazo inda yake ta sake ƙare masa kallo sai yanzu ne take ƙara ganin kamarsa da Nihal yama fi Nihal kyau nesa ba kusa ba.
Sauke lumfashi tayi tabbas Fu'at ɗin san kowacce mace ne.
Kamar zata juya tabar wajan saboda sai take ganin kamar ma bacci ne ya ɗaukesa bata son tayar dashi, ta inama zata fara masa magana ita?.
"Kin gama kallon nawa?"
Da wani irin sauri ta juyo gaba ɗaya tana dakatar da tafiyar data fara domin barin wajan.
Gabanta na faɗuwa take satar kallonsa saita saki murmurshi ganin shima yadda yake jifanta da wani kalar murmurshin nan nasa mai zautar da wasu ƴan matan.
Girgiza kai tayi tana wasa da hannunta, ita bata taɓa ɗauka ma zata ji kunyar wani kamar yadda take jin tasa ba yanzu da nauyinsa.
"Yeah mana hakane, kin gama kallo na kin gama gano muni na shine zaki tafi ki barni?"
Wannan lokacin dariya sosai Maryam ta saki harda rufe baki, ai sai ya shagala da kallonta dan dariyar shi kam ba ƙaramin tafiya tayi da imaninsa ba.
Ai kamar wasa sai gashi sun saba a wajan nan kamar wasu wa'inda suka daɗe da sanin juna sosai, dan bata bar wajan ba har saida yasa mata number nashi, kamar karsu rabu, ya ce ta kira masa Nihal zasu wuce dare ya fara, suma ya kamata a tashi haka nan karta sake wahalar masa da kanta.
Tana murmushi ta koma cikin hall ɗin dan wasu ma tuni sun fara tafiya gida.
Bayansu Nihal sun wuce sai wajan tara na dare aka tashi aka maida kowa gida...
***********
"Washh Allah na, na rantse jikina ciwo yake min"
Hannah ta faɗa tana zama akan kujerar parlo bayan sun dawo daga wajan Kamu.
"Ni ce zan faɗi haka ai Hannah dan tunda naje ban zauna ba"
Cewar Maryam tana cire gyalenta ta zauna itama.
Su Aunty Haja tuni sun haura sama bedroom nasu, dan su gajiyar da sukai ba'a magana.
Su Ammi ma tuni sun shige domin watsa ruwa a huta zuwa gobe kuma a miƙa amarya ɗakinta.
Saida suka ɗan huta kamin kowanne ya shige bedrooms nasu.
Maryam dama ita da Aysha ɗaki ɗaya suke itama Aysha tana dawowa bata iya zama parlo ba ta wuce bedroom nasu.
Washe gari wajan sha biyu aka aiko da wasu jifga-jifgan motoci har guda biyar domin ɗaukar amarya.
Dama kayan amarya tun ana saura kwanaki biyar a fara hidimar biki Maryam tayo Order kayan ɗakinta dan da Maryam akaje aka jera su, maza ne ma suka shirya part ɗin Aunty Haja ɗin, Maryam ce kawai tasan yaya gidan Alhaji Ma'aruf yake, sai yanzu da zasu je su gani.
Daga cikin masu kai Amarya harda su Inna Hindatu dasu Hadiza saida suka zo wai suma zasuje, su Aunty Bintu badan sun so ba sunso suyi magana amma sai Ammi ta nuna kar suyi kar azo a tada rigima daga kai amarya azo a yada hali gidan kishiyoyi, subi komai a hankali abunda ba kwana za'ai gidan amaryar ba, tunda ita ba yarinya bace ba kuma auren fari bane.
Haka tafiya gidan amarya ya kasance cikinsu Maryam dukkansu saida suka je Aunty Sa'a ce kawai bata je ba, ita sai lokacin da Ammi zata je ganin ɗaki su je tare, ai ko Aunty Haja tasha kuka yadda kasan aurenta na fari ne zatai, har saida tasa Aunty Sa'a kukan da Ammi, su Hannah ma ido yayi jawur dan sun saba kam ta jima a gida bata sake wani auren ba, shi yasa suke ganin wannan kamar ma yanzu ne zatai aure na fari, saboda wancan cikin unguwarsu ne kusan kuma kullum tana gida, shi yasa wannan da za'a ɗauketa a kaita wata unguwar mai nesa dasu sai suke jin kamar ma garin zata bari.
Gida fa yayi kyau dan su Hadiza kasa rufe baki sukai suna mamakin wannan narkeken gida, kusan part huɗu ne.
Na mai gidan sai na kuma uwar gida, saina su Aunty Haja a haɗe yake ita da Haj Saratu.
Amma kowanne da nasa wajan amma babban parlonsu a haɗe yake, saika shiga parlon sana zaka iya wucewa part ɗin kowanne.
Ai su Inna Hindatu da suka shiga part ɗin Aunty Haja bayan sun shiga da ita ɓangaren uwar gida Haj Binta, kuma ta tarbesu cikin sakin fuska ita da yaranta bata nuna komai ba, kuma sai suka sake ganin darajarta. Hamshiƙiyar kuwa Haj Saratu ƙulle ɓangare tayi koda suka zo, ai ko Maryam taja su ta ce koda ma yana buɗe baza su je ba wallahi, saboda sun san baza'a kwashe ta daɗi dasu ba, da suka zo jeri da yake da Maryam kaɗai aka zo saida akai rigima ita da Surayya da kyar aka raba su, taso tayi ma Surayya dukan da zata kasa tashi gobe ma idan ta ganta bazata sake gangancin gaya mata maganar banza ba.
Sosai fa ɓangaren Aunty Haja yayi masifar kyau, kyan da yayi ma ne yasa Haj Saratu ƙara jin haushi da jin tsanarta da duk wasu danginta, dan hassada sosai ta motsa mata, dan taga fa ba raini itama ta shigo a hajiyarta ne, duk yadda suke tunanin ai talakwa ne futuk ai da gidan ƙasa suke ma, dan saida Haj Saratun tasa aka je aka mata bin binciken wacece ita ta kuma samu makaman tusa mata baƙin ciki da gaggaya mata maganganu masu zafi.
Sai wajan dare sana su Aunty Bintu suka ƙara gyara mata part nata suka fara shirin tafiya.
Maryam ta dubi Aunty Haja bayan su Aunty Bintu sun fice zuwa parlo ta ce.
"Aunty Haja saifa kinyi da gaske kamar yadda Aunty Sa'a ta faɗa miki, ki nuna ma waccar mata kema fa ba kanwar latsa bace, dan wallahi lokacin da muka zo jerin kayan ɗakinki wallahi ƙanwarta Surayya kinji maganganun data rinƙa yaɓa min?, kamar ma fa zuwa tayi ta bincika asalinmu da abubuwa da suka faru a rayuwarmu, sun samu makamin yaƙarki da baƙaƙen maganganu kenan, dan nima dasu tayi amfani, amma naso ranar nayi mata dukan da idan ta ganni ko kallo na sai taji shakkar tayi sa wallahi, Allah ya taƙaita Alhajin yazo ya raba faɗan, amma duka da haka sai da ita Haj Saratun ta rinƙa zagina tana min kallon wulaƙanci, dan haka wallahi karki raga mata, dan idan kika ce shiru-shiru zakiyi to sun samu abunda suke so ne su rinƙa sukarki da maganganu wa'inda zasu iya saka miki ciwon zuciya ne nan take, amma kinga idan suka gaya miki kema ki mayar masu dan kar kije tana miki ciwo daga baya"
"Haba Maryam ai kisha kumurunki a shirye nake da duk wani iskancinta wallahi daga ita har ƙanwarta tata, dai-dai nake dasu, karma kiji komai, ai tunda ta nuna ita sakarai ce to zan gyara mata zama ne, ai uwar gidan ta fita wayo da sanin abunda duniya take ciki, ko an gaya mata ita Haj Binta bata jin kishi ne?, ai kawai ita taku ne data fita iyawa da duniyanci, ita da yake bata da ilimin zama da mutane shi yasa take duk wannan, kodan ada taga ina mata hidimar siyasa shi yasa tafi ɗaukar abun da zafi?"
"Ohho mata ma dai, ai aure ne dai anyisa sai dai kuma ta mutu wallahi"
Sun daɗe suna magana sosai har saida Aunty Badiya ta shigo ta kira Maryam akan driver zai mayar dasu yana jiransu a waje.
Badan sun gama maganganun ba ta miƙe Aunty Haja ta ce.
"Shikenan dan Allah zuwa nanda sati ɗaya ki shigo ina so mu tattauna yadda za'ai Hannah ta dawo nan da zama a hannu na, saboda nasan zaman nata ma sai anyi da gaske dan ba ƙaramar rigima za'ai ba na sani"
"Ai bari cikin hikima zata dawo gaba ɗaya, saboda nasan komai zai iya faruwa, bawai gaba ɗaya zata dawo ɗin, baza su rinƙa zuwa ne ita da Fannah suna miki weekend daga nan saita dawo kawai ai ta duniya za'ai"
"Hakane kuma fa"
"To shikenan dai sai munyi magana"
Da to ta amsa mata saida ta rako su har ƙofar fita babban parlon daya raba part ɗinta dana Haj Saratu, sana ta koma. Duk sai taji ba daɗi tafiyar ƴan gidan nasu, kaɗaici ya rufe ta, ko aurenta na farko bata ji haka ba gaskiya, kodan wancan tafi kusa da gida ne oho?, amma wannan ai tafi ɗokinsa da kuma son wadda ta aura ɗin, kowanne dai aure da yadda yake zuwar maka..........
PAGE 62
*JAFAR POV*
Zama yayi kansa a ƙasa yana jin jikinsa a mugun sanyaye bayan ya shigo ya gaida Hajja ta ɗauke kai, duk sai yaji jikinsa ya mutu. Shi kam wai mi yayi ma Hajja ne?, waye ya sauyama Hajja tunani ne akan Mimi?, tabbas yasan dasa hannun su Shamsiyya da uwarta.
"Hajja ko nayi wani laifi ne?, dan Allah ki yafe min"
Wani kallo ta jefa masa tana gyara zamanta sosai kan ta ce.
"Wato sai yanzu kaga damar zuwa inda nake ko?"
"Hajja ba haka bane wallahi, yaufa na diro garin Allah kinji na ran...
Ɗaga masa hannu tayi ta ce.
"Kaga bana son rantsuwar nan taka ta ƙarya, ai dama ku yaran zamanin nan bafa wani sanin darajar rantsuwa kukai ba, kuyi ta akan ƙarya ai ba wani abu bane a wajanku. Ni bama wannan ba miye ya haɗaka da Shamsiyya da har zaka kamata kayi mata wannan irin duka?"
"Yawwa Hajja da tun farko wallahi haka kika tabbaye ni da tuni na baki amsa an wuce wajan. Hajja zuwa nayi fa isketa tana wasu saka ƙananun kaya matsatstsu wa'inda kwata-kwata basu dace ta saka su ba a wajan da maharramanta ba, kai kayan ma kwata-kwata mijinta ne kawai ya kamata ace ya ganta dasu, shine fa daga mata magana sai ta fara min rashin kunya ni kuma...
"Kai kuma ka kamata da duka kai ga ubanta ko?"
Shiru yayi kawai dan shi kam yama rasa abun cewa a gaba, ai ya ɗauka Hajja zata goyi bayansa ne bayan ta gama jin abunda ya faɗa game da abunda Shamsiyyar tayi.
"Na ce shine ka kama ƴar mutane kayi mata wannan dukan?, to bari kaji daina ganin na tsaya ina wani sauraronka nasan fa komai, ni zaka tsaya kana tsarawa wato?, ko nufinka ban san gaskiyar abunda ya faru bane?, matar nan taka duk ba ita ce ke zugaka ba kana wani abun ba?"
"Hajja wallahi babu ruwan Mimi a wannan maganar kawai dan sun tusa miki ƙin Mimi ne yanzu"
"Au ni zaka tsaya kana gaya ma magana akan kucakar matarka?. To bari kaji idan har ni ce na zuƙunna na haifeka to Shamsiyya na baka nan da sati mai zuwa a ɗaura aurenka da ita, idan har ni ce uwarka ba wata ba"
A mugun gigice Jafar