Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
fa abunda ya faru, ai anyi gumurzo in gaya miki, ke baccin Ma'aruf yana mutuwar sonki ai da yanzu wata maganar ake ba wannan ba"
Wata irin ajiyar zuciya Aunty Haja ta shiga saukewa hawayen murna da farin ciki na lulluɓe ta. Wayarta ce dake gefe tayi ƙara jiki na rawa ta ɗakko wayar ganin mai kiran yasa ta ɗauka jiki a mace.
Tana ɗauka ko ya shiga ce mata an ɗaura kamar wani ƙaramin yaron da zai fara aure yanzu. Ai sai Aunty Haja ta sakar masa kuka ata cikin wayar tana zamewa ƙasa tayi sujjada a ga Ubangiji tana kuka tana godema Allah.
Mi Maryam zatai ai sai ta fara ɗaukarta video tana shewa suna mata dariya, ai sai abun ya bada kala, dan har mayafi Aysha ta yafa mata sai tayi kamar sabowar amarya dama can.
Rungumeta Aunty Sa'a tayi tana shafa bayanta dan kukan da take harda irin shaidar dasu Kawu Sani suka rinƙa bawa mutanen da suka zo neman aurenta, da yanzu kenan sunja an fasa auren?. Sai dai Allah idan ya ce abu ba mahaluƙin daya isa ya hanasa faruwa.
"Ki daina kukan nan haka nan please, kinga ma kukan naki ya hanaki amsa wayar mai gidan naku dole sai dai ya katse wayar"
Aunty Sa'a ta faɗa tana aje wayar Aunty Haja a gefenta dan ganin kiran ya datse.
"Ai wallahi dole ne tayi kuka, saboda abunda bata taɓa tsammani bane sai gashi ya faru a ɗan ƙanƙanin lokaci haka, lallai Allah-Allah ne wallahi"
Aysha ta faɗa da wata irin murna a cikin muryarta.
"Ai lamarin Ubangiji ya wuce duk yadda kuka zato, yanzu ba gashi ba kamar wasa Hannah ta fara bata shawarar tashi cikin dare ta roƙi Ubangijin talikai ya jawo mata hankali Alhaji Ma'aruf yasa masa sonta a ransa, ba gashi ba ta ɗaure ta cije da kamar ta fara nuna gajiya da addu'ar kanta amma Hannah ta sake bata kwarin gwiwa yanzu baga shi ba yadda ma Alhaji Ma'aruf ke nuna rawar ƙafar auren nata abun har mamaki yake bani ni wallahi"
Cewar Maryam.
Hannah kam miƙewa tayi tana cewa.
"Ai idan har zaka miƙe lamarinka wajan Ubangiji ka bashi zaɓi ka kuma yi hakuri to insha Allahu Ubangiji bazai taɓa baka kunya ba, ai addu'a ita dama makamin mumuni ce, addu'a tana da mutuƙar tasiri ga bawa, ita addu'a bata taɓa faɗuwa ƙasa banza, duk wani abu daka san ka roƙa yanzu ko anjima to fa tabbas Ubangiji majin roƙon bayinsa ne, zai amsa, sai dai idan abun nan daka roƙa babu alkhairi a tattare da kai dashi, sai Ubangiji da yake shi Adili ne sai ya musanya maka da mafi alkhairinsa, kai ko ba'a baka wannan abun daka roƙa ba a nan gidan duniya to idan aka je lahira Allah zai baka shi a can"
Su duka kallon Hannah kawai suke cike da alfahiri, dan Aunty Haja saita miƙe tana zuwa ta rungumo Hannah jikinta, ai sai abun ya sake bada kala Maryam nata aikin video tana murmushi.
Ai ko nan take Maryam tayi posted ɗin abun a WhatsApp nata da duk wata kafar sada zumunta, tasa Mrs Ma'aruf Kangiwa aure dai ya riga da ya ɗauru ƴan baƙin ciki sai dai a mutu.
Tofa tunda tayi posted abun nan su Ihsan suka ci karo da posted ɗin, ita dai Ihsan bata ce komai ba amma ta gani tabbas amma kam Surayya harda zage-zage da tsinuwa sai da ta aiko ma da Maryam su, ai ko su Ammi najin lokacin da Maryam ɗin ke maida mata magana, suna jin voice ɗin da Surayya ta rinƙa aiko mata dashi tana cewar. Talakawan banza da wofi uban waye bai san yadda suke ba?, ƴan iska masu bin mazajen mutane. Kai zagi kala-kala yarinyar nan ta rinƙa aikowa wadda yasa Aunty cewa.
"Kinga Maryam barta haka nan karki sake tanka mata, na lura Surayyar nan ita da Haj Saratu sun matuƙar ɗaukar auren nan da zafi, amma uwar gidan tasa Haj Binta naga ba wani abunda ta ce har yanzu ita"
"Ai har Ihsan ɗin taga posted nawa wallahi bata ce komai ba, da alama sun fisu kirki ko a gidan"
"To wato Haja ke da Haj Saratu zaku zuba kishi kenan?, dan naga ita ce tafi ɗauki abun da zafi. To abunda zan gaya miki wallahi idan kika sake kika nuna mata sanyi to ba ƙaramin raini ne zai shiga tsakaninku ba, ki fa nuna mata kema dai-dai kike da ita, sana wannan ƙanwar tata Surayya naga kanta rawa ub*anta zaki ci itama sai kiga an zauna ƙlau dasu"
Aunty Haja ta ɗago daga jikin Hannah da take tajawo hannunta suka zauna akan kujera a tare kamin ta ce.
"Amma Maryam miye yasa ki ɗora abun nan?"
"To wai miye a ciki idan ta sa ɗin, ai kawai garama a san aure ne dai an riga da an ɗaura shi, ni banga aibun abunda nayi ba"
Aunty Haja zatai magana wayarta tayi ƙara, miƙo mata wayar Aunty Sa'a tayi ganin baƙuwar number ce yasa Aunty Haja ɗauka kawai da sallama. Sai dai kamin ta idasa sallama daga cikin wayar taji an fara cewa.
"To munafuka burinki ya cika kin aure mana miji, to ki sani na rantse da Ubangiji saina hanaki zaman lafiya a gidanmu, ba dai ke mai kwaɗayin abun duniya ba?, to billahir azim gidan Alhaji Ma'aruf sai ya zame miki abu mafi munun da zaki aikata wadda zakiyi danasanin da baida iyaka, ni Haj Saratu saina saka kin gudu da ƙafafunki wallahi, Mtswww aikin banza kawai idan baccin maza ma da iskanci Alhaji ya rasa wacce zai ɗakko sai ƴar gidan matsiyata wa'inda suke yawon ta zubar"
Kusan duk abunda Haj Saratu ke faɗa Aunty Sa'a naji dan tafi kusa da aunty Haja ɗin, ganin tayi shiru kuma zata katse kiran yasa Aunty Sa'a fisge wayar tana sakata a amsa kuwwa ta fara ce mata.
"Ai baiwar Allah gidan Alhaji Ma'aruf Hajara ta shigesa kenan sai mutuwa ita kaɗai ce ta isa ta rabata dashi, kuma da kike cewa ya rasa wacce zai ɗakko maku sai ƴar gidan matsayita, ke kije ki binciki naki asalin iyayen mana, kuma idan ta shigo ɗin idan baki fasa fitar da ita ba kin raina Ubangijin daya halicce ki kinji ko, aikin banza kawai"
Tana ƙare faɗar hakan ta datse kiran tana jan dogon tsaki.
Sai kuma ta dawo da dubanta wajan Aunty Haja da mamaki ya gama rufe ta, iya saninta dai tayi blocked ɗin number Haj Saratu saboda a kwanakin kiranta take yi ba ƙaƙƙautawa tana zaginta, shi yasa tayi blocked nata kawai, sai gashi ta samu wata number ta sake kiranta dashi.
"To bari kiji idan kika ce haka zaki shiga gidan Alhaji Ma'aruf kina yin wannan shegen shirun naki da sanyin nan na rantse da Allah gaki canma kin fito daga gidan nasa, dan yadda nake jin furucin matar nan tsaf zata iyayin komai akanki, dan haka sai kisan abunyi wallahi"
"Haba dai Aunty Sa'a ai nima bari nayi ta ƙarashe tata maganar na maida mata tawa sai kuma kika amshe wayar, wallahi zan baki mamaki ne ki bari kawai na shiga gidan, ai dai-dai nake da duk wani iskancinta wallahi, dan lura tafi kowa bala'i a gidan"
"Kuma tafi kowa ɗaukar auren da zafi, dan haka saikin dage akanta wallahi"
Cewar Maryam.
Ammi dai tayi gyaran murya zata fara magana kenan suka juyo sallamar su Kawu Sani, hakan yasa tayi shiru tana ɗaure fuskarta, suma su Aunty Haja ɗin fuskarsu ce ta sauya jin sallamar tasu.........
PAGE 56
"To Ikon Allah, ya naga daga jin sallamarmu kun sauya fuska?, koma amsa sallamar tamu ba wadda yayi cikinku?"
Tashi Ammi tayi tsaye tana kallonsu da kyau kamin ta ce.
"Miya kawo ku gidan nan?"
"Kamar ya miya kawo mu?, baccin kin san akwai maganar da zata sake shigowa damu, sana ga sadakin Hajara nan a hannunmu"
Miƙa hannu Ammi tayi ta amshi sadakin da Kawu Sani ya fiddo.
Bayan ta amshe sadakin ta sake cewa.
"To tunda kun kawo sadakin nata sai ku fice min daga gida ko?"
"Kaii"
Suka haɗa baki wajan cewa, da mamaki kwance akan fuskarsu.
"Ohh wato mun gama miki amfani shine harda fara korarmu?, wai shin ƴaƴan nan da kike taƙama naki ne muma ai idan da mutumci da dajara ai mun isa dasu"
"Kunga dakata da'allah Yaya Sama'ila, karfa ku mance irin abunda kukaje kuka rinƙa faɗa ma bayin Allahn nan fa, duk fa wani abu da kuke faɗa akan kunne na naji duk wani abunda kuka ce wallahi a tafin hannuna kuke ku dukkanku, ai sai yanzu ne ma na sake gaskata cewar baƙin ciki kuke mana nida yara, kai hatta ɗan uwan naku ai baƙin cikinku ne ya idasa kashesa wallahi ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba"
"To wani ni Yaya Sama'ila mima muka ce ne ai ban sani ba?, ga dai aure an ɗaura shi, idan da munyi niyyar mata baƙin cikin da kike ta ikirarin muna yi matan zamu amshi auren nata ne kike gani?, yo ba sai muce auren bazamu bada shi ba, sai muga ƙaryar baƙin cikin da kike ta faɗa"
"Kaga Sani kyale ta, na lura yanzu dan taga sun fara jiyo ƙamshin arziƙi shine har za'a fara wulaƙantamu ko?, to yayi kyau, ai da yake akwai sauran yara a tare dake, kuma ko anƙi ko anso mudai zamu aurar dasu ɗin, tunda haka kika ce basai mu janye hannunmu ba daga shiga sha'anin auren nasu ba"
"To sai mine idan kunyi ɗin, ai ni da abunda kuka je kuka rinƙa faɗe a wajan manema auren Haja wallahi gara ace cewa kukai bazaku bada auren nata gare su ba, nafa ji duk irin abunda kuka rinƙa faɗa akan kunne na, ace wai ku ko kunya ma bakwai ji?, ƴaƴan cikinku jini ɗaya yayoku da Mahaifin yaran nan amma wai har zaku iya buɗe baki a gaban wasu kuna aibata su, tirrrr da baƙin hali irin naku wallahi"
A zabure Kawu Sani zai maida mata martani har yana shirin nunata da yatsa Kawu Sama'ila yayi saurin riƙesa yana ce masa a kunnensa.
"Kaga Sani kabi matar nan a hankali fa, dan wallahi idan har muna so muci arziƙi muma mubar arziƙi a inda yake to saifa mun rinƙa lallaɓasu yanzu, domin dai na lura sunsha kwana, ace wai Haja ce ke auran mataimakin gwamna?, ai kaga abun sai anayi ana kwantar da kai. Nifa na ɗauka ma ƙarya suke da suke cewa wai Alhaji Ma'aruf dai dana sani shine zai auri Hajara sai da fa suka zo ai kaga dai jifga-jifga Motocin da su zo dasu, bafa ƙarya a wannan al'amarin al'qurnin Allah da gaske Alhaji Ma'aruf ne muka aura ma ƴarmu"
Wani miyau suka haɗa kusan ta tare suka ɗago suna duban Ammi.
"Kinga Salame shikenan dai magana ai ta wuce, kuma ya za'ai ki ce muna ma ƴaƴan nan baƙin ciki?, kawai fa mun faɗa masu wasu maganganun ne akan yaran nan dan kar ma suje wani waje su jiyo ace ko mun cucesu ba'a faɗa ba, abu yaje ya dawo ai kinga babu daɗi ai ko?"
Taɓe baki tayi tana dubansu da mamaki jin yadda suke mata magana cikin ruwan sanyi da kwantar da murya.
Su Maryam ma mamaki duk ya gama cikasu, sai binsu da kallo kawai suke.
"Koma dai miye ai ta faru ta ƙare, dan haka sai a tari gaba kuma, ai dama na ce maku insha Allah yaran nan sai sun zama abun kwatance kuma gashi kun fara ganin alamar hakan, yo addu'ar uwa wasa ce"
"Ai wallahi mun fara shaidawa kam"
Kusan suka haɗa baki wajan faɗa.
"To tsayuwar mi kuke ne wai?, ba an gama komai ba?, ko akwai wani abunne?"
"Uhm dama na ce cikin kuɗin neman auren ne baza'a bamu wani abu ba?, tunda harda sadakin duka muka haɗo gasu nan duka"
Ɗaga kuɗin Ammi tayi tana jujjuya su, bandir ɗin ƴan dubu-dubu ne kusan guda biyar ta ce.
"Ai na tabbata wa'innan kuɗin sunfi haka aka bada, kawai kun kwashi wasu ne na sani wallahi, nifa na sanku kamar yinwar cikina, kuɗin ido ga kuɗi jikinku har rawa yake tsabar son abun duniya idan kukaga kuɗi tsirara mance kanku ma kuke, sana wai ku ce ba abunda kuka ɗauka daga ciki ai ina wallahi nasan ƙarya ne"
Kusan haɗa baki sukai zasuyi magana Aunty Haja ta miƙe tana cewa.
"Ammi ya isa haka nan please"
Ta ɗakko jakarta dake kusa da ita ta buɗe ta fiddo wasu kuɗi masu kauri ta miƙa masu, ai ko jiki na rawa Kawu Sani ya amsa yana washe hakora.
"Kaga irin albarka, amma ke Salame baki mance abunda ya riga da ya wuce ne wai?, yanzu baga shi ba ita da yake tamu ce ta ɗauka ta bamu ba?"
"Ohho dai ni ai dama bata inda aka haɗu kam, ita dai da yake jininku na yawo a jikinta ai dole taji tausayinku duk irin abunda kukai masun ai bazasu ƙiku ba, da dai kune nasan ko mutuwa zasuyi bafa zaku ɗauka ku basu ba"
"Haba Salame wacce irin magana ce wannan?, ya za'ai mu hanasu abun hannunmu baccin ƴaƴan nan muma namu ne?"
"Ahhh yo ai nake ganin sadda ma Mahaifinsu na raye yana buƙatar taimakon ku ko tsinke baku iya ɗauka kun bashi da sunan gashi ya ƙara ba, har ya koma ga Ubangiji yana baƙin cikin irin abunda kuka rinƙa yi masa lokacin da yana kwance ba lafiya, kuka ƙaurace masa ko inda yake bakwa zuwa, sai yanzu zaku wani zo kuna cika ma mutane baki?"
Shiru sukai dan kam ta kashe masu bakin maganar.
Cike da borin kunya da kyar Aunty Sa'a ta lallaɓa Ammi tayi shiru su kuma suka tafi, cewa wai nan da sati ɗaya Hajara zata tare a gidan aurenta dan haka ranar tarewar su Hadiza da sauran ƴan gidan zasu zo rakiya, kamar Ammi ta tanka cewar bata buƙatar ayi yayar mutane amma sai ta kyale kawai ganin yadda Aunty Sa'a tayi saurin girgiza mata kai.
"Ni wallahi dakin barni na faɗa masu Sa'a bamu buƙatar jama'a da yawa wajan tarewar tata, ai sai aje ana wasu maganganu da gutsiri tsoma kuma, ita da za'a kai gidan kishiyayo"
"Kuma wallahi tsabar gulma ce zata kaisu ba wani abuba ba"
Fannah ta faɗa tana taɓe baki.
"To ke Aunty Fannah miye idan sunje ɗin? duk dai ba ƴan uwa bane"
Wata harara Fannah ta zafga ma Hannah tana cewa.
"Yo ke dama ai haka zaki ce tunda ke ciwon kanki ma baki sani ba, da har...
"Kinga nifa banga laifin idan an barsu sunje ɗin ba, saboda mi suje su gano ma inda za'a kaita suga fa eh babu raini kuma ba ƙarya bane ai hakan shine dai-dai"
"Yawwa Maryam abunda nake so na ce kenan nima kika riga ni ai"
Aunty Sa'a ta faɗa tana nuna Maryam.
"Hmmm ni wallahi da an biye ta tawa da kawai daga ni sai su Aunty Bintu da Aunty Badiya kaɗai sai ku sun isa su kaini ba sai anyo kwasar ƴan can gidan ba masu bakin magana, suda abun magana baya masu wahala"
"Ni jiya ma mukai waya dasu badai su san an ɗaura auren ba, dan Bintu sai murna take wallahi har tana cewa wai tunda wuri zasu taho, kun sansu akwai sun harkar girma suma"
"Ammi waye zai so harkar ƙaranta, ai harka irinta arziƙi tayi kawai Mlm"
"Ai inaga wajansu kikayo gadon wannan halin nasun huɗɗa da masu kuɗi, dan karki so jin yadda suke murnar Haja zata auri wani a ƙasar nan wallahi, su dama haka suke su ai yaran nan su samu mai maiko-maiko, ni wallahi dariya ma suke bani"
"Ai banga laifinsu ba"
Cewar Aysha.
"Yanzu dai zan kira su na gaya masu anma dai ɗaura aure saura kuma zuwa ya rage masu ayi bikin tarewa. To ku miye kuka shirya na bikin tarewar?"
"Nifa Ammi ba wani abunda zanyi, nida ba auren farko ba"
"Ai wancan daban wannan ma daban, dan gaskiya wannan auren ai mai class ne, dole ki barmu mu shirya koda party ɗaya, kuma ɗayan tamƙar dubu wallahi, dan dole ne ma a shiryashi dan zan gayyaci ƙawaye na, ke ƙarewa ma harda su Ihsan ɗin da ita kanta Surayya ɗin sai dai su mutu wallahi amma dole na aika masu da invitation na party da zamu shirya"
"Kai Aunty Maryam ina rabaki da mutanen nan fa"
"Mtsww kin san Allah Aysha saifa an gayyace su Allah kuwan, idan yaso suƙi zuwa ba ruwana"
"Hmm nida kun biye da ba abunda za'ai wallahi"
"Kinga Haja kifa kyalesu suyi abunsu, ai biki idan ba'ai ɗan wani abuba ba daɗi yake ba"
Aunty Sa'a ta faɗa.
"Yawwa Aunty Sa'a dan haka kawai zamu shirya cocktail party na gani na faɗa wallahi. Ke Hannah ke ce zaki haɗa mana Cakes wadda za'a ci a wajan, sauran abubuwan da za'a ci kuma Aunty Sa'a zata ɗauki nauyin yi mana su gaba ɗaya saimu taya ta yinsu"
"Ubanwa bafa zanyi aiki da bikin gidan nan ba yawwa, kawai ku kira Fulanys kitchen zata zo har nan ta jagoranci komai da kuka sani"
"Kai nama mance da ita, to shikenan zan kuwa kira ta a waya ai ina da number ta, ta iya abubuwan irin wannan na party haka tana zuwa sosai"
Aysha ta ce.
"To yanzu dai wane kalar kaya zamu saka, ita kuma Amarya fa wane kala zata saka, ke kifa saka ango sai yazo wajan nan dan wallahi har ango na zuwa"
"Tabɗi jam ai ko wallahi bazansa yazo ba, abu duk na yara kawai yana babban mutum da yaransa sai kawai ya kama zuwa wajan party na da ƙananun yara a ciki?"
"To wai miye a ciki?"
Cewar Maryam.
"A'a kunga kudai yi abunku iya ku kawai"
Ammi ta faɗa.
"Amma Ammi..
"Kinga ai kema kin san abun bafa yiwuwa zaiyi ba, kawai ku shirya iya naku kawai"
"To gaskiya sai dai a sake ayi Kamu kawai, domin shi ango yana zuwa a sanin da nayi"
Fannah ta faɗa.
"Shikenan hakanma yayi anyi