Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   39 / 47

114K to 117K   out of 140.3K words

kawosa nan kwata-kwata baya zuwa, ko hanyar shashinku, yanzu na gansa fa ya fito kinga kuwa ai daga can yake, ƙilama Alhajin yana ciki dashi suke tare"

Jinjina kai Haj Saratu tayi tana cewa.

"Ahh lallai ba shakka, mu tunda muke dashi ya taɓa takuwa har inda muke ya gaida mu ne?"

"Ni ba wannan ba Aunty kin san dai halin Abeed ba zuwa zaiyi ba, wannan ɗin ma sa'a ta taka dan bai taɓa ganinta bane, ƙila Alhajin ya matsa masa sai yazo ya gaida itan. Ni wallahi jikina ya fara sanyi dashi anya bazan fitar da wani ba kawai nabar Ya Abeed"

Ido waje Haj Saratu ke duban Surayya, a ɗan tsawace ta shiga ce mata.

"Ashe baki da tunani ban sani ba?, wato kema sarewar zakiyi irin yadda Ihsan ta sare kenan?"

"To ai Aunty naga kwata-kwata muna ta aiki ne ba wani ci gaba, har tsawon yaushe ne zamu ɗauka?, duk tsawon lokacin nan Abeed baifa taɓa min kallon ko minti ɗaya ba, wata ƙilama ko gama sanin kamannina baiyi ba wallahi, kallo ɗaya yake ma mutum ya ɗauke kansa baya ƙara kallon kota inda ya biyo fa, ni kam bazan iya da baƙin hali irin nasa ba gaskiya, yo wannan ko auren akai ai matar tashi ta shiga uku dashi wallahi, inaga Aunty Zahra ce kaɗai ta cire tuta wajan sauya masa hali, itama tasha wahala kamin komai ya dai-daita, daga baya kuma ta rasu bata ma ci gajiyar sauya halin nasa da tayi ba, sai gashi ya sake komawa gidan jiya, yo bama gara da can baya ba kamin rasuwar tata, yanzu mutuwar matarshi duk ta ƙara sakawa ya zama miskili wallahi"

"Koma dai miye sai inda ƙarfinmu ya ƙare, amma bazan bari ki taɓa sarewa da Abeed ba, idan kika auri Abeed ai kin kece raini ko a wajan ƙawaye ne, ke duk duniya ma kin wuce raini wallahi, ke baki gansa bane ki hasko kanki a matsayin matarsa mana, ai ko baya miki magana dole dai a kira ki a matsayin matarsa"

Ai sai Surayya ta shiga sakin murmurshi tana jinjina kai harta fara hasko kanta a matsayin matarsa, tana wani murmushi harda su ƙanƙame jikinta tana ɗan sakin ihun murna ta muƙe tana rungume Haj Saratu tana cewa.

"Kuma fa hakane Aunty, ni wallahi ko kallo na bayayi ko magana bata shiga tsakaninmu ni dai kawai na amsa sunan matar tashi, nasan ma yadda yake da ilimin addini dole ne ya kulani ya bani haƙƙina na aure, kawai auren nasa ne keda mutuƙar wahala"

Ta idasa maganar jikinta na sake yin sanyi.

"Ke wai mi yasa kika fiye sarewa ne?, da faɗar maganar da zata rinƙa sawa kiji bazaki iya ba?, ki rinƙa sakama kanki kamar ma kin auri Abeed na gaya miki"

Surayya na shirin magana tana ɗan sakin Haj Saratu suka ji fitowar Alhaji tare da Aunty Haja na biye dashi suna dariya a tare.

Wani baƙin ciki ne yazo ya tokare zuciyar Haj Saratu dake binsu da wani irin kallo, Surayya ma kallon nasu take tana taɓe baki.

"Mtsww wai ke kam baki girma ne shin?, kun manyanta kun zama tsofaffi amma kuna abu irin na yara. Sana Alhaji tsakani da Allah ace har Abeed zai shigo gidan nan ya tsallake mu yaje ya gaida wannan abar wacce ita ce ƙarama a cikinmu?"

Alhaji ya girgiza kansa yana kallon Haj Saratu data idasa maganar tana wani cika tana batsewa, yasan neman rigima ce kawai take, amma ai tasan Abeed ba shigowa yake wajansu ba tafi kowa sanin hakan.

"Alhaji kayi shiru ka kyale ni ina magana?"

"To mi kike so na ce miki Saratu?, baccin maganar da kikai kina da amsarta a wajanki, dan haka banga abunda zan iya ce miki ba ni"

"Eh lallai ba shakka wallahi, an baka kasha ai, shima Abeed ɗin ya dawo ai za'a gama mana dashi ko?. To ki sani Abeed dai nan gani nan bari, bari ganin kin tara wasu Ƙannanki mata masu kama da Aljanun farko, ba wacce zata birge Abeed a cikinsu bari na sake gaya miki wallahi, gara ma idan da wannan a zuciyarki kiyi maza ki farka daga wannan mafarkin ko tunanin ki gogesa a ranka wallahi"

Aunty Haja ranta a ɓace zatai magana Alhaji ya ɗaga mata hannnu, ganin hakan yasa Aunty Haja haɗe maganar tata tana juyawa da sauri ta koma part ɗinta tana jin zuciyarta kamar zata fashe da Alhaji ya hanata maida mata magana wallahi.

Haj Saratu tabi bayanta da wata uwar hararara kamar idonta zasu faɗu ƙasa tana sakin tsaki mai ƙara.

Sakin baki tayi kuma ganin Alhaji ya juya zai bar parlon.

"Wato Alhaji ni ka maida mahaukaciya ma ko?, ina magana ka tafi kabar ni tsaye kamar wata sakarai?"

Nan ma bai juyo ba bare ya tsaya ya bar parlon yabarta tsaye tana cizon yatsa.

"Wallahi Aunty an gama da Abbey fa, wannan matar dama can da mugun abu da shigo maku gida, da yana maku hakane?"

"Hmm ai wallahi shi dai ta gama dashi amma ni nafi ƙarfinta wallahi shegiya mai baƙin hali wadda tayo gado a can gidansu, matsiyatan banza da wofi kawai, anzo an samu waje ai dole a baje ƙafa ai ko?"

"Kuma wallahi tsaf kiga abunda kika faɗa na Ƙannan nata ne a ranta taga ɗaya ta auri Abeed, ai babu wacce zata ga Abeed batai sha'awarsa ba"

"Rabu da ita, ai idan baku samu Abeed ba har abada suma ba samun nasa zasuyi ba, yo da ubanmi suka fi ku, naga ma dai Abeed ɗin nan ko turawa ba birgesa suke ba shida ke zaune a can ƙasarsu bare wa'innan masu kama da Aljanu"

Ta ƙare maganar tana baƙin cikinsu Hannah da suka fi Surayya abubuwan da ɗa namiji ƙaryarsa ya ce basu birgesa ba, idan kyau ne tasan fa sunfi Surayya surarr jiki kam ai ba'a maganarta ma, dan Surayyar irin siraran matan nanne wadda kwata-kwata basu da fasalin jiki, ranar ko data fara ganinsu Hannah saida gabanta ya faɗi ganin yadda Ubangiji ya zuba masu sura kamar sune sukai kansa, ita kanta Aunty Haja ɗin tasan tafi su komai na kyan jiki da sura, shi yasa taso tada rigima da zamansu Hannah gidan, amma Alhaji ya murje ido ya watsa mata ƙasa a ido, ita kanta shi yasa tafi kishi da Aunty Haja saboda duk ta gama susuta masu mai gida, daɗinta ɗaya Abeed ɗin yanzu baizo ya iskesu Hannah ɗin ba.............

PAGE 71

*HANNAH POV*

"Ba dake ake magana ba Hannah?, ke ce kika sa a turo azo neman aurenki?"

Kanta na ƙasa ta ɗago tana duban Ammi dasu Aunty Bintu dasu Kawu Sani da suka tsare ta da tabbayoyi.

"Eh Ammi nin...ni...ni ce na ce"

Jinjina kai kawai Ammi tayi tana duban Aunty Sa'a dake zaune itama sai ta dawo da dubanta wajansu Kawu Sama'ila ta ce.

"To ya kukai dasu ma, muda bamu san da zuwansu ba?"

"Anyi komai dai kamar yadda al'ada ta ce, amma daka ganin mutanen basu da dattaku gaskiya, kuma sunce suna so asa bikin nan da watanni uku masu zuwa"

"To wai ɗan gidan waye ma a ƙasar nan?"

Cewar Aunty Bintu.

"Eh to sanne ne uban nasa D.S.P Sada Bin Umar, da yawa mutane sun sanshi tsohun ɗan Sanda ne amma dai yayi ritaya a yanzu, suna kuma zaune a garin Kano ne, amma asalinsu ƴan jahar katsina ne"

Jinjina kai suke kamin Ammi tayi gyaran murya tana duban Hannah da kanta ke a ƙasa jikinta sai rawa yake.

"Kina sonshi?"

Ɗaga kanta tayi kamar mai tsoron wani abu.

"Baki zaki buɗe kiyi magana?"

"Eh..e...Eh.. Ammi"

"Yayi dai-dai tashi kije. Yaya Sani zaku iya komawa ku basu damar sai a tsaida ranar nan da wata ukun kamar yadda suke so ɗin, tunda an riga da ansan waye ubansa"

"Amma Salame ni fa mutanen da suka zo neman auren yadda suke mana magana a wulaƙance ne bai kwanta min ba, gaskiyar magana ni basu kwanta min ba, koba hakane Sani?"

"Eh to kware da gaske, ni nayi shiru ne dan kar ace ko muna baƙin ciki ne, amma gaskiyar magana mu yanzu inda zasu huta muka fi so suje"

"Shin badai shi take so ba?, to ku kyale ta da abunda take so ɗin, dan Haja ma ta kira ni jiya tamin bayanin komai ai, dan haka kawai a rabu ita dan Allah"

Jinjina maganar sukai sai suka miƙe a tare dama sunzo su shawarci Ammi ne da ƴan uwanta da kuma jinta bakin ita Hannah ɗin saboda basu san da zuwan baƙin ba, suna can sun baro su suna jiran abunda iyayen yarinyar zasu yanke akan auren.

Jiki a sanyaye Hannah tabar parlon.

"Amma Aunty kina ganin hakan yayi kenan?"

Ammi ta ɗago tana duban Aunty Bintu ta ce.

"Ya kike so nayi, ta nuna ba wadda take so sai shi, tsabar ma rashin mutumci irin nata tasan za'a zo amma taƙi faɗa?, saifa jiya Hajara ke kirana tana gaya min fa"

"Amma gaskiya nima wannan Annur ɗin da take ta faɗa kwata-kwata bai min ba, duk dai na gansa a photo amma gaskiyar magana...

Murmushi kaɗan Ammi ta saki tana cewa.

"Badiya kenan ai shi yaro idan ya ce abu to kawai ka sa masa ido, bare idan ya faɗa soyayyar zamanin nan"

"Kinga ni ba wannan bama, an kira mana mai kwalliyar nan ne, kusan ƙarfe uku ne za'a tafi wajan Kamun nan kamar dai yadda akai na Haja"

Cewar Aunty Bintu ta ƙare maganar tana miƙewa tsaye.

Babu kowa dama a gidan dan Maryam tuni ta wuce gidan kwalliya, dama shekaran jiya suna isowa ta tafi gidan ƙunshi washe gari kuma taje aka gyara mata kai akai mata Saloon.

Komai suna yi ne tare da Nihal ƙanwar ango gata babbar ƙawar amarya, dan yau ma sai da Nihal ɗin tazo ta ɗauki Maryam ɗin dan tare zasu je kwalliya.

Dama gidan Hannah ce kaɗai aka bari dan ita ta ce wannan karan bazatai makeup ba, Fannah kam tuni ta tafi tata kwalliyar Aysha ma wajan mai mata kwalliya da nata saurayin yazo ya ɗauketa, dan shima ansan dashi a gida dansu Kawu Sani ma sun san shike neman Ayshar shi yazo ya kaita Naseer Belloh Rabe kenan, shima ɗan asalin jahar Katsina ne a nan iyayensa suke suma sannannu ne dan ubansa suke da Munaj event center, dan haka wannan Kamun ma kusan kyauta aka shirya masu komai saboda Aysha Naseer yasa aka basu waje mai girma a event ɗin aka shirya wajan sosai.

Su Inna Hindatu ma wannan karan anyi ɗinki mai kyau ba laifi saboda yanzu sosai su Kawu Sama'ila ke samun ƴan kuɗi wajansu Ammi dasu Aunty Haja ba laifi duk da irin abunda sukai masu sun mance komai suna taimaka masu, yanzu kam komai za'ai sai an tuntuɓe su, babu abunda zai taso a family ba'a fara sanar dasu ba.

Hannah ce ƙarshen fita daga gidan dan ita saida Annur yazo ya gaida su Ammi ya jirata danshi zai miƙata wajan Kamun.

A Mota suna tare sai yaba kyan da tayi yake tana murmushi tana binsa da kallon so, dan ba ƙaramin so take ma Annur ba, ya rigada ya gama da zuciyarta a ɗan ƙanƙanin lokaci.

Cike da so da ƙauna suka ƙarasa wajan dai-dai wajan biyar da ƴan mintoci, dan har an fara Kamun ma a tare suka shiga wajan yayi kyau sosai ba kaɗan ba.

Hango Aunty Haja da tayi zaune akan kujera can kusan sune farko a hall ɗin, tasha wani mugun leshe sai walwali take ɗan cikinta harya fara tasawa ya ɗan taso kaɗan dan daka mata kallon tsaf zaka san cike ne da ita, a ranar da suka haɗu dasu Aunty Bintu murna sukai tayi dansu gane tana ciki, kamar su maida ta ciki haka suka rinƙa ji, ita kanta Ammi sosai taji daɗi sai murna take ganin ƴar tata da rabo gata cikin wadata da jin daɗi dan cikin sabuwar Motarta aka kawo ta driver ya kawota ya kuma tsaya jiranta dan ana gamawa zata koma sai kuma gobe tazo tunda safe bazata koma ba har sai an kai amarya dan gobe juma'a za'a ɗaura aure.

Hannah ta kawota Annur suka gaisa Aunty Haja na dariya tana tsokanarsa akan bazata amsa gaisuwar nan ba har sai an kawo mata shi gida sun gaisa, shima da yake akwai barkwanci ya shiga biye mata yana cewa insha Allah bayan biki zaizo har gida ya gaida ta.

A nan suka samu waje suka zauna, Aunty Haja sai taji daɗi ganin kamar baida matsala, amma taso ace Hannah ce zata shiga gidan Abeed a matsayin mata, dan bata ga ta inda Annur yafi Abeed ba, bama zaka taɓa haɗawa ba ai hanyar jirgi daban ta mota ma daban, duk dai tasan ita zuciya ba ruwanta da duk wani abu idan taso mutum duk yadda yake baka ganin aibunsa.

Sosai aka gudanar da Kamu yadda ya dace dan yaso ma yafi na Aunty Haja tsaruwa da kyau, anyi komai cikin tsari ƙarfe bakwai na dare aka tashi aka fara jidar mutane komawa gida.

Ita kam Amarya tare da Nihal suka dawo gida dan a nan Nihal zata zauna har sai an ɗaura aure.

Tunda zasu dawo Maryam ke waya da Fu'at sai tsinkar fire suke Nihal sai sakin tsaki take tana cewa.

"Ni dai abunku ya fara isa ta haba, wai Ya Fu'at ke wannan zuba ƙauna haka kamar ba shi ba?, kinbi kin lalata mana Yaya"

Nihal ta ƙare maganar tana makama Maryam hararar wasa.

Duka Maryam ta kawo mata a baya tayi saurin gocewa tana dariya haɗe da kanne mata ido ɗaya ta ce.

"Wallahi dama kin daina biye masa dan nan da jibi sai kin gwammace dama-dama...

"Kefa baki da kunya wallahi Nihal yanzu zaki iya ɓaro wata maganar daban"

Maryam ta faɗa tana murmushi da sauri ta miƙe tana shigewa toilet ɗin taga Nihal bafa shiru zatai ba.

Washe gari gida fa ya ƙara ɗaukar harami dan tun wajan ƙarfe tara na safe hayaniyar yidan ta ƙara yawaita, tunda safe Maryam taji muryar Aunty Haja ta iso. Gajiya da ciwon kai ya hana Maryam miƙewa ta shiga wanka, da kyar Nihal ta matsa mata ta tashi ta shiga lokacin Aunty Haja ta leƙo ɗakin da suke tana tabbayar Maryam Nihal ke faɗa mata yanzu ta shiga wanka, a nan ɗakin Aunty Haja ta samu waje ta kwanta itama dan yanzu tafiya kaɗan ke gajiyar da ita. Tana kwance sai ta tuno da Haj Saratu da yau ta gane tana ɗauke da ciki, harda yada mata magana ai ko saida ta tabbatar ta gaya mata maganar data barta sake da baki.

Wani tsaki ta saki tana gyara kwanciyar ta dai-dai lokacin da Maryam ke fitowa daga toilet sai zuba wani abun ƙamshi take na sabulon wanka da kuma wani turaren wanka da Aunty Haja ta bata shi take wanka dashi gaba ɗaya ɗakin ya ɗume da ƙamshin nata, har saida Nihal tayi magana tana jan Maryam da cewar so take ta ruɗa mata Yaya ya susuce.

Girgiza kai kawai tayi tana murmushi ta barta sai magana take tana janta da wasa harta shige toilet itama danta samu tayi wankan itama, dan lokacin har sha biyu ta gota gashi ana sallamowa masallacin juma'a za'a ɗaura auren.

"Aunty Haja yaya dai na ganki a haka?"

Ɗan tashi tayi zaune tana kallon Maryam dake shiryawa a tsanake ta ce.

"Hmm bari Amarya nida Haj Saratu mana, nazo tahowa gida kawai naci karo da ita, sai yanzu wai ta gane ina da ciki, shine ta shiga gaggaya min magana wai ai dai kamin nazo anyi ciki yakai nawa a gidan, sana ƴaƴa ne dai Alhaji yagama ganin yara da har za'ai ciki baza'a sanar dasu ba, sai ka ce wani cikin gwal bana mutum ba, ke karki so jin irin maganganun data rinƙa faɗa wasu ma daga ji baƙin ciki ne ya isheta ta rasa ma abunda zata faɗa zaro su kawai take. Kuma harda ƙarin baƙin cikin yanzu Abeed duk abunda zaici a gidan idan har yazo waje na yake zuwa na zage nayi masa abinci mai rai da lafiya, danma na lura yana son Cake sosai gashi Hannah bata nan bare ta rinƙa masa sai an gama hidimar bikin nan dai idan sun dawo, to shine fa kullum saita yada min magana wai shima na gama mallakesa da abinci ana masu barbaɗe-barbaɗe, ke wannan mata na rasa miye ma tsare mata?, bamu haka da Haj Binta ita harkokin gabanta ma sun isheta, kuma ni banma gaya miki ba jiya ba sai ga manema auren Ihsan sunzo ba, har na saka rana wata uku itama masu zuwa kamar yadda aka saka na Hannah wallahi ni kam na tayata murna dan itama wadda zata aura ɗin ubansa sananne ne a ƙasar nan, bama nan zasu zauna ba, ɗan kwallon ƙafa ne saurayin ga kuɗi shima"

"Kai gaskiya na taya ta murna, ai ƴan ball suna da kuɗi Aunty Haja sosaima, ai ko ta dace gaskiya, gara data rage ma kanta wahalar zaman jiran Abeed yafi mata, ita dai ƴar wahalar Surayya sai taita kaya ita ta sani, ta tsaya taita korar samarin nata akan wadda baima san tana yi ba. Ita kuma wannan ta daɗe batai magana ba wallahi ciki ne dai sai an haife shi a gidan nasu, kuma rawar ƙafa saima kin haihu zata ga yadda ake rawar ƙafa indai Alhaji ne sai yayi wacce zata kusa sa zuciyarta bugawa"

"Ai ni lamarinta ma mamaki yake bani, ranar fa da manema auren Ihsan suka zo karkiso jin yadda ta rinƙa nuna jin daɗi harda su maida ma Haj Binta magana wai gara dai a daina jiran gawar shano"

"Hhhhh kan uba tana nufin su daina jiran Abeed kenan fa, wannan mata halinta sai ita, to miye ita Haj Bintar ta ce mata?"

"Mifa zata ce mata ai shiru ma magana ce Maryam, ai Haj Binta da kike ji da gani ta fita iya duniyanci, wallahi murmushi kawai tayi mata magana ɗaya ta faɗa data sa bakinta mutuwa, haka ta ce mata, ai

39 / 47