Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
su Hajiyar suka fara cewa Allah dai yasa masu lafiya ne kar azo duk uwar dukiyar da Jafar ɗin ke taƙama da ita yaran suzo su lamusheta da wannan ciwon na Sikila da ake gudar masu.
Ai ko Shamsiyya jin wannan maganar da zugar ƙawayen nata yasa ta fara yadama Mimi magana har magana takai kunnan Hajja ai ko ranar sunga ɓacin rai dan duk saida ta watse masu karama, dan saida Shamsiyya tayi danasanin faɗar maganar, ranar harda kuka dan furucin da Hajja tayi akanta cewar wallahi sai tasaka Jafar ya sake ta akan yaran nan, da suka ci sunan Mahaifin Jafar ɗaya aka saka masa sunan mahaifin Hajja ɗin macen kuma aka saka mata sunan Hajja, ai shine ya sake sakama Hajja son yaran a cikin ranta kamar zata maida su ciki haka take jin yaran, ai ko shi yasa ta murje ido tayima Shamsiyya da uwarta tass harda kukansu suna bata hakuri..........
PAGE 76
*HANNAH POV*
Washe garin ranar taje gidan Maryam ta wuni washe gari kuma su duka suka tattara suka wuce gida dan a ranar ne za'ai yinin biki na Aunty Sa'a a ranar kuma za'a miƙata Kano.
Aunty Haja bazata iya zuwa Kanon ba saboda cikinta daya yayi nauyi ya tsufa.
Dama su Aunty Bintu sun iso tun jiya dan haka suna zuwa aka ci gaba da hidimar yinin biki, sai wajan yamma lis aka aiko da Motoci har guda biyar.
Su Hadiza ma harda su zasu je Kano dan dama ita akwai son yawo.
Maryam kam Fu'at ya hanata zuwa wata Kano ya ce shida kansa zai kaita daga baya, harda kukanta.
Fannah Shamsu ya hore mata kunne ya hanata zuwa Kano itama amma taso taje ita ƴar daɗi soyayya ta ce wai kanta ke ciwo. Hannah ma Aunty Haja ta hana aje da ita saboda tare zasu koma gida za'a fara mata gyaran jiki ita da Aysha amma ita Aysha harda ita aka tafi Kano da ita dasu Aunty Bintu sai sauran mutane na can babban gida.
Ammi taita faɗan bai kamata ace Aysha ce kawai zata je ba, amma ganin kowanne da nasa uzurin daya hanasa zuwa Aunty Sa'a ta ce ai zasu zo duk daga baya, dama kai amarya ya gaji hakan ai bare ita daba yarinya ba karsu damu.
Sai dare Aunty Haja suka koma gida washe gari tunda safe kuma ta farama Hannah gyaran jiki.
Inda su Aysha suka ɗakko video na gidan Aunty Sa'a suka turoma su Hannah sai santin gidan suke duk da dama dai sun gansa amma yanzu ɗaukar tafi kyau.
Ayshar ma na dawowa ta taho gidan Aunty Haja ita da Fannah dandanan ta fara masu gyaran jikin ita da Aysha hardama Fannah dan dagewa tayi itama sai an mata gyaran jikin, haka ta haɗasu su uku tana masu, su Hannah nama Fannah tsiyar ita ba aure ba sai ta ce dole sai an mata, ai Aunty Haja ɗince ma ta biye mata, ita dai bata ce masu komai ba sai ta bisu da gwalon jan faɗa.
Saboda bikin nasu nata matsowa dan yanzu baifi sati haɗu ba wata ɗaya kenan.
Gaga-gaga aka shafe sati biyu tana masu gyaran jiki ciki da waje sosai suka canza sukai haske ga wani irin shayinin da fatar jikinsu keyi kota ina suka gifta baza ƙamshi suke, dasun zauna waje sai sun barsa da ƙamshinsu.
Kota ina shirye-shiryen bikin Hannah dana Aysha ake dansu Aunty Bintu ana saura sati ɗaya suka iso, dan a ranar da suka zo ɗin aka kawo lefen Aysha akwati har goma dai-dai masu azabar kyau da tsada, kaya kam sunyi kota ina zuwa ake ganin lefe duk wadda yazo saiya tafi da san barka, dan lefen yayi kyau su Naseer sunyi ƙoƙari.
Na Hannah ma da kwana ɗaya aka kawosa ita nata akwati takwas ne sosai kuma sukai bala'in kyau kayan ciki masu tsadar gaske ne.
Ranar da aka kawo lefen a ranar akaje jeran kayan ɗakin Aysha gidanta yayi masifar kyau dan wa'inda suka je jere suka dawo sai san barka suke baki yaƙi rufewa dan wasu harda video suka yi na gidan dan gidan nata harda bene hawa kusan uku.
Na Hannah ne dai da aka kira Annur ya ce wai sai bayan ana ɗaura dai za'a sanar da inda za'aje ayi jere iyayen nasa ne keta rigimar sai dai ya zauna da ita a Kano shi kuma yana aikinsa ne a Abuja dan haka rigima sosai ake kamar za'a fasa bikin.
A jita-jitar da ma wasu mutane suka fara ji cewar wai iyayen nasa ne suka gano cewar su Hannah basa da tarbiyya ai ƴaƴan mace ne da can sunyi yawon ta zubar kaza da kaza ƙananun maganganu nata fitowa, saboda gaba ḍaya Katsina suka dawo saboda hidimar bikin kuma basu da nisa da unguwar su Hannah ɗin shi yasa ƙananun maganganu keta fitowa.
Sosai kuma hankalin Hannah yayi mugun tashi dan kiran Annur ɗin tayi tana kuka kamar mi shima tabi ta tayar masa da hankali inda ya rinƙa rarrashinta cewar bafa abunda zai faru insha Allah.
A ranar suka je awon jini na genotype, harda Aysha da Naseer. Fannah ta ce zata bisu itama ayi mata awon jinin idan bikinta ya taso bata da fargabar komai.
Aysha da Naseer tun a nan asibitin aka shaida masu babu wata matsala su duka A'A ne.
Suna murna suka dawo, su kam su Hannah ma tsabar tashin hankali da kukan da take masa basu tsaya jin sakamakon awon jinin nasu ba takardar kawai suka amsu suka taho, kuma dama ba waje ɗaya akai masu dasu Aysha ba, suda Fannah waje ɗaya akai masu dan haka
Annur ɗin ne ya riƙe duka takardun saboda dama dole saida sakamakon awon jinin za'aje ɗaurin aure wadda za'ai jibi juma'a.
Maryam na gidan tun ana saura kwanaki uku ta iso, Aunty Sa'a ma ta iso yau dan ya barta dama ta ce masa akwai ƙannanta da za'a aurar dan haka gara data gaya masa da wuri sai ta kama ma ranar ba'a wajanta yake ba dan yanzu haka yana Ibadan can wajan abokiyar zamanta da sau ɗaya suka taɓa ganin juna shima kuma ranar auran ne bayan an kaita.
Kowa rarrashin Hannah yake ganinta cikin damuwa dan Maryam cewa take wai mi yasa baza'a fasa auren nata bane?. Tunda har danginsa basa son auren ɗansu da ita.
Ganin tashin hankalin da maganar ke sata yasa kowa ya rufe bakinsa aka daina maganar, dan Maryam da Aunty Haja sosai suka ji tsanar haɗa zuru'a dasu suma dan dai ba yadda zasuyi ne.
Ana saura kwanaki biyun a ɗaura aure aka aiko aje jere amma jere a Abuja za'ayi sa. Motoci maza aka aika kawai sai Aunty Badiya da Aunty Sa'a ne kawai suka je Abujar.
Gida kam yayi kyau itama dan unguwar masu hannu da shuni ce a Abujar zasu zauna, sosai gidan yayi kyau, washe gari tunda safe su Aunty Sa'a suka dawo daga jeren.
Suna bada labarin unguwar musu kuɗin da za'a kai Hannah ɗin gidanta kam da Aunty Sa'a ta shiga nuna masu videon gidan sai kowa yayita mamakin kalar gidan dan ginin gidan irin na ƙasashen waje ne, kwata-kwata ginin ba irin namu bane na nan dan sosai gidan ya birge kowa sai maganar ginin gidan ake.
Sai lokacin ne Hannah ta samu ɗan sassaucin abunda take ji a ranta, dan dama rashin jeran ne da ba'ai mata ba da kuma yadda maganganu keta fitowa take ganin kamar ma auren fasawa za'ai.
Sai ranar da suka dawo ne ta bari suka tafi ƙunshi da Saloon amma da taƙi, ita Aysha tuni dama anyo mata ƙunshinta Saloon ne suka tafi tare, sune basu dawo sai dare saboda ƙunshin da aka tsaya yima amarya Hannah.
Fannah kam dama tuni tayo nata ƙunshin ranar da Aysha taje a tare suka je, ta dage sai an mata irin na Aysha har Ayshar na ce mata bata isa ba wallahi, ai ko ta dage wallahi sai an mata, dama haka tayi masu a wajan gyaran jiki harda ita Aunty Haja ta haɗa ta rinƙa yimawa.
Da haka dai da rigima-rigima suka dawo gidan saboda Aysha keta mitar ta raina su ne ma taga wajan kwananta shi yasa amma baccin raini taya za'ai kawai ta wani ce ayi mata irin ƙunshin amarya tsabar ta raina ta?.
Ita dai Fannah tana ƙunshe dariyarta suka dawo gidan dan saida akai mata ƙunshi irin na Aysha.
A daren suka shirya Kamu dan ba'a tashi zuwa wajan Kamun bama sai wajan tara na dare, dan basu dawo daga ƙunshin da wuri ba, danma su Naseer ne suka shirya komai dama.
Anyi Kamu kamar yadda aka saba ango Annur bai samu damar zuwa ba amma Naseer shi dashi akai komai.
Wajan ƙarfe goma sha ɗaya aka tashi kowa ya dawo gida.
Washe gari tunda gari ya waye na safiyar juma'a wacce ta kama safiyar ɗaurin aure, Hannah ta tashi ta wata irin faɗuwar gaban da duk sauran kwankin bata ji hakan ba sai yau data farka, ga wani irin ciwon ciki daya tasar mata. Zawo sosai ta tashi dashi, kusan shigarta toilet ya kai nawa har saida aka bata magani tasha da kyar gudawar ta tsaya mata, amma daka kalleta harta rame lokaci ɗaya tayi wani irin zuru-zuru da ita, dan harda ƙarin ruwa aka zo aka sa mata leda ɗaya.
Kowa ta basa tausayi Ammi dai tausayin ƴarta duk ya hanata wasu abubuwan da walwala haka nan dai ta ɗaure suka ci gaba da tarbar baƙin da suka fara cika gidan, ga hayaniya tayi yawa a gidan, danma ɗakinsu Hannah ɗin ba yawan hayaniyar a nan take kwance.
Da kyar Aunty Haja ta lallaɓata tayo wanka bayan an cire ƙarin ruwan tasa wani leshe marar nauyi, ta koma ta ƙara kwanciya dan ita kwata-kawata jikinta ne ke ƙara yin sanyi ƙlau.
Lokaci na tafiya zuciyar Hannah na sake bugawa jikinta na ƙara sanyi dan har wani zazzaɓi ya rufeta.
Tunda taji an fara huɗubar jama'a Aunty Haja dake kusa da ita tana waya da Alhaji dake gaya mata sun iso suma suna wajan ɗaurin auren harda ma Abeed suka zo, ya jawosa dole suka taho tare saboda Alhajin ne zai jagoranci ɗaurin auren nasu gaba ɗaya.
Tana murmushi sukai sallama dashi tana sauke wayar sai taga Hannah na rawar sanyi hankali a ɗan tashe Aunty Haja ta ƙara matsowa inda take kwancen tana cewa.
"Subhallahi Hannah ko zazzaɓi ne?"
Ta tabbayeta tana saka hannunta akan wuyanta, ai ko da sauri ta ɗauke hannunta jin jikin Hannah zafi rau kamar an saka mata garwashin wuta.
Da sauri Aunty Haja taja mata abun rufa ta rufe ta zata miƙe da sauri Hannah ta riƙe mata hannu tana ce mata.
"Aunty Haja karki gaya ma kowa, kinga hankalinsu yanzu ma ba'a kwance yake ba, kuma nasan duk saboda ni ne"
"Amma taya kina cikin wannan halin zaki ce kar a gaya ma kowa?, ki bari naje na samo miki magani ko a kira Doctor ya duba ki"
"A'a karki fita dan Allah, akwai maganin zazzaɓi a cikin durowar can ki bani shi nasha insha Allah zazzaɓin zai sauka"
Badan Aunty Haja taso ba ta ɗakko mata maganin ta ɓallesa ta miƙa mata sai ruwa data je parlo da kyar ta raɓa jama'ar da suka cika parlon ta ɗakko mata ta ɓalle murfin ruwan ta taimaka mata da kyar ta miƙe zaune tasha maganin, ta lallaɓa ta koma ta kwanta dan harda wani azababben ciwon kai taji ya saukar mata, dan tana miƙewa zaune taji ya sara mata kamar zai rabe biyu, bata rabi dai Aunty Haja ta ƙara gane wani abun ba ta koma a hankali ta kwanta Aunty Hajar na sake rufe ta da abun rufa.
A ɗakin ta zauna tana fuskantar Hannah dake kwance sai tausayinta ya kamata.
Allah yasa ba wadda ya sake shigowa ɗakin dansu Aysha na can ɗakinta ita da Maryam daya kasance yanzu ita ɗaya ke kwana tunda Maryam tayi aure.
Suna zaune har wajan ƙarfe ɗaya da rabi ana gaf ɗaurin aure, dan ƙarfe biyu suke tayar da sallar masallacin.
Fannah ce ta shigo ɗakin tana dariya da alama a waje aka bata dariyar amma shigowarta ganin Hannah a kwance ta ƙudundune da abun rufa yasa ta shanye dariyar tata tana matsowa da sauri ta ce.
"Aunty Haja wai har yanzu gudawar bata tsaya ba?, gashi har an kusa ɗaura auren"
"Ta tsaya ita, kawai dai ta ce min tana jin sanyi ne na lulluɓeta, amma dai da sauƙi ma dan naga kamar ta fara samun bacci ma"
Duk sai itama taji jikinta yayi sanyi ta samu waje ta zauna suna iya juyo huɗubar masallaci da aka gama yanzu ana kabbara sallar juma'ar.
Dan gaba ɗaya ba abunda basa ji wadda ake a masallacin dan yana kusan manne da gidansu ne, shi yasa ma Fannah ke cewa ƙofar gidan nasu yanzu bata shiguwa saboda jama'a da Motoci dake damƙe cike da wajan.
Duk firar da suke kusan tana iya juyo komai dan ba wani bacci da take yi baccin ma kwata-kwata bata jinsa, zuciyarta ce keta faman duka a ƙirjinta ta rasa mi yasa hakan, kodan yau ne za'a ɗaura mata aure oho?.
Ana idar da sallar juma'a dubbanin jama'a suka fara shaida ɗaurin auren Aysha da angonta Naseer Belloh Rabe, akan sadaki naira na gogar naira dubu ɗari uku.
Daga baya mai shela ya sake faɗar an ɗaura auren Hannatu da angonta Abeed Kangiwaaa akan sadaki naira million ɗaya, sai mai shela ya sake faɗar an sake ɗaura auren Annur da amaryarsa Fannah akan sadaki naira dubu ɗari uku lakadan ba ajalan ba.
Tofa gaba ɗaya gida ya hargitse jin wannan ɗaurin aure da akai, dan mai shela har gidan kana iya juyo karajinsa.
Mamaki da al'ajabi ya hana wasu motsawa.
A wajan Aunty Haja ma so take ta gasgata shin dai-dai ne taji ko kuwa dai kawai mai shelar ɗaurin auren ne baiji da kyau ba ya faɗa ne kawai.
A mugun gigice Hannah da Fannah suka miƙe dan ita kanta Aunty Haja da kyar ta miƙe ga cikinta daya tsufa.
Jikinsu kusan rawa yake bare Hannah da hawaye dama suka riga suka wanke mata fuska.
Ammi ce dasu Aunty Bintu suka shigo ɗakin harma da Maryam kai kusan gaba ɗayansu kowanne an rasa wadda zai fara magana.
Baki na rawa Hannah ta shiga cewa.
"Aunty Haja dan Allah ki ce ba haka bane abunda kunne na ya jiye min?"
Ta ƙare maganar tana hawaye kamar mi.
Jikin Aunty Haja na rawa ta ɗakko wayarta tana jin lokacin dasu Aunty Bintu ke cewa ya akai hakan zata faru?.
Ammi na basu amsa da suma amsar da suke so suji kenan, kuma dole sai mazan sun dawo daga wajan ɗaurin auren zasu ji koma miye abunda ya farun?.
Kiran Alhaji Aunty Haja tayi da kyar ya iya ɗauka saboda jama'a da hayaniya datai yawa, abu ɗaya ta tabbayesa cewar da gaske ne Abeed aka ɗaura ma aure da Hannah?, ya kuma tabbatar mata da cewar hakane, amma su bari zasu shigo gaba ɗaya koma miye zasu ji ne ai dole.
Ai Aunty Haja na sauke wayar Hannah ta fara girgiza kai dan taji abunda Alhaji ke faɗa kawai sai dai suka ji ƙarar faɗuwarta ƙasa ta zube a sume. A mugun gigice sukai kanta suna kwala kiran sunanta da ƙarfin gaske..............
PAGE 77
Kusan gaba ɗayansu ne zaune a babban parlon baƙi.
A hankali Alhaji yayi gyaran murya yana kallon kowa dake zaune.
Su Kawu Sani ne dasu Ammi harma da Fannah harda su Annur kusan gaba ɗaya Aysha ce da Hannah kaɗai ne babu a parlon, saboda an saka mata ƙarin ruwa anyi mata allurar bacci.
Hatta Abeed yana zaune wajan yadda kasan bashi a wajan, kai yadda kasan bashi ne aka ɗaura ma aure yanzu ba.
Su Ammi ba abunda suke sai binsa da kallo dan kam kamar yadda ake basu labarinsa yama wuce duk yadda suke tunani. Tunda suka shigo aka taru ya gaida kowannensu cike da ladabi da biyayya bai sake magana ba saima waya daya ɗakko yana yin wani abu da ita, saida Alhaji yayi gyaran murya ne ya dakata da abunda yake yi, ko a kwalar rigarsa yadda kasan ba abunda ke damunsa.
Dan har cikin ransa shi wannan auren da Yayansa ya amsar masa ya kuma roƙesa daya amince karya basa kunya saboda biyayyar da yake ma Yayan nasa yasa shi amincewa ba tare da jayayya ba, baya jin auren a kansa dan ko amaryar ma bai taɓa gani ba, hasali sunanta kawai ya riƙe shima dan yana yawan jinsa wajan Aunty Haja.
Allah yayi ne ma zaiga ɗaurin auren amma da yau ne tafiyarsa Malesia sai aka ɗaga tafiyar sai zuwa gobe, abunda yasa harya halacci ɗaurin auren kenan, ashe da rabon harda shi za'a ɗaura harma mamaki yake wai shine da aure a karo na biyu.
Alhaji ya ce.
"Nasan ku duka zakuyi mamakin wannan haɗin auren daya kasance haka ko?". To kai Annur ka fara bayanin abunda ya faru"
Alhaji ya faɗa yana nuna Annur da kansa ke ƙasa.
Ya ɗago yana cewa.
"Munje asibiti awon jini, to mu duka daga ne har Hannah bamu tsaya an gaya mana sakamakon namu ba, dama mu biyar muka je awon harda Fannah lokacin data matsa itama sai taje an mata nata ta gani tun yanzu idan auren nata yazo bata da damuwa.
Su Aysha ne kawai dama aka gaya masu nasu sakamakon da yake ba waje ɗaya akai mana awon ba, mu namu mu uku ni ne na amso mana takardar awon namu domin waje ɗaya akai mana shi. To sai da aka zo wajan ɗaura aure ne takardar awon namu nida Hannah ta nuna mu duka AS da AS ne, akwai matsala kenan, a nan aka fara cece kucan akwai matsala kuma wakilai bazasu ɗaura aure takardar awon ta nuna akwai matsala ba, kamar dai yadda kuka sani yanzu wannan zamanin ba'a yin aure sai anyi wannan awon jinin, saboda gujema haifar yara masu sikila. A lokacin hankalina yayi mugun tashi dan kusan ruɗewa nayi saida Kawu Sani