Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   45 / 47

132K to 135K   out of 140.3K words

ya shiga rarrashina yana bani baki, ga masu jiran ɗaurin aure har magana ta fara fita, dan haka Alhaji ya ce"

Sai yayi shiru yana kallon Alhaji daya gyara zama ya ce.

"Shine ni kuma kai tsaye na yanke hukuncin cewa mai zai hana a dawo da auren Hannah akan Abeed saboda mu gaba ɗaya familynmu babu mai AS a cikinmu mu duka mun kasance nau'in jininmu A'A ne, dan haka nan take nayi shawara da ƙanina kuma cikin yardar Ubangiji ya amince, saboda shi kansa yaga idan ba'a ɗaura auren ba mutanen da suka taru da yawa a masallacin za'aje a fara yaɗa wasu maganganu marassa tushe, sai kaga anje an yaɗa abunda bashi kenan ba.

Daga nan shi Annur ya roƙi wata alfarmar a basa auren Fannah saboda ita jininta ya kasance A'A ce ita, saboda takardar sakamakon nata na hannunsa a nan ya gabatar masu da takardar, su kawu Sani basu ja ba su dai kawai a samu asiri ya rufu a ɗaura ba tare da an gane wata matsala ce tasa aka fasa ba, duk dai matsalar ba abar ashsha bace, to amma an riga da an tara jama'a wani ma yana sane zaije ya rinƙa yaɗa labarin daba shi kenan ba, dan haka ni kaina na yarda da hukuncin da suka riga suka yanke, nan take kuma aka shiga ɗaura aure, mu duka mun yanke wannan hukuncin ne saboda mun hango alkhairin abun, sana kar wani yayi zargin wani abu, dama can Allah baiyi Hannah matar Annur bace, dama can Ubangiji ya riga da ya hukunta cewar matar Abeed ce komi za'ai kuma bazata taɓa auren wani idan ba shi ba, dan haka idan akwai mai magana a cikin ku matan muna jiran jin abunda zaku ce"

Kowa yayi shiru sai Fannah dake kuka, shashshakar kukan kawai ake ji a parlon, dan ita harga Allah bata jin son Annur itafa Shamsu tayi burin aura amma gashi komai yazo ya sauya mata cikin ƙanƙanan lokacin da bata taɓa kawowa ma zatai aure a yanzu ba.

Aunty Badiya ce ta kamata ta fitar da ita daga parlon.

Ammi tayi jam tana cewa.

"Ai Alhaji duk abunda ka yanke akan yaran nan ya yanku, tunda har ƙananan Mahaifinsu sun amince suma ai shikenan, sai kawai ayi masu fatan alkhairi kawai"

Jinjina kai Alhaji Ma'aruf yayi yana jin daɗi har cikin ransa, duk dai dama yasan babu ahalin da bazasu so Abeed ya zama sirikinsu ba, kawai dai ya faɗi hakan ne dan su ma aji ta bakinsu.

Da haka taron ya tashi amma Alhaji ya nemi da suje suga jikin Hannah ɗin, har ɗakin da take kwance Aunty Haja tayi masu jagora suka je suka duba jikinta da sosai ya rikice dan zazzaɓi ne jikin nata ringis dan har an cire mata ruwan da aka saka mata, tana kwance wani wahalallan bacci ya ɗauketa. Kallo ɗaya Abeed yayi ma Hannah yayi saurin kauda kansa daga gareta, dan lokaci ɗaya yaji wani irin yarrrr har cikin jininsa, daya rasa mi yasa shi jin hakan daga kallonta, basarwa yayi kamar baiji komai ba, dan sai ka rantse ma ko kallon nata baiyi ba.

Hatta Aunty Haja ta ɗauka ma ko kallon mata baiyi ba, har jikinta ya fara sanyi ta shiga tausayama ƙanwar tata tasan tabbas zata sha wahala wajan shawo kan Abeed suyi zaman aure kamar kowanne ma'aurata.

Bayan sun tafi ta shiga sauke lumfashi tana bin Hannah da kallon tausayi tsantsarsa.

Gidan hayaniya mutane sun ɗan ragu yanzu saboda yanayin yadda abun ya kasance sai ƴan uwane kawai a gidan wadda suka zama dole su zauna.

Aysha ce aka fara zuwa ɗauka dan haka ba wasu jama'a ne suka kaita ba, saboda duk bikin saiya rage armashi.

Su Aunty Bintu ne da wasu sauran jama'a dasu Aunty Sa'a suka je kaita gidanta dake nan cikin garin Katsinar.

Sai kuma washe garin da aka ɗaura aure masu kai Fannah suma suka zo, Fannah na wani irin kuka kamar zata mutu ita da Hannah data farka cikin dare dan tunda ta farka take hawaye, ta rasa mike mata daɗi, dan kuka suka rungume juna ita da Fannah suna yi, bare cikin daren Shamsu ya kirata yana mata fatan alkhairi bayan ya kashe wayar taita kallon cikin wayar tana rusa kuka, har saida Aunty Badiya ta tasasu a gaba ta rinƙa masu faɗa tukunna suka ɗan sassauta da kukan.

Lokacin da za'a ɗauki Fannah a wuce da ita Abuja kukan da suka rinƙa yi ne yasa Aunty Bintu ta rufe su da faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba, dan rarrashin duniya an masu an basu baki amma kamar ma ƙara turasu ake, dan haka ta zage masu tass, tana cewa ai bawa baya wuce ƙaddararsa, kuma gata akai masu dama can haka Ubangiji ya tsara masu kuma dama baka taɓa auren mijin daba naka ba, dan haka su shiga hankalinsu wallahi.

Da haka aka ɗauki Fannah da kyar aka ɓanɓareta daga jikin Hannah shikenan ƙaddar ta raba su, ƙaddara ta zaɓa masu mazajen da basu taɓa tsammani ko tunanin aura ba.

Ita kanta Hannah a ranar aka zo aka ɗauketa wai za'aje ayi mata biza ta tafiya Malesia dan dama jirgin nasu wajan ƙarfe tara na dare zai tashi, dan haka kuma Abeed a ranar zai tafi, kuma Alhaji ya saki kuɗi da yawa dan a samu bizar Hannah ta kammala a ranar, Hajiya ta bada umarnin itama ya tafi da matarsa.

Su Haj Saratu a ranar data ji auren nan hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, Surayya kam sumewa tayi, Haj Saratu na kuka taje ta samu Alhaji tana gaggaya masa maganganun ya ceceta, mi yasa yasan Surayya ita ce ke son Abeed dama can sai kawai yaje ya nemarwa wata aurensa?, dama tasan wallahi Aunty Haja asiri ta masa ba haka kawai ta barsa ba.

Maganganu data rinƙa faɗa masa saura kaɗan ya furta mata saki a ranar Hajiya ta tsawartar masa, Hajiya ce ta ceceta, amma irin wulaƙancin da Haj Saratu ta rinƙayi a wannan rana ko kare baya ci ba, ita kanta tasan wata maganar bata dace na faɗarta kawai take bacin rai yasa tunaninta ya gushe.

Haj Binta kam fatan alkhairi tayi, dan itama ranar da aka ɗaura aurensu Hannah a ranar itama can Family house ɗinsu suke bikin Ihsan dan kusan rana ɗaya ne ta kama bikin, ita Ihsan a Kaduna aka aje ta, da sunyi wata ɗaya zasu tafi ƙasar waje inda yake harkokin ball ɗinsa.

Baƙin ciki da damuwa ya taru yayima Hannah yawa lokacin da suka dawo daga yi mata duk abunda ya kamata na tafiyar tasu saita dawo da zazzaɓi mai zafi harda amai ta rinƙa yi amma bata bari mutane sun gane yanayin da take ciki ba, Aunty Haja ce kawai tasan bata da ishashshiyar lafiya a hakanma ɗaurewa kawai take yi.

Aunty Haja taso a ɗaga tafiyar da Hannah, Abeed ɗin yayi gaba daga baya idan yaso ta samu lafiya saita ɓiyo shi, amma Alhaji ya nuna mata mahimmancin binsa a hakan shi yasan waye Abeed wannan rashin lafiyar da take yi yasan tabbas Abeed da tausayi zai bata kulawa wata ƙilama daga haka sai taga komai ya dai-daita sun dai-daita kansu.

Ta fahimce shi sosai dan haka suka ci gaba da shirye-shiryen tafiyar Hannah.

Duk wani abun buƙata Aunty Haja ke haɗama Hannah shi a akwati, kusan akwati biyu tayi manya. Wajan ƙarfe takwas na dare suna filin jirgi.

Hatta Maryam da ita aka zo raka Hannah Aysha ce babu dan itama jiya ne aka kaita gidanta.

Su Aunty Badiya da Aunty Sa'a dama suna can Abuja sai yau zasu dawo dan haka daga Aunty Haja sai Aunty Bintu ne kawai suka zo rakota.

A can ɓangarensu Alhaji kuwa harda Hajiya tazo rakosu filin jirgi. Ta rungume Hannah tana saka mata albarka inda ta kamo hannun Abeed tasa a cikin na Hannah tana ce masa ya riƙe ɗiyar mutane da amana dan Allah, ta basa amanar Hannah idan yayi mata wani abu Ubangiji zai tabbayesa ranar gobe, idan har ya cuce ta to ya sani bata yafe masa ba duniya da lahira, sosai sai yaji jikinsa yayi sanyi da kyar ya ɗago suka haɗa ido da Hannah a karon farko, da sauri Hannah tayi saurin janye nata idon, shi kam sosai ya kare ma kyakykyawar fuskarta kallo, ta faɗa sosai fuskar tata tayi jawur saboda kukan da take yawan yi a kwanakin.

Hatta hannunta daya riƙe zafi rau yaji, zafin har yana jinsa sosai cikin jikinsa, wani irin tausayinta yaji ya fara kamasa dan haka da sauri ya janye hannun nasa dake cikin nata, yana ɗauke idonsa daga kallonta da yake yi, yana basarwa kamar bashi yayi ba.

Lokacin da aka fara kiran sunayen fasunjojin jirgin da zai tashi ƙarfe tara dai-dai sai Hannah jikinta ya ƙarin yin sanyi hawaye ta fara tana rungume jikin Hajiya, daka ƙarshe ta rungume Aunty Haja tana sakin wani irin kuka, taje wajan Maryam ma ta rungumeta tana sakin kuka nanma, idonsu gaba ɗaya yayi jawur su duka dan Aunty Haja harda hawaye ta goge tana jin wani bala'in tausayin Hannah ɗin.

Gogan naku ma fa jikinsa sai ya sake yin sanyi ganin halinda take ciki kukan da take yi ne yaga ya fara yawa, dan haka kawai ya fara jin zafin kukan nata har cikin ransa.

Suna gani Hajiya ta sake kamo hannunta ta damƙama Abeed suka nufi jirgi saboda kiran sunansu da akai.

Hannah na tafiya tana waigensu hawaye na sake zubo mata.

Kujera kusan ɗaya suka zauna dan tana fuskantarsa shima haka.

Bayan an sanar da jirgi zai tashi shine da kansa ya ɗaura mata belt yana dai-daita zamansa shima ya ɗaura nasa yana ɗan kallonta ta ƙasan ido.

Saboda damuwar da Hannah take ciki ko tsoron tashin jirgin bata ji ba sosai sai dai kawai lokacin da zai tashi gaba ɗaya sama yaga ta runtse idonta tana ƙanƙame jikinta.

Yana gama dai-daita a sararin samaniya, Hannah ta shiga sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa.

Buɗe idonta tayi sai karaf ta kamasa yana kallonta,

duk ta kamasan hakan baisa ya ɗauke idonsa akanta ba, ganin har lokacin hawaye take, saita sami kanta da taɓe masa baki tana saurin kauda fuskarta daga garesa.

Miskilin murmushi ya saki na gefen baki yana ɗauke idonsa daga gare ta.

A hankali ya fiddo wani farin hankicif ya miƙa mata baice komai ba.

Kallon kyakykyawan hannunsa tayi wadda hutu da jin daɗi yasa shi yin wani irin luwai-luwai dashi kamar na wata mace.

Da kyar tasa hannunta ta amsa ta buɗe baki murya na ɗan rawa ta ce masa.

"Na gode"

Saiya jinjina mata kai kawai.

Zaman korame sukai har Ubangiji Allah yasa suka sauka a Malesia, a lokacin da suka sauka su lokacin tsakiyar rana ne kusan sha biyu na rana ma.

Sai Hannah ta cika da mamaki wato dai Allah ɗaya gari ban-ban.

Gari ne mai kyan gaske wadda take gani da a TV wai sai gashi yanzu ita ce a cikinsa.

Wasu motoci ne suka zo ɗaukarsu, ita dai duk inda yayi da ita tana biye dashi, hannunsu cikin na juna.

Jikinta yana jin yadda yake ƙara ɗaukar ɗumi ita kanta tasan bata da lafiya dan kyar take iya taka ƙafarta danji take kamar zata faɗi, ga gajiyar tafiya da zama waje ɗaya daya ƙara sama jikin nata ɗaukar zafi.

Bayan sun shiga Mota tafiya ce sukai kusan ta rabin awa kamin suzo wata unguwa mai dogayen gine-gine.

Unguwar babu yawan hayaniyar jama'a kota ina fitilo ne ke haskawa.

Wani dogon gini taka motar tasu ta tsaya, driven ne ya fita da sauri ya buɗe nasu ƙofar Motar a hankali Abeed ya fito yana kamo hannunta.

Ginin taka sun nufa driven yana ɗakko masu kaya.

Ginin taga bene-bene ne hawa-hawa har baka iya ganin ƙarshen ginin.

Wani abu taga sun hau yayi sama dasu ya kaisu can sama suka fita sai taga sun ɓilla wane waje daban.

Sai taga yawan ƙofofi a inda suka ɓilli ɗin kowacce ƙofa an kafe number ta ɗakin a jikin wani allo.

Wata ƙofa taga sun nufa mai number 35.

Taga ya latsa wani waje sai ƙofar ta buɗe.

Baki buɗe Hannah ke kallon wani tsararren parlo daya bayyana a gabansu.

A hankali suka shiga ciki gida ne sosai parlo ne babba irin na kasashen turai ba irin parlonmu ba na nan na ƙasar hausa ba, irin ginin turawa ne zam.

Dan har kitchen Hannah ta hango a parlon zaka iya hango komai a cikinsa.

Kusan kujeru kala uku ne a parlon zata iya kira da kusan parlo uku kenan akai a parlo ɗaya.

Driven daya ɗakko sune ya shigo masu da akwatunansu, yayi masu sallama ya fice.

Tana jin ya sakar mata hannu ya nufi wani bedroom dake can ciki yana ja masu akwatunan nasu ya shigar dasu ciki.

Ita kam saita tsaya a parlon tana ƙare masa kallo kawai.

Ƙirjinta ne ke mata zafi sosai tsayuwar ke neman kayar da ita dan haka da sauri ta dafe hannun kujera tana saka hannu ta dafe kanta da take jin yana sara mata.

Jin kanta tayi a cikin jikin mutum ya riƙota. Mayan ƙamshinsa ne yayi mata sallama dan haka da sauri ta wastsake tana son barin jikinsa.

A dai-dai kunnanta taji ya raɗa mata cewa.

"Shittt ki natsu"

Abunda ya faɗa kenan taji kawai anyi sama da ita, ya ɗauketa kamar baby yayi hanyar bedroom da ita.

Tana jin yadda zuciyarta ke rawa, ƙirjinta na duka tayi luf a ƙirjinsa tana jin ƙamshin turarensa da bata taɓa jin irinsa ba mai daɗin shaƙa gashi yana haifar mata da wani irin yanayi na daban.

Kwantar da ita yayi akan gado, sai taga ya fice daga ɗakin ya daɗe bai dawo ba, can taga ya shigo hannunsa riƙe da wasu magunguna sai wani ruwa a cikin wani abu fari ƙarami da wani tawul da alamar ruwan mai ɗumi ne.

Binsa da kallo kawai take bata taɓa ɗauka zai bata kulawa kamar haka ba, duk da dai ba magana a tsakaninsu, sai aikace yake mata hidima kawai badai uhm ba uhum-uhum.

Da kansa ya miƙar da ita zaune ya shiga bata magani saita sami kanta da taɓe masa baki bata son shan.

Ta ido ta fahimci yana mata magana, taga ya lumshe mata su a hankali alamar please tasha.

Ai Hannah bata san lokacin data amsa ba tana sakawa a baki, dan salon nasa ya kusasa ta ruɗewa, kyakykyawar fuskar nan tasa na fisgarta ga kyawun idonsa da suka kasance sexy eyes ke son ruɗa Hannah bata sani ba, dan bata ma san lokacin data shanye maganin ba, tana mamakin kanta.

A kanta yasa mata tawul ɗin daya jiƙa da ruwan zafi ya matse ya saka mata.

Yana gamawa ya miƙe, tana rufe idonta kamar wacce bacci ya ɗauka.

Shi kam toilet ya shiga yayo wanka dan shima ya gaji sosai.

Bayan ya fito ya shirya cikin wasu kayan bacci ya feshe jikinsa da turarukansa masu masifaffen ƙamshi, dan Hannah har wani ƙara buɗe hanci take dan turaren nasa nada daɗin ƙamshi sosai gashi da wani irin mayen ƙarfi baida hawa kai amma akwai kama jiki.

Tana jin lokacin da zai fita ya matso kusa-kusa sosai saitin kunnanta ya raɗa mata cewar zata iya tashi ta lallaɓa tayi wanka, shi zaije ya dawo.

Yana ƙare maganar ya fice ya barta da mamakinsa.

Wato shi dai hayaniyace baya so, magana ma sai ya matso ya mata raɗa tsabar baya son magana sosai koya tada muryarsa?.

A hankali ta miƙe tana mamakinsa ta shiga toilet.

Saida ta shiga ta kuma dawo tana buɗe akwatinta ta ɗakko wasu kayan bacci ta aje saman gado tana komawa toilet ɗin ta ɗakko tawul ta cire kayan jikinta ta ɗaura tawul ɗin daya tsaya mata iya cinyarta, santala-santalan cinyoyinta rabi duk a waje, gata Allah ya hore mata tudun ɗuwawo da kyar tawul ɗin ya iya ritsata ma, ga dukiyar fulaninta da suka taso kamar zasu fasa tawul ɗin, dan idan ka kalleta a hakan ma har saida suka billitso daga saman ƙirjin nata data ɗauresa da tawul ɗin.

Takawa take a hankali komai na jikin nata yana rawa.

Ta daɗe a toilet ɗin kamin ta fito bayan ta gama wankan.

Tana tafiya tana goge jikinta da wani ƙaramin tawul.

Dai-dai lokacin shima Abeed ya buɗe ƙofar ya shigo.

Kusan suman tsaye yayi ganinta a haka.

Dan ita bata san da shigowarsa ba, hankalinta nacan wajan goge jikinta da take yi.

Tana yi tana takawa a hankali tana nufo tsakiyar ɗakin, taku ɗaya zatai sai albarkatun jikinta sun motsa, shi kam gaba ɗaya ta kusa kwance masa notikan kai, dan sosai ya shagala da kallonta, mamaki duk ya rufesa. Yanzu wannan ƴar yarinyar ce keda wa'innan kayan alatun a jikinta?, ai shi kallon ƴar haka yake mata, koda yake fuskarta ce kawai keda yanayin yarinta daka kalleta akan fuskar tata zaka san yarinya ce sosai, amma a jiki kam kota ina ta cika mace, macen da kowanne namiji zaiso ace shine keda mallakinsa.

Lokacin da Hannah zata ɗago kawai idonta ya faɗa cikin nasa, ai bata san lokacin data saki ihu ba, tana saurin ƙanƙame jikinta tana turo baki.

Sai taga shi ya saki wani ɗan iskan murmushi na gefen baki wadda yake ƙarama fuskarsa kyau da cikar zati. Ai bata san lokacin data murguɗa masa baki ba ta shiga masa ƙunƙuni........

PAGE 78

*HANNAH POV*

Zaune take akan kujera tayi shiru, tayi ɗan tagumi da hannunta.

Wata ajiyar zuciya ta sauke, tana tuna yau kusan satinsu biyu da zuwa ƙasar tunda suka zo bata fita ko nan da can ba, gogan nata kam idan ya tafi wajan aikinsa sai dare yake dawowa, ba abunda yake haɗasu sai gaisuwa sai idan zai sha shayi ta dafa ta bashi, dan ta lura yafi son shan shayi fiye da komai a rayuwarsa, bai wani cika son abinci ba sosai, ita dai ke dafa masa bata bari yana sayo na wajan nan, dan abincin ƙasar baya mata wani daɗi.

Gyara zamanta tayi tana kallon kayan jikinta daga ita

45 / 47