Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ukun ba ai keda shi har ba'ada, ai kinyi masa nisa kuma, sai dai abi wani sarkin"
Girgiza kanta Hannah tayi tana jin har cikin ranta bata ji daɗin wannan sakin da aka matsa sai anyisa ba. Saboda ita dai tasan a Islamiyarsu ansha masu wa'azin cewar babu kyau saki, Ubangiji baya sonshi.
Kamar zatai magana sai kuma tayi shiru kawai, dan tasan idan ta ce zata tanka tofa yanzu gaba ɗayansu zasu taso mata, ta sani, dan haka kawai a cikin ranta ta furta. (Ubangiji yasa ku gane gaskiya kamin komai ya ƙure maku).
Ta ƙare maganar zucin tana miƙewa dan zuwa cikin shagon da suke yin girke-girke, wadda ya koma kamar kitchen ko wani ƙaramin gidan cin abinci haka.
Binta sukai da kallo ganin kowa na tofa albarkacin bakinsa, wajan taya Aunty Haja murnar rabuwar auren daya so zame mata damuwa da matsala a cikin rayuwarta.
"Wannan yarinyar na rasa wane irin baƙin hali ne da ita wallahi. Ace da an fara maganar arziƙi yanzu sai kaga ta wani miƙe ita ga tsohuwar munafuka?"
"Hmm Ammi rabu da ita kawai, amma tabbas dole zan tafi da ita gidan Alhaji Ma'aruf Kangiwa, saboda ina so itama ta auri wani ƙaninsa na nan dake rayuwa a ƙasar waje, yanzu haka baya ƙasar, kusan shekarunsa biyar yanzu ba aure, tunda ya auri wata da sukai soyayya da ita kamar ransu, ya sota sosai amma sai kawai aka tashi akaga ta mutu, daga ita har jaririn da bata daɗe da haifa masa shi ba a lokacin. A iya bincike ance wai kamar guba ce aka samu masu suna shaƙar lumfashi da ita, hakan ne yayi sanadiyar mutuwarsu, kuma har yanzu ba'a gane wanene ko wacece ta aikata hakan ba. Tabbas nasan gidan Alhaji Ma'aruf Kangiwa cike yake da munafukai masu matuƙar hatsari"
"To ke yanzu kina ganin zan iya bada Hannah a irin wannan gidan da kashe rai basu ɗaukeshi komai ba?"
"Hmmm Ammi kenan, nima da nawa shirin ai zan tafi, bawai haka nan zan shiga gidan Alhaji Ma'aruf ɗin ba, ai idan haka ɗinne zan shiga ma shigar tawa bazata taɓa yiwuwa ba Ammi"
"Kin san abunda za'ai yanzu dai Haja, ina da wata ƙawata Sa'ade sunanmu ɗaya da ita Takwara nake ce mata ma, tana nan cikin gari unguwar ɗanɗagoro take, anjima idan Maryam ta dawo da Mota nida kaina zanja ki mu tafi har gidanta, tasan Malamai wadda idan sukai miki aiki to wallahi shi da kansa Alhaji Ma'aruf ɗin zaizo neman auren naki a gigice nake gaya miki"
"Abunda nake shirinyi kenan, tunda kuma na samu zamu je ɗin, da na samu wani Malami a wani ƙauyen Kano, zamu je gobe, to amma sai a raba biyu, ba'a san inda za'a dace ba ai"
"Ni abunda nake so na gaya maku shine Hajara bance karku nemi sa'a wajan Malamai ba, da taimakon Malamai, amma bance ku sake ku cutar da waninku ba, ko ta hanyar masa wani mugun abu ya fita daga hayyacinsa, kawai abunda nake so daku shine, kuyi iya abun naku iya kan shi Alhaji Ma'aruf ɗin"
Ammi ta faɗa tana binsu da kallo.
"Ai dama Ammi iya kan nashi yanzu zamu tsaya tukunna, kamin na shiga gidan nasa naga iya takun kowa dake cikin gidan, Ammi ki sani duk wadda bai shiga gona ta ba, to bazan shiga tashi ba abunda na sani kenan, amma duk wacce a cikin matanshi ta ce zata taɓa ni to tabbas sai tasan wacece Haja"
Murmushi Aysha ta saki tana cewa.
"Ke kina ganin Hannah ɗin zata yarda?"
"Dole ma ta yarda, ai bazan gaya mata gaskiyar abunda yasa zata koma gidan da zama gaba ɗaya ba, kuma bazan hanata sana'arta ba"
"To nifa wai Aunty Haja?, kuma fa itama Aunty Maryam tana son haɗata da wani na nan shima masu kuɗi ne fa, rannan shi yasa ma taja mu muka je har gidansu sai akai sa'a baya ma ƙasar, kuma itama daga gani wani ƙuduri take son cimmawa da haɗin auren Hannah ɗin dashi"
Su duka sai suka shiga binta da kallon mamaki.
Aysha ce ta kasa haƙuri ta ce.
"Ohh ikon Allah, to wai dole sai Hannah kaɗai za'a rinƙa sakawa a cikin wannan abun?"
"Kin san mi yasa aka ce sai ita ɗin?"
Cewar Aunty Haja na kallon Aysha dake riƙe da baki.
Girgiza kanta tayi tana sauraron abunda zata ce.
"Saboda ita ɗin bata san komai ba, duk yadda muka ɗorata a haka zata tafi, kuma duk yawanci saboda ta fimu kyau ne ta fimu kalar ƴan gayun, ita ce dai-dai sakawa abun shine kawai, ita ce ta dace, dacewa kawai ake hange ba wani abu ba"
Taɓe baki kusan Fannah da Aysha sukai.
Aunty Sa'a na kallonsu da ɗan murmushi ta ce.
"Kuma da kanku zaku samo naku mazajen auren, amma dai yanzu bari ita Maryam ɗin ta dawo, dole ta barma Haja Hannah, sai dai ko idan zata haɗa abun da Fannah ne ko Aysha"
Ammi ta kasa haƙuri ta ce.
"Nifa ko hankali fa bai kwanta da gidan da Hajara zatai aure ba a yanzu da take shirin kai kanta, kuma har tana shirin haɗa Hannah da jinin gidan again. Mtsw gaskiya zuciyata ta fara wasiwasin abun sosai"
"Haba Ammi?, wallahi na miki alƙawarin ba abunda zai faru da Hannah, ba muna tare ba. Idan kina ganin wani abu ma sai ta rinƙa zuwar miki weekend duk sati a nan kamin dai nasan yadda za'ai na haɗa su da Abeed Kangiwa ɗin"
"Ke wai Abeed Kangiwaaa?"
Aysha kusan da Fannah suka haɗa baki wajan faɗa a gigice.
Jinjina masu kawai tayi dan dama tasan bazasu rasa saninsa ba, ko a social media.
Hannun Fannah na rawa ta shiga Instagram tana shiga wani shafinsa tana shiga wani picture nashi da aka ɗaukesa kamar ba bai sani ba, yana zaune akan wata matsiyaciyar kujera a wani parlo mai azabar kyau da tsari, daga gani a ƙasar waje ne ba Nigeria ba. Yayi murmushin gefen baki irin na miskilan mutanen nan, sanye idonsa yake da wani baƙin gilashi, kayan jikinsa kuwa ƙananun kaya ne irin na turawa gasu kalar ja ne, yayi bala'in yin kyau, fatarsa mai kama da chocolate tayi wani irin haske da ɗaukar ido sai shayinin take, yadda kasan ba jikin namiji ba, ƙaramin bakinsa dake ɗauke da wani irin jan lefe ya taimaka wajan ƙawata kyakykyawar fuskarsa, hancinsa ko a nan madarar kyan take, saboda ya mugun dacewa dashi sosai, sosai yake da karan hanci wadda ya taho kamar zai taɓo masa baki, daga ƙasan hancin nasa ya ɗan baje kaɗan hakan kuma ba ƙaramin taimakawa yayi ba wajan ƙara fiddo da kyansa da kamalarsa yayi ba, a kallo kawai na photo zaka san kwarjini garesa ga wata haiba da Ubangiji ya zuba masa.
"Wai ba wannan ake magana a kansa ba dai ko Aunty Haja?"
Fannah ta ƙare maganar tana nuna masu picture nashi.
Aunty Aysha ce ta amshe da cewa.
"Yawwa dama nima shi zan kamu photon nashi, wadda dai na sani da ake kira da Abeed Kangiwa, anya kuwa shine?"
Murmushi kawai Aunty Haja ta saki tana dubansu gaba ɗaya ta ce.
"Kuda kunji na ce Kangiwa ai kunsan duk ƙasar nan bamai irin wannan inkiyar sai familynsu"
"Wai dai a taƙaice kina nufin dai shine kenan?"
Aysha ta faɗa da wani irin mamaki tana zaro ido waje haɗe da ɗaga hannayenta sama.
"Kware kuwa shine dai da kuka sani. Kuma wannan shafin nasa da alamar ba nashi bane, dan wasu mutane da yawa suna shiga social media suna posting pictures na ƴan gidansu ma gaba ɗaya, suna buɗe shafi da sunansu"
"Kai wannan da alamar nashi ne Aunty Haja, saboda suna saka wata alama"
Cewar Fannah ta ƙara duba cikin wayar tata sosai.
"Wata ƙila"
Ta faɗa kawai tana maida hankalinta ga Aysha da har lokacin ke cike da mamaki kamar zai karta.
"Wai miye Aysha naga kinyi shiru kamar ruwa ya cinye ki?"
"Hmmm bari Aunty Haja haddar kaina ce ke neman gogewa ai. Abeed dai?, kai jama'a, ai ko Ammi wallahi koma miye zai faru kawai ki bar Aunty Haja ta tafi da Hannah gidan nan, kota samu shiga itama, dan wallahi Abeed Kangiwa dai dana sani to ba ƙaramin mutum bane, kuma yadda ƴan mata ke haukan sonshi, ace ita tayi dacen aurensa, ai ba ƙaramar takar sa'a tayi ba kam"
Aysha ta ƙara maganar tana jinjina kai.
Ammi dai tayi shiru dan itama taga picture ɗin shi Abeed ɗin da aketa magana akansa.
"Ai wallahi ko nima Aunty Haja ko ƙila gidan naki zan tare ko Allah zaisa na ci karo da ko ƙanin matar gidan ne na aure shege, yo ni ina ruwana, sai dai ayi duk yacce za'ai. Wai ko kunga yadda ƴan mata masu class ke bibiyar shafinsa a Instagram suna masa comment na so da ƙauna?"
Dariya suka kwashe a tare har suna tafawa.
"Yo ai gaskiya ce waye bai san Familyn Kangiwa ba wajan arziƙi?, gasu da ɗan banzan kyau da Allah ya zuba masu?. Ai banga laifinki bama Aunty Haja da kika maƙalema Alhaji Ma'aruf Kangiwa ɗin ba wallahi, Allah kuwan yi yaƙi kawai kiyi mai yiwuwa ki shige daga ciki, ko muma mun samu malasa mu maƙale muma"
Sosai maganar da Ayshar keyi keba su dariya suna dariya suna tafa hannu. Sosai suke tattaunawa akan familyn Kangiwa da Aunty Haja ke son shiga ta kafa gwamnatinta itama a cikinsa........
PAGE 19
*MIMI POV*
Ranar da akai ball washe gari ma saida akai party iya mata ne kawai suka je.
Ranar Juma'a kuma ana tasowa daga masallacin juma'a aka ɗaura aure Mimi da Jafar da kuma na Yayansu Hajiya sai kuma na Hajiya ɗin.
Duk cikinsu Hajya ce aka fara ɗauka dan ana gama ɗaurin aure aka kawo motoci suka tafi kai Hajiya gidanta.
Mimi ce ƙarshe dan sai kusan yamma aka kawo motoci.
Aka wuce da ita gidanta dake Gwajawa Rimaye, ita kuma Hajiya tayi nesa da cikin gari sosai dan gidan mutum ɗaya aka ajeta ba cikin gari, sai dai ba wani nisa ke akwai ba, duka ɗari biyu ne zuwa gidan mutum ɗayar da Rimayen.
Su Maryam sunga gidan Mimi kam ba ƙarya yayi wani irin kyau sosai, an tsaya an tsarashi gini ne irin na wadda ƴan gayu suke yi, sosai gidan ya haska dan harda solar aka saka ma Mimi, ko ina na gidan haske ya gauraye shi.
Ƙawayenta kam wasu sai cewa suke.
(Tabɗi jam wannan ub*an gida haka?, ai dole Mimi take maƙale kam, ba nau'in jini ba koma miye ba kowacce mace ce ma zata iya yarda ta rasa mutum kamar Jafar ba).
Irin wa'innan maganganun kawai kake ji.
Da yake ana kwana gidan Amarya su Maryam ne da wata ƙawarsu Zahra wacce tazo daga Kano suka kwana a gidan.
Washe gari akai walima cikin tsari tun wajan yamma Zahra tayi bankwana dasu ta wuce Kano ta koma cike da kayan biki, ita kam Maryam saida abokan ango suka kawo ango har ɗaki kamin wani abokin ango mai suna Farouk ya ɗauketa a Motarshi ya maida ita gida.
Mimi kuka dai kam tasha shi kamar bazata daina ba, bare ma da Maryam zata tafi da kyar ta iya sakin hannun Maryam.
Sai dai can cikin zuciyarta wata irin murna ce kwance da wani irin jin daɗin yau wai ita ce zaune a gidan masoyinta Jafar, wadda take ganin ada kamar zata rasa shi, amma yau gata zaune a matsayin mallakinsa nata ne.
Cike da wata irin zazzafar soyayya mai tsayawa a rai Mimi da Jafar suka fara gudanar da rayuwar aurensu.
Watan su biyu da aure Jafar yayi wata tafiyar da zata ɗaukesa tsawon sati biyu kamin ya dawo.
Mimi ce zaune tana latsa wayarta a babban parlonta dake gidan.
Sallama taji kamar ta Maryam hakan yasa ta miƙewa tana murmushi haɗe da cewa.
"Wa nake ji kamar Maryam?"
Maryam data idasa shigowa tana murmushi, da wani irin sauri Mimi taje ta rungumeta tana murmushi da murnar ganinta tana sake cewa.
"Wallahi naji daɗin ganinki, ace kusan watana biyu ban sake ganinki ba"
Zama sukai tare Maryam na cewa.
"Uhmm ya za'ai kawai na rinƙa kwaso ƙafa ina zuwa gidan Amarya?, ai kema kin sanni dai ba zuwa zanyi ba, yanzu ma wallahi kawai danna sami labarin shi Ogan naki yayi tafiya ne shi yasa ma nazo"
"Wallahi baki da kirki"
"Haka zaki ce ma?"
Murmushi ta saki tana miƙewa haɗe da nufar wajan da aka jera mata darning table a gefe aka saka mata firizarta, daga can ciki koma wata ƙofa ce kitchen ne a wajan, ciki ta shiga tana ɗakko wani faranti ta zo kusa da firizar ta ɗakko ruwa mai sanyi dake cikin roba da lemo ta zo ta aje kusa da Maryam tana zama itama kamin ta ce mata.
"Yo eh man ya za'ai na ce kina da kirki?. Kowa fa ya sake dawowa gidan nan, ke hatta Hajiya dake da aure sati ɗaya kenan da mijinta ya kawo ta cikin dare wai ganin gidana suka zo"
"Ai sunzo dama?"
"Hmmm sunzo mana Maryam. Hajiyar duk sai naga tasha wani jinin jikinta, ko shiga ɗakina ma batai ba, iyakarta kitchen da parlon nan, naga dai fuskarta ba yabo ba fallasa"
"Kai jama'a ba abunda ke damunta wallahi sai baƙin ciki"
"To baƙin ciki nami?"
"Ke baki ga gidan Hajiyar bane wai?"
"Na gani man, an nuna min datai photo a cikinsa"
"To ai ko wannan ya saka suyi miki baƙin ciki, saboda gidanta bai kai ko kama ƙafar naki kyau ba bari na gaya miki, kinga kuwa ai ba haka aka so ba, wai ƙanin miji yafi miji kyau"
"Hmm Allah dai ya kyauta"
"Amin dai amma gidan nan naku dama cikin familyn nan naku suna da damuwa wallahi"
"Su suka sani Maryam, ni dai ba nayi aure na ba?, to can suji dashi. Kinga ma sha ruwa gashi nan ki taso muje kitchen ki tayani yin girki please"
Cire gyalen dake jikinta Maryam tayi tana ɗaukar ruwa tasha ta miƙe tana cewa.
"Muje ciki to, dan yau yini dama nazo miki"
Tashi tayi suna nufar kitchen ɗin Mimi na sake cewa.
"Wallahi kamar kin san dama na gaji da zama ni ɗaya, da wata yarinyar makwafciyata na shigo min wai kamar sunyi tafiya ne naga kwana biyu ta daina shigo min, zaman ni ɗaya ba daɗi wallahi"
"To dama sauƙi tunda kina da waya a hannunki"
"Eh da sauƙi kam ita ke ɗebe min kewa, dan kin san karatun novels ɗin da nake yi yana taimaka min sosai wajan ɗebe kewar da kuma ƙarin ilimin zama a gidan auren kansa wallahi"
"Hmm dana ce miki da can ki fara ai gani kikai kamar ba gaske nake yi ba ko?, ai wallahi karatun hausa novels yayi, dan ni bana jin zan iya dainawa"
"Wai ni kam Zahra Royal Star ta gama book ɗin nan nata GAWA TAFE kuwa?"
"Babban bala'in nan wai baki sani ba dama ai ta daɗe da gamasa yanzu ma wani take yi wai mai suna TSANIN ƘADDARA shima ya haɗu wallahi"
Zama Mimi ta ɗanyi akan wata kujera dake cikin kitchen ɗin suna gyara kayan miya a tare Mimi ta ce.
"Dan Allah fa ashe ta gama GAWA TAFE?, kin saye shi kuwa ki tura min please?. Ai labarin yayi wallahi ta baje basirarta wajan tsara labarin Zombies ɗin nan, labarin ina mugun sonshi wallahi"
"Ai kin san dama dole na saye shi, duka ɗari haɗu ne fa tasa shi, kin san bata saka labarinta da tsada da yawa, daga ɗari biyar sai dubu ɗaya, kamin ma tasa dubu ɗaya gaskiya da wahala"
"Eh gaskiya book ɗinta da sauƙi bata cika tsawwala labari bama kuma. Wai ya aka ƙare ne dasu Hanan da Al'ameen dasu Farida?"
"Hhhh ai in gaya miki gaba ɗayansu sai sun gwammace dama basuyi wannan tafiyar ba in gaya miki, kuma fa wallahi hatta Sojan nan sai sunje wajan nemansu suke haɗewa, amma tafiyar tasu na rabuwa, amma daga ƙarshe dai suna haɗewa, Abbakar ɗin nan mai masa baƙin ciki in gaya miki shima yana kamuwa da cutar nan a ƙarshe, shege"
Dariya Maryam ta saki tana cewa.
"Ke dan Allah?"
"Wallahi kuwa nake gaya miki, baiwar Allah Farida tana shan wahala suma dai tayisa har ba adadi"
"Baiwar Allah ai dole tasha wahala wannan bala'i na zombies da ake sakawa a wannan littafi ai dole"
"Bari ai ta iya tsara labarin horror sosai ita da meenat yandoma, kin san tare sukai kowa ya ɗebo da zafi, shima na zombies ɗin ne, ya kuma haɗu ba ƙarya shima. Danma wannan GAWA TAFEn ne mutane keta ce mata wai kamar taso ta kwafi wannan film ɗin na GAWA TAFE wadda sultan ya fassara. Sai dai a zahirin gaskiya labarinta ya banbanta da film ɗin GAWA TAFE, labarin ma kwata-kwata baiyi shige ba, bare ace shine ta kwafa tayi, kawai dai dan mutane sunga sunan book ɗin nata yayi iri ɗaya da film ɗin, kuma ni nake ganin ai dacewar sunan ta gani shi yasaka tasa masa sunan GAWA TAFE dan sosai sunan ya dace da nata labarin itama"
"Ai idan ta biye ta jama'a ma kullum sai sunyi mata abunda zai ɓata mata rai, ai nima naga film ɗin GAWA TAFEN, ba ta inda labarin yazo ɗaya, kawai dai shima Zombies ne itama kuma labarin nata na zombies ne, amma yanayin tsarin kowannen daban yake"
"Ai kuwa dai"
Suna yi suna labarin books ɗin hausa daga su kamo wannan sai su kamo wancan a haka suka ci rabin girkin, suna ɗora komai suka fito parlo Mimi na miƙa mata wayarta ta ce.
"Kinga tura min book ɗin nan karma ki manta, nima kuma nazo na manta. Shi wadda take yi ɗin ta gama free pages ne ya labarin yake ne?"
"Wai baki cikin channel nata ne?"
"Eh ke kina ciki ne?"
"Tab sosaima har group nata"
"Tom dan Allah kisa a saka ni nima"
"Shikenan zan turo miki linke nasu saiki shiga da kanki. Shi kuma sabon labarin nata ai harta fara posting