Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   24 / 47

69K to 72K   out of 140.3K words

ta a wani waje ta yadda wani na takawa zata tsinke.

Tabar wajan ta koma ciki.

"Miye kika je kika yi ne?, naga sai share zufa kike yi"

Zama Maryam tayi tana sakin wani dogon lumfashi kamin ta ce.

"Hmm yanzu zaki ji kiɗan ya yatsa, ba dai iskanci suke taƙama dashi ba to zasu gani suma"

Ai ko da rufe bakinta ba jimawa suka ji shiru kiɗan ya ɗauke gidan sai yayi tsittt sai kuma hayaniyarsu ke tashi.

"To miye yasa kiɗan ya tsaya?"

Murmushi kawai Maryam ta saki tana cewa kawo kunnanki.

Matsowa kusa tayi tana murmushi ta raɗa mata abunda tayi yasa Mimi sakin wata dariya haɗe da tafawa a tare.

Dai-dai lokacin da Shamsiyya ta shigo parlon ranta kamar duk a ɓace.

Ai ganinsu a hakan yasa Shamsiyya dakatawa tana masu wani duba na mamaki da kuma zargi.

"Lafiya dai Mlm da tsaya mana a kai?"

"Lafiyar ce ta kawo haka ai, idan ma ɗaya daga cikinku ce tayi min wannan muguntar to wallahi tallahi dai-dai nake da duk wani iskancinta"

"Ke dalla can Mlm dakata, ina ruwanmu da ke?, ina ruwanmu da abunda ke faruwa?, mima ya farun?, da har kike ikirarin an shirya miki mugunta?,.waye yake take ma?"

Mimi ta faɗa tana nunata da yatsa dama cike take da ita, kuma ganin kamar zata gano su ta ƙara raina su ne yasa Mimi fara faɗa mata maganganu kanta tsaye.

Ganin yadda Mimin ke masifa yasa Shamsiyya fara zargin kodai basu bane?, to amma waye zai fita har ya tsinke masu wayar injin?.

Cike da burin kunya Shamsiyya ta ce.

"To waye ya sani ma?, ai dai nasan zaku iya aikata min komai keda wannan jigaggar ƙawar taki ƴar karere"

"Ke kinga Shamsiyya idan zakiyi maganarki to kiyi ta iya tsakaninku, na gaya miki karki ƙara sanyo ni a ciki, dan ni nan nima da kike gani bafa kanwar lasa bace, tsaf da kika gani na nan bafa haƙuri ne dani ba yawwa ki kama kanki dani"

Wata hararara Shamsiyya ta zafga ma Maryam cike da jin haushinsu gaba ɗaya ta ɗaga hannu tana nunasu da yatsa zatai magana kenan Ayra ta shigo parlon tana cewa.

"A fara raba kayan birthday ɗin kawai mutane sun fara gajiya saboda ba disko, amma dai na aika gidan Rafee za'a amso mana ƴanfi ɗinta, kin san itama kamar rikoda haka take"

Murmushi Shamsiyya ta saki tana kamo hannun Ayra ta ce.

"Kai amma kin kyauta, muje a fara raba abubuwan, kinga hakan ma yayi ai sai dai ƴan baƙin ciki su mutu wa'inda basa so abun nan ya yiwu"

Ta ƙare faɗar hakan tana janta suka fice haɗe da sakin tsaki mai sauti.

"Wato Shamsiyya da wannan shegiyar ƙawar tata anyi ƴan iskan shaiɗanu wallahi, tabɗi jam, tsakani da Allah Mimi kina da aiki a gabanki bama ƙarami ba, da alama Shamsiyya ta shirya zama ne a gidanki dama can tasan abunda ta taka"

Mimi shiru kawai tayi tama kasa cewa komai dan ita kam zuwa yanzu kanta ya fara ɗaukar zafi da, lamarin Shamsiyya ya daina bata mamaki ya koma fara bata tsoro.

"Kinga ni dare ya fara zuwa zanyi na koma gida gaskiya"

"Yanzu haka zaki barni ni ɗaya?"

"To ya kike so nayi Maryam, ni dai kin san ba kwana zanyi a gidanki ba, yini ma na ce ma Umma zanzo nayi, amma gani nan har kusan bakwai da rabi na dare, gara nazo na tafi kawai, sai da safe munyi waya naji ya aka ƙare"

Kamar Mimi zata saki kuka ta miƙe suka shiga bedroom a tare Maryam ta ɗakko gyalenta da jakarta ta rako daga ƙofar parlo ta wuce ita kuma ta komo ciki tana jin wani kaɗaici da ƙuncin zuciya sun sake rufe ta, dama ganin Maryam a kusa da ita ne yake sakawa take jin sauƙin wani abun.

Bata zauna parlon ba ta wuce bedroom, ta daɗe a ciki har ta gama sallolinta har kusan ƙarfe taran dare tana jiyo kiɗan dasu Shamsiyya suka sake kunnawa, haɗe da hayaniyar jama'ar data tara mata a gida, hardasu shewa ake saki ana sakin buɗa.

Tun tana iya jiyo su har bacci ya ɗauke ta.

Bata kuma tashi farkawa ba sai gabanin asuba.

Da kyar ta tashi tayo alwala tana leƙawa ta window da hasken tsakar gidan tana iya hango yadda duk aka ɓata harabar gidan da abun abinci ledoji ne duk gasu nan a watse a tsakar gidan.

Jinjina kai kawai tayi ta kabbara sallah bayan ta gama a nan ta zube bacci mai daɗi ya ɗauke ta, dan jiya ta daɗe batai wani baccin kirki ba, tunanuka duk sun hanata sakat.

Wani irin ƙamshin turare ne yayi mata sallama a cikin hancinta, can cikin bacci taji kamar an ɗauke ta anyi sama da ita.

A ɗan firgice ta farka tana buɗe idonta a hankali. Zaro ido tayi da mamakin ganinsa ta ɗan ƙara riƙesa sosai tana ƙoƙarin ya sauke ta daga jikinsa sai ya sake matseta yana zuwa baƙin gado ya zauna tare da ita a jikinsa, ganin hakan sai yasa Mimi sake kwanciya a jikin nasa tana sake ƙanƙamesa ta ce.

"Amma bana ce karka dawo yanzu ba?, why ka dawo kuma?, zaka ƙara hargitsa abubuwa ne idan har kana nan"

"Ba abunda zai faru love, nayi kewarki ma sosai gangar jikina tana son kasancewa tare dake, amma naga ke koma farin cikin ganina baki yi ba ko?"

Girgiza kai tayi da sauri tana ɗagowa kaɗan daga jikinsa ta dubesa sosai tana kallon cikin idonsa da take hango tsantsar sonta da son kasancewa tare da ita a cikinsu ta ce.

"Nayi kewar abun ƙaunata mana, kawai damuwa ce jiya taso tayi min yawa"

"Am so sorry kinji Love, naga abunda ya faru a tsakar gidan nan, naga duk harabar gidan ta ɓaci, wato dai saida ta shirya partyn nan ko?"

"Hmm yaya bazata shirya ba?, baccin kasan Hajja ce tasa ta ci gaba da shirya koma miye ta shirya ɗin"

Ganin maganar na sake sashi ɓacin rai da ita kanta cikin damuwa yasa Mimi riƙo kansa sosai ta kamo fuskarta tana matso da tata kusa da tashi, a hankali ta ɗora bakinta saman nashi. Shi kam jin haka dama yayi mugun kewar matarshi yasa shi ƙara riƙe ta yana bata haɗin kai. Zaman ne ya gagaresu suka zube akan bed suna sauke lumfashi haɗe da ƙanƙame juna daga nan labari ya sauya salo, dan sosai itama tayi kewar mijin nata, wannan safiya haka ta kasance masu mai cike da farin ciki da farantama juna, dan sosai Mimi ta shiga farantama mijinta kuka iri-iri da shagwaɓa yasha shi, shi kam bawan Allah shima kusan kukan yayi mata dan Mimi ƙarshe ce ta idan akazo wannan harkar tasan kan yadda zata zautar da mijin nata ya gigice ta yadda ba wacce yake iya tunowa a lokacin sai ita ɗaya.

Tsaye Shamsiyya take a parlo fitowarta kenan sanye take da kayan bacci dan tashi tayi a gajiye, ga yinwa data tayar da ita, gashi jiya duk ta kashe sauran kuɗin da suka rage mata.

Tsaki taja tana kallon parlon, sai take jin kamar wani gurnani-gurnani a cikin ɗakin Mimi.

Gabanta ne ya bada wani irin rassss, jin kamar ƙamshin turaren Ya Jafar.

"Kar dai shine ya dawo da safen nan?"

Ta faɗa da mugun mamaki.

Sai kuma taji zuciyarta na mata wani mugun zafi.

"Daga dawowarsa za'a fara tarbarsa da wani salon iskanci?"

Ta ƙare maganar tana matsawa kusa da ƙofar bedroom ɗin.

Abunda taji ya kusa saka jinta ɗaukewa na wucin gadi.

Lumfashinta na barazanar ɗaukewa gaba ɗaya.

Wasu zafafan hawaye ne kawai ta fara ji suna saukar mata a ƙunci.

Jiki na rawa tabar ƙofar bedroom ɗin, wata muguwar nadamar fitowarta ta rufeta, mima yasa ta tashi a irin wannan lokacin ne?. Gashi taje ta juyo abunda ya kusa sawa zuciyarta daina aiki.

Wani irin azababben kishi ne ya rufe mata zuciya da ruhi, dan kwata-kwata ko ganin gabanta bata yi taka ƙafarta kawai take Allah ne kawai ya taimaka mata ta idasa ɗakinta, dan saura kaɗan wani irin jiri ya kwasheta ta faɗi ƙasa. Tana shiga ɗakin ta zube akan katifa tana sakin wani irin nishi idonta jawur kamar wuta naci a cikinsu, wata irin wutar kishi ke taso mata can ƙasan zuciyarta, danji take kamar zatai hauka, ji take kamar ta fasa ihu kota samu taji sassaucin abunda ke taso mata............

PAGE 46

*MUBEENA POV*

Ta ɗauki jakarta ta saƙala a kafaɗa bata ce kanzil ba ta juya zata fice daga ɗakin Na'ima ta riƙe hannunta da sauri kamin ta ce.

"Yanzu haka zaki tafi baki tsayawa koma muyi sallama dake Mubeena?"

Mubeena ta sauƙe wani goran lumfashi bata juyo ba ta ce.

"Mi zance maku Ya Na'ima?, baccin kina ji kina gani yau za'a tafi dani wata uwa duniya inda ban san kowa ba, banda kowa kuma baki hana ba, wai dan kawai na ce zan kwato miki ƴancinki shine har na cancanci wannan hukuncin?"

Na'ima hawaye ne taji sun cika mata ido a hankali tasa hannunta tana juyo da Mubeena tana fuskantarta.

Khadija ma dake tsaye saita matso dan Allah ya sani ba ƙaramin kewar Mubeena ɗin zasuyi ba, tunda tafiyar ta tabbata kwata-kwata daga Mubeenar harsu ba wadda ke walwala kamar wa'inda aka aikoma da sakon mutuwa.

"Kiyi hakuri Mubeena, da ina da dama wallahi da ba inda zaki je, to anfi ƙarfinmu ne ai kin sani"

Cewar Khadija tana kallon Mubeena dake murmushin daya fi kuka ciwo.

"Ai shikenan ni zan tafi sai kuma Ubangiji ya ƙaddara saduwarmu, idan kuma ba rabon a sake haɗuwa ne to, sai na ce Allah ya ƙaddara haɗuwarmu a Aljannah"

Ai sai hawaye suka yanke ma Na'ima cike da wani irin rauni ta buɗe baki ta ce.

"Haba Mubeena wacce irin magana ce haka kike yi?, baccin kin san Aunty Zubaida an riga da an same ta a waya kuma ta saurari Inna tayi murna da kawo ki da za'ai kin kuma sani, bafa wajan bare zaki tafi ba"

Ta sake gyara tsayuwarta tana dubansu gaba ɗaya yadda jikinsu yayi sanyi ta ce.

"Na sani, kuma nima ina murna da samun nata da akai, amma ai kin san yanzu-yanzu sai Ubangiji ai ko?, sana yanzu kana magana da mutum sai a tashi aga babu shi ya mutu, dan haka dole na ce Allah ya ƙaddara saduwa, sana kuma a yayyafe juna, saboda ba'asan gawar fari ba"

"Innalillahi waike Mubeena miye haka kike yi ne?, wa'innan maganganun naki sai su sakawa mutum fargaba da tashin hankali, insha Allah ma zaki dawo ki iskemu, nasan da akwai mutuwa amma insha Allahu ba yanzu ba"

Murmushi kawai ta saki zata juya ta fice daga ɗakin suka ji muryar Iya na cewa.

"Wai ub*anme suke a ɗakin da bazata fito su wuce ba?, Lagos fa ba nan bace, ga rana harta fara takewa"

"Iya suna sallama ne fa"

Wata uwar hararara Iya ta watsama Inna dake tsaye suna magana da Musa ta sake gaya masa saifa yayi hakuri da yanayin Mubeena dan Allah Ya kula da ita harsu isa.

"To uwar son ƴaƴa, su kwaɗata su cinye namanta ƙarewar sallamar"

Kawu Isa ne dake tsaye shima ya ce.

"Wai kuna ina ne?, ku fito ko sai nazo na iske ku a ɗakin, sallama sai ka ce bazata ƙare ba, tun ɗazu kunbar mutane a tsaye sai ka ce wasu sa'anninku ne ke jiranku?"

Fitowa sukai da sauri dan sun san Kawu Isan da wutar ciki yama fi Iya faɗa da azalzalar mutum, sunma yi mamakin yadda tun ɗazu baiyi magana ba.

Ganin yadda Na'ima ke wani share hawaye Khadija kuma idon ya cika da ruwan hawaye kaɗan take jira tana iya fashewa da kukan, ita kam mutuniyar taku ko a jikinta ba alamar ma zatai wani kuka, amma daka kalleta zaka san bata ƙaunar tafiyar sana jikinta a sanyaye yake.

"Ohhh ni ƴaso naga Ikon Allah, ke yanzu Na'ima goɗai-goɗai dake zaki zauna a gaban yara kina kuka?, kema Khadija kukan ne zaki saki ko?, ita wacce kuke yi domin gata nan ido a bushe ba alamar ma zatai kewar taku"

Ba wadda ya tankama Iya hasalima Na'ima wajan Musa dake tsaye ta matsa tana ce masa.

"Musa dan girman Allah kayi a hankali da Mubeena harku kai Lagos, kaga dai ba wani jin magana take yi ba, sana yarinya ce ƙanwar-ƙanwarka ce, dan haka kayi hakuri da duk sharmen da zata maka kaji?"

"Shikenan masoyiya zanyi ne kawai domin ke da kuma Inna data roƙe ni, zata ci arziƙinku wallahi, amma da niyyata tana min rashin kunyar nan tata yadda ba idon kowa a cikinku na kamata nayi mata hukuncin da zata gane kuranta wallahi, amma dai zata ci arziƙinku kawai"

"Yawwa dan Allah masoyi kayi hakuri ta ci arziƙin namu kawai"

Na'ima ta faɗa da sauri tana mamakin wato da mugunta ya shirya mata tafiyar tasu kenan.

Sauke lumfashi mai zafi tayi tana ganin yadda ya wani saki murmurshi yana washe hakora ya ce.

"Yau ni Masoyiya kike kira da masoyi?, gaskiya yau ranar sa'a ta ce kawai, ai kawai ki kwantar da hankali kamar na kai Mubeena ne cikin jin daɗi ba takura kodan ma farin cikinki ai ni duk abunda zanyi kiyi farin ciki shine nake so, karki wani damu"

"To kai sakarai sai ka zo ku wuce ko?. Kai wai a haka za'ai auren yarinya nason gamawa da kai tun yanzu?, jibeka sai wani washe hakora kike yi a gaban yarinyar salon ta raina ka tun kamin auren?"

Iya ta faɗa tana taɓe baki dan ita yadda Musan ke nuna so ga Na'imar haushi abun ke bata, itafa so kawai take taga Musa bawa wani bata kulawa ko tasha wahalar zama dashi, ai ita bata san ma Musa nason Na'ima ba sai da akai haɗin auren, data sani bata gigin haɗa auren wallahi, amma waje ya ƙure mata, yanzu idan ta ce zatai magana sai aga kamar takurawar da take ma yaran ta fara yawa ne za'a kuma iya gano wahalarsu kawai take so basu ba, gashi magana takai har cikin dangi da maganar auren batai nisa ba da wallahi ba'a yinsa.

"Haba Iya ai nake ganin abun farin cikinmu ne, ya fara jin maganarta ya kuma fara sonta, itama baki ga ba ta kwantar da hankalinta ba?"

Taɓe baki ta sake yi tana kallon Kawu Isa da yayi maganar yana ɗan murmushi ta nunasa da hannu ta ce.

"Miye abun murna a nan ɗanka na hannun mace?, tana son gamawa dashi tun kan aje daga ciki?, ni wallahi baccin maganar ta kai cikin dangi da an fasa ta ma"

"Wallahi kuwa Iya da shikenan ba sai mun wani tafi Lagos ba a barni a gidanmu, ai dama kece baki gane ba, ba ta inda Musa suka dace da Ya Na'ima. Iya na baki wata shawara ma?....

"Ke dalla gafara can kiyi ma mutane shiru"

Musa ya faɗa a zabure kamar zai kai ma Mubeena naushi a fuska.

Da sauri Na'ima ta riƙe masa riga tana girgiza masa kai haɗe da masa magana ta ido, sai ya tsaya yana sauke lumfashi yana danƙarama Mubeena wani mugun kallo Iyar ma dake kallonsa ta samu nata rabon hararar.

"Kyale ni da ita Musa. Mubeena wallahi Allah ki fita daga ido na rufe, manya na magana kika sake sako bakin nan naki sai nayi mugun saɓa miki wallahi"

Inna ta ƙare maganar tana nuna Mubeena da yatsa.

Kawu Isa na ɗan murmushi kaɗan ya dubi Iya ya ce.

"Iya wacce irin magana kike yi haka?, dama can bake ke son haɗin auren bane?, ke ce fa da kanki kika kawo maganar haɗin auren, amma yanzu kike wannan maganar?"

"Mtswww nayi maganar ai gaskiya na faɗa, kana ganinfa yadda idan ta ce abu jiki na rawa yake mata shi, inaga anyi auren?, ai juyasa zatai tayi kamar wata waina"

"To ni Iya ai banga abun tada hankali ba, ni dama haka nake so Musa ya samu wacce yake so ta yadda idan akai auren zata fiddosa daga halin shaye-shaye da yake yi da duk wani halin banza, nasan yanzu Na'ima ce kaɗai zata iya wannan aikin, dan haka gaskiya Iya kima daina wannan maganar ta fasa aurensu, karma wani yaji yawwa"

Kawu Isa ya faɗa kansa tsaye ba ko kunyar Mahaifiyar tasa.

Cike da borin kunya ta ce.

"Kaifa daɗi na dakai baka cin ribar zance fa, bafa cewa nayi a fasa auren ba"

"Ai wai idan ma haka kike nufi Iya ba abu bane da zai yiwu"

Cike da mamaki su Inna ke kallonsu, wato dai tana shakkar su Kawu Isa kenan?, da ace Jamilu ne Mahaifinsu Mubeena ke duniya bai isa yayi mata gaddama ba bare yayi musu da ita, amma dubi yanzu yadda Kawu Isan ke gaggaya mata magana amma tayi shiru, bama ta ganin laifinsa sai ƙoƙari take taga ta nuna masa ba haka take nufi ba. Ohhh duniya.

Inna ta ƙare maganar zucin tana jinjina kai.

Mubeena ta taɓe baki zatai magana domin itama abun ya ɓata mata rai, da Abbansu ne da wallahi wata ƙila yanzu ta fara zaginsa ko ta fara kuka tana faɗar ya rainata dama ba sonta yake yi ba, kuma dole ayi abunda take so ko anƙi ko ansu ko kuma ta nuna masa iyakarsa, ko kuma bata yafe haihuwarsa da tayi ba, amma sai yanzu gasu Kawu Isa nan sunyi mugun raina ta, shi mai mata biyayyar shine abun wulaƙantawa ƴaƴansa ne kuma bata son ganinsu cikin farin ciki.

"A gaskiya Iya kina bani mamaki dan......

"Ke ban ce karna sake jin bakinki a nan ba?"

Inna ta katse hanzarin Mubeena da sauri.

Turo baki tayi tana yin ƙasa da kanta.

"Ai kawai da kin barta ta faɗi abunda ke ranta, ai dama ta raina ni ne, kuma duk bake ce kika ja ba suka raina ni ɗin?"

"Ni kuma Iya miye nawa a ciki?, duk ƙoƙarin da nake yi akansu?"

"Wane ƙoƙari ne kike yi Binta?, saima salon ɓata so da kike yi, ace yara sai abunda suka ce miki shine kike yi"

"To wai Iya kema baga su Kawu

24 / 47