Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   15 / 47

42K to 45K   out of 140.3K words

wahala ne shima. Amma dai zan duba"

"Yawwa dai dan Allah sis ki duba mana ko ƙarfe ɗaya ne muzo mu amsa please kinji?"

"Shikenan insha Allah"

"Yawwa to ki turo min account number zan saka maki kuɗin cake ɗin"

"Amma kamar na nawa kuke so ne mai girma ne?"

"Eh mai girma ne gaskiya kamar hawa biyar muke so fa"

"To ba damuwa mai hawa biyar muna yinsa akan 30k ne"

"Okey kisa min account kawai, cake naki ma da sauƙi da wani wajan ne har 40k ana sayar da mai hawa biyar wallahi, shi yasa zakita ganin jama'a nason sayan cake naki wallahi"

"Hakane. Kisa ta Opay nawa a wannan number ɗin"

"Okey yanzu kuwa sis mun gode fa sosai"

Hannah ta sauke wayar tana amsawa da madallah ta sauke ajiyar zuciya tana jin Fannah na faɗin.

"Gaskiya wallahi kina da sauƙin cake, yo da ni ce ke yinsa Billahir azim bazanyi mai hawa har biyar akan 30k ba haba ai sauƙin naki yayi yawa ma, kinsan nawa kuwa na taɓa ganin mai hawa biyar ɗin nan a Instagram wata nayi kusan fa 50k tasa kuɗinsa fa"

Hannah ta dawo kusa da Fannah ta kwanta tana kallon saman rufin ɗakin ta ce.

"Ni albarkar abun nake so bawai na tsawwala ba Fannah, idan ka cika saka riba a abun saidawarka to Allah ma bazai taɓa saka maka tashi albarkar ba, gara dai kasa saisa-saisa yafi, a nan fa naci riba nima ai anayin abu a lissafe ne"

"Ribar duka nawa kike ci dubu biyar ce fa Hannah"

"To ina laifi Fannah, ni bazan iya cika kuɗi ba gaskiya"

Fannah ta taɓe baki tana sake faɗin.

"Wato dake kinyin ƙunshi da mutane sunci banza kawai zance"

Murmushi tayi tana juya mata baya ta ce.

"Kinga ki barni nayi bacci akwai aiki zuwa anjima, ga ƙarin wani na samu ma"

"Hmm ai dama tashi kikai naga har bakwai fa tayi yanzu, kun daɗe kuna waya ai. Nifa ma abunda ke sake ɓata min rai ma aikin gidan nan wallahi, ga aikin kamar ƙara shi ma akai, wai mi yasa ma bazasu samo mai aiki bane ko almajiri ne?"

"Nima gaskiya aikin ya fara min yawa, saboda wanke-wanken gidan ya ƙaro ne saboda abincin da Aunty Sa'a keyi ne ya ƙara aikin gidan shi yasa kawai, amma dai haka zamuyi ta hakuri ya zamuyi tunda mune ƙananu a cikinsu?"

"Mtswww billahir azim da safe sai nayi maganar asamo mana almajiri, ai muma yanzu kowacce da nata aikin. Taya za'ai ace daga tashinka tun safe ka kama aiki, ga wani na jiranka kuma, ni gaskiya na gaji"

Murmushi kawai Hannah ta saki tana kuntse dariyar dake taso mata, dan yadda Fannah ke magana aikin naci mata rai sosai sai faɗa take........

PAGE 28

"Hannah kifa tashi rana ta fara fitowa sosai"

Fannah ta ƙare maganar tana kwaɓa wani lalle dake a cikin leda, sai kayan haɗin ƙunshi dake zube a gabanta tana haɗawa.

Miƙa Hannah tayi tana tashi zaune ta fara murza idonta dake cike da bacci, dan baccin bawai dan ya isheta bane.

"Wai ƙarfe nawa ne ma yanzu Innalillahi"

Cewar Hannah da sauri ta miƙe ganin rana sosai tayi.

"Kamar ƙarfe takwas da rabi ne yanzu"

"Haba amma Fannah kin tashi mi yasa baki tayar dani ba tun ɗazu?, kuma kin san akwai aiki a gaba na tsakani da Allah fa"

Fannah na aikin kwaɓa lalle bata kalleta ba ta ce.

"Kiyi hakuri wallahi na sha'afa ne kwata-kwata, kuma naga baccin na miki daɗi ne shine yasa kawai na barki, kuma harda naga kina ciwon kai kwana biyu be shine yasa"

"Koma minene wallahi da kin tayar dani kawai"

Ta faɗa tana matsawa kusa da inda suke aje makilin ta matsa tana ficewa waje ranta duk ba daɗi.

Tana fita tsakar gidan ta iske su Aysha na zaune, gidan tabi da kallo kamar an gyara shi ma.

"Ammi ina kwana?"

Ta shiga gaida su gaba ɗaya suma.

"Lafiya yau kika makara?, hala yau ko baki da aikin yin Cake ne kina hutawa"

"A'a wallahi Aunty Sa'a ina dasu harna mutum huɗu ma,makara nayi ne shine yasa, amma yanzu zan fara"

"Tabɗi ai ko kin makira sosai"

"To ai Aunty Maryam duk laifin Aunty Fannah ne fa"

Ta ƙare maganar tana kwaɓe baki kamar zata saki kuka.

Sai lokacin ta waiga tana kallon wasu mata su uku zaune a gefe guda. Sun girmeta ko a jiki da fuska, dan haka ta shiga gaida su suma tana matsawa da sauri wanke bakinta ta da fuskarta ta dawo.

"Yawwa Aunty Sa'a ki bani key ɗin kitchen ɗin can naje yanzu na fara nasan yanzu za'a fara kira na ma naga har tara ta idasa ma"

Miƙe mata key ɗin tayi tana yanka wani ɗanyen nama dake gabanta sai wasu kayan miya dasu kabeji harda su kokonba da kayan haɗi harda kwai.

"Nima yanzu zan shigo dana idasa yanka wa'innan abubuwa na fara ɗora sanwa dan mutane nima sunyi Order na abincin da yawa wata ƙila harda na ɗaurin aure, dan cikin takeaway zan zuba wasu"

"Na ɗaurin aure ne ma ƙila, takeaway nawa zakiyi yau"

"Na mutum uku ne nima Aysha kowanne ana suna son takeaway guda ɗari da hamsin da hamsin, shi yasa abincin yau sai kun kama min yinsa, duk da dai rabinsa duk nama yafi yawa amma shi jiya duk naci rabin aikin naman kamin mu fita, soya shi kawai ya rage min yana nan na tanana shi"

"To bari kawai nabi Hannah saina soya miki na rage miki wani aikin"

"Yawwa dan Allah ki bita Aysha nima gani nan zuwa yanzu"

Ta faɗa tana binsu da kallo har suka wuce ta ƙofar cikin gidan suka bi suka buɗe shagon suka shiga.

Aunty Haja ce ta miƙe tana latsa wayarta ta dubi mutanen dake zaune suna zaman jiran Fannah ta ce.

"Wai ina wannan yarinyar ne tabar mutane a zaune suna zaman jiranta?, wannan ai wulaƙanci ne"

"Ai haka take ka rasa uwar da take yi a ɗakin"

Ammi ta faɗa ƙarshe ta kwala mata kira.

Amsawa tayi tana fitowa da sauri jin za'a fara mata mita gaba ɗayansu yasa tana fitowa tana fara turo baki tana cewa.

"Ammi fa haɗa lallen nake yi"

"To baki yi da jiki ki zo ko kin masu sai lanƙanji kike yi ma mutane, tunfa ɗazu suke zaune"

"A'a Hajiya ai ba komai gara ta haɗa lallen da kyau, dama masu ƙunshi sun gaji haka ai"

Cewar wata da zata kai sa'ar Aunty Haja a cikinsu.

"Duk da haka dai zaman jiran bashi da daɗi"

"Yanzu zan fara masu ai"

Fannah ta faɗa tana zama akan tabarmar da suke zaune ta gaba haɗa komai har kwarkwaro ta haɗa tasaka lallen a ciki.

"Wace za'a fara mawa?"

Ta tabbaye su tana ɗakko lalle baƙi dashi zata fara masu.

"Anya baza'a fara da jan ba kuwa Fannah, dan yafi daɗewa"

Cewar wata daga cikinsu.

"Awa biyu ne fa kawai kusan duk zaman dai ɗaya ne ga duk wadda aka fara dashi ɗin, amma bari na fara maku jan kawai tunda haka kuke so"

"Ki fara ma Intee"

Babbar cikinsu ta faɗa, sai mai bima Intee ɗin ta taɓe baki kamar zata saki kuka ta fara ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.

"Kefa teema anyi babbar banza wallahi, ƙanwar taki kike ma fushi dan an fara mata ƙunshin"

"To ni Aunty Ummi kullum idan muka zo ƙunshi ko kitso ita fa ake fara mawa"

Dariya Fannah tayi tana cewa.

"Kinga teema ko?"

Ta faɗa tana kallonta saita ɗaga mata kai, Fannah ta ce.

"To kiyi haƙuri yanzu zakiga shaf-shaf na gama mata na fara miki, ita baki ga Auntyn taku ba ita ce ƙarshe taci girma ba?"

Ɗaga kanta kawai tayi tana share hawayen da suka fara zubo mata kamar wata ƙaramar yarinya.

Tsaki kawai Ummin ta saki tana girgiza kanta, dan itama ta tsani zuwa dasu ƙunshi dan dai ba yadda zatayi ne kawai.

Dandanan ta fara masu ƙunshin kamin a rufe awa ɗaya ta gamama Intee ɗin harna hannun baƙi, yarinyar sai murmurshi take dan Fannah sosai ta iya tsara ƙunshi yadda kasan ba ɗan adam ke yinsa ba.

"Kai masha Allah wallahi kin iya kin huta"

Murmurshi Fannah ta saki tana cewa.

"Tun ɗazu kika cewa haka fa"

Fannah ta faɗa tana kallon Ummi dake ta santin ƙunshin, itama teemah sai da ta tanka dan murmurshi kawai suke.

Teemah ta faramawa itama mai wani irin kyau Ummin ta kasa haƙuri ta ce.

"Kai kai kai karfa azo kaina aidiyar yau ta ƙare duk kin gwangwaje su da mai kyan"

Ta ƙare maganar da zolaya. Dariya Fannah ta saki tana cewa.

"Sha kuruminki naki ma wata ƙila yafi nasu kyan, ki dai saka ido kawai kiyi kallo hajiyata"

Murmurshi ta saki itama tana ci gaba da kallon yadda take tsara ƙunshi a ƙafar teemah, ji take kamar ta dawo dashi a ƙafarta.

Daga can gefensu da yake ba wani jinsu suke sosai ba kowanne na harkar gabansa ne.

Aunty Haja ce ke waya tana cewa.

"Eh ranki ya daɗe insha Allah yau zamu zo da P'A ɗin"

Daga cikin wayar aka ce mata.

"Ina so ne kece zaki jagoranci taron ne Haja, dan yau ina gida ba inda zani saboda muna da babban baƙo ne da zai dawo ƙasa Abeed Kangiwaaa yau ne zai dawo, shi yasa gidan yau sai a hankali a cike yake, anata hidimar tarbarsa ne"

Wani iri Aunty Haja taji har cikin ranta, inama dai tana gidan ta shiga a matsayin mata ne Abeed ɗin zai dawo yau, amma dai ai ba yau ne kaɗai ba, koma ya sake komawa zai dawo ne tunda ita da zata shiga cikin familyn ma nasu gaba ɗaya. Cike da jin ɗan kishin Haj Saratun ta amsa mata da bibbiyar da take mata kamin suyi sallama.

"Tabɗi jam da kishiyar taki kike waya halan?"

Aunty Sa'a ta faɗa tana kallon Aunty Haja dake wani irin cije baki.

"Ita ce mana munafukar ba, har wani gayan wai Abeed ne zai diro ƙasar shi yasa ta wakiltani naje taron mata da aka gayyace ta, kuma dama taga matan talakawa ne suka gayyace tan shi yasa bazata je ba ai, da ace wani taro ne da wasu jiga-jigan suka shirya ai bazata taɓa bari ya wuce taba koma waye zai dawo, kai ba Abeed ba ko Alhaji Ma'aruf ɗin ne zai dawo daga wani wajan wallahi sai taje, ai ita kawai son asani, da son asan ita ɗin wata ce"

"Tsakani da Allah akwai aiki a gabanki Aunty Haja, tabɗi jam shiga irin gidan Alhaji Ma'aruf ai saika zama marar tsoro ka ɗakko rashin kunya ka yafama kanka, tukunna zaku iya shiryawa dama ko waye"

"Ai shiryen nawa zan shiga gidan nasa Maryam, na ɗauri ɗamarar komai zan koma shinye koma mi ya biyo baya, ke dai kawai yanzu babban aikina shine naga na zama matar Alhaji Ma'aruf Kangiwa shine mai babban aikin"

"Hakane kam"

Cewar Aunty Sa'a tana miƙewa ta sake cewa.

"Ni bari naje kitchen ɗin can na gani. Please Maryam ɗan biyo ni da sauran kayan muje ko na idasa aikin nan"

Da to ta amsa tana ɗaukar wata ƙatuwar roba mai cike da kayan yanke-yanke na abinci da sauransu.

"Fita zanyi nima yanzu zan nufi wajan taron dan naji ta ce min na ƙarfe sha ɗaya ne dole na shirya yanzu. Sana ina key na Mota yake please da ita zan fita"

"Ki duba a cikin jakata da nake fita da ita yana nan a ciki"

Aunty Sa'a ta faɗa tana yin gaba zuwa kitchen ɗita Maryam na take mata baya........

PAGE 29

*MIMI POV*

A hankali ta fara neman number ɗin Maryam, saida ta kusa tsinkewa kamin taji Maryam ta ɗauka, da har ta sadaƙas bazata ɗauka ɗin ba, saboda Maryam hidimar dake gare ta yayi ma kanta yawa. Sai kayi ta kiran number ɗinta baka samu, ko idan ta shiga ba'a ɗauka.

"Hello Maryam"

Mimi ta faɗa tana lumfasawa a hankali, daga cikin wayar Maryam ta amsa da cewa.

"Mimi yaya dai?, ya naji muryarki a haka?, naga kira tunda sanyin safiyar nan Allah yasa dai lafiya?, wallahi ina ganin kiran naki saida gaba na ya faɗi haka kawai"

Mimi ta sake sauke ajiyar zuciya tana cewa.

"Bari Maryam ina cikin matsala ne wallahi, maganar bazata yiwu a waya ba, please anjima ina so kizo gidana please zamuyi wasu maganganu ne akwai magana ne sosai"

Maryam ta sauke lumfashi mai ɗumi kamin ta ce.

"Shikenan zanzo zuwa anjiman, dama ina da niyyar ƙara zuwa ma gidan naki, amma da sai juma'a, amma dai zanzo ɗin yau"

Ta faɗa a ƙarshe sukai sallama Mimi ta kashe wayar tana sauke wata ajiyar zuciyar a fili.

Motsin data fara ji a parlon sosai ne da wani sautin maganganu kamar waƙa aka kunna yasa Mimi saurin miƙewa tana fita parlon.

Turus taja ta tsaya ganin Shamsiyya ce zaune akan kujerar parlo ta ƙure ƙarar TV tana jin waƙa a tvn.

Ta daɗe tana bin Shamsiyyar da kallon mamaki da nuna isar da take yi shike ƙara bawa Mimi mamaki sosai.

Mimi ta taka har inda TVn take tasa hannu tana kasheta gaba ɗaya.

Shamsiyya ta wani bita da kallo tana cewa.

"Malama lafiya dai zaki kashe TV?"

Mimi ta gyara tsayuwarta kamin ta ce.

"Naga dai TVn mallakina ce Okey?"

"Kamar ya ban gane ba?, ya za'ai nazo gidan Yayana ina abu kina wani nunan ban isa ba?, naga dai gida nashi ne ko?"

"Ni kuma na ce kayan cikinsa nawa ne right?, kuma TV ɗin ma daga gidanmu aka kawo ta, dan haka na kashe koda magana?"

"A'a babu kam ai gori kuma ya tashi, ai dama auren irinku ko jidali, mace mai gori dai batai ba a rayuwarta wallahi anji haushi duniya da lahira"

Mimi zatai magana sai taga Shamsiyya ta miƙe tana sake faɗin.

"Yawwa kima ƙara masa godiya ya tura min naira dubu ɗari kuɗin abincin da zan rinƙa ci da kuma na gudunmuwar birthday party na"

"Birthday party?"

Mimi ta faɗa iya laɓɓanta kawai tana jinjina kai.

Shamsiyya dake taunar chingum ta wani saki kwai tana faman sakin wani sauti ƙas-ƙas.

Ta sake cewa.

"Hala bai sanar dake bane?"

"Ai hatta yawan kuɗin bari na gaya miki saida na bada umarni kamin ya tura mikin, ni ce na ce masa ya kamata ya baki su kawai ya nemi shawarar kamar nawa ya kamata ya baki na faɗa masa"

"Kambu*hun ub*an nan, ai dama sai da ya nemi shawararki da izinin ki tukunna zai ɗauki kuɗi ya bani?. To na rantse da Ubangiji bana son wa'innan kuɗin"

"To ke da yaya nufinki?, nifa matarshi ce kefa?, dan kawai kina matsayin ƴar uwa sai aka ce kawai idan zaiyi abu taki shawarar zai nema ma kenan?"

"Ai bari kiji uwar data kawosa duniya ita ce kaɗai ta isa ta basa umarni yayi amma bake ba"

Shamsiyya ta faɗa tana jefa mata wani irin banzan kallo kamin ta ɗauke wayarta dake aje a hannun kujerar data zauna tana wucewa bedroom ɗin da aka bata tana wani sakin tsaki ciki-ciki.

Tana wacewa Mimi ta zauna akan kujera tana dafe kanta jin yadda yayi mata wani irin nauyi ya sara mata gefe guda kuma.

"Ya rabb"

Kawai ta furta a hankali tana jin zuciyarta ba daɗi, kwata-kwata zuwan Shamsiyya ita a wajanta babban jidali ne da tashin hankali, tasan wallahi da biyu yasa akasa ta zuwar mata gida ta zauna ba wai haka nan kawai ba.

Tana nan zaune har lokaci mai tsawo a nan ta fara jin kamar muryar Maryam nayo sallama.

Ai ko da wani irin sauri ta miƙe tana ƙaƙalo murmushin dole.

Maryam na shigowa parlon sai ta kama bin Mimi da kallo tana tahowa gare ta tana cewa.

"Ƙawata ya haka kuma naga duk kin wani faɗa fuskarki duk ta rame?, mike faruwa ne?"

Kamo hannunta kawai Mimi tayi tana zaunar da ita akan kujera itama saita zauna tana sakin ajiyar zuciya ta sake kallon ƙofar bedroom ɗin da Shamsiyya take kamin ta ce.

"Bari Maryam akwai damuwa ne dake cin raina dole ne nayi rama haka mana"

"Ke kam mi zai dame ki haka Mimi?"

"Akwaifa Maryam, ke dai kawai kiga mutum na rayuwa ne kawai amma shi kaɗai yasan abunda yake fuskanta a cikin tasa rayuwar kawai"

"Shikenan naji ke mike faruwa dake ne haka?"

"Matsalar dangin miji mana Maryam"

"Dangin miji dai?, ai nake ganin ke uwar mijinki bata da matsala, su Shamsiyya ne kawai matsalar kuma naga ai tana ƙoƙarin taka masu birki"

"Hmmm to banda yanzu wallahi, na rasa miya sauya mata tunani, dan in gaya miki yanzu haka ma Shamsiyya na gidan nan wai tazo tayi har wata uku a gidan nan da sunan wai hutu, kuma Hajja ɗin ta sani"

"Whatttt kika ce wata har uku?"

"Kware kuwa hakane, dan yanzu haka ma an bata ɗaki a gidan nan, tana nan tazo in gaya miki ta isheni da rashin kunyarta maganganu duk maganar data zo bakinta faɗa min take, shi yasa ma na ce kizo please na rasa yaya zanyi ni"

"Tabɗi jam tsakani da Allah akwai matsala fa Mimi. Amma ni kaina banma san miye zan iya ce miki ba. Amma shawara ɗaya ce kawai zan iya baki Mimi ki riƙe girmanki, karki sake cacar baki ta sake shiga a tsakaninku, itama tana zubar da kima da mutumci, sana karki sake ki rinƙa dafa mata abinci tazo ta ɗiba taci kawai, kuma dole ki ce mata ta fito ta rinƙa miki aiki, idan yaso ku rinƙa aikin a tare, bance kuma ki tsaya ki rinƙa sakar mata fuska ba Mimi"

"Hmm Maryam kenan, ai duk abubuwan da kike faɗa nayi ƙoƙarin nayi su amma ina, kinji maganganun data rinƙa faɗa min kuwa?. Ita fa ba ƴar aiki aka kawo min ba, dan haka wallahi ban isa na sata aiki tayi ba, idan abinci ne nawa bazata ci ba, zata saka shi Jafar ɗin ya turo mata kuɗi ta rinƙa sayen na waje tana ci"

"Kuma shi Jafar ɗin ya tura matan?"

"Hajjar su ta kira ta haɗata

15 / 47