Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 47

3K to 6K   out of 140.3K words

Ammi dama an cinye tuwon nan?"

Fannah ta faɗa tana dawo da dubanta inda Ammi take zaune.

"Eh wallahi tun cikin dare ma"

"Gaskiya yinwa nake ji fa"

"Ahh shiryawa zakiyi ki fita mana ki samo abincin da zaki ci. Ko kuma idan kinyi sa'a azo miki ƙunshi kin samu nacin abincin, danma baki son yin ƙunshin, kinga kuwa ai kin rinƙa yini da yiwa, ace ayo mutum ya iya sana'ar da zata kawo masa kuɗi koda yaushe amma baya son yi"

"Amma Ammi yanzu fa naga kin shigo da kuɗi a hannunki, ina zaki kai su to?, gaskiya ki fito dasu kawai yau muci daɗi muma"

Wata hararara Ammi ta zafga ma Fannah tana nunata da yatsa ta ce.

"Ashe baki da hankali ban sani ba?, kuɗin dana shigo dasu nake maku tarin kayan ɗaki dana kitchen shine kike sakama ido wato?. To bazan fito dasu ɗin ba. Kuna dai gani dangin uban nan naku idan auren naku ya tashi babu uwar da zasu iya maku, yanzun ma kamar babu su a rayuwarku inaga kuma wata hidima ta taso taku, kuna ganin zasu taimaka ne?. Kowacce ai nasan bata rasa kuɗi a ƙugunta, dan haka ta fitar da ciyar da kanta yawwa"

Aunty Sa'a ce ta girgirza kai tana fiddo da Naira dubu biyu ta kwalama Hannah kira.

Fitowa Hannah tayi tana amsawa da.

"Gani Aunty Sa'a"

"Yawwa jeki nan bayanmu ki sayo garin masara kizo ki ɗora mana abinci, ki sayo duk abunda ya dace, ko dambu ne ki murza mana"

"A dubu biyun Aunty Sa'a?"

"To karda Allah yasa ta isa, inama laifi?, ai nayi ƙoƙari ma, ita kaɗai ce dani na ƙundige na bayar"

"Kinga Hannah amshi kije koma yata kama ki sayo azo ayi haka nan aci"

Cewar Ammi.

Aunty Haja ta tashi tana matsowa kusa da Ammi ta ce.

"Ammi bani kaso na"

"Kamar ya na baki kason ki kuma?"

"Ammi wadda Alhaji ya baki man. Dan ni gaskiya na gaji da cin Masarar nan, kawai ki bani wani daga ciki naba Hannah ta sayo min ko ƴar indomi ce na dafa na ci gaskiya"

"A'a ai ban gane ba, na ɗauka ai kin amso naki kason ko?"

"Ban amso ba Ammi, baccin na gaya miki Umar ne ya zo wajan duk ya ɓata min bajat ba"

"Mtsww ke kika kyale sa ai"

Faɗin Aunty Sa'a cike da jin haushin Umar ɗin. Dan tasan dama da akwai kuɗi a hannun Haja ɗin da yau basa su ci wata masara ba, tana da kyauta, dan ma duk ta fisu sakin kuɗi a gidan, amma dama ka sake kuɗi ya biyo ta hannun Ammi ko za'ai mi bata bada su, ita da kuɗi kamar mi, dan idan zata rabu dasu gani take kamar za'a rabata da ranta ne.

"Gashi nan"

Ammi ta faɗa tana damƙama mata dubu uku a hannu.

Ai sai Haja tabi kuɗin da ido kawai tana mamaki, sanin halin Ammi da kuɗi, sai ta shinye mamakinta kawai, tana amsar kuɗin, tasan ma a hakan da ita ce, kuma ta dalilinta ne aka samo kuɗin, amma baccin hakan tasan bata isa ta bata kamar hakan bama.

Miƙama Hannah tayi kuɗin gaba ɗaya ta ce.

"Ki haɗa da wadda Aunty Sa'a ta bayar, ki sayo shinkafa rabin tiya da wake kwata, sai ɗan cefane, kizo ki ɗora mana dafaduka"

Murmushi kaɗan ta saki tana amsawa da to, dan itama taji daɗi yau dai ba cin tuwo ko garin kwaki ko ƙanzo........

*TAURIN KAI*

*Zahra Royal Star*

PAGE 3

*Unguwar Dokoki Rimaye, Kankia LGA, Katsina state Nigeria*

A hankali Mama ta aje tsintsinyar dake hannunta bayan ta gama sharo ɗakin Abba.

Dubanta ta sake kaiwa inda take zaune, ganin yadda tayi tagumi hannu biyu-biyu yasa Mama sakin wata ƴar ajiyar zuciya tana girgiza kanta. A hankali ta taka zuwa inda take.

Tana ƙarasawa inda take tasa hannunta tana cire mata tagumin da tayi.

Zama Mama ta ɗanyi kusa da ita tana sake kallonta a tsana ke ta ce.

"Mimi lafiya kike kuwa?. Kina tagumi baccin duk iyayenki gamu nan a raye"

Wata ajiyar zuciya mai zurfi Mimin ta saki tana sake ƙasa da kanta tana murja hannunta a hankali ta ce.

"Mama wallahi ina son Jafar, ni dan Allah Mama a barni dashi haka nan ayi aurenmu"

Riƙe baki kawai Mama tayi tana ƙara kallon Mimi da mamaki sosai kamin ta sauke hannunta tana nuna Mimi dashi ta ce.

"Wato ban taɓa ɗauka baki da hankali ba sai yanzu. Ke yanzu ko ance kije ki auri Jafar ai kince a'a"

"Amma Mama fa muna son junanmu, dan kawai yana AS ina AS ai bai kamata ace dan wannan ya rushe mana auren da muka daɗe ana fatan zuwansa ba, Mama duka fa baifi saura wata ɗaya ba, shi yasa wallahi ni kwata-kwata awon jinin nan banso zuwansa ba wallahi"

"Saboda baki da hankali ai, ya za'ai kuwa ki so zuwan nasa. Ke ana hango maku gobenku daga ke har Jafar ɗin amma soyayyar zamani na son rufe maku ido gaba ɗaya, sai nan gaba idan abu yaje ya dawo azo ana wallahi tallahi ko?"

"Mama ki gane mana, kinga fa ko su Hajiya dama jira kawai wani abu ya shigo tsakani aje a basa wata dama can so suke ya auri wata ƴar uwarsa ana min baƙi cikin aurensa, dan anga kawai yafi nasu Hajiya, duk yafi Mazajen da suka kawo fa nagarta da komai"

Ɗan shiru Mama tayi tana Jinjina kai. Da wannan dan wannan fa. Domin gaba ɗaya dangi abunda ake jira kenan, yanzu ma daga yo awon har an fara yaɗa jita-jitar an fasa auren, wadda su dai da bakinsu basu faɗi hakan ba, ana jiran shi Jafar ɗin ne aji miye zaice.

"Hmm kin gane Mimi ni bawai bana son aurenki da Jafar bane a'a. Ki sani fa ƴaƴan da zaku zo ku rinƙa haifa da wannan cutar Sikilar shine abun gudu, duk wani tattalin arziƙin shi Jafar ɗin wadda yanzu yake taunƙaho dashi fa sai ya zo babu shi, saboda wannan cutar Sikila ɗin da kike ji da gani ta wuce duk tunaninki wallahi, bafa ƙaramin ciwo bane cutar Sikilar nan, shi yasa ma yanzu ba'a yarda ayi aure ba tare da anje anyi awon nan ba saboda gujema matsala irin wannan"

"To amma Mama kinji abunda Likitocin fa suka ce, zasu fara ɗoramu akan mugunguna, da tazarar haihu, kuma zamu iya haihuwar masu lafiya, ai abun Allah ne fa"

Miƙewa kawai Mama tayi tana cewa.

"Ko na yarda ko kar na yarda Mimi ba lallai Mahaifinki ya yarda ba wallahi dan hak...

"Ai bazan ma taɓa yarda ba. Wato kudai yaran zamani kun cika hauka da shirme. Ke idan banda baki da tunani ma kin ƙara jin shi Jafar ɗin yayi maganar bikin, sai ke kawai kin wani zo kina tada hankalinki a banza. To ki ma buɗe kunnan ki da kyau kiji ni, aurenki da za'ayi nanda wata ɗaya baza'a ɗaga shi ba, za'a ɗaura miki aure ne da ɗan uwanki Mubarak"

Wata irin zabura tayi tana miƙewa tsaye ido waje zuciyarta na bugawa sosai tana riƙe da saitin zuciyarta faɗi take.

"Abba dan girman Allah kar kayi min haka, wallahi ba wadda zan iya zaman aure dashi sai Jafar"

Sosai Abba ya zuba ma Mimi ido yadda take kuka tana maganar kamar wacce ta zare.

"Na gama yanke hukunci, na ma kira su iyayen Jafar ɗin duk wasu abubuwa nasu na biki za'a zo a amsa nanda gobe"

Kamin ma Abba ya rufe baki sai gani sukai Mimi tayi wani irin luuu tana shirin zubewa a sume.

Mama ta saki wani irin salati mai ƙarfin gaske tana nufar inda take kusan a tare suka isa ita da Abba hankali a tashe suna tarbota jikinsu, sai dai tuni ta sume dan bata motsi.

*************** *Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*

"Tsakani da Allah na gaji na gaji wallahi"

"Wai ban gane tsakani da Allah kin gaji kin gaji ba"

Wata uwar hararara ta zafga mata tana riƙe ƙugunta ta ce.

"Talla ce bazan je ba"

"Keee Binta kina ina ne"

"Gani Iya miya faru kuma?"

Nuna mata ita tayi tana cewa.

"Wato Mubeena ni zata nuna yau cewar ban isa da ita ko?"

"Haba Iya ba haka bane kiyi hakuri dan Allah"

"Sai anyi magana kiyi wani ƙasa da kanki kina bani haƙuri, ai duk halinku ɗaya, ke sakawa ƴaƴan nan naki namin rashin kunya ai"

"Kinga Iya nifa bance ki kira min uwa kina tsare ta da faɗa ba yawwa, kawai Talla ce bazanyi ba na gaji, su Khadiji da Naima ai suna miki, dole ne ni sai naje?. Mu shikenan kenan a haka zamu ƙare da miki talla, dan kawai kin haifi mahaifinmu shikenan zaki rinƙa nuna mana isa da gadara?, baccin ma lokacin da uban namu na raye kinfi kowa tsanarsa saboda kawai bashi da shi, kinfi son Babansu Ikilima"

Wani kalar kuka Iya ta fashe dashi tana cewa.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, yanzu Binta a gabanki ƴarki ke cimun wannan mutumcin amma ki kai shiru?"

Wata ajiyar zuciya ta sauke tana duban Mubeena ta ce.

"Mubeena ɗauki tallar nan ki wuce kibar gidan nan. Wai Mubeena so kike kisa min ciwon zuciya ne?, Yayyenki basu sani magana ba sai ke?"

"Haba Inna gask...

"Riƙe gaskiyar taki, tunda ba abunda kika sani sai rashin kunya ke, amma su Khadija kinga suna yin wannan rashin kunyar ne ace sai ke?"

"Ai wannan yarinyar anya-anya babu iska a saman kanta kuwa"

"Iya karki sake ce min ina da iska, talla ce zan ɗauka naje amma ki sani darajar Inna kawai kika ci wallahi"

Ai sai Iya ta ƙara sakin kuka tana fyace majina da haɓar zaninta tana nuna Mubeena ta ce.

"Billahir azim bari Kawunku ya zo dashi zan haɗaki yau sai jikinki ya gaya miki a gidan nan"

"Haba Iya ai da ne na zauna Kawo Isa ya jifge ni, amma koshi ya zo yanzu dai-dai nake da shi wallahi"

Ido kawai Iya tabi Mubeena dashi harta ɗauki tallar shinkafa da waken da take masu ta fice tabarsu da mamakin canzawar Mubeena a ƴan kwanaki.

Inna kam juyawa tayi ta koma ɗakinta tana jin ciwon ɗorama ƴaƴanta talla da Iya keyi. Itama bawai bata sana'ar ba, tana yi amma har gida ake zuwa saye, sai Inna tunda ta kyalla ido taga ana mata ciniki shikenan wata ƙawarta Inna saude ke ƙara zugata tana ɗorata akan hanya, dan ko yin abincin nan tana ɗora masu tallar ita ce ta zuga ta, idan kuma zatai magana sai ta fara ce mata ai idan ta sake zata tattara kayanta tabar gidan, kuma dole tabar su Mubeena tunda dai bada su ta zo ba, ƴaƴa dai nasu ne, taga ubanda zai raba su.......

*TAURIN KAI*

*Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSO......*

PAGE 4

*Ƙofar Marusa, Katsina state Nigeria*

Sanyin safiya ce sakali, iska na busowa, yanayin sanyi sosai na sake ƙutso kai.

Hannah ce tsaye a filin tsakar gidan, tana shara iskar sanyin safiyar na kaɗa ta, sharar kuma wata na sake dawo mata baya.

A hankali ta sauke lumfashi tana bin sharar da ido kawai.

Fannah ce ta fito daga ɗakinsu tana hamma taja ta tsaya tana ɗan duban Hannah zuwa can ta ƙara sakin wata hammar tana cewa.

"Wai Fannah har yanzu ba'a ɗora komai a gidan nan ba?"

Wani kallo Hannah tabi Fannah dashi tana ci gaba da shararta, tana ce mata.

"Lallai ma Fannah ashe kin mance halin da ake ciki a gidan nan"

"Mtswww nifa wallahi na gaji da rayuwar talaucin nan haba, ace mu shikenan bamu gaba sai baya"

Sharar ta samu ta tattara ta kwashe ta zuwa inda suke zubar da shara ta zubar ta dawowa inda Fannah ta zauna ta kada turmi dake tsaye ta zauna itama tana faɗin.

"To ba gara ke ba, kina yin sana'ar ƙunshi, ko banza ai kina riƙe kuɗi, nifa ba inda nake samo su"

Taɓe baki Fannah tayi tana faɗin.

"Wannan kuma ai ke kika so, kina da kyanki da dirinki amma kullum ke a cikin Hijab ai dole kiyi baƙin jini, a Hijab ɗinma fa maza biyo ki suke, ni da ni keda kyan nan naki hmm ai da yanzu bana a nan a zaune. Kuma ƙunshi da kike magana nifa ba son yinsa nake ba, bazai yiwu na zauna na lalata jikina da baƙin lallai ba ko ja, na zama kamar mahaukaciya sabon kamu"

Riƙe baki Hannah tayi ta ce.

"Haba Aunty Fannah, ni dama ni ce na samu na iya ƙunshin da kika iya, ai da na samu madogara a gidan nan"

"Ke ai ƴar gatan Ammi ce idan ta samo tana baki"

Suka ji maganar Aunty Sa'a akansu.

Kallonta sukai tana fitowa daga ɗakinsu dake jikin nasu Fannah. Da yake ɗakin su Aunty Haja da Aunty Sa'a daban yake, su Aunty Aysha da Fannah da Hannah ɗaki ɗaya suke, sai kuma Ammi da Aunty Maryam ɗaki ɗaya. Ginin gidan irin na zamanin da ne, amma akwai yawan ɗakuna a gidan kusan ɗaki huɗu ne, wani ma sai dai suka maida shi wajan aje kayan wanki da wasu abubuwan, dama akwai ɗakin sanwa, duk da basu cika yin sanwa dashi sunfi yi a waje, sai lokacin damuna ne suka fi yin sanwar a ciki.

"Kamar ko kin sani, Ammi bata fiye ma Hannah haka ba tana cin kuɗin Ammi kota hana kowa zata bata ne"

Faɗin Fannah.

"Kai Aunty Sa'a wallahi nima sai taga na kusa kuka take bani fa"

Ta ƙare maganar tana faman turo baki cike da shagwaɓa.

"Ke miƙo min tabarma na shinfiɗa na zauna"

Cewar Aunty Sa'a tana duban Fannah dake zaune.

Tashi Fannah tayi tana ɗakko tabarmar ta kawo ta shinfiɗa bayan ta zauna ta dubi Hannah ta ce.

"Yarinya ai ke kika so, kinfi mu farin jini, wajan jama'a amma kin wani maƙale ma wannan faƙirin wadda bai aje ba bare yaba wani"

Turo baki Hannah tayi tana sake ɓata fuska ta juya ƙeya tana cewa.

"Ni dai a haka nake son abu na"

"To ai ke kika sani, kin mutu cikin talauci da wahalar rayuwar kika sake kika auri wannan Ustaz ɗin"

"Ke dalla rabu da ita Fannah tayi kaɗan dan ubanta, wallahi bata auransa indai ina raye"

Faɗin Ammi tana fitowa daga ɗakinta tana bin Hannah da wani mugun kallo.

Ai sai Hannah ta ƙara kwaɓe fuska hawaye na son zubo mata.

"Hmm sai fa kin tashi tsaye dan wallahi Ammi naga alamar ba ƙaramin hure mata kunne yayi ba. Yanzu fa ina magana akansa ina gaya mata gaskiya amma tana sake botsare min"

"Ai barni da ita Sa'a nasan matakin da zan ɗauka akanta wallahi"

"Tuni Ammi...

Sallamar da akai ce ana shigowa gidan yasa Hannah yin shiru, su duka suna bin wacce ta shigo da ido.

"Assalamu alaikum, ina wuninku?, dan Allah Fannah na nan kuwa?"

Amsawa sukai a tare Fannah na miƙewa tana duban yarinyar da bazata wuce sa'arta ba ta ce.

"Eh ina nan"

"Yawwa dan Allah Fannah zamu samu ƙunshi kuwa?"

Taɓe baki tayi tana juya baya ta ce.

"Gaskiya bazan iya yin ƙunshi ba ni yau, fita ma zanyi"

"Dan Allah ki taimaka kiyi mana wallahi biki muke, kuma ƙunshinki yafi na kowa kyau a unguwar nan please"

"Ni fa...

Ammi ce ta yi saurin katse ta tana cewa.

"Ke keda waye za'ai ma ƙunshin?"

"Nida ƙanne na ne sai wata Auntynmu da zata je tayimawa a gida dan Allah"

"Tabɗi jam wallahi bazan je gidan kowa nayi ƙunshi ba"

"Kefa baki da kirki Fannah, dan kinga ana son ƙunshin naki sai kiyi ta ma mutane wulaƙanci?"

Cewar Aunty Maryam data fito daga ɗaki yanzu.

"To ni Aunty Maryam gaskiya ma ni na daina ƙunshi, ai duk wahala ne ma wallahi"

"Ke baiwar Allah kije gidan Auntyn taku ki ce mata idan zata iya zuwa nan ayi mata to, sai kuzo tare ayi maku, amma kuzo yanzu dan idan ta fice tabar gidan bafa zaku samu ba"

Cike da jin daɗi yarinyar ta dube Ammi datai maganar tana amsawa da to ta fice daga gidan.

"Haba Ammi mi yasa zaki ce su zo?"

Fannah ta ƙare maganar haɗe da turo baki gaba.

"Ke naci ubanki wallahi. Kinyi ma sa'a kina da sana'ar hannu wacce Allah yasa kika iya, ta samu kuɗi shine kike wani botsarewa haka?, to muddun ina gidan nan wallahi ana zuwa ƙunshi sai kinyi sa nama gaya miki. Ai ko banza kin rage mana wata hidimar gidan"

"Na rage ma dai kaina"

Fannah ta faɗa ciki-ciki tana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.

"To dan ubanki sai mi idan kin rage ma kan naki, dama ke ai ba'a cin abun hannunki wallahi, duk nan ciki Haja tafi ku kyauta da sakin abun hannunta"

Hannah zata miƙe tayi cikin ɗakinsu dan taga Ammi yau da faɗa ta tashi. Taga gaf shigewa Aunty Sa'a ta tsaida ita ta ce.

"Kinga Hannah sanyo Hijab ɗinki ki zo nan na aike ki"

Da to ta amsa tana shigewa ɗakin nasu ta ɗakko Hijab tana zuwa inda Aunty Sa'a take zaune ta ce.

"Gani"

Ɗari biyar ɗin data rage mata ta ɗakko ta tana miƙama Hannah ta ce.

"Amshi kije wajan Idi mai shayi ki ce ya haɗo min shayi da biredi na duka, ki zo nasha na rage miki"

Amsa tayi tana murmushi ta fice tana jin maganar Ammi na cewa.

"Ke yanzu fisbilillahi Sa'a ke kaɗai zaki miƙa kuɗi a sayo miki karin safe?, to mufa?"

"A'ato Ammi kowanne ya fito da nashi kuɗin yayi karin safen mana, nima ita kaɗai ce ta rage min, kin gani jiya na bada dubu har biyu akayi abinci, shi yasa yau dole saina fita. Ai ni shi yasa fa su Fannah ke ban mamaki, yo da ni ce na iya ƙunshi ko nake da kyau irin da Fannah ai kuɗi bazasu yanke min ba"

"Hmm ai basu da hankali ne, ana cikin wannan rayuwar har ka samu abun samun kuɗi a hannu amma kake wasa da wani nuna kai wani ne, suna wannan gida

2 / 47